Showing 1 words to 3000 words out of 103469 words
[3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽🦳
Story& Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*
Marubuciyar⤵️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES (Daukar fansa) paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE)
Now
*_GALADIMA FAMILY_*
Page 01
Tafe take cike da natsuwa kamewa,long Hijjab ne ajikinta sky blue Wanda ake cema jalbab fuskarta sanye da madaidaicin glashi wanda yasake fito da ainahin kalan fatanta sanye take da facemask sky blue tayi matuqar kyau ,kafanta sanye da halfcover golden colour,jakane rataye a kafadarta golden.
Duk dacewa bazata gaza shekaru sha takwas ba sai dai natsuwarta nasa amata kallon tafiye haka.
Taqaraso dai² kwanar layinsu,lokaci daya taji wani irin qunci da takaici ya lullubeta badon komai ba sai don masu zaman kashe wandon layin nasu(sunan da tasanya musu kenan),sake tamke kyakkyawar fuskanta tayi duk dakuwa facemask din da ke lullube da fuskarta,a hankali yasake qarfafa saurin tafiyan nata don burinta baiwuce ace kauce inda masu zaman kashe wandon suke ba.
"Zuhra sannu da dawowa,fatan kindawo lafiya?kalmar da tatsinkayo daga cikin kunnenta kenan.
Da hanzari tajuyo cike da mutumtawa tadubi inda maganar tafito tare da dan rissinawa tace"barka da gida baba me icce inayini?tayi maganar tare da fadada murmushinta.
Amsawa yayi cike da mutumtawa tare da sanya mata albarka,sosai taji dadin albarkan da yake sanya mata.
Walwala kwance akan fuskanta taqariso bakin gate din gidan nasu,madaidaici mai matuqar kyau da tsaruwa,hannu takai da niyyar knocking gate din,ahankali taga anbude taciki.
Koda tadago ido four eye's sukayi dashi,sosai kirjinta yayi saurin bugawa wanda yasa da hanzari ta sunkuyar da kanta qasa,shiko ta bangarensa kallo daya yamata sannan yadauke kai,rabata yayi yawuce ta gefenta.
Bayanshi driver dinsu ne janye da trolly bag yanufi wata mota dake fake a kofar gidan nasu,kafin zuhra tajuyo taji hayaniyar yaran gidansu nafitowa,maimoon ce tafito da gudu cike da yarinta da rigima tace"pls yah Sauban katafi dani mana inaso naje masarautar su bodejo.
"A'ah ya Sauban kada kaje da ita dani zakaje saboda nayi missing din bodejo kuma bantaba zuwa masarautar ba,Amma maimoon ita taje.
Wani dan murmushi wanda suke kira da ya Sauban din yaqaqalo tare da dafa kan ateek yaron dan shekaru goma cike sanyayyar muryan shi mecike da taushi yace"kada kadamu my aboki insha Allah bazan dadeba zandawo I know lokacin kunsamu hutu a school so insha Allah idan nadawo zan tafi daku,Ok?
Cike da murna yaran suka hau tsallen murna,zuhra kuwa gabadaya tamkar andasata a tsaye ita batayi gababa kuma batayi baya ba,a hankali tasauke wata sihirtaccen ajiyar zuciya tashiga cikin gidan,direct apartment din mommy tanufa,bude kofan tayi tana sallama cikin siririyar muryanta,wanda idan mutum beyi dagaske ba bazaiji abinda tafada ba,mommy kuwa da tataso da alamu fita zatayi hannunta riqe da wani hadadden ledabag tace"My zuhra welcome!
Murmushi zuhra tayi cike da gajiya tace"mommy!tayi maganar tare da langabar dakai tace"nagaji mommy gaskiya nikam nagaji da zuwa jamb class dinnan.
Wucewa mommy tayi tare da cewa"kedai kije ki watsa ruwa kici abinci nasan meke damunki duk baiwuce gajiya ba so nasan dakin watsa ruwa zakiji dai² tayi maganar tana fita daga farlon.
Ajiyan zuciya zuhra tasake saukewa akaro na biyu tanufi stairs tahaye,shiga dakin mommy tayi tare da cire hijjab dinta,wow Masha Allah tsarki yatabbata ga ubangijin daya halitta wannan halittan,Ashe zuhra kyanta ba'a fuska bane kadai harta da halintan sura Allah yahore mata,ahankali tacire kayan jikinta yarage daga ita sai undies farare tass.
Addu'an shiga toilet tayi sannan tasakai cikin hadadden bathroom din wanda yatsaru kota ko'ina.
Bata bata lokaci ba tafito daga toilet din,agurguje tasanya English wears na riga da wando purple wanda suka sake daukan suran nata,kobi takan lotion batayi ba.Hulan kayan tasaka a gyararren gashin kanta,tazura slippers,zare handbag dinta tayi taciro wayarta qirar iPhone 13 pro max tafito tare da sakkowa daga kan benen,kallo daya tayima dinning din tahango warmers dinda ke Kai anjejjera abinci.
Fita tayi daga farlon tanufi dayan apartment din dake hannun dama,cike da qwarin gwiwa ta Isa farlon sai dai wacce tahango zaune kan one sitter din dake farlon yasa jikinta tsananin yin sanyi,cikin sanyayyar muryanta tayi sallama,ahankali taqarisa shiga tamkar wacce kwai yafashewa a ciki ta isa inda babban mace take zaune wacce aqalla zatayi shekaru hamsin da duriya, fuskarta sanye da medical glass ta'aza kafa daya kan daya.
Gefe guda laptop ne akan cinyarta take sarrafashi,cike da fargaba zuhra ta isa inda take tare da rissinawa tace"Ummi sannu da gida! batare da tadago daga abinda take a ta amsa da "yawwa sannu dawowa.
Cikin sanyin murya zuhra tare da tsantsar mamaki tafurta "yawwa.
Miqewa tayi tanufi stairs,kai tsaye dakinta tanufa,ahankali tazauna akan tsadadden gadonta tare da sauke wata qarfaffan ajiyar zuciya a fili tace"Ummi yau tayi abin mamaki,yau ta amsa gaisuwata batare da kyara ko shakku ba,amma meyasa?kafin tabawa kanta ansa anturo kofan bedroom din nata.
Nihal ce da Laila,murmushi tasaki kamar yanda suma suka saki,nihal tace"kai zuhra yau gaskiya kundade a jamb class dinnan meyafaru ne? Laila tace"tun sanda ya sauban ya dawo damu muke tambayarki akace ai kinshiga jamb class,wai kinanan akan bakanki na zuwa Danfodio din?kizo muyi joining gabadaya a ABU mana.
Zuhra tace"hmmm Laila kenan bazaku gane ba nisam banason harkan takura,kunsan ya Aseef a ABU yake lecturing wallahi takurama rayuwa zaiyi muddin nashiga ABU kunsan halinsa fa tamkar bunsuru yake shiyasa nafison Danfodio akan ABU bawai don wani abuba sannan duk abinda yake aikatawa Ummi bata gani,kunsanta akan ya Aseef zata iya batama kowa rai so shiyasa nahaqura da ABU so Kuma kuyi a hankali dashi.
Da mamaki suke dubanta Nihal tace"wai zuhra menene lefin ya Aseef don yace yana sonki dahar kike kiransa da bunsuru?don kawai yace yana sonki?to wallahi kikiyaye bakinki da furta wannan munanan kalmomin akansa don da zarar Ummi taji kema kinsan sauran.
Laila tace"taya Ummi zataji inba wani yafada mataba gaskiya kila yanada wani boyayyen hali wanda zuhra ce kawai tasani.
Dasauri zuhra tadago da daradaran idanuwanta tace"nibansan wani boyayyen hali dayake daba just bana ra'ayinshi ne kawai.
Tabe baki nihal tayi tace"ke dama matsalarki kenan miskilanci.
Murmushin iya labba zuhra tayi batare da tayi magana ba ta miqe tare da nufan bathroom.
*-WASHEGARI-*
Saukowa takeyi daga saman stairs inda tacidda gabadaya 'yan gidan zaune akan dinning sunan breakfast,a hankali tadubi kujeran da Abbie yake zama amma bashi hakan yasa sam bataji dadi ba,jikinta yaqara sanyi,mommy ce tace"a'ah zuhra qaraso mana da sauri kiyi breakfast don kinsan shagon saloon din hjy asiya akwai layi barinma yau Wednesday amareda dama zasuje gyaran kai.
Qarasawa zuhra tayi tare dajan ajiyan zuciya,kujerar da take zama taja ta zauna a hankali cikin muryanta wanda batafiye son magana ba tace"Barka gida Ummie Ina kwana?batare da Ummie tadubeta ba tace"barka dai a takaice.
Duban mommy da ya taufeeq daya Aseef tayi tace"gud morning mommy gud morning yaya's.
Murmushi ya taufeeq yayi yace"morning sweet sister,shima Aseef murmushin yayi yace"morning sis, idanunta nakan ya taufeeq tana murmushi har tabude mouth daniyar sake magana Ummie tayi gyaran murya, duban inda take zuhra tayi a rashin sa'a kuwa sukayi four eye's da zuhra,wani rikitaccen kallo ta aika mata dashi wanda yasata saurin dukar da kanta,a hankali ta dauki spoon da plate ta aje agabanta tare da bude warmer din wanda chips ke ciki,kadan tadiba tazuba a ciki.
Laila tace"shikenan abinda zakici?batare da tayi magana ba tadaga ma Laila kai alamun eh.
Nihal kuwa kyabe baki tayi don Allah yasani tana tsananin takaicin wannan miskilancin na zuhra.
A hankali tacigaba da cin abincinta aqasan zuciyarta kuwa tarasa dalilin da yasa Ummie tatsaneta tun tasowarta,inda sabo yaci ace tasaba sai dai sam hakan taqi yuwuwa,ita da zasubi ta nata dasun maidata maidugri wajen bodejo don tafi samun natsuwa da kulawa,maganar mommy ce takatse mata tunani.
"Zuhra kiyi kigama ci mana yanzu fa kusan 11:28 yakamata ace kinje har kindawo.
Cikin sanyin muryanta tace"tohm mommy ai yanzu zan gama,cikin natsuwa tagama cin abincin tare da daukan tisue tagoge bakinta, miqewa tayi tare da rataya jakanta tace"Ummie,mommy natafi,sister's sai nadawo.
Laila tace"Bari nazo narakaki sis,murmushi zuhra tayi najin dadi tace"yawwa aiko naji dadi, duban ya taufeeq Laila tayi tace"Yaya pls ko zaka saukemu al shagon ne?kafin yayi mgn mommy tace"a'ah kuda kukeda shiririta?taufeeq sauri yake zashi company don yakusa ma late sai dai Aseef yakaiku.
Wani irin dadi Aseef yaji a ransa,sai dai kafin wani yayi magana taufeeq yace"No no no no mommy bari na'ajesu sharp ² saina wuce.
Fuska kwance da fari'a mommy tace"toh shikenan taufeeq ka ajesu,duban nihal yayi yace"keba zakiyi rakiyar ba nihal?
Murmushi tayi tace"a'ah Yaya bazani ba,dariya Laila tasaki cike da sharri tace"ae Yaya nihal tana takaicin zuwa saloon taga yanda ake wankema masu gashi kai Amma ita kai kamar na jariri dan wata hudu😃
Gabadaya farlon dariya akasa harda Ummie idan kacire Nihal da tataso aguje tabiyo Laila tana zazzage mata kwandon masifa,da gudu Laila tafita tana dariya, Nihal dinma baya tarufa mata,mommy tace"Kai Laila Laila akwai sharri.
Fita ya taufeeq yayi yana dariya, Ummie ma miqewa tayi tanufi main farlo.
Daqyar ya taufeeq yadawo da Nihal ciki sannan suka tafi,a mota kuwa banda dariya babu abinda zuhra keyi,sosai hankalin ya taufeeq dana Laila yakoma kan zuhra don rabonda tayi irin wannan nishadin tun ana saura sati daya Abbie yatafi Indonesia,sai gashi yau tayi,hakan baqaramin dadi ya taufeeq yajiba dagashi har Laila,a haka suka karisa shagon saloon din,saukesu yayi sannan yajuya yatafi,sukuma suka shiga cikin shagon.
WAI WACECE ZUHRA?MENENE MATSAYINTA A CIKIN GIDAN?AKWAI TURKA-TURKA DA HAUTSIMA ANAN GABA KUDAI KUBINI MUJE
Xahratty Ce🥰
Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️
[3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): https://chat.whatsapp.com/LNYjzpjYlHH8OHTK0bdHGw
👨🏽🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨??🦳
Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*
Marubuciyar⤵️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now
*_GALADIMA FAMILY_*
Page 02
A can kuwa Zaune suke gabadaya a farlon Galadima Daddy,Abbiey,Abba,baba hasheem, Galadima ne zaune a lallausan kujeran sa mekama da gado na irin wanda ake kishingidar nan akai cikin muryanshi me kama dana babban mutum me cike da dattako yafara magana tare da gyaran muryan"Taleeb a matsayinka na babba acikin family dinnan idan kacire ni da bodejo da Kuma guggon ku Laure to kaine babba,magana guda ne ta taramu anan kowa yasan magana ce baiwuce na yaran nan ba tundaga kan Sauban har zuwa kansu mashahuda,wai boko hauka ne?meyasa kuke nema kukoma koyi da yaren yahudawa ne?yaranku sun girma kuma ko wannensu idan aka masa aure zama zeyi to akan mene?ga Sauban nan dashi da taufeeq sun cika ko wannensu ba master's ne dashi ba?
Galadima yayi maganar yana dubansu cike da nazari, Daddy yace"hakane Alhaji munaso ne dama munemi yaran idan anzo saka ranar su mashahuda kan maganar saka nasu ranar idan yaso komai yazo yanda kowa keso sai a hada bikin nasu rana daya ayi ko sadeeq?yayi maganar yana duban Abbie.
Abbie yace"Ea yaya nima inaso nakira Ummien yaran ne nace sutaho gabadaya dama abinda yahanasu zuwa maganar jamb class dinda zuhura keyi ne so zankirasu zutaho nan din kawai.Galadima yace "gaskiya kuwa,anjima idan an idar da sallar la'asar inaso muje daku gabadaya mu duba jikin Laure ance tanata zazzabi tana kwance.
Gabadaya suka amsa da insha Allah sannan suka miqe suka nufi masallaci gabadayansu harda Galadima.
Zaune yake a dakinsa yana duba wani saqo a laptop dinsa da aka turo masa ta Email dinsa,wani company a qasar maleyshia taturo dashi kan suna son daukanshi aiki idan babu damuwa suna nemanshi Nanda 4days kan yazo za'ayi musu interview a cikin su goma Sha shida 'yan nan Nigeria.
Sosai yaji dadin hakan aransa wanda inba kalura dakyau ba bazaka fahimci hakan ba, duk da fuskanshi takasance me tsananin kyau tamkar jinin larabawa,dama shidin jinin shuwaarab ne,miqewa yayi a fili yafurta"ALHAMDULILLAH,Masha Allahu laquwwatu illa billah,jallabiya wata blue black yadakko ta yasaka wacce tayi tsananin yimishi kyau yafita,kaitsaye masallacin dake layinsu ya nufa.
Koda aka idar da sallah tare suka fito dasu Daddy,wajen Abbie yanufa fuskanshi dauke da murmushi duk cikansu da mamaki suke dubansa baba hasheem yace"A'ah Sauban yaushe Kuma kadawo garin?Abba yace"tambayeshi dai kam.Dariya yayi tare da dan rissiniwa yafara gaggaishesu, cike dajin dadi gabadayansu suke amsawa.
Murmushi yayi wanda yasa dimple din gefen kumatunsa lobawa yace"Ai Ina ajesu kawai najuyo don banma shigo gida ba sai wajejen asubah.
Galadima yace"kunji koh?kunji irin gangancin nasa Koh?inbanda kasada mezesa kadawo a wannan lokacin kamar Wanda ake kora? Abbie yace"Sadauki ba na hanaka tafiyar dare ba?ai wannan ganganci ne kadena sam baida amfani.
Rissinawa yayi kadan yace"insha Allah za'a kiyaye.
Shiga cikin gidan sukayi gabadaya inda su suka nufi farlon Galadima,domin muddin Abbie da Daddy na garin sun shigo to a farlon Galadima akecin abinci,shiko Sauban kaitsaye apertment dinsu yanufa.
Da sallama yashiga cikin farlon hayaniya yaran dake farlon keyi Amma jin sallamar shi yasa farlon yakoma shiru inda banda sautin amsa sallamar da yayi bakajin komai, 'yan matan kuwa dake zaune ko wacce wayarta tasaqe suka fara boyewa.
"Barka da shigowa Bro Sauban!!!abinda 'yan matan suka fara fada kenan,suko sauran yaran oyoyo suka nufoshi suna mai,sai sai suna qarisowa gabansa sukaja birki suna dariya don sunsan basu isa suyi hugging nashi ba donbshi mutum ne wanda befiye son daqunar yara ba.
Murmushi yayi iya lebe tare da cewa"yawwa sannunku,ina Ammi take?nuna masa wani dogon corridor sukayi,yamike kenan da niyyar zuwa sai gata tafito.
Da murmushi yatare ta yace"sweetheart,dan hugging nata yayi,hararar wasa ta aika masa dashi wacce da alama babbace don zatayo sa'a da Ummie.
Murmushi yayi yace"Me Kuma nayi sweetheart?irin wannan harara haka?Ammi tace"Hmmm zaka sani Ina ganin sanda kashigo gidan nan,wallahi Sauban bakajin tsoro zaka sani ne,muje dinning kaci abinci.
Dariya yayi tare da dan kamo shoulder dinta suka nufi hanyar kitchen suka shiga,babu wani jimawa ya Sauban ya fito hannunshi rike da plate biyu ya aje akan dinning yajuya baijima ba yafito riqe da ruwan gora cup,zama yayi kan dinning din yadubi inda 'yan matan suke yace"Mashahuda kije kitchen ki amsa abincin su Daddy kikai farlon Galadima,kekuma muneefa kizo kidauki na boddejo,da to suka amsa don kafin ma ya ida maganar suk sun miqe.
Sallama akayi tare da shigowa,Kareem ne yashigo abokin ya Sauban da sauri yaran suka nufeshi suna Oyoyo bro Kareem,bude musu hannu yayi duka su ukun suka fada jikinshi,itakuwa inteey kaitsaye inda ya Sauban yake tanufo,ta wutsiyar ido yadubeta don yasan yarinyar mayyanshi ce duk abinda zai mata tananan kwafufe dashi,kusa dashi tazo ta tsaya tace"ouncle mommy na tace zaka siyomin hollandia idan kadawo tace koka manta natuna maka idan batazo daukana ba kai zaka maidani gida.
Dago manyan idanuwansa yayi yana duban yarinyar don yana tsananin mamakin wayon yarinyar don inteey bata wuce 4 yrs ba,murmushi yayi mata yace"bby inteey kenan ainasan mekike nufi nikadai nake gane dama wannan yaren naki,dakko ta yayi yadorata a cinyarsa yafara feeding dinta,idan yayi 1 spoon itama yabata.Sarai yagane abincin zataci shiyasa ta bullo masa ta wannan surutun,Hakeem ne yakariso inda yake yana murmushi donshi mutum ne wanda sam murmushi baya gushewa a fuskarsa,yaron abokin Daddy ne sosai suke zumunci shiyasa yaransu ma Sauban da Hakeem suka dinki.
Mikomai hannu Sauban yayi alamun musabaha yace"mutumin Ashe kadawo?shine ko kakirani?Koda yake nayifa lefi ne shiyasa sorry,yaqarisa maganar yana kunshe dariya.
A daidai nan Ammi dasu muneefa suka fito kowacce hannunta riqe da basket sai dai na mashahuda sunfi yawa,kowacce doguwar riga ce ajikinta sai veil,gaishe da Kareem sukayi suka fice,Ammi kuwa dinning din tanufo ta zauna tana fadada murmushinta tace"a'ah Kareem kashigo gidan ne?
"Aikuwa Ammi inayini munsameku lafiya?
"Lafiya lou ya hajiya sakinan dasu bahijja?
Lafiya Lou Ammi,dubanshi Ammi tayi tace"tashi kaje kitchen kasa abincin mana don yau mutumin ka akayi.
Murmushi Kareem yayi yace"Ammi gurasa kikayi?Amma 'yan matanki suka miki koh? Saboda naga kinaji da kanki don ma Allah yasa Ammin namu macece jaruma,yaqarisa maganar cike da zolaya.
Harara Sauban ya aika masa dashi donshi yana mamakin surutun Hakeem haka ko gajiya bayayi,shiga kitchen din Hakeem yayi ya hada gurasar sa yafito abinshi.
Inteesar ta sauka jikin ya Sauban takoma wajen Kareem tunda sun cinye nasu don shi Kareem ne wanda baifiye cin abinci ba.
Harara yabita dashi tana dariya ta falfala da gudu tabar farlon don sauran yaran dama sunfice sun nufi sashen Mom.
A bangaren su mashahuda kuwa suna mikawa su Daddy abincin suka nufi sashen Mom bayan sun gama tsokanar Galadima,don bodejo batanan tana wajen guggo Laure don haka suna bude bedroom dinta suka ajiye mata.
Shiga apartment din mom sukayi,mom na kitchen don haka kaitsaye kitchen din suka nufa, Mom sannu da gida,cike da fari'ah tajuyo tace"yawwa sannunku daga ina haka?
Muneefa tace"abincin su Daddy muka kaimusu farlon Galadima dana Galadima.
Mashahuda kuwa batasan sanda tayi subul da baka ba tace"kai gaskiya matar ya Sauban wallahi ta shiga uku dashi,da yasani ma aikin soja kawai yashiga,tab irin wannan mazurai haka?
Dariya mom da muneefa tasaka tace"ai shiyasa bansan sanda nasaqe wayata ba gudun kada ayi sezing dinta.
Mashahuda tace"Kuma wallahi kar yagammu kawai dai ya share ni yayi kakar be ganiba.
Muneefa ta diddilo Ido cike da tsoro tace"wai dagaske?mashahuda tace"Allah gashi ko amso gurasar mu bamuyi ba,ai wallahi bazan koma ba sai yafita.
"Nima bazani ba don nasan halinki sai ki'iya cewa _don Allah muneefa jeki amso Mana abincin_,babu inda zani ahto kadama kiqarisa.
Dariya Mom tasaka tace"lallai ne big broo yacika big broo ai haka akeso.
Su Daddy Koda suka gama cin abinci basu wani bata lokaci ba suka shiga motocinsu,kaitsaye gidan guggo Laure suka shiga,itama tanada dan nata rufin asirin sai dai ko kwatan kafar na Galadima da iyalensa baikai ba,baba hasheem ne ke driving nasu,gefenshi Abba ne,sai abaya Abbie, Daddy, Galadima.
Fitowa sukayi sannan suka budema Galadima shima yafito tare da hadadden sandarsa mai matuqar kyau da tsada yafara dogarawa yana gaba suna biye dashi,maqota sun leqo sai kallansu akeyi.
Wani yaro ne da alamu jikan guggo Lauren ne yashiga da gudu yana cewa tayi baqi,duka da cewa flat dinta daban sai na yaranta su biyu maza kowa da nashi flat din da Alhaji sani da