Showing 72001 words to 75000 words out of 98004 words
mafita, kukan rashin gata, bani da kowa sai Allah, haka nayi me isata na share hawaye na nayi shiru, ciki ka koma na tarar har tayi bacci, ashe baccin tafiya ne,baccin da ya tafi da duk wani sauran farin ciki na, a ranar nayi kuka kamar ido na zai makance, na riga nasan tabbas rayuwa ta ta gama yawo, bani da kowa bansan kowa ba, bansan in da na kama ba.
Bayan rasuwar ta sai na fara tunanin yadda zan rike kaina,duk in da naji labarin masu kawo yan aiki sai naje ko Allah zai sa na samu, sai dana sha bakar wuya sannan na samu aiki a wani gida.
Zuwa na gidan nan shine asali ko nace tushen da ya saka duk abinda ya faru yanzu ya faru, tun bayan zuwa na gidan komai ya chanja, bayan fuskantar kalubale da nayi ta fannin yaran gidan,Mero ita tafi kowa bani matsala, kyara da wulakantawa babu wanda bata yi min, duk da cewa na girme ta,amma hakan be saka ta daga min ba, haka nayi ta hakuri saboda idan ma nayi fushi bani da in da zan kama. Gida ne babban gida family house, Yaran da yawa iyayen su basa gidan sai dai matan uban, shiyasa babu wata gamshashiyar tarbiyya a tattare da gidan. Ni dai na kama mutunci na bana shiga sabgar kowa aiki na kawai nakeyi.
Akwai watarana da saurayin Mero yazo, bayan taje wajen sa sai ta bukaci na kawo masa abin sha, ba asan raina ba na dauka na kai masa, tun daga ranar shikenan sai reshe ya juye,, wannan shine asalin abinda ya haɗa mu da ita har taci alwashin daukar fansa tana ganin munci amanar ta, duk da da farko ni kaina ban amince ba, ganin yadda kowa na gidan ya juya mun baya har ana shirin kora ta ya sa na amince, haka akayi auren ba tare, na bar Kaduna na dawo Kano, ashe ban sani ba har lokacin abin be bar zuciyar ta ba, wannan shine babban dalilin daya saka ta shigo rayuwar mu, ta tarwatsa mu ta tarwatsa dukkan farin cikin mu."
Dukka falon babu wanda jikinsa be yi sanyi ba da labarin Ummi, Alhaji ne kawai be ji komai ba saboda ya san komai, sai kuma Arkel da ya nuna kamar be san me yake wakana ba, dukkan su sunyi shiru kowa na tunanin wannan al'amarin. Kan Arab a kasa cikin dararradin abinda zai tarar yace
"Ummi..."
Murmushi tayi
"Karka damu, babu abu daya daya faru da kake tunani, Allah ya duba zuciyar mu, ban cuci kowa ba, Allah ba zai bari irin wannan abun ya faru da mu ba, dukkan shi shirin ta ne, ita ta shirya komai, ita ta tsara komai dan ta dauke hankalin kowa daga kaina."
Wata iri yar ajiyar zuciya ya sauke, farin ciki ne yake ratsa dukkanin kofofin jikin sa,abinda ya dade kenan yana dako a ransa, abinda ya hanashi walwala da jin dadin rayuwar ma baki daya.
Daki Ummi ta shiga ta fito da akwatun, duk wasu abubuwa masu mahimmanci na ciki ne banda takarda guda daya, sama ko kasa ta duba takardar nan babu ita, kayan aka sauke komai amma babu, Kallon su kawai Arkel yake har aka gama be tofa komai ba, tuno da in da ya ajiye takardar yayi, lokaci yayi da amfanin ta zai tashi, sai ya sake gyara zaman sa kawai yana ji ana neman da ya riga yasan babu yadda za'a yi a ganta. Hotuna ne guda biyu a cikin kayan, wasu maza ne masu kama daya a cikin shigar Fulani daya ya rataya sanda a kafad'ar sa, hoton irin Black and White din nan ne gashi yayi mugun dade wa, motsawa Ummi tasa sukayi sannan tace
"Wannan shine Arkel, wannan kuma Arabu, gashi nan kowanne an rubuta sunan sa a kasan hoton sa, wannan hoton shi kadai nake dashi daya rage min, shi din ma bansan ya akayi na same shi ba, a cikin kayan da Baba Yelwa ta bani ne na gansu, na san dai yana tattare da wani abu game dani, hakan yasa dana haife ku na sa muku sunan, Muhammad shine sunan ku, Arkel kuwa da Arabu inkiya ce, nayi hakan ne dan ko watarana Allah zai sa ta hanyar sunan na samu wani nawa, suna ne da ba kowa ya san shi ba, hasalima sunan Fulani ne, wannan tunanin ne ya saka ni kiran ku da sunan, ko da aka zo za'a saku a makaranta ni na saka lallai a saka muku sunan, ina fatan wannan dalilin ya hadani da ahalina, dangi na kamar kowa."
Duk sai suka kalle ta cike da tausaya wa, Maryam Sarkin kuka sai share hawaye take dan ba karamin tausayi Ummi ta basu ba.
Kowa sai da yayi magana a wajen amma banda Arkel, ko da aka ce yayi sai ya nuna ba yanzu ba, akwai abinda yake so ya karasa. Sai kawai aka kyale shi aka tafi cin abinci da Sallah ganin lokacin ya ja.
***
*Bayan Kwana Biyu.*ne
***
Sai data sauke komai na wardrobe dinta, kallon ta yake ta gefe yana so yayi dariya amma sai ya dake, ranta duk babu dadi haka ta sake maida kayan ta jera su ba tare da ta san dalilin da yasa ta sauke ɗin ba, tana zuba na karshe ya ajiye wayar hannun sa ya tako a hankali ya rungume ta ta baya, da sauri ta juyo, suna hada ido tayi kicin kicin da fuska kamar zatayi kuka, jan ta yayi a haka har gaban gadon sannan ya zauna ya jawo ta jikin sa
"Bak'ya so na tafi ne?"
Da Sauri ta daga kanta
"Umm."
"Toh me yasa? Ko zaki bini?"
Kallon sa take kawai tasan ba zuwa zai yi da ita ba, ga makaranta ma karatun su ya fara zafi, sai ta girgiza kai kawai alamar a'ah. Zama ya gyara mata a jikin sa sosai ya dan zamota
"Karki damu, na shirya komai just one week zanyi, Idan na dawo si ki rakani muyi weekend ko?"
"Da gaske?"
"Da gaske mana, ko bak'ya so.?"
"Ina so wallahi."
Nan danan ta saki fuskar ta, kayan sa ta tayashi ya karasa haɗawa, dambun naman da aka yi jiya ta zuba masa a wata roba me kyau, ta hada masa da doughnut tayi rapping d'insa ta hada masa dashi.
Abinci suka ci a saman dan yace ba zasu sauka ba yau, so yake su soye abin su, dakin sa suka shiga ya dauko laptop dinsa da charger suka koma nata dakin, Frozen 2 ya kunna musu, dan a dan zaman da sukayi ya lura da ita tana son irin films din shiyasa yayi mata downloading dinsu da yawa. Pillow suka saka guda daya suka jingina dashi, kafadar sa na gogar tata a haka suka zauna suna kallon Film ɗin, gaba daya hankalin ta ya tafi wajen kallon, hakan ya bashi damar tunanin abinda ya kamata yayi kuma. Idon sa ya rufe ya sake mike ƙafarsa sosai, kallon sa tayi ta jima sosai kafin ta dauke idon ta tana sauke ajiyar zuciya, ranar kawai take jira da zai furta mata yadda yake ji game da ita, da haka bacci ya dauke ta, gyara mata kwanciyar yayi ya kashe komai ya ajiye a in da ya dace, sai daya sauka kasan ya tabbatar da komai daidai sannan ya dawo ya kwanta kusa da ita yana tofa mata addu'a.
***
Yana tsaye gaban mirror yana sharce ruwan kansa da hannu daya, hannun sa daya ya dora shi a saman kugun sa yana kallon duk wani motsin ta ta cikin mudubi, gaba daya bata ta kuzari da walwala a kasalance take komai, duk sai yaji ba dadi, sai dai ya zama tilas yayi wannan tafiyar ko dan ya cika wa Ummi burin ta, kallon kananan kayan data ajiye masa a gefen gadon yayi ya dauka ya saka, yana daure belt ta sake shigowa dauke da kayan tea da flask, da sauri ya karbe ta ya ajiye a saman carpet din dake gaban wajen, idon ta yake nema ya saka cikin nasa amma sam taki yarda su hada ido, ta juya ya riko ta yana juyo da ita .
"Menene?" Yace yana kallon cikin idon ta, hawayen da ya biyo fuskarta ya kalla da sauri yasa hannu ya tare
"Kuka dai? Wai ko na fasa tafiyar nan ne?"
"Um um."
"Gosh, toh ki saki ranki please, kar kisa na kasa aikata komai, kinji? I ll come back for you in Sha Allah."
Gid"a kanta tayi, ta saka hannun ta tana share hawayen fuskar ta.
"Ki shirya mu fita tare, sai kije ki kwana biyu a gidan umma."
"Da gaske?" Nan da nan ta saki fuskarta, dariya yayi kawai ya zauna don karyawa. Karamar trolly ta fito da ta zuba kayan ta kala biyu sai under wears da sauran kayan da zatayi amfani, sai murna take tana sauri yana zaune yana kallon ta yana murmushi. Wankan ma a gurguje tayi ta fito, ta saka wata atamfar ta super ta cikin lefenta Lemon Green and Orange me zanen ganyen bishiya, mayafi ta yafa orange ta saka flat shoe, fuskar ta babu komai daga powder sai dan wetlips data murza, sosai tayi kyau ta fito fes, har wani sheki da kyalli fuskar ta take yi, tana gaban mirron sai jin mutum tayi ya zuro fuskar sa a saman kafad'arta, tana dagowa ya dauke su hoto, ba karamin kyau sukayi ba, sunyi matukar dacewa da juna, bata wayar yayi ta kura wa hoton ido tana ta aikin kallo kamar me sunyi kyau.
Ummi suka sauka sukayi wa sallama ya fada mata zata je gidan kwana biyu, komawa tayi daki ta dauko mata yan abubuwa tace ta kaiwa umma kafin tazo zuwa na musamman. Arab na ganin su ya hau tsokanar sa yana cewa ko dai tare zasu tafi zai wani waske da gida zata, shi dai be kula shi ba dan yasan sarai so yake ya sashi yaji kunya a gaban ummi, waje ya rako su aikuwa ya kai mishi duka yayi saurin gocewa yana dariya.
Shine zai kaishi airport din, a baya suka zauna suka barshi shi kadai a gaba aikuwa ba karamin shaka yayi ba, babu yadda be yi akan Arkel ya dawo gaba ba fafur yaki haka ya hakura ya tada motar yana ayyana kalar rashin mutuncin da zai shuka masa idan suka ajiye Maryam.
A kofar gidan suka tsaya, da sauri aka saki gate din gidan Hajiya Mama alamun akwai mutum da yake labe da a jiki, kalla sukayi sai kuma suka dauke kai basu ga kowa ba, tare suka fito ya sauke mata jakarta suka shiga zauren gidan, a kasa ya ajiye mata kayan ya jawo ta jikinsa. Ya dade a haka kamar kar su rabu sai da Arab ya ishe su da horn sannan ya sake ta yayi mata sallama ya tafi. Sai ta kasa daga kafa daga wajen tana jin babu dadi, sati dayan da zai yi jin sa take kamar shekara daya, bata taba tunanin ta shaku dashi har haka ba sai yau, yanzu da take ganin zai tafi ya barta, hawaye taji masu zafi sun fito, hannu tasa ta goge sannan taja jakar ta shiga gida.
****
Hafiz
Saukar sa kenan daga adaidaita sahu yaga wucewar motar Arkel, da kallo ya bita har suka wuce shi, juyawa yayi zai shiga yaji wata motar ta taho, tsayawa yayi yana kallon motar, da gudu take har suka kusa bin kansa yayi saurin ja baya, zaro ido yayi a daidai lokacin da glass din bayan motar ya sauka kasa, kallon sa tayi ta sakar masa murmushi sannan ta daga masa hannu, a hankali glass din ya koma ya rufe, kansa ne ya kulle ya rasa me zai yi, wayar sa ya ciro da sauri ya kira Number Arkel , har ta gama ringing ba'a d'aga ba, da sauri ya shiga cikin wajen, machine din baba me gadi ya ara ya bi bayan motar da mugun gudu, sai da yayi da gaske sannan ya kamo su, a hankali ya shiga bin su duk in da sukayi dan san tabbatar da abinda idon sa ya gani.
[3/18, 22:27] Hafsat Rano: SK 43-44
Na kudi ne, kina so ki karanta ki nemi wannan Number. 08030811300
Greetings to u *Fatima Hussayn Isari* (Maman Walid).
***
Suna daukar hanyar Arab yace masa
"Wai tafiyar me zakayi ne."
Dan jim Arkel yayi kafin yace
"Akwai abinda zan saro ne, ba wani jimawa zan ba."
"Kai kuma yaushe zaka koma?" Ya ɗora
Sai daya sha kwana sannan yace
"Bana jin komawa wallahi, na fiso nayi ta zama a cikin family na."
"Ya zakayi kenan, kazo kayi joining bussiness din nan, its very good."
"Allah ko?"
"Emana."
"Owk tam, da yake ma suna ta shirye shiryen bude branch anan Kanon, zan koma na nemi transfer cikin wanda zasu kawo Kanon, in sun ki sai na ajiye musu aikin su na dawo gida, amma zaman crossriver kam na gama shi."
"Owk hakan yayi sosai, Allah ya taymaka Mr Kanu."
"Kut.. ni ne kanun?"
"Toh ko Samuel ne?"
"A ah okonkwo ne, dan air.
Dariya sukayi gaba daya, haka suka karasa har airport ɗin suna hira dan ma sun hadu da holdup ne.
Yana ajiye shi ya daga kiran Lubna, tun suna tare da Arkel take kira baya so ya daga ne yasan sai ya rama abinda yayi masa shi yasa yaƙi d'agawa
"Hello."
"Barr. Kina lafiya?"
"Lafiya lou Moha, ina ta kira ina ka shiga ne?"
"Ina nan na kawo kid bro dina airport zai yi tafiya, amma na juya gida ma."
"Kai haba,kuma babu nisa fa da unguwar mu, please ka biyo mana, tun ranar bamu sake haduwa ba."
Kallon agogon jikin motar yayi
"Beyi safiya ba kuwa?"
"Haba dai, sha biyu fa ta kusa."
"Kinsan yan gayu basa tashi da wuri fa."
"Su waye yan gayu?"
"Manyan Barristers mana."
Dariya tayi
"Babu wani wayo da zakiyi min, I'm waiting for u, zan tura ma address ɗin, bye."
Ta kashe kiran bata bari yayi magana ba, girgiza kai yayi yana dariya ya sake kallon kansa ta cikin mirror, text ne ya shigo wayar sa ya duba, address ɗin ne, location ɗin ya duba a wayar sa, juya wa yayi ya dau hanya yana jin sa wani iri kamar wanda zai je aikata wani abu, tsoro tsoro haka yake ji har ya karasa, Babban gida ne dan har sai daya dan tsoro ta da yanayin girman gidan, yana tsayawa ya kirata a waya, lokacin ta gama shiryawa ta hade cikin doguwar riga baka tayi rolling mayafin sai flat shoe data zura a kafarta, Babu makeup din komai tayi kyau kana gani kasan boko, hutu da tsantsar wayewa sun zauna a wajen.
Lekowa tayi ta hangi motar sa a dan gefe, yana ganin ta ya kashe motar ya fito, kallon sa take ba dauke ido har ya karaso, dan kunya taji ta ja mayafin ta ta rufe gefen fuskar ta.
"Sannu da zuwa."
"Sannun ki, yau dai gani a gidan ku."
"Da na takura ba,Allah Muhammad ka iya shariya."
"Ayi min afuwa toh, ba zan kara ba ai."
"Yawwa dai, mu shiga ciki toh.".
Kallon kansa yayi
"Ƙananan kaya ne fa jiki na, no gaskia."
"Toh menene? Kamar wanda zai shiga gidan surukan sa?"
Ta fada don son jin me zai ce
"Kuma fa haka ne, na manta ba gidan surukan bane, sorry muje toh."
Da sauri ta kalle shi, ya dauke kai kuwa kamar be san me yace ba, jikin ta yayi sanyi sosai har sai da ya sake magana sannan ta juya ciki ya bi bayanta yana danne dariyar da tazo masa, tuni ya gano ta sai dai har yanzu be san a wanne stage ya ajiye ta ba tukunna, zai cigaba dai da bin ta a hakan zuwa lokacin da zai gama tabbatar wa kansa komai, sai dai shi a tsarin sa yafi don yarinya karama yar secondary School ma so samu, amma dai zai bar komai a wajen Allah ya zaba masa mafi Alkhairi dan gani yake kamar Lubna tafi ƙarfin sa.
***
Zuwan ta gida yayi mata dadi sosai, wunin ranar tare da yan uwan ta tayi shi. Har lokacin Arkel be kira ta ba, ta kira wayar sa kuma bata shiga, lokaci zuwa lokaci take dubawa har yamma tayi babu wani labari, ganin gidan shiru Umma ta je kasuwa yasa ta dau Hijabin ta ta zura ta tafi gidan Maman Walid (Fatima Hussayn Isari), a bayan gidan su take suna dan shiri da ita kafin tayi aure, da sallama ta shiga gidan, a share gidan yake tas babu ko tsinke, kamshin turaren wuta ne yake tashi irin na tsinken nan ta sakale shi daga jikin bangon tsakar gidan, da murna ta tarbi Maryam ta shinfida mata tabarma, sosai yanayi da tsarin gidan hade da tsaftar ya burge maryam, girki take yi shi yasa ta saka mata tabarmar a dan gefen dan madaidaicin Kitchen din ta.
Tana zaune suna yar hira Abban Walid ya dawo, da sauri Maman Walid ta tashi ta tarbe shi, kayan hannun sa ta karba tana mishi sannu a jere, gefen jikin sa ya dan jawo ta ganin da bakuwa, dariya tayi babu kunya ta rike mijin ta sukayi ciki tana cewa Maryam tana zuwa, sosai hakan ya birgeta ta fara ayyano ta a irin yanayin, zata so ace gidan su su kadai ne daga ita sai shi, duk da har yanzu ba wai yace yana son ta bane amma dai ita kam ta riga ta gama fadawa kogin son sa, bata jin kuma akwai abinda ba zata iya aikata masa ba, jira tayi Maman Walid ta fito dan akwai abubuwan da kuma take son sake gani kafin ta tafi, sai ta gyara kafarta ta mike ta kawai tana murmushi ita kadai.
Fitowa Maman Walid tayi ta mika mata Walid daya tashi daga bacci sannan ta koma ciki, karbar shi tayi tana masa wasa, chan sai maigidan ya fito, da sauri Maman Walid ta dauki buta ta zuba masa ruwa sannan ta saka masa yar karamar kujera yar tsuguna, zama yayi yayi alwala bayan ya gama ya fita, har zauren Maman Walid ta rakashi sannan ta dawo ciki. Sosai abin ya birge Maryama, tashi tayi ganin magriba na kawo kai tace zata tafi, daki Maman Walid ta shiga ta hado mata wasu abubuwa a cikin leda yar madaidaiciya, kallon ledar Maryam tayi tana neman karin bayani
"Gashi nan ba yawa amarya, ki bani number ki in yaso sai nayi miki bayani ta waya, sauri nake na karasa girki kafin Mu'allim ya dawo daga masallaci, ga baban rigima Walid ya tashi
27, January 2025
Rukayya
Good