Showing 3001 words to 6000 words out of 98004 words
kokarin magana Ummi, karki jawo wata matsalar kuma dan Allah."
Hawaye ne ya gangaro daga idon ta ya sauka a fuskar ta, hannu yasa ya goge mata. Turo kofar akayi aka shigo nurse din da take kula da Ummin ta shigo rik'e da ruwan allura da ake mata duk kwanan duniya, murtuke fuska yayi kamar be taba dariya ba ya kalle ta a wulakance, in da sabo ta sab'a da halin sa dan haka ko a kwalar rigar ta tayi abinda ya kawo ta ta fice, tun shigowarta ummin ta kafe ta da kallo har zuwa lokacin da tayi mata allurar ta tafi, a hankali idonta ya koma ya rufe alamun tayi bacci. Gyara mata blanket d'inta yayi ya fita yana jin sa wani iri. Kai tsaye yayi hanyar part d'insa dake saman gidan, matattakalar dake shinfide a tsakiyar falon ya kama yana kokarin hawa muryar Alhaji ta tsaida shi
"ARKEL..."
Chak ya tsaya da hawan ya juyo fuskar sa babu yabo ba fallasa, kallon sa daddy yayi na yan sakanni kafin yace
"Ya jikin nata?"
Cire kansa yayi kad'an kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru, ganin hakan yasa Alhaji dorawa
"Ya aiki? Hope komai yana tafiya yadda ya kamata."
"Alhamdulillah, ya hanya?"
Ba tare da jiran amsar sa ba ya juya zai haye saman ya katse shi
"Ka bawa Hajiya kuɗi zatayi amfani dashi."
"Nawa zai ishe ki Hajjaju na?"
Hajiya Mero dake zaune kusa da Alhaji tayi murmushi tana kanne masa ido cikin kissa tace
"Dari ma ai ina ganin zata isa, kar abun yayi masa yawa."
"Kin tabbata?"
Daga masa kai tayi tana murmushi.
"Toh kaji."
"In na fita anjima zan sa Salim ya tura mata."
Ya k'arasa hawa saman ba tare da ya sake juyowa ba.
Kallon ta Alhaji yayi cikin jin dadi yace;
"Nagode k'warai da irin yadda kike kula da Yaron nan da mahaifiyar sa, bani da bakin gode miki sai dai nace Allah yayi miki albarka."
Dadi ne ya kama Hajiya Mero ta wani karya kai tana sake kashe murya tace;
"Soyayyar da nake maka ce ta jawo komai, karka wani gode min ai yiwa kaina, bayan haka ma ai Arkel ni kallon sa nake a matsayin wanda na haifa ba wai d'an miji ba."
"Nagode miki, Allah yayi miki albarka."
"Amin Alhaji na."
***
Tsaye yake gaban mirror yana fashe jikinsa da wasu shegun turaruka masu matukar kamshi da tsada na companing Rexona, agogo ya d'aura a tsintsiyar hannunsa yana kokarin taje sumar kansa Zee ta bud'o kofar, kallo daya yayi mata ta cikin mirror ya cigaba da abinda yake, kasa karasowa tayi ta tsaya jikin kofar tana admirring irin kyaun da taga yayi, a gaskiya guy din yana kashe ta da wanka, har ya gaama tana tsaye tana imagining yadda zata bullo masa. Takalmin sa sau ciki samfurin John Lobb Dark Blue ya ciro a jikin shoe rack ya zura bayan ya sa Dark blue din half socks, dark blue yadi ne a jikin sa hakan ya sake fito da wankan sosai, a hannu ya riko hular ya dauki abinda zai dauka
"Please." Ya nuna mata hanya alamun ta matsa zai wuce
"Wajen ka nazo fa Ya Arkel."
Kallon hannu sa yayi kadan sannan yace
"Sai dai Next time."
Tsaye tayi tana kallon sa ya wuce barta kaman statue, yadda yake tafiya cikin takunsa na cikakken namijin duniya me ji da kansa ta fanni da dama yasa ta sakin ajiyar zuciya a hankali ta furta
"Take your time, I ll wait."
Kallon kanta tayi daga sama har kasa cikin shigar red gown, babu karya tayi kyau ko ta ina amma me yasa ko kallo bata isheshi ba, a sanyaye ta d'aga kafarta ta bi bayansa. Lokacin har ya isa dining yana had'a tea, kujerar kusa dashi taja ta zauna tana kafe shi da ido, haushi ne ya turnik'e shi ganin yadda ta zuba masa ido kamar sabuwar mayya, kasa ci gaba da cin abincin yayi ya ture ya tashi.
"Ya Arkel."
Ta biyo shi da sauri ganin yana neman fita, tsayawa yayi kamar zai rufe ta da duka, tun da yake be taba ganin mayya irin Zee ba, duk yadda yake wulakanta ta ta kasa ganewa, daraja daya take ci ta mahaifiyarta da wallahi sai yayi mata abinda zata yi zuciya ta daina damun sa.
"Ya Arkel."
"What!!!" Ya fad'a a dan tsawace
Tsoro tsawar ta bata tayi saurin ja da baya, juya kansa yayi yana saita kanshi kafin yace
"Am sorry."
Dadi ne ya kamata tayi murmushi,
"Dama so nake naji when zaka dawo yau? it's my birthday and I want..."
"I can't gaskiya, kinsan bana son irin shiriritar nan, I have no time to waste a irin stuffs like birthday."
"Help me pls na fad'a ma friends dina."
"And so? Zee please, Am running late see yha."
"But you are the CEO, you don't need to be in such a hurry, i know u are just avoiding me."
"Sai kuma kiyi."
Motar sa ya shige ba tare da ya sake magana ba yayi ficewar sa ya barta a wajen, Hajiya Mero dake kallon komai ta tab'e baki ganin Zee din ta dawo ciki jikin ta a sanyaye, ganin Hajiya Mero yasa ta k'arasawa wajen ta kamar zatayi kuka tace
"Mummy..."
"Wuce muje."
Rano
[3/18, 22:22] Hafsat Rano: *SAUYIN K'ADDARA*
*©HAFSAT RANO*
*®Haske Writers Association 💡*
(Home of expect and perfect writers)
*PAGE 2*
Hannun ta taja har cikin bedroom d'in ta kafin ta sake ta tana fuskantar ta
"Shine kawai matsalar ki?"
'Daga kai tayi tana jin kamar tayi kuka, murmushi Hajiya Mero tayi ta jawo ta jikinta, bubbuga bayan ta tayi cikin isa da kasaita tace.
"Karki wani damu kanki, uban ma yayi saurin bi balle shi, shi 'din banza! Zanyi maganin abun."
"Yawwa Mom, please kisa shi ya aure ni da wuri please and please kinji my love."
"Aure kuma zainab?" Ta fad'a tana kallon ta
"Eh Mom."
"Shikenan zan san yadda zan."
Da sauri ta rungume ta tana murna, fita tayi da gudu tayi d'akin su.
Zagaye Hajiya Mero ta shigayi hannun ta sakale ta bayan ta, tunanin yadda zata bullo wa Zee kawai take don babu yadda zatayi ma ta yarda ta had'a su aure kafin cikar burin ta, ta sani sarai Zee na bala'in son sa, ba zata taba yarda da duk bukatar da zata zo mata da ta akan sa ba.
Kayan jikin ta ta sauya zuwa wani tsadadden lace purple ta zuba sar'ka da d'ankunne na zallan gold, yafa mayafin tayi a kafada ta gyara zaman hudar hancin ta daurin nan ya zauna daram irin na ture kaga tsiya. A tsakiyar falon ta tsaya tana kwalawa Sadiya me aikinta kira, da sauri ta fito ta zub'e a 'kasa jikin ta na rawa, a yatsine ta shiga yi mata bayanin komai kafin ta juya ta fice hannun ta rik'e da mukullin mota. Buzu na hango ta ya taso da gudu ta cilla masa mukullin tana shiga owner's corner.
Sai da suka daidai ta akan babban titi kafin ya tambayi ina zasu je, cikin tsoro yayi tambayar saboda ya san kad'an da aikin ta ta ki amsa masa, aikuwa sai data ja fasali sosai kafin tace ya kaita gidan Hajiya Mama.
Remote na a hannun ta tana neman tashar arewa 24 ta rasa, gefenta Sultan ne yana shan kunu me zafi had'e da kosai daya karbo a wajen Umma, ta gefen ido yake kallon ta yadda ta dage sai ta nemo ta kasa ta kuma ki cewa ya taymaka mata, mik'ewa yayi dauke da kofin bayan ya gama sha ta tsaidashi cikin borin kunya tace
"Sa min arewa 24 malam."
"Da kika kasa?"
"Oho."
Yana sa mata ya bar falon, hararar bayan sa tayi ta sake gyara zama tana murmushi, jin an budo kofar ne yasa ta maida hankalin ta wajen.
Fad'ad'a farar ta tayi ganin Hajiya Mero ta shiga yi mata sannu da zuwa, amsawa tayi ta samu gefe ta zauna, daidai lokacin Rauda ta fito tana hamma, hankalin su baki daya ya koma kanta.
"Hajiya Mama yunwa."
Ta fad'a tana matsowa wajen da suke, sai a lokacin da lura da Hajiya Mero dake kallon ta, da sauri ta matsa wajen ta tana dariya
"Mummy yaushe kika zo?"
"Zuwan kenan Rauda, sai yanzu aka tashi kenan."
"Wallahi Mom baccin ne akwai sugar, yunwa ce ta tashe ni ma wallahi.
"Yayi, maza jeki ki nemi wani abun kici."
Tashi tayi tana kwala kiran me aikin su Ummu, ajiyar zuciya Hajiya Mero ta sauke kafin ta maida kallon ta wajen Hajiya Mama
"Magana zamuyi Mama."
"Toh muje ciki kenan, kafin waccan ya shigo yaji muna magana kinsan shi yanzu sai ya hau kunci."
"Yaya Alhaji ba zai taba chanja wa ba, sai yayi tayi ai ya tare baki daya a wajen matsiyatan chan, muje kafin Alhaji ya fara kira kuma."
A gefen gadon suka zauna Hajiya Mama ta tattare hankalin ta gaba daya ta bata,
"Me ya faru?"
"Aure nake so muyi wa Rauda Mama."
"Aure kuma!?"
"Aure, kinsan yaron chan ya dau wata rayuwa ya d'orawa kansa, gaba d'aya ma ya daina walwala tun abin da ya faru da uwar sa, toh dazu Alhaji ya fara min zancen Aure ya kamata ya ajiye iyali, toh kinsan fa shegen kudi ne da yaron, so nake na had'a auren shi da Rauda in yaso sai ta taimaka mana muyi aiki a kansa."
"Uhum..." Hajiya Mama ta sauke ajiyar zuciya
"Kina ganin zai yadda ya auri Rauda? Kin fa san shi da shegen taurin kai."
"Idan na biyo ta hannun uban, be isa ya ketare ba, cewa zaiyi muyi duk abinda muka ga zamuyi nasan. Matsalar d'aya ce, Zainab ta nuna min tana son shi, sai dai kinsan banbancin halin Zainab da Rauda, Zainab bata min plan xatayi wallahi na sani."
"Gaskia kar ma mu fara hada shi da Zainab, yanzu ki bar komai na bangaren Rauda a hannu na, zan sanar da ita komai nasan ba zata k'i ba, sai kiji da shi mijin naki da ita zainabun, idan komai ya tabbata ai mun warke har ita."
"Sosai wallahi."
Sallama yake tayi a tsakiyar Falon, suna jinsa suka ki amsa masa, Alhaji Farouk wanda suke kira da Yaya Alhaji ne ya shigo falon a daidai lokacin
"Yaya..."
Juyowa yayi fuskar sa d'auke da murmushi cikin tsantsar farin ciki ya ƙaraso shima
"Umaru, ashe kana ciki baka fita aiki ba "
"Ina kwana yaya?"
"Lafiya lou, kaga nazo gaida Hajiya ne kafin na wuce kasuwa ko bacci take ina ga."
Kallon kofar dakin yayi yasan ba wani bacci suna ji tun da ai ya ga shigar Mero gidan yana part din sa, ransa ne ya ɓaci yayi kokarin danne wa ya kalalo murmushi yace
"Ko dai tana bayan gida ina ga, ka zauna Yaya bari na kira ta."
"Okh toh ba matsala."
Buda kofar yayi suka kalle shi a tare, d'an sakin fuskar sa kad'an yayi ya rissina har k'asa
"Ina kwana Hajiya?"
Amsawa tayi Hajiya Mero ta gaishe shi, ba yabo ba fallasa ya amsa ya maida kallon sa wajen Hajiya Mama yace
"Yaya Garba yana ta sallama baku ji ba, gashi chan a falo yazo gaishe ki ne zai wuce kasuwa."
"Bamu ji ba, kasan shi baya bud'e murya in yana magana."
A cewar Hajiya Mama
Ko kuma kuna ji kuki amsawa ba, ya fad'a a ransa, a zahiri kuma sai ya girgiza kai kawai ya juya, tashi Hajiyan tayi tabi bayan shi tana wa Mero nuni da hannu akan ta taso ita ma.
Yana zaune ya bawa Tv hankalin sa baki daya suka fito, yana jin fitowar su ya zamo har kasa ya gaida Hajiyan, a sake ta amsa masa ganin yadda Alhaji Faruku ya tsare gida, gaishe shi Mero tayi ya tambaye ta mutanen gida da yaran, amsawa tayi a yatsine ya girgiza kai kawai yayi musu sallama ya tafi. Tare suka fita da Alhaji Faruku ya sauke shi a kasuwa shagon da yake sai da kayan d'inki da yadin hijabai sannan ya wuce office.
***
A nutse take tafiya tana kallon gaban ta har ta isa wajen, addu'a dauke a bakin ta ta shiga tana sa ran samun abinda taje nema, a farfajiyar wajen ta hangi Salim yana magana da masu kula da customers d'in dake zuwa wajen, yana hango ta ya sallame su fuskar sa d'auke da fara'a ya nufo ta,
"Zuwan kenan?"
Ya tambaya yana karasowa, dan rissinawa tayi kad'an ta gaishe shi kafin ta amsa masa, yar dariya yayi ganin bata cikin nutsuwar ta kafin yace
"Ki shiga yana ciki, kinci sa'a yau dana bashi ya karba har ma yace in kinzo na tura ki ciki."
"Ba zai mun masifa ba?" Ta tambaya cike da fargaba
"Kila..." Ya dora
"Ke dai ki nutsu kawai karki wani ji tsoro, duk tambayar da yayi miki ki amsa kai tsaye ba in-da-in-da, bari naje na sauya wa fingerlings ruwa kafin naji kira."
"Please ina so na gani, ka jira na shiga na fito dan Allah."
"Owk best of luck."
"Thanks."
Juya tayi yanayin bugun zuciyar ta ya sauya lokacin data isa kofar, sai data karanto addu'a kafin ta saka kanta ciki bakin ta dauke da sallama, a tsaye yake ya bawa kofar baya yana duba wata locker, ciki-ciki ya amsa sallamar ya cigaba da abinda yake yi, sai daya gama tsaf kafin ya juyo hannun sa rik'e da wani k'aton littafi na Fisheries and Aquaculture, d'an kallon ta yayi kad'an kafin ya zauna yana fuskantar ta.
Dakewa tayi ta isa gaban table d'in taja kujera ta zauna tana gyara zaman yar karamar jakar dake makale a hannun ta. Share wa yayi ya shiga duba littafin yana nazari,
"Good morning sir."
"Morning..Ya akai?"
Ya dago kan sa idanun su suka sark'e da juna, wani irin abu yaji ya bige shi, tuno da maganar Salim yasa ta daidai ta kanta tace
"Siwes Student ce daga Buk, na kawo request form ina so ayi min signing ne."
"Wanne course kikeyi?"
"Applied Biology."
"Bana son un-serious student, are you hard-working da zaki iya aikin wajen nan?"
"In sha Allah." Ta fad'a confidently
Be sake magana ba ya ciro request form din ya sa hannu had'e da stamp ya mik'a mata, kanta a kasa tana wasa da hannun ta zuciyar ta cike da tsoron kar yak'i sa hannun, saboda haka bata san ya yana mikowar ba, hannun nata ya zuba wa ido yana kallan yadda yan yatsun ta suka sha jan lalle, be taba gani a hannun wani ba sai ummin shi, ita ma rabon da ya gani a wajen nata an jima, tun kafin ta shiga halin data ke ciki a yanzu, d'an siririn tsaki yaja ya d'an daki table d'in, d'agowa tayi da sauri ta kalle shi, daure fuska yayi ya nuna mata gaban table d'in, hannu tasa ta d'auka cikin tsananin farin ciki ta hau yi masa godiya, cigaba yayi da duba littafin yana amsawa a zuciyar sa.
Fita tayi ta tarar da Salim a chan wajen wasu manyan tankuna, wajen ta nufa ta tarar zasu fara chanja ruwan cikin wajen, tsaye tayi tana kallon komai cikin tsananin farin ciki, sai da suka sauya wa kananun kifayen ruwa suka gyara wajen kafin tayi musu sallama ta tafi, direct Buk ta tsallaka tana addu'ar samun Malam Bahahuddin a office, a kofar gate tayi kichibis da Saddi da yan clique d'in sa, dauke kai tayi kamar bata gansu ba tayi shigewar ta, maimakon su fita sai suka fasa suka koma ciki, tana jin hayaniyar su a bayan ta, basu dai yi mata magana ba har suka k'arasa ciki.
A bud'e ta tarar da office d'in, babu kowa ciki sai shi kad'ai yana aiki a na'ura me k'wak'walwa, sai daya k'arasa sannan ya karba ya duba komai, murmushi yayi kawai yace mata shikenan.
Zuciyar ta fes ta fito tayi gida tana Allah,Allah ta isa gida ta bawa Umma labari, ko ta kan su Saddi bata bi ba ta dai hange su chan tare da su Zahra da Sophie suna hayaniya, sauri tayi kafin ma su lura da ita ta fice daga makarantar.
***
Tsaye yake gaban layin kad'an yana amsa waya, tun daga nesa ta gane shi, gaba d'aya tun ranar da tunanin taimakon da yayi mata take bacci, ganin ya cigaba da tafiya still yana wayar yasa ta daga kafa ta cimmasa, sallama tayi masa ya amsa yana juyowa, d'an sakin fuskar sa yayi kafin yace
"Bari zan kira ka dai."
"Sannu... ina wuni?"
" Lafiya lou Maryama yan jami'a."
"Ka san sunana kenan?"
"Ga zahiri."
Mamaki ne ya kamata ta yi dariya kad'an kafin tace
"Tun ranar nake son yi maka godiya wallahi, nagode sosai fa."
"Uhum, sun sake matsa miki ne?."
"A ah, kawai dai naga dacewar nayi ma godiyar ne."
"Ba damuwa."
"Nagode fa, sai anjima."
"Ki gaida gida."
Dan sosa kai yayi kad'an yana kallon ta, kansa ya kalla da shigar sa ya sake kallon ta, dawowar sa kenan daga aikin leburan ci zai wuce gida ya tsaya yana amsa wayar abokin sa, har ta kule be bar kallon ta ba, sauke ajiyar zuciya yayi ya juya ya nufi gida zuciyar sa na saka masa abubuwa da yawa.
***
Tun daga zauren gidan ta fara jiyo kamshin alala, murnar ta ce ta karu don ba karamin son alala take ba, da Habubu ta fara cin karo da kwanon sa yana ci, hannu tasa ta dauki guda yayi saurin saka ihu, Umma na jin ihun sa ta san an taba masa abinci ne, bata ce komai ba har Maryam ta karasa Kitchen din
"Nasan dama ke ko Ahmad ne wallahi, a dinga jan girma gaskiya."
Dariya tayi ta zauna kawai tana cire hijab kamar yadda ta saba ta rataye shi a igiya kafin ta shiga ciki, labarin yadda sukayi da mutumin da kuma malam Bahahuddin ta shiga bawa Umma, sai data kai aya ta dire kafin umman tace a takaice
"Allah ya bada sa'a."
Kwanon alalar Baba ta dauka tayi cikin dakin sa, sai data ajiye masa sannan ta dauko sabon flask ta zubawa Hajiya Mama.
"Maryam."
"Na'am."
"Zo ki mika wa Hajiya Mama alalan nan, daga nan ki gaishe ta, kwana nawa rabon ki da ki shiga gidan ne ma ni."
"Ranar nan fa naje gidan."
"Karya ne, dauki maza ki kai mata."
"Tom."
Kamar ta fasa ihu taji, babu yadda ta iya taja Habubu suka shiga tare.
Hajiya na ganin su ta sake hade rai kamar ta ga kashi, Sultan ne yayi saurin karb'e flask d'in yana murmushi, a cunkushe ta gaida ta itama don ita sam matar bata cikin sabgar ta, sai data sha kamshi sannan ta amsa.
"Muje Abbakar."
"Sai kace ana korar ku?"
Sultan ya fad'a yana juye alalar a plate da ya dauko, murmushi tayi kawai ba tare da tayi magana ba tayi hanyar fita, da k'yar Hajiya Mama ta daga baki tace su ce ta gode. Bata amsa
27, January 2025
Rukayya
Good