Showing 18001 words to 21000 words out of 98004 words
ciro karamar wayar sa yana dannawa.
Sama ta fara hawa ta dudduba ba kowa ta sako, bin kowa na wajen tayi daya bayan daya sukayi sallama kafin ta nufi office din Salim in da ta san zata same shi, yau ma kamar kullum ya zaune gaban computer yana dube dube, jin takun tafiyar ta yasa ya d'ago da sauri, dogon hill shoe ta saka sai dogon Hijab me hannu, fuskar ta fayau babu ko powder sai d'an wetlips data matsa a lips din nata, tun daga sama ya kalle ta har k'asa, kallon glasses din idon ta yayi kafin ya sauke kansa kasa, simple and cheap shiga tayi sai dai tayi kyau ainun, fatar jikinta chocolate colour ta dace da tsarin ta
"Ina kwana?" Ta katse mishi tunanin daya tafi
"How are you?" Ya d'ago yana kallon ta a karo na biyu
"Alhamdulillah, sir dama yau ne last day d'ina anan, log book d'ina kuma ba'a yi signing kowanne page ba, gashi na duba oga salim be zo ba."
"Sai ki jira shi." Ya faɗa kai tsaye yana mai da kanshi kasa
Sake dagowa yayi yaga ta a tsaye, mika mata hannu yayi alamar ta bashi log book din, dan tsaki yayi yana bude pages d'in ganin babu wajen da aka yi signing d'in, gashi kowanne page sai anyi signing hade da stamp.
Gefe ya tura computer tasa ya ciro pen ya matso da abun stamp din, kallon handwriting din yayi yaga kamar computer ce tayi shi saboda tsaruwa, kasa hakura yayi har sai da ya tambaya
"Waye yayi miki rubutun nan?"
Kai tsaye tace
"Ni nayi sir."
"Hmm... Are you sure? Kece zakiyi rubutu haka me kyau." Ya furta ba tare da ya sani ba, kallon sa tayi da sauri dan tasan shi komai akayi ba'a iya ba.
"Yayi kyau?" Ta fada tana murmushi, da sauri yace
"Ni nace kyau?" hararar littafin yayi ya cigaba da bubbud'e pages d'in, shiru tayi bata kara cewa komai ba, chan kamar ba zai sake magana ba sai kuma yace
"So nake nace wannan jagwalgalon,rubutu kamar tafiyar tsutsa, nema yake ya kashen ido ma, mtsw."
"I'm sorry sir." Ta fada yana kunshe dariya, kallon ta yayi tayi saurin hadiye dariyar ta, kwafa yayi ya cigaba da sa hannu, chan ya ture kawai ya maida kansa baya, a hankali taji yace
"Sai na huta gaskiya, ki jira."
Kallon agogon office din tayi ta kalli kofa, Hafiz na chan na jiran ta, mik'ewa tayi yayi saurin bude ido
"Ina zaki?" Ya tsare ta da idon sa
Da hannu ta nuna masa kofa, kada kai yayi ya maida idon sa ya rufe
"Cewa nayi ki jira ba ki fita gulma wajen maza ba."
Kallon sa tayi taga idon sa a rufe kamar bashi yayi maganar ba,sosai maganar sa tayi mata ciwo, dan ma ya raina mata wayo wai gulma, cikin bacin rai ta koma ta zauna tana hararar sa ta gefe.
"Harara ta kike?" Taji ya fada,da sauri ta kalle shi, idon sa akanta fes yana kallon ta, dan motsa baki tayi kadan ta yi kasa da kanta.
Rufe log book ɗin yayi ya kalli sunan, a hankali ya furta
"Maryaaam."
"Na'am." Ta kalle shi
"Meye cgpa dinki?"
"Sir?"
"Barshi ma,daga gani ba wani kokari ne dake ba."
"Allah ina da kokari..."
"Ban ga alama ba."
*Jin shirun yayi yawa yasa shi baro kofar ya shigo ciki, tun dazu ya hango ta shiga office din Amma shiru bata fito ba, a daidai window ya tsaya yana dan lek'awa ciki, ransa ne ya baci ganin su zaune su biyu a ciki, Arkel yana facing din ta, lokaci lokaci yana dagowa yana kallon ta, haushi ne ya turnik'e shi wani azababben kishi ya taso masa, da sauri ya juya ya bar wajen ba tare da ya shirya ba.
Arkel ya ganshi, take ya tuno fuskar, shine wanda yazo ranar, hade fuska yayi ya cigaba da abinda yake yi.
Gaba daya ajiye komai yayi ya tashi ya fita daga office din, bin sa tayi da kallo,me yake nufi? Ta zauna tayi ta jiran sa kenan? Buga kafar ta tayi kamar ta saka ihu. Dialing number Hafiz tayi har ta k'araci ringing be dauka ba, lekowa tayi ta hango shi ya sakale hannayen sa ta bayan sa suna magana da wani, daidai kofar shiga office din suke babu ta yadda za'a yi ta fita, komawa tayi ta zauna tana jan tsaki.
Sai da ya dade kafin ya dawo, rufe log book din yayi ya mika mata, ashe dama tuni ya gama signing din yana sa ne yak'i bata kenan? Juyar da kanta tayi gefe kwalla na taruwa a idon ta, karba tayi ta juya kawai ta fita da sauri ba tare data ce komai ba, jikin sa ne yayi sanyi ya bita da kallo, haushi taji? Ya tambaya a ransa, komawa yayi ya zauna yai shiru yana so ya tuna abinda yayi mata da zataji haushi har haka.
***
Ganin babu Hafiz tasan za'a rina, tun data kira taji be daga ba tasan yayi fushi kenan, samun kanta tayi da jin haushin Arkel, a haka ta karasa gida duk bata da kuzari saboda tasan fushin Hafiz sai yayi kwana uku be kulata ba. Ko data koma gida zaman ta tayi a daki tayi kwanciyar ta, abincin ma bata da muradin ci a halin yanzu, tana nan kwance ta jiyo muryar Anty Maryam a tsakar gida, da sauri ta fito ta tare ta, saurin karb'e Areef tayi daga hannun me aikin ta tana dariya
"My baby." Ta daga shi sama
"Ba'a son daga yaro sama fa."
Umma tayi magana tana fitowa, karbar Abid tayi suka shiga falon.
Zuwan Anty Maryam yayi mata dadi sosai, daki suka shige bayan sun gama hira da umma kamar wasu kawaye suka dora sabuwar hira,a cikin hirar ne take bata labarin yadda sukayi da Hafiz, idan abu ya haɗa su shikenan sai ya dau gaba da ita, gashi da saurin fushi abu kadan sai ya hasala ya hau zargi, tun abun baya damun ta har yaxo ya fara damunta, auren irin masu halin nan akwai wahala, gashi komai kayi baka birge ba abubuwa dai da yawa sai dai kawai ayi kurum.
Shawarwari Anty Maryam ta bata masu kyau, taji dadi sosai dan ba karamin haske ta kara mata ba, dole ta koyi hakurin xama da shi da halin sa kuwa tun da dai shi ta zaba. Sai wajejen Isha'i sannan mijin anty Maryam ɗin yazo daukar ta, har waje suka rakota umma dai ta tsaya a zaure Maryam ce ta rakata har gaban motar ta bude mata, sai data shiga sannan ta mika mata Areef, Abid dama yana wajen me aikin ta a baya
Sai da suka fita daga layin sannan ta juya zata shiga gida, sosai taji tsoro ganin mutum a tsaye kikam a jikin kofar gidan su, ja tayi da baya da sauri,
"Matsoraciya."
Ya fada yana matsawa jikin gate din, kallon sa tayi shine kuwa, tunanin abinda yake yi ne yasa ta tsaya, kallon ta yayi ganin ta a tsaye yasa yace
"Gidan ku?"
Ya nuna gidan da hannun sa, kafin tayi magana an turo gate din, kamshi ne ya fara yi musu sallama kamar anyi barin turare, Rauda ce ta fito tana taku daidai kamar wata sarauniya, a gaban sa taja ta tsaya tana taunar cingum, haushi ne ya turnik'e shi yaji kamar ya shaketa, mamaki ne sosai ya kama Maryam, kallon da take yi masa na mutum ne me tsaurin ra'ayi da akida, idan kuwa har hakan ne toh me yakeyi a wajen Rauda? Duk da alaka ce me karfi a tsakanin su da Raudan amma bata tunanin shi a irin mazan da zasu zo wajen Raudan ko dan saboda yanayin rayuwar ta daban da tashi, duk da ba wai tayi masa sanin sosai bane ba, a dan zaman da tayi ne ta fuskanci hakan, jikin ta a mace ta juya ta shige gida jin maganar Umma tana bawa Walid sakon yazo ya dubo yaga me ta tsaya yi bayan ta ji tafiyar tasu tuni, tana shiga umman ta rufe ta da fadan abinda ta tsaya yi.
"Me kika tsaya jira duk kowa ya dawo ke kin ki shigowa?"
"Gidan Hajiya Mama na shiga ne."
"Karki yi min karya, kece zaki shiga gidan? Da ban san halin ki bane dai."
Shiru tayi ta wuce daki kawai.
***
Bin ta yayi da kallo har ta shige ciki, kallon sa Rauda take babu ko kiftawa,
"Wacece ita?" Ya jefo mata tambayar, cikin halin ko in kula tace
"Yar brother Abba ce, step brother fa amma."
"Owk, cousin dinki ce kenan."
"Cousin? Ah no ba cousin d'ina bace."
"Kamar ya?"
"Please ka share kawai, muyi maganar da Mummy tace zaka zo muyi akan biki, kaga zamuyi dinner, moctail, barbaque tea party,...."
"Aina? Bana son shirme, babu ko daya da zamuyi, in ma zakiyi dai ni count me out, ba zan iya wannan haukar ba, send me ur account details sai na tura miki kudi kiyi abinda kika ga zakiyi."
Buɗe baki da hanci tayi tana kallon yadda ya dage yake xubo mata rashin mutunci, gaskiya ba zata dauka ba, daddagewa tayi ta tsaidashi
"Malam gaskia ba zai yiwu ba, komai daka ji na lissafa sai anyi kazo ko kar ka zo wannan ruwan ka, zaka tsaya kana gaya wa mutane magana,ba fa rasa masoya nayi da zan aure ka ba ehe,ka sani ka daina jin kanka a sama."
Dafe kansa yayi kawai ya juya da sauri, ba zai iya daukar maganganun nan nata haka ba, tsaki ta ja ta juya tana mita,
_"Idan banda kudin ka da takurawar su Hajiya ka isa ma, ni ba wai na shirya aure ne ma yanzu ba, mutum na tsaka da life din sa ace za'a takura shi, aikin banza matsoraci kawai."_
Ji tayi ta bige da abu, da sauri ta juyo, Abba (Alhaji Faruku) ne a tsaye ya harde hannayen sa a kirjin sa ransa a matukar b'ace, tsoro ne ya kamata ta hau karkarwa
"Biyo ni." Yace kawai yana wucewa part din sa.
***
Tun da ya koma gida ya shiga tunani, tunanin maganganun yake, tun da yake ba'a taba ma gaya masa magana me zafi irin hakan ba, sosai yaji zafin maganar har yaji gaba daya komai ya sake fice masa akai, tashi yayi ya hau hada yar karamar trolley d'insa da zai tafi da ita Cross river, rashin me kula da Ummi ne yasa ya jinkirta ta tafiyar har zuwa weekend saboda su samu su tafi tare da Kamal in yaso sai Yaya Nabila tazo gida ta zauna, kaya kala biyu ya dauka sai single da boxers, perfumes da brush sai chargers din sa na pad din sa,waya da computer.
Fitowa yayi kasa ya tarar da Hajiya Mero da Zainab a zaune suna kallon Mbc, kamar ya wuce sai ya fasa ya dawo zauna, kallon gefen Zainab yayi yace
"Hajiya kiyi mata magana, ba zan dau rashin kunya ba gaskiya."
Da sauri Zainab ta kalle shi,sannan ta kalli Hajiya Mero,
"Mummy!..?"
"Bake ba." Ya fad'a yana mikewa
"Kayi hakuri zanyi mata magana."
Hannayen sa ya zuba a cikin aljihun wandon sa ya sa kai yayi ficewar sa, wajen su buzu me gadi ya nufa yana tafiya yana tunani, shi fa ko yaushe cikin tunani yake ya rasa yadda za'a yi ya bar tunani gashi hakan ba karamin chusgunawa ransa yakeyi ba.
Gefen Hajiya Mero Zainab ta koma tana kallon fuskar ta bakin ta dauke da tambaya
"Wa yake nufi wai?"
"Wai Rauda, kinsan ita zai aura har ansa bikin saura three weeks ma."
"What!!!" Ta ja baya da sauri
"Zanyi miki bayani, muje daki."
Fusge hannun ta tayi ta saka kuka, sake riko hannun ta Hajiya Mero tayi ta kwace ta shige daki da gudu ta saka key. Dafe kai tayi a hankali tace
"Yaran nan zasu haukatani."
***
Bangaren Hafiz ya rasa ina zai tsoma kansa, duk in da ya buga babu, gashi dama fushi yake da ita sai abin ya sake yi masa yawa, duk yadda yaso ya saukaka wa zuciyar sa idan ya tuno sai yaji komai ya kara dagulewa, inna tayi tafiya ta tafi chan garin su Gumel ta sanar wa yan uwa da abokan arziki tun da kowa nasu suna Gumel din su ka dai ce sai Kawun su Hafiz din.
Yana zaune a kofar wani shago yana kokarin kiran wani wan Innan da yake aiki a Jigawa FUD ko zai taimaka masa da wani abun kiran ta ya shigo, rejecting yayi ya ja dogon tsaki yana kashe wayar gaba daya, haushin ta sosai yake ji duk da kasan ransa yana son ta baya so kuma ya rasa ta, sai dai zafin rai irin nashi ya hanashi sam ya gane irin son da take masa ita ma duk da talaucin sa, duk da su ɗin ma ba wani shine dasu ba amma ba za'a hada su da su Hafiz din ba.
***
Jirgin karfe 10 zasu shiga zuwa Abuja daga nan sai su hau wani, a tsanake ya shirya ya dauko wani yadi fari kal me masifar kyau, tsayawa yayi rike da yadin yana tunani, ajiyar zuciya ya sauke ya maida yadin ya ciro wasu daban ya saka, taje sumar kansa yayi ya fesa turare ya saka hula, kwantancen sajen sa da ya sha mai ya sake kwantar wa sannan ya makala Bluetooth a kunne sa ya riko jakar ya fito, dayan hannun nasa rike da wayar sa yana kokarin neman layin Kamal.
Dan Dan....... Ko Arab zai yarda su hadu a CR ɗin? Ko zai yarda da abinda zasu j masa? Ko zai sanar dasu dalilin sa na tafiya ba sallama? Ko asirin da yake binne zai fito? Ko za'ayi auren Maryam da Hafiz? Arkel da Rauda? Wacce irin kaddara ce zata zo musu? Me zai faru? Me zai kasance? Ku biyo ni, akwai soyayya me zafi da tsayawa a rai a gaba, za kuma kuji asalin labarin kowanne family, mu bi komai a sannu
Nagode sosai da kauna😍😍🚴🚴
Kuyi hakuri wlhi ciwon ido ne ya sani gaba, kallon screen yayi yawa shiyasa kuke ji na haka, kar naje garin neman gira.....🚴🚴🚴
***
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
👇🏻karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon
Rano🚴🚴🚴
*SAUYIN K'ADDARA*
*11-12*
©*Hafsat Rano*
*_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_*
*08030811300*
*07067124863*
*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_Kai min halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin kaddara_*
_hafsat rano_
***
Saurin bude kofa tayi ta fito jin kamshin turaren shi daya gauraye tsakiyar falon, a gaban sa ta ja ta tsaya tana kallon sa, idon ta da yayi jajawur yake kallo, dauke kansa yayi ya daga wayar kamal,
"Ok gani nan."
"Lafiya?" Ya tambaye ta yana watsa hannun sa gefe
"Aure wai zakayi?"
"Yes. Akwai matsala ne?" Ya fada cikin halin ko in kula
"Anty Rauda zaka aura kuma?"
"Are you asking me?"
Daga kai tayi alamar eh
"Jeki tambayi Hajiya nima ban sani ba."
Rabawa yayi ta gefen ta zai wuce ta saka kuka, tsaki ya ja ya dauki jakar hannun sa zai fita Hajiya Mero ta fito da sauri, kallon Zainab tayi dake kuka ta kalle shi, idon ta ne ya kai kan hannun sa tayi saurin cewa
"Kai kuma ina zaka? Na ganka da jaka."
"Ni wai?" Ya juyo yana kallon ta
"Da wa?" Ta fada a ƙufule jin yazo da rainin wayo,
"Ohh okh... zan je wani waje ne."
Fita yayi ta saki tsaki tana hararar Zainab,
"Shegiya me k'aton baki, ubanki ne da zaki saki baki kina masa kuka? Kin wuce ko sai na kakkaryaki?"
Buga kafa ta hau yi cikin kuka tace
"Dama nasan kin tsaneni, kuma wlhi yau zan koma gidan Hajiya Mama, ba zan sake zama a wajen ki ba."
"Kifi ruwa gudu, in Zaki birgeni ki koma wajen dangin ubanki mana kiga idan zasu tsinana miki komai."
Juyawa ta ta shiga daki ta shiga hada kayan ta.
Da baya ta zauna tana dafe kai,rigimar zainab ta soma isarta, tun jiya suke abu daya, ga wannan ɗan rainin hankalin ya soma daga mata hankali, tsoron ta daya kar ya lalata mata aiki, shiyasa ma take so ayi ayi ayi auren ko ta dinga jin komai akan sa wajen matar.
Tana nan zaune Zainab ta fito da jakar kayan ta da tarkacen abinda zata bukata tayi ficewar ta, ci kanki bata ce mata ba sai ma dauke kanta da tayi ta cigaba da aikin tunani.
***
Yana harabar gidan suka shigo, gefe kamal ya samu yayi parking ya karkace yana kallon matar sa
"Dear ba zakiyi missing dina ba ne naga kina zumudin sauka?"
"Kasan zanyi sosai,kawai an eager naga Ummi ne, kuma kaga Malam Sammani yana jiran mu." Ta fada tana kallon windon motar, kallon Arkel yayi da ya zuba wa motar ido yana jiran fitowar su,
"Wai shine Sammani?" Ya fada yana dariya, dariyar tayi ita ma tace
"Ba ruwana wlhi, yanzu sai ya hau kamar bread din da aka sawa yeast."
"Zaki bayani ne, ai sai na faɗa masa."
"Ba yadda zai ba ai." Ta fada tana kokarin danna central lock din motar. knocking yazo yayi a jikin glass d'in, dan sauke glass din Kamal yayi yana kallon sa
"1 mint muyi sallama da Madam kaji malam Sammani."
Zaro ido yayi, da sauri kamal ya daga glass din motar ya jawo ta jikin sa, peck yayi mata a both cheeks din ta sannan ita ma tayi masa, sakin ta yayi ta balle murfin motar ta fito, kallon su Arkel yayi ya taɓe baki a ransa ya ce
"Iyayi kawai."
"Morning babbar Yaya." Ya fad'a yana murmushi
"Morning small kani." Ta amsa tana daukar Amna a bayan motar
"We are running late fa, nasan kece kika rike shi."
Dariya kawai Nabila tayi ta daga wa kamal hannu,
"Safe Dear."
"I ll miss u." Ya fad'a yana marairaice murya
Saurin fadawa motar Arkel yayi ganin zasu sake bata lokaci kuma, dariya kawai sukayi masa ta shige ciki.
***A airport suka ajiye motar sannan suka daga zuwa birnin tarayya, daga nan suka dauki hanyar CR.
Runtse idon sa yayi lokacin da suka shigo garin, ajiyar zuciya ya sauke ya bude idon sa yana kallon ko ina, Uber suka kira ya kai su babban hotel din garin na Calabar,
27, January 2025
Rukayya
Good