Showing 12001 words to 15000 words out of 98004 words

Chapter 5 - SAUYIN KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

06 Jan 2025

11606

ya k'ark'are da

"Shine dai maganar dama, ya kike ganin za ayi tun da dai nasan kun riga kunyi maganar tun ba yau ba."

Kallon shi Inna tayi ya sunne kai k'asa, rasa abinda zatace tayi dan bata san kan zancen ba, numfasawa tayi tace

"Duk yadda kukayi ai yayi, sai aje a tambayar masan."

"Shikenan, zuwa karshen satin nan in sha Allah xamu zo dasu Bashari sai shi yayi mana jagora zuwa gidan."

"Kana zuwa zance wajen yarinyar ai ko?" Ya fad'a yana kallon sa

Girgiza kai yayi yana sake kasa da kai dan ba k'aramin nauyi ne da maganar aure ba, tafa hannu Inna tayi yayi saurin cewa

"Ai yanzu ne idan aka tambaya min idan mahaifin nata ya san dani zai barni naje gidan nasu, haka tsarin gidan su yake sai an fara tambaya kafin a fara zuwa."

"Hakan ma yayi ai, zamu zo zuwa karshen sati sai a sanar da iyayen yarinya."

"Allah ya nuna mana, Allah ya saka da Alkhairi." Inna ta amsa

Mik'ewa yayi ya musu sallama ya tafi, yana fita inna ta rike habarta tana tafa hannu

"Yanzu Hafizu aure zaka jajibo wa kanka muna fama da wannan kauma- kaumar?"

"Ai ba auren zasuyi mata yanzu ba fa, tace kawai a san dani ne dama."

"Lallai, aka ce ma jiran ka zasu zauna yi kenan? Lallai baka da hankali."

"Inna...ki sa albarka kawai dan Allah."

"Shikenan, Allah ya tabbatar da alkhairi."

"Amin Inna, ko ke fa."

Har ya mik'e ta tsaidashi

"Nace Allah sa baka yi mata saurin fushin nan naka da zafin rai? Kasan dai ina ce maka ka rage ko."

"Ah haba banayi mata."

"Allah yasa."

Fita yayi shagon unguwar su ya karbi bashin katin dari biyu ya saka, gefe ya koma ya kira Maryam ya fesa mata abinda ya faru, ranar wuni sukayi suna farin ciki kamar an musu albishir da zama ma'aurata.

****
Ranar jumma'a ta kama ranar sunan Anty Maryam, da wuri suka tashi ta shirya su Habubu da Walid ranar ba zasu makaranta ba, Umma da asubah ta tafi saboda aiki su kuma sai su tawo daga baya, tana gama shiryawa kiran Salim ya shigo wayar ta, ta san kwanan zancen, tana d'agawa taji yace

"Baki zo ba har yanzu, zaki shigo kuwa?" Ahaap zancen kenan, dariya tayi tace

"Afwan Oga, yau sunan Aunty na ne wallahi, na manta shaf jiya nace ba zan zo ba, ka bawa oga hakuri."

"Toh... Amma kinga baki zo Monday ba fa, zaki hadu da fushin babban oga ba ruwana."

"Ni dai ka taymaka min, ko kace ma bani da lafiya."

Shigowar sa kenan office din yaji maganar ta a cikin waya saboda a handfree salim ya sakata yana cike wasu takardu, be taba tunanin ogan zai shigo a wannan lokacin ba, zama yayi ya harɗe kafa ya sa hannu ya dauki wayar ya matso da ita wajensa

"Dan Aallah kace ban da lafiya, ko kuma kace dai wani abun idan yazo d'in, ogan ne baya d'aga kafa wallahi gashi kullum fuskar sa a turbune ba ya ko yar dariya."

Jin yayi shiru ne yasa ta cewa

"Ka dai taimaka, nasan kaima tsoron sa kake ko? Shi din ne da abin tsoro wallahi ba fara'a, sai dai anjiman yadda kukayi naji."

"Kin gama." Ya fad'a cikin husky voice d'in sa

Wani irin das taji tun daga saman kanta har kafarta, kiris ya rage ta subutar da wayar hannun ta,

"Kin gama zagin nawa? Kizo yanzu kar ki wuce minti goma ."

Kafin tayi magana ya kashe, kallon Salim yayi da yayi cilli -cilli yace

"Wacce irin magana kuke haka da yarinyar nan har take irin wannan zantukan?"

Share zufa salim yayi yace

"Yau ne farko oga, ka yarda bamu taba magana makamanciyar wannan ba, ita ɗin ma tsautsayi ne kayi mata afuwa dan Allah dani baki d'aya."

Daga masa hannu yayi kawai ya bar office d'in

Tashin hankalin da ba'a sa masa rana, gidan Hajiya Mama ta tura su Habubu tace suje bangaren su Sultan su jira taje wajen aikin su ta dawo, sun saka rai da fita haka ta raka su gate d'in gidan ta dau hanya, ko gaban ta bata gani wulla kafar ta take ko ina, tsoron ta daya kar yayi rubutu a kanta ya aika dept, shikenan ta kad'e har ganyen ta, kad'an kad'an take saka gefen hijabin ta tana share hawaye har ta isa cikin kankanin lokaci, yanayin tafiyar ta kawai zaka kalla ka gane yanayin tashin hankalin da take ciki, ko ta kan me gadin wajen dake ta gaishe ta bata bi ba tayi ciki kawai,wajen salim ta wuce yana ganin ta ya saka hannun sa kasan bakin sa

"Ya zanyi?" Ta fada a marairaice

"Kije yana office d'in sama."

"Na shiga uku, kar yayi reporting d'ina a makaranta."

"Kai anya, jeki dai kiji."

Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka ta ja ƙafafuwan ta da k'yar ta hau saman tana wasi-wasin abinda zata tarar, knocking tayi yace ta shigo, wayyo Allah ,kunya kamar ta nutse haka taji, bude mata idon sa yayi baki daya ya zuba su akanta, kallon ta yake babu dauke ido yana danne dariyar da take son taso masa dan raban da yaji abinda ya bashi mamaki da dariya ya dade, tun da ya baro wajen salim yake dariya yana tuno yadda ta dage yana munafurcin sa, muryar ta tar babu alamun tsoro, amma ji ta yanzu kamar tsohuwar munafuka sai sunne kai take, sai daya gama kallon ta tsaf kafin yace

"Me ya hanaki zuwa Monday?"

"Kayi hakuri dan Allah."

"Haka kawai?"

"A ah wanki nayi.".

"Wanki?" Ya fad'a yana kallon ta

Daga kai tayi,

"Yau ma wankin kike?"

"A ah."

"Mene?"

"Haihuwa akayi mana yau suna."

"Wa kika gaya wa?"

"Ba kowa."

"Me sa?

"Ba komai."

"Hmm."

"Kayi hakuri."

"Ni masifaffe ne? Tsoro na kike ji?"

"A ah." Ta girgiza kai da sauri.

"Hmm, shikenan."

"Toh kayi hakuri dan Aallah."

"Kinyi min laifi ne?"

"Eh..."

"Laifin me?" Ya sake gyara zama

"Dama... Dama maganar ka nayi da bata...."

"Magana ko gulma?" Ya katse ta yana yin murmushi kad'an

"Gulma?" Ta fad'a da sigar tambaya

"Are u asking me, ba gulman bane?"

"Shine,amma kayi hakuri."

"Jeki kawai, nayi magana da yawa kaina har ya fara ciwo."

A ranta tayi tsaki kad'an ta juya da sauri zata fita taji yace

"Kin san haramcin mace ta saka turare ta fita waje?"

Tsayawa tayi chak dan bata yi tunanin maganar ba

"Kin sani?" Ya sake tambaya

"A ah." Ta fad'a a sanyaye

"Ba kyau toh, ki daina."

"Tom... Nagode."

Rufe idon sa yayi be kara magana ba, tunani ya fara yi, a hankali ya furta

_"Where are you? I need u please come back soon"_

***
Maryam na fita tayi waje kawai tana saurin tafiya gidan suna, ashe yana da kirki haka ta dinga raya wa a zuciyarta, bata tab'a tunanin iya kar abinda zai ce mata kenan ba, gaskiya ya iya rud'a mutum.

***
Shafa kowa a jikin hoton yake daya bayan daya, su biyar ne cif hadda shi, sanye suke da kaya iri daya shadda dark ash, mazan sun sha babbar riga matan kuma doguwar riga, a tsakiya suka saka Ummi da Alhaji su biyu yaya Nabila ta sunkuyo ta bayan Ummi. Dariya suke gaba daya akayi hoton da wata karamar Sallah, kana ganin hoton kasan anyi shi ne cikin so da kaunar juna. Girgiza kansa yayi ya share kwallar data zubo masa, ba zai taba manta wa da komai ba, tsawon lokacin da ya dauka ba tare da su ba yanayin rayuwar ne a cikin mawuyacin hali, bashi da wani walwala ko farin ciki shi dai gashi nan ne, a duk san da ya tuna gida da abinda ya faru ya kan ji kamar rayuwar sa zata kare, kamar bashi da wani sauran amfani a duniyar ma baki daya, amfanin me zai yi da rayuwar sa bayan abinda ya aikata? Gaba daya ya cire tsammani da wata rayuwar jin dadi shi yasa yake abubuwan sa kawai da yake ganin sune daidai, hakkin mutanen biyu ba zai taba barin sa ya cigaba da rayuwa me dadi ba.

Ƙatuwar kwalbar giyar da ke gaban sa ya sake kafa wa a bakin sa, sai daya tabbatar yayi mata tatas sannan ya ajiye yana lumshe idon sa, wannan shine kadai abinda yake ganin shine daidai da rayuwar sa.

*Waye wannan? Mene asalin labarin sa?*😳🤔

***
Kiran ta Hajiya Mama tayi tana son ganin ta,sam Rauda ya kafe akan ita fa ba zata aure shi ba, bata a wulakanci, Babu bata lokaci ta taho gidan. A gaba suka saka ta suna ta yi mata huduba, ta in da suke fita ba tanan suke shiga ba, sai da suka tabbatar da amincewar ta suka kwadaita mata abinda suke so ta samu, dama ita a tsarin ta tana son huta, ba wuya suka hilace ta suka sa ta amince da abinda suke so. Duk abin nan a kunne Alhaji Faruku, fasa shiga yayi ya koma yana jin zuciyar sa na tafasa,be taba tunanin abin nasu ya kai haka ba, gaba daya Rauda halin Hajiya mahaifiyar su ta dauka shiyasa kullum tana wajen ta, ba halin su daya da Sultan ba shiyasa sam baya shiri da ita, da yana murnar auren nata ne kawai zai sa ta dawo hankalin ta dan har ga Allah babu wanda baya son dansa ya zama nagartacce sai dai babu yadda zaiyi da ita dan ance uwa uwa ce kuma tafi gaban wasa.

Bangaren sa ya koma kawai yana jin ba dadi,be sake fita ba har sai da Baban su Maryam ya turo yana son ganin shi
***********

_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._

*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)

👇🏻karku bari ayi babuku

*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.

*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon

Rano🚴🚴🚴
[3/18, 22:23] Hafsat Rano: *Sauyin Kaddara*

*7* *Littafin nan na kudi ne me so ya karanta ya nemi wannan number 08030811300*

*
***
Dogon Hijab purple ta saka har k'asa ta nufi gidan Hajiya Mama, Alhaji Faruku na falon sa yana ganin ta ya sake fuskar sa, a kasa ta zauna duk kunya ya ishe ta, waya yake sai da ya gama sannan ya ajiye yana duban Sultan dake kallo

"Bamu waje malam."

Sosa kai yayi ya juya ya fita yana hararar ta kasa kasa ba tare da ya bari ya gani ba

"Maryama." Ya kira sunan ta

A hankali ta amsa,

"Ajin ki nawa yanzu?.

"Level 3 muke last semester."

"Masha Allah, iyayen yaron nan sun zo sun same ni akan maganar, toh alhamdulillah na yaba da su, har ma na saka an gudanar min da bincike akan shi yaron, abun farin ciki shine ban same shi da wani abu naki ko na batanci ba, abu daya na ji a game dashi da yasa ni dan shakku akai duk da shima ɗin ina ganin ba wani babban abu bane dama mutunci ake so, kina ganin zaki iya zama dashi a hakan kinga dai ke kinyi karatu daidai gwargwado amma shi ance min iya kar sa NCE ita ɗin ba ance be karbi result ɗin ba har yau, kina ganin hakan ba zai jawo muku matsala ba?

Shiru tayi tana tuno wata rana da suke waya daga tayi magana akan karatu shikenan ya hau fushi yace ta fada masa magana dan taga be je jami'ah ba, haka dai da k'yar ta samu suka shirya gashi ta kwallafa rai akan sa sosai, Alhaji Faruku na ta kallon ta yana lura da yanayin ta, sai data gama tunani kafin ta sauke kanta kasa ba tare da tace komai ba

"Na fadawa iyayen sa zai iya zuwa wajen ki tun da kin aminta dashi"

Wani irin farin ciki ne ya taso mata har ta kasa boyewa, ganin haka yasa shi cewa

"Bana son dogon zance sannan bana son zuwan dare, in Sha Allah da kun gama fuskantar juna za'a saka komai ayi a gama, ita ma yar uwarki Rauda na faɗa mata kamar haka."

"Nagode Abba Allah ya kara girma."

"Amin."

Jiki a sanyaye ta taso ta fito, tunanin maganar take idan Hafiz yaji, zancen gaskia idan aka ce maganar aure nan kusa tasan ba lallai Hafiz din ya iya ba, gida ta koma ta zabga tagumi tana tunanin mafita. Umma na kallon ta ta share ta, tun daga lokacin ta daina walwala kwata-kwata.

Lokacin da Hafiz ya fara zuwa ranar kasa fada masa komai tayi game da maganar, sai da yayi zuwa na uku sannan ta daure ta sanar masa, maimakon taga ya shiga tashin hankalin sai taga al'adun haka, wakewa yayi suka cigaba da hirar su har lokacin tafiyar sa tayi ya tafi.

Ko da yaje gida ya sanar wa Inna komai dama tasan za'a rina, shawarwari kawai ta bashi tun da dai ya riga ya kai kansa kuma dole ayi, haka dai ya koma daki yana tunanin mafita.

Tun daga ranar ya shiga fafutukar yadda zai yi, bashi da lokacin kansa sai bige-bige, sosai take tausaya masa dan ba karamin wahala yake sha ba, yar wayar ma ba sosai suke samu suyi ba.

Watan ta uku ta daina zuwa Siwes sai dai taje sau daya a sati, rabon da ta hadu da shi ba zata iya tunawa ba, Allah Allah take ma tayi tayi ta gama gashi da sauran wajen wata uku.

***
Fito da komai yayi ya ajiye shi a saman centre table, d'aya bayan d'aya yake bin su da ido kafin ya tsaya akan farar takardar dake ninke, kura mata ido yayi yana nazari, chan k'asa ya mai da ita ya rufe komai, daukar abinda zai dauka yayi ya fice kawai yana ayyana abubuwa da yawa.
Dakin da Ummi take ya kalla, har zai wuce sai kuma ya dawo da baya ya bude kofar, Hajiya Mero na zaune a gefen gadon nurse tana goge wa Ummi jikinta, magana suke k'asa-k'asa tana ganin shi tayi firgigit, cikin salon waye wa ta fadada fara'ar fuskar ta

"Son, Ashe kana ciki, sai ina kuma?"

Dan kallon ta yayi yace "cafe" ya maida hankali akan nurse din dake matse towel daka cikin ruwa, saurin kauda tunanin sa tayi ta hanyar sakin ajiyar zuciya cike da jimami tace

"Akwai improvement sosai a tare da ita, shi yasa nake so kayi aure saboda kai kanki sai kafi samun kwanciyar hankali da matar ka wajen ta akan nurses din, su sai suzo su dinga dubata ko duk sati ne."

"Hmmm. Dan bamu waje mana" ya fada yana kallon nurse din, tsam ta mik'e ta raba ta gefe ta fice, takowa yayi har wajen gaban gadon ya zura wa ummin ido, ya rasa dalilin da yasa hankalin sa yaki yarda da barin ta da nurses din, maida kallon sa yayi kanta ta sake gyara zaman ta

"Hajiya... Me ya sami Ummi ne wai ni? Tsawon wannan lokacin babu abinda aka ce sila, me hakan ke nufi ne?"

Sosai gaban ta ya fadi ta kalle shi da sauri dan bata yi tunanin tambayar ba,


kamar daga sama ta kuma jin tambayar sa data sake dagula lissafin ta

"Shi fa? Ina yake? Me ya faru a ranar ne? ke kadai kike gidan nan, ya kamata ace kinsan komai."

"Zanyi maka karya ne? Bansan komai ba, ranar na fita unguwa, kuma wallahi tallahi bansan komai akai ba, ka yadda dani."

Runtse idon sa yayi kawai ba tare da ya tanka ba, jijiyoyin kansa ne suka sake fitowa sosai cike da bacin rai, kaf duniyar nan ya rasa wanda zai warware masa komai, me ya faru? Me ya faru? Ya shiga tambayar zuciyar sa.

"Arkel..."

"Shikenan."

Juyawa yayi da sauri ya fita daga dakin, fasa fita yayi ya koma saman zuciyar sa a cunkushe, kansa wani irin sarawa yake kamar zai rabe biyu, saman gadon sa ya fada kawai ya kudundune a bargo yana jin wani irin yanayi yana huda ko ina na jikin sa.

Kiran sa Ya Nabila take tayi yana jin ta ya kasa d'agawa, yau duk tsawon ranar a daki yayi kamar mara lafiya, Forex din da yakeyi ma yau be samu ya duba ba, komai ya taso masa kamar farko, tunanin sa ya kasa wuce masa in da ya tsaya, menene dalili ko sababin da yasa komai ya tarwatse? Ya akai haka?


Kiran sallar magriba da ake tayi a masallatai yasa ya yunkura ya tashi da k'yar yana cije lebe, alwala yayi ya cire kayan jikin sa ya mayar da jallabiya ya dora hula ya nufi masallaci, ya dade yana addua akan komai kafin ya fito daga masallacin, ji yayi ba zai koma gida ba kawai ya tafi titi ya tari me napep ya tafi gidan yaya Nabila, a waje ya tarar da mijinta da wani abokin sa suka gaisa ya shiga ciki, mamaki sosai tayi ganin shi dan tasan ba karamin abu ne yake kawo shi ba, yaran ma haka su ka hau murna ga uncle ga uncle, daya bayan daya ya bisu da chocolate da ya siyo musu a hanya sannan ya samu suka barshi.

Kallon sa tayi bayan ta kora yaran dakin su,

"Suprise visit inji Bature." Ya riga ta yin korafin da take shirin yi, dariya tayi kawai tasan baya son korafin nata ne, gaisawa sukayi ta mike ta shiga Kitchen, tuwo da miya ta hado masa akan tray sai zobo me sanyi, yana ganin fitowar ta daga kitchen yayi saurin sauka kasa ya gyara zama tana nad'e hannu riga

"Wai har ka gane?" Tayi dariya tana ajiye wa

"Tun da na ga yallabai a waje ai nasan kwanan zancen."

"Wato har kasan idan yana nan tuwo nake kenan."

Dariya yayi kawai ya wanke hannun sa a d'an bowl d'in data kawo masa ya shiga cin tuwon, kurbar zobo yayi ya kalle ta yana dan bata fuska

"Dama zan dinga samun irin tuwon nan naki kullum, da ai ni na huta."

"Aure fa?" Ta yi dariya

Nan danan ya bata rai da ya tuno da Rauda, tsaki yaja kawai ya ce

"Har kin tuna min wallahi."

"Toh sai me? Ni ai hankali na ya kusa kwanciya wallahi, ka rage wannan masifar taka."

"Masifa kuma? Haka nake?" Ya tambaya yana bata attension din shi gaba daya

"Yes masifa mana, abu kadan sai ka hau kayi fam."

Murmushi yayi kadan yana tuno wayar ta, wai shine masifaffe? Wallahi yarinyar nan ma taci abinci.

"Wa fa?" Ta tambaya tana kallon sa ganin yana magana har da murmushi

Saurin girgiza kansa yayi dan be

27, January 2025
Rukayya

Good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login