Showing 84001 words to 87000 words out of 98004 words
tafiya zuwa Mali. A ranar duk suka shirya komai suka saka rana.
***
Yana zaune a gaban system din sa bayan ya gama abinda zai yi, so yake ya shirya da wuri ya shiga office, kwana da yawa duk ya zama unserious dan ma akwai Salim ne. Wucewa tazo yi ya kalle ta, tashi yayi yabi bayan ta Matse ta yayi a jikin kofar yana hararar ta
"Me kika ci yau?"
Cikin in da in da tace
"Naci fa abinci, Walid ya siyo min awara kuma naci."
"Awara abinci ce? Kina so kiyi min wasa da baby ko?"
Bata fuska tayi ta turo baki
"Ni wacce baby Kuma?"
"Ta nan." Yasa hannu a saman cikin ta, kwace jikin ta tayi ta bar shi a tsaye yana murmushi
"Zan kamaki ne, dura zan miki Allah."
Gwalo tayi masa ta wuce ta barshi a tsaye yana cije yatsa.
Wayar sa dake saman kayan takardun sa ya dauka, karawa yayi a kunne
"Ya akayi?"
"Oga wallahi ina taso na fada maka Hafiz fa kwana biyu shiru be shigo site ba."
Daga dayan bangaren akayi magana,
"Subhanallah, tun yaushe amma be zo aikin ba?"
"Almost a week kenan fa."
"Shine amma baka sanar min ba? Wannan ai kuskure ne kana aiki da mutum kwana kusan biyar babu shi babu aike sannan ace baka neme shi ba, baka kyauta ba gaskiya."
***
Sosai ya farfad'o, duk ciwukan jikin sa anyi masa dressing din su, hannun sa da kafar sa guda dai-dai ya samu karaya kuma suma an dora shi, sosai yake samun kulawa daga mutanen da be san su ba, wani masinja aka saka yake jinyar sa.
A chan Gumel kuwa hankalin inna a tashe yake, babu irin kiran sa da batayi ba, amma amsar daya ce kullum a kashe, gashi babu wani da ta sani da zata kira shi akan Hafiz din, ta dai san wajen da yace mata yana aiki, ganin babu wata hanya yasa kawai ta shirya ta nufo Kanon ita da suwaiba.
***
Duk da shirye shiryen da ake tayi na tafiya amma hankalin Arkel baya jikin sa, gaba daya tunanin sa yana wajen in da Hafiz yake, duk ya bincika in da zai bincika amma shiru babu labarin sa, da wuri ranar ya fita ko breakfast be samu yayi ba, da salim suke waya har ya karasa, yana zuwa shima yana zuwa, sai suka shiga office. Bayan sun gaisa yake tambayar sa
"Baka san wani da suke harka anan ba?"
"Gaskiya ban sani ba wallahi, amma bari a tambayi sauran ma'aikatan ko za'a samu wani ya san shi."
Dafe kansa Arkel yayi ya juya baya yana jin a ran sa tabbas babu lafiya, shiru yayi yana ayyana komaai zai iya faruwa, kar dai ace sun kashe miciji ne amma basu sare... Shigowar Salim yasa ya kalle shi da sauri
"An samu?"
"Me gadi yace ranar ya karbi machine din sa a gurguje, sai dai be san in da ya tafi ba, rabon sa dashi kenan, daidai ranar da mukayi tafiyar nan kenan, da safe."
"Kana nufin tun ranar be dawo ba, kenan babu shi babu machine din."
"Babu, kasan Baba Megadi da dattako, baya so ya tada maganar shi yasa ya tsaya ya ga ko za'a yi magana, yana da yakinin dai ba zai gudar masa da abin hawa ba, ya yarda dashi dari-bisa -dari."
"Akwai matsala." Arkel yace yana mik'ewa
"I'm afraid to say that evil witch is still alive, ya Allah, tayi wasa da hankalin mu."
"Ko dai yaje gida ne, kasan fa yace mahaifiyar sa ta koma Gumel, ko mu fara tuntubar su chan din."
"Ba haka bane, babu yadda za'a yi yaje gida be sanar ba, idan lissafi na yayi daidai da ranar da Megadi yace zaka ga daidai ne da ranar da mukayi tafiyar nan, babu dalilin da zai sa ya tafi gida ya dau wannan tsawon lokacin, bayan haka ma ai yana da Number ta, zai kira ni ai, something is fishy gaskia,baka kyauta min ba kuma da baka sanar dani da wuri ba, getting to three weeks kenan fa, haba!"
"Ayi hakuri Oga."
Be yi magana ba ya fice daga office din Yana tunanin in da zai yi, yana zuwa gate su Inna suna sauka daga adaidaita sahu, kallon su yake har suka sallami me keken suka nufo shi, babu wani dogon tunani ko nazari ya gane su saboda tsantsar kamar da ya gani da Hafiz.
"Sannu da Zuwa Hajiya."
"Yawwa sannu dan nan, dan Allah nan ne wajen da Hafizu yake aiki?"
Gaban sa ne ya fadi, sai yayi saurin dakewa yace eh
"Dama kwana..."
"Ku shigo ciki Hajiya."
Ciki suka shiga ya basu kujera suka zauna sannan ya zauna yana sauraron ta
"Dama kwana biyu Hafizu shiru babu wani labarin sa, babu waya be zo ba kuma, shine nace bari na zo naji menene yake faruwa, jiki na yana bani na lafiya ba."
Abinda yake tunani ya tabbata, sai ya mike da sauri yana kallon su, tunanin yadda zai sanar mata yake, idan ya boye mata be mata adalci ba tun da uwa ce, ko ba komai zatayi masa addu'a a duk in da yake Allah ya tsare shi, sai daya ja numfashi kafin ya daure yace
"Hajiya muma nan rabon mu dashi wajen sati biyu kenan da doriya, sai dai nayi tunanin ko nan gida ya taho, zancen da nake miki yanzu maganar muka gama da ma'aikata na."
Inna na Jin haka ta ɗora hannu aka ta saki kuka.
"Shikenan abin da nake tsoro ya faru, sai dana ce masa ya hakura da zaman Kanon nan, amma yaran yanzu ka haife su ne amma baka haifi halinsu ba, sai su nuna maka ma sun fika wayo da sanin abinda yafi, yanzu na shiga uku ina ya shiga?"
"Kiyi hakuri Hajiya, in Sha Allah zamuyi iya kokarin mu, kiyi hakuri kiyi masa addu'a."
Share hawayen ta tayi tana addu'a, sun dade suna tattaunawa kafin ya dauke su a motar sa ya kaisu gidan Ya Nabila bayan ya basu tabbacin zai nemo Hafiz a duk in da yake.
***
Dariya sosai tayi bayan ta gama waya dashi, sai ta ajiye wayar ta mike ta shiga dakin ta, kayan jikin ta ta rage ta jawo karan sigari guda daya ta zuk'a ta kwanta dan so take ta dan rage baccin da take ji, tana kwanciya wayar ta dake falon ta hau karar neman agaji, sai data yi tsaki sau ba adadi ganin kiran yaki daina shigowa ta tashi ta fito falon, a fusace ta dau wayar sai dai sunan data gani a saman wayar yasa ta tsaya ba tare daga ba, duk da kasancewar ta jaruma mara tsoro amma tabbas ganin sunan ya saka taji wani yar har sai da wayar ta tsinke bata daga ba, tana kallon kiran ya sake shigowa sai dai bata da kuzari ko ƙarfin zuciyar d'agawa dan bata shirya wa hakan ba, bata shirya nuna kanta ba har sai ranar da zasuyi tafiyar da suka shirya, a ranar ne kowa zai san abinda da ta ke so a sani ɗin. Ganin bata da niyyar daga kiran sa gashi dai dama be yi tunanin zata daga ɗin ba amma jin wayar a kunne ya kara bashi tabbacin abinda yake tunani, abu daya zai yi shine kawai yake ganin mafita, sai ya juya akalar motar sa zuwa gidan su maryam. Yana zuwa ya tsaya daga chan nesa da gidan ya kira Zainab, yace tazo zasuyi magana, kamar mintuna biyu sai gata ta fito taana kalle kalle, horn yayi mata ta nufi wajen, kallon ta yake har ta karaso ya bude mata kofar ta shiga, kafin tayi magana ya ja motar.
"Babu gaisuwa?" Yace yana hararar ta, da sauri tace
"Ina wuni."
Sai ya sassauta maganar sa tunowa yayi da sai ya lallabata idan har yana so ta taimaka masa
"Haba dear, shikenan daga tafiya sai ki manta da kowa, ba waya ba komai? Ko baki dauke mu yadda muka dauke ki bane?"
"A'ah, kawai ina jin kunya ne."
"Kunyar me? Common abun da ya faru ai ya riga ya wuce, and am sorry for making u sad, a time din bansan me ya hau kai na ba, amma ni yanzu komai ya wuce a waje na."
"Da gaske?"
Daga mata kai yayi
"Nagode bro."
"Karki damu."
Shiru sukayi sai chan yace
"Ya jikin Mummym? Ranar naga wata kamar ita ai, jikin ya samu sauki da alama."
"Uhum."
Tace a gajarce tana tuna maganar da sukayi, warning ɗin da tayi mata akan karta faɗa wa kowa haukan karya tayi, yana lura da ita yadda ya tafi tunani gaba daya,murmushi yayi irin na gefen bakin nan yayi parking a daidai kofar store din.
"Shiga ki dau duk abinda kike so, ga Atm d'ina nan sai kiyi payment din Ina jiran ki a mota."
Da sauri ta kalle shi ya sakar mata lallausan murmushin dake narkar da ita, har gaban gobe tana nan da soyayyar sa a ranta, sanin yayi mata nisa ne yasa ta hakurr wa zuciyar ta, ta rungumi kaddarar ta, sai dai abinda ya faru yau gaba daya yasa ta sake dawo da tsohon tsumin dake boye a karkashin ranta.
Tana gama daukar abinda zata dauka wanda mafi aka sari kayan kwalliya ne ta fito, yana waya yana ganin ta ya ajiye yana sakar mata murmushi
"Are You Done?" Ya tambaya yana tada motar, daga mishi kai tayi ya ja motar suka bar wajen, duk ya gama tsara yadda zai ɓullo mata, sai da suka kusa zuwa gida sannan yace
"Zaki aure ni?"
Ras gaban ta ya fadi, yadda taji maganar, duk sai ta duburburce, murmushi yayi ganin ta kasa controlling kanta ya dan rage tafiyar da yake
"Na shirya auren ki idan har kin yarda, amma da sharad'i."
"Zaki fad'a min komai da kika sani game da Mummy, Ina take yanzu haka? Ita dawa suka harka?"
Sai ya dora
"Nayi miki alƙawarin babu abinda zan yi da zai cutar dake, Ina son dai nasan halin da family ne yake ciki, kinsan halin ta, kinsan me zata iya, idan kika yi shiru kika bari aka cutar da wani ta sanadiyyar ki, Allah ba zai barki ba, hakki ba zai barki ba, ki taymaka mu haɗa karfi da karfi mu ceto ta daga fadawa halaka, ina ji a raina akwai wanda yake sakata komai."
Ga koshi ga kwanan yunwa, babban burin ta shine auren Arkel, ga kuma tsoron abin da zai faru da mahaifiyar ta idan ta tona mata asiri, shiru tayi tana aunawa da zuciyar ta, dole zabi daya zata dauka, abu guda biyu da ana ta tunanin take ganin sun fi komai muhimmanci a rayuwar ta. Jin tayi shiru a karo na biyu yasa ya gangara gefe yayi parking ya juya jikin sa sosai yana kallon ta
"Ki taimake ni, ki dubi rayuwar da mukayi a baya, bana fatan sake shiga irin ta, karki tunani na kawo maganar aure ne saboda na yaudare ki ki faɗa min abinda baki yi niyya ba, ban yi hakan ba sai dan son kubutar dake da dukkan wani sharri."
"Kayi alƙawarin babu abinda zai same ta idan na fada ma?"
"In Sha Allah."
"Ka rike amana."
"Mummy ba ita kadai bace take aikin ta, sannan Mummy tayi rashin lafiyar karya ne saboda ta kubuta daga abinda kake shirin yi mata, bana son yadda yake tsara mata komai, sannan duk wani abu shine yake fada mata akan ka, duk wasu shirin ka ta sani, ba kowa bane face yaron daka yarda dashi fiye da kowa, wanda kake ganin yafi duk wani makusanci kusanci da kai, Salim shine abokin aikin Mummy, tare suke aikata komai."
Tsabar rudewa kusan daskarewa Arkel yayi a wajen, a take jin sa ya nemi daukewa na wani tsawon lokaci, sunan salim dake karakaina tsakanin kunnuwan sa da ƙwaƙwalwar sa ne ya hadu ya cunkushe masa a waje daya ba tare da ya san takamaimai me yake shirin faruwa ba. Ba karamin kokari yayi ba wajen tattaro dukkan nutsuwar sa, cikin Muryar sa da ta gama dishewa saboda tsabar k'aduwa yace
"Tana ina yanzu? Karki kuma ki faɗa min, taymakon ta zanyi."
Sai data kalle shi ta kara kallan sa dan ba karamin tsoro ya bata ba yadda a lokaci daya yanayin sa ya koma, cikin in da in da tace
"Badawa Lay-out."
***
Nagode sosai Affan ya samu sauki, kuyi hakuri da rashin jina kwana biyu.
#Not edited
****
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
👇🏻karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp
08030811300
Ga masu turo da katin waya
kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Sai kayi wa Number magana ta WhatsApp
[3/18, 22:28] Hafsat Rano: SK 51
HAFSAT RANO
***
Tana shiga dakin ta ganshi a zaune akan drawer yana duba abu a wayar sa,ja tayi ta tsaya daga bakin kofa ta kasa shiga, sarai ya ganta sai ya nuna kamar be san tana wajen ba, ya tashi ya shige toilet d'in, zagaye idon ta tayi a dakin cikin sakan da bazasu wuce biyar ba, dakin yayi mata kyau ainun, duk sai taji tana sha'awar zaman gidan ba kamar chan ba da suke a hade. Fitowa yayi yana gyara link din rigar sa yazo zai wuce ta kusa da ita, riko shi tayi ta dawo dashi baya, idon su suka hadu waje daya, kasa tayi da kanta da sauri ganin yadda ya tsare ta da idanun sa yana neman lallai sai ya sata dole taji kunyar sa.
"Mu tafi ko?" Yace yana basarwa, kallon hannun sa yayi ya kalle ta alamun ta sake shi, jiki a sanyaye ta cika shi ya juya ya bar dakin, da kyar ta ja kafufuwan ta ta fito falon jikin ta a matukar mace, sai dai bata karasa ba taji an rufe mata ido, a hankali yake janta har ya kai ta gaban wajen, a hankali ya cikata ya na ja da baya da baya har ya fice daga falon, duhun daya mamaye ko ina na falon ne ya dauke haske ya bayyana, idon ta ne ya sauka akan babban allon dake manne a jikin falon yana fitar da wasu irin kaloli masu ban sha'awa da birgewa, a hankali rubutun dake jiki ya fara bayyana daya bayan daya wata irin waka me kama da busar sarewa na tashi a hankali.
``` _At first i never care who you are, but now I don't know who I'm without you, you walk lightly into my heart,captivating and lovely to my heart._ ```
``` _My life has forever change, the first time we met, I could see that you and I were meant to be together, your eyes were so gentle, your smile so true._ ```
```_For you are my heart, My Soul and my oneness, with you I know I will find my completeness, my eternal peace_ ```
``` _You are the better half of me, you mean the world to me, both of our hearts will forever bond into happiness, falls, pains and sorrow. I promise you together we will meet tomorrow._ ```
``` _These little words I have written speaks some of my love for you._ *I LOVE YOU SO MUCH CARIAD*
Wani irin yanayi ta shiga me kama da almara, sosai maganganun suka taba ta, cigaba da kallo tayi in admiration kamar zatayi me dan murna, yana tsaye a bayan ta yana kallon ta, hannun sa sark'e a kirjin sa ya kasa ko da kwakkwaran motsi yana jin wani irin yanayi, nauyin da yake ji a zuciyar sa ya kau a dan lokacin nan, babu wata fargaba ko shakku sai dumbin soyayyar ta, soyayya me karfin gaske da mutum ba zai iya kuje mata ko juya baya ba, amma ba irin wanda idon mutum zai rufe ya kasa gane daidai da akasin sa ba, ganin yadda take juya jikin ta da kanta cikin tsananin farin ciki yasa yaji kamar ana ingizashi, cikin sassarfa ya isa gareta sai ji tayi an zagaye hannu a tsakiyar cikin ta, ajiyar zuciya ta sauke da karfi tana daidai ta nutsuwar ta,maganganun yaa shiga rada mata a kunnen ta wanda ni kaina bazan ce ga su ba sai Echo din husky voice d'in sa sake yin fita kamar bugun ganga kawai zaka ji, ita kadai take jin me yake ce mata, duk ya gama sagar mata da jiki babu sauran shakku ko noke wa, ta gama aminta dashi da soyayyar sa wadda take ganin kamar a mafarki. Tsawon wasu lokuta suka dauka a wajen yana sake fallasa mata asirin zuciyar sa, da wayo da wayo yake mata har ya samu ta fallasa ta ta zuciyar cike da karsashi da son faranta wa wanda kake so, a duniya bashi da wani sauran damuwa, yadda ya bata shekaru masu yawa yana faman rayuwar kunci a yau ya ajiye komai, dole ne shima ya dandani ruwan soyayyar da yake gani a tattare da Kamal mijin ya Nabila, a rayuwa mutumin na yawan fado masa a rai saboda yadda yake nuna soyayyar sa ga matar sa a gaban kowa wanda muka rasa hakan a wannan society din namu, Kamal mutum ne daya san daraja da kimar iyalin sa, baya fatan bata musu ko wulakanta musu sai dai duk da hakan akwai lokutan da suke samun sabani tun da dama aure ya gaji haka, babu ya yadda zakayi kashe zaka dawwama a cikin farin ciki babu wani kalubale, dole ne akwai kalubalai masu yawa sai dai mutum ya san yadda zai yi handling komai ba tare da tsangwama ko wulakanta abin zaman ka ba.
***
Duk da kowa ya gama aminta da rayuwa me dorewa a dan uwan sa, sai dai har lokacin Arkel na ji a ransa akwai sauran abubuwan da ya kamata ya sanar mata, tashi tayi daga jikin sa ganin dare yayi sosai tace
"Ya kamata mu tafi gida."
Noke kafada yayi yana sake miko mata hannu
"Ba yanzu ba gaskiya, zo kiji."
Dawo wa tayi ta sake kwanciya a jikin sa, hannu ya saka cikin gashin kanta yana yawo dashi a hankali.
"Bani labari.."
"Uhmm.. Abu daya na kasa mantawa, time da kayi min tsawa nazo office din ka, har kuka nayi."
"Wayyo I'm sorry, ban kyauta ba, kinsan yadda naji ba dadi kuwa? Bayan kin tafi nayi ta damuwa."
"Ba wani nan, Allah ni ba zan yarda ba."
"Allah da gaske, nace me yasa nayi wa me kyau masifa, sai daga baya
27, January 2025
Rukayya
Good