Showing 51001 words to 54000 words out of 92582 words

Chapter 18 - MATAR MUKHTAR COMPLT

SAKINA   

16 Aug 2024

7146

inda zai gayawa Jamila zai kara aure, amma ya san dole ya gaya mata don ba zai fasa ba. A yanzu ma yana jin kamar idan an ce ya zabi daya tsakanin Jamila da Fatima to lallai Fatiman zia zaba sai dai duk abinda zai fari ya faru.

KARSHEN BABI NA ASHIRIN DA BIYU.

MATAR MUKHTAR

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA ASHIRIN DA UKU

23
Tun ana sallacewa Sabir ya fara sanarwa duk wani wanda ya san gidansu akwai mata cewa ana kitso a gidansu, har matan ajinsu sai da ya gayawa duka da dai sun yi candy amma yawancinsu gidajensu na nan kusa da unguwar.
Babu wanda ya zo kitso ko sau daya, ita kuma da yake bata sa a rantaba babu abinda ya dameta. Ta riga dai ta fara zuwa islamiyya tunda ana sallacewa Yaya Habibu ya kaita. Sosai take jin dadin zuwa islamiyyar nan domin ko babu komai yana debe mata kewa da kuma rage damuwa, gashi za a hadu da mata idan babu malami a aji ayi ta hira; duk da dai ita din bata fiya shiga hirarrakin ba amma dai ana yi tana ji.

Ranar Juma'a da safe suke zuwa sai kuma Asabar da Lahadi da yamma, don haka har Allah Allah take Juma'a ta zagayo.

Yau Juma'ah tana dawowa daga islamiyya suka hadu da Sabir a kofar gida ya dawo daga makaranta; inda Yaya Habibu ya saka shi ya koyi computer tunda yanzu yana zaman jiran admission; da fara'arsa ya karaso suka jera yana ta dariya ya dubeta yace

'Ya Safiyya albishirinki!'

Itama murmushin take tace

'Goro.'

'Yau dai na sami kwastoman kitso, in sha Allah da yamma zata zo.'

'Ummm! Kace yau zamuyi sharholiya da kudin kitso.'

'Kwarai kuwa don ni naira dari biyar nace mata kudin kitso.'

Ta dube shi tana zare ido

'Kai Sabir! Allah ya yaye maka son kudi, ina ma laifin dari biyu.'

'Haka za a dinga biya gaskiya, ba wani ragi. Ai first class kitso ne.'

Har sun kusa shiga tsakar gidan ya janyota baya yana magana kasa-kasa

'Don Allah dai kada ki bawa Umma kudin, idan an baki ki bani na samo canji sai ki bata dari biyu ki dauki dari uku ki boye. Ko ma dai kawai ki bani na ajiye miki.'

Tayi 'yar dariya tare da yin dage ta doki kansa

'Allah ya shiryeka jai dai.'

Suka shiga gidan suna ta yiwa juna dariya.

Sai bayan sallar la'asar Sabir ya shigo da 'yar ajin tasu tare da kannenta su biyu. Ya raka su suka gaida Umma sannan ya kirawo Safiyya. Har tana jin tsoron kada Umma tace bazata yi kitson ba sai ta dafa musu abincin dare sai kuma Umman tace su je rumfar bakin gate suyi kitsonsu. Don haka nan da nan suka fito suka fara kitso.

Daf da magriba suka gama kitson, Babbar ta mike ta zaro kudi naira dubu daya da dari biyar ta mikawa Yaya Safiyya, sukayi mata sallama suka fice. Kafin ta nade tabarmar Sabir ya shigo da yake dama yana waje, da hanzari ya karasa ya karbe kudin daga hannunta yana murmushi. Ya wari naira dari biyar ya bata yana fadin

'Rike wannan kina shiga ki cewa Umma ga kudin kitson, wannan dubun kuma zan shige na saka miki a jakarki idan sun kai uku sai mu bude account.'

Ta karba da bakinta a bude, kafin tace wani abu ya karbi tabarmar hannunta ya shige gidan ya barta a tsaye tana masa dariya. Bayan ta shigo ta sami Umma tana kwashe ruwa, ta tsuguna daga gefe tace

'Sannu da aiki Umma, bari na wanko hannu nazo na karasa miki. Kinga kudin kitson.'

Ta karasa tana mika mata dari biyar. Umma ta dan yi murmushi tace

'Kada ki zo min kichin ba so nake gashi ya shiga miyar ba.'

Ta kalli dari biyar din tana murmushi ta cigaba

'Babu laifi ma suna biyan kudin kitson, Allah ya sa albarka kuma ya sa an fara a sa'a.'

Har cikin zuciyarta taji dadin addu'arnan tana fara'a tace

'Amin Umma.'

Ta mike ta shige dakin. Tana shiga ta saka kudin a jakarta ta wanko hannu tare da alwala. Bayan ta idar da sallar Magriba tana kan dadduma tana addu'a da yiwa Allah godiya. Bata taba tunanin kudin kitso zasu sakata farin ciki haka ba, amma dai yanzu wasai take jin zuciyarta musamman da ta san Umma bata san da dubu dayan ba.

Ta dade rabon da ta rike kudi haka nata na kanta wanda take da tabbacin Umma ba zata kwace ba. Lallai ta yarda yanzu kam da kanta zata dinga gayawa mutane tana kitso.
Tun daga wannan kitson kuma bata sake samun masu son kitso ba har aka yi sati biyu. Ranar Asabar suna aji a islamiyya Hajiya Saliha wadda take zaune a teburin da yake gaban na su Safiyya ita da kwayenta suna hira take ta mita; matar da take yiwa yaranta kitso tayi tafiya don haka gashi yau asabar basu samu an yi musu ba, tana tunanin dai ta kaisu saloon. Sai da kyar Safiyya ta bude baki tace

'Anti Saliha ina yin kitso fa, zan iya zuwa na yi musu in kina so.'

Ta juyo da murmushinta

'Allah Safiyya? Shine baki taba gaya min ba? To yaushe zaki zo kiyi mana? Wallahi duk yaran babu mai kitso a ka har ni ma.'

'Ko gobe ma sai na zo idan dai kun shirya.'

'To Allah ya kai mu, nan wajen masallacin Juma'ah gidan yake. Kina zuwa masallaci idan kika je karshen katangar ki tambayi gidan su Abbale za a nuna miki gidan. Don Allah ki zo da dan wuri.'

Aka cigaba da karatu. Bayan Malam ya fita daga aji Safiyyan tana jin Maman Afaf wadda take kusa da Anti Saliha tana radawa Anti Salihan magana
"Sai fa kin yi a hankali yarinyar nan bazawara ce, kin san zawarawan nan yanzu sai ta fara zawarce miki miji."

Tana jin Salihan ta bata amsa

"Ke kin fiye kishin banza wallahi, to menene ba shikenan ba."

Abun ya tsayawa Safiyya a rai amma ta danne, tunda Allah ya sani ita ba wannan ne zai kaita gidan ba. Irin wadannan maganganun zuwa yanzu ta saba jinsu, don haka ma abun ya daina bata haushi.

Haka taje ta yi musu kitson nan su shida; yaran Anti Saliha su hudu, yarinyar makociyarta daya da kuma ita Anti Salihar. Da ta gama anti Salihan ta kirgo kudi naira dubu uku ta bata tana ta godiya.
Tana shiga gida ta boye dubu uku ta nunawa Umma dubu daya, washegari kuwa suka fita ita da Sabir ta bude account a banki don da kanta tace sana'ar kitso ma yanzu ta fara.
_

Kawo yanzu Fatima ta sakawa Mukhtar ka'ida a kan lallai duk Juma'a a Zariya zai wuni, haka zai je gidansu su zauna a falo su sha hira sannan ya taho. Shi da kansa yake tambayarta ta fada masa ranar da za a kawo kudin aure da sa rana amma ta ki, sai dai kawai tace masa akwai shirin da takeyi da kanta zata gaya masa.

A yanzu bata san ko tana son Mukhtar ko bata son sa ba, shi yasa ma ta kasa amincewa ya aiko. Kullum sai tsara Mommy take tana gaya mata zai aiko, ita kuwa Mommy bata so ta janyo abinda zai rusa maganar auren don haka ta kyale tunda dai nan cikin gidan suke zance kuma Fatiman tace zai turo.

Don haka duk Juma'ar duniya sai ya je Zariya wajen Fatima, ragowar ranakun kuma su wuni suna waya. Ga kashe kudi don duk abinda tace masa tana so to idan zai tafi Juma'a sai ya Kai mata.
......

Tana sauke abincin safe ta mayar da na rana kamar yanda yanzu take yi tunda cikinta ya girma, idan ta zauna bata yi ba tashin yana mata wahala gashi ta rasa mai aiki mai kwana dole sai mai zuwa da dawowa aka samo mata a unguwar.

Ta zuba na Nurain na makaranta karfe takwas saura Abbanshi ya tafi kaishi makaranta. Bayan ya dawo ya zauna yaci abincin safe wanda ta zuba sannan ya wuce daki.

Tana sauke abincin ranan ta juye musu a flask sannan ta fito falon ta kwanta a kan doguwar kujera yayinda Nana take zaune tana kallon cartoon.

A shirye tsaf ya fito ya samesu, ya dan yi gyaran murya

'Ni zan wuce, ba lallai na dawo da wuri ba don zan je Zariya.'

Ta yunkura ta tashi zaune ta gyara zama da bakinta wanda yake cike da yawun tace

'Allah ya kiyaye hanya. Wai ita Zariyan nan yanzu duk Juma'a sai an je ta ne kamar attendance?'

Ya dan yi murmushi

'Ai na gaya miki wani aikin kwangila na samu a Zariyan shi yasa ranar Juma'a da aiki bashi da yawa sai na tafi na duba wancan. Kada ki damu kwanan nan zan gama ai in sha Allah.'

Cikin halin ki in kula tace

'Allah ya bada sa'a.'

Yayi mata sallama Nana tayi masa a dawo lafiya ya fice. Yana fita ta sa Nana a daki suka rufe gidan sai bacci; tunda mai aikinta sai sha biyu da rabi take dauko Nurain ta taho da shi sannan ta zo ta fara aikin gidan.
Haka ta kwanta tana ta tunane tunane; wannan zaryar da Mukhtar yake yi Zariya ta isheta, kuma tabbasa sai ta lalubo bakin zaren. Ta riga ta gane yanda yake bude wayarsa don yanzu kusan kullum sai ta bude ta lalube wayar. Bata ga komai ba amma akwai lambobin wayar da ta kwafa domin tana zarginsu, a ciki harda wata lamba da yake kira kullum da safe ranar Juma'a kafin ya fita. Ko yanzun ma kuma akwai kaninta da ta saka ya binciko mata me Mukhtar din yake yi a Zariya duk Juma'a.

Ta kusa haihuwa yanzu domin saura abinda bai fi wata daya ba, don haka bata son ta ja fitna don bata cikin yanayin da zata iya dauka don haka ta bari sai ta haihu don tabbasa tana zargin wata karuwar yayi a Zariya yake raina mata hankali. Ko a Kanon ma Kuma akwai lambar da ta dauka a wayarsa wadda take zargin ta wata karuwarce. Jiran lokaci kawai take da shi da karuwan duk sai ta tayar musu da hankali.

KARSHEN BABI NA ASHIRIN DA UKU
MATAR MUKHTAR

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA ASHIRIN DA HUDU

24
Tunda watan haihuwarta ya tsaya take ta gaya masa idan ta haihu event center take so ya kama mata don yin taron suna, ta riga tayi masa lissafin abubuwan da take bukata kama daga abinci, DJ, kudin liki da sauransu. Baya son wannan tsarin nata domin ita Safiyya a gida take yin suna kuma duk abinda ya bayar karba take bata neman kari. Gashi kuma baya son harkar DJ, don haka ma da taga ya dameta da mita tace to taji yayi sauran ita ta biya DJ da kanta.

Kusan kullum sai tayi masa wannan lissafin kuma duk ya amsa zai yi, DJ ne kawai ba zai dauko ba kuma wannan tace zata dauko sai kuma kudin kayanta na fitar suna da ta nemi dubu saba'in ya bata dubu talatin yace ba zai kara ba; haka ta hakura.

Ranar Talata har ya fita aiki ta kirawo shi ta sanar dashi ta fara nakuda, don haka nan da nan ya dawo suka wuce asibiti. Kafin azahar ta haifi yarinyarta mace, da yake ya riga ya sanar musu baya son wankan gida nan da nan yayar mahaifinta wadda suke kira Inna ta iso asibitin inda suka wuce gidan tare.

Ranar da ta haihu da daddare bayan tayi wanka ta shirya ta sameshi a falon sama yana cin abincin dare, yayinda Nana da Nurain suke bacci a gefensa.

Tunda ta shiga yake ta faman kallonta yana murmushi, tana zama yace

'Mai jego, ba kiyi bacci ba? Ai na zata Inna ta hanaki zuwa mu gaisa.'

Tayi dariya

'Wanka nake lokacin da ka shigo fa.'

'To ya jikin dai, kalau kuke duk ko?'

'Alhamdulillah, wanka Inna takewa Baby sai ta gama zan kawo maka ita.'

Sukayi shiru na dan lokaci suna kallon TV, jim kadan tace

'Maganar suna fa, na sami event center har munyi magana da su. 120k ne kudin zuwa ranar Saturday sai a tura musu duk da yanzun ma suna so a tura deposit.'

Ya dan tsuke fuska

'Wai yanzu event center din ne 120k, haba ku ko tausayin kudi ba kwa ji?'

Ta karkata kai tana kallonsa

'To ya za ayi, ai kaga dai mun gama magana don yanzu ma nayi booking wajen.'

Ya jijjiga kai yayi shiru, ita ma shiru din tayi domin in dai a kan taron suna ne zata iya yin komai don babu wanda ya isa ya hanata. Jimawa kadan yace

'Allah ya sauwake, zuwa Juma'a ko Asabar sai na tura miki kudin.'

Nan da nan ta saki murmushi ta matsa ta dan kwanta a jikinsa

'Yauwa sahibi ko kai fa.'

Yake kawai yayi ya lakace mata hanci, ta tashi ta fice daga falon. Jimawa kadan ta dawo dauke da Baby ta mika masa ya karba yana murmushi. Ya karewa Baby kallo ya dago ya dubeta yana murmushi yace

'Ma Sha Allah, fine girl mai kama da babarta.'

Tayi dariya Sannan tace

'To wanne suna ka saka mata ne?'

Ya zubawa fuskar yarinyar ido yana murmushi, haka kawai zuciyarsa take raya masa ya sa mata Safiyya amma da yake ya san rigimar uwarta sai ya dubeta yace

'Halimatu Sa'adiyya.'

Tayi murmushi tace

'Ma sha Allah, Allah ya raya Halima.'

Suka dan taba hira sannan ta tashi ta dawo dakinta yayinda Inna ta hau saman ta dauko mata su Nurain.
..........

Tun ranar laraba ya fara sayayyar abubuwan da za a bukata na taron suna, ya sayi rago ya kawo nan ya daure haka ma abinci, masu lalacewa ne kawai bai saya ba. Ga wani nama kuma da kaji da ya siyo ya kawo gidan yace a gasawa maijego. Duk wadannan hidimomin a cikin damuwa yake yinsu don tun safe har magriba bai sami Fatima a waya ba, ce masa ake yi wayarta a kashe. Sai yayi kamar ya kirawo Mommy ko yayanta sai kuma ya fasa don da kunya, haka ya wuni ba a hayyacinsa ba saboda yanzu da zarar bai ji muryar Fatima ba sai ya shiga damuwa.

Bayan ya dawo gida da daddare ya gama shirin kwanciya yayi sallama da Jamila ya koma gefen gadonsa ya zauna, wayarsa ya zaro ya kara kiran Fatima a karo na babu iyaka.

Kamar wanda aka tasa daga bacci ya ji wayar tana ringing, kafin wani lokaci aka amsa. Cikin zakuwa ko sallamarta bai amsa ba yace

'Fatima ina kika shiga ne yau duk kin daga min hankali, tun safe na nemeki a waya na rasa.'

Da damuwa a muryarta tace

'Hmm! Honey yau abun haushi ne ya sameni, wayar tawa ce ta fada cikin tafasasshen ruwa ta dauke don ko kunnuwa ma taki. Yanzu ma wayar Baba Habi na aro na saka sim dina kuma sai na rasa lambarka don ban haddace ba.'

Yayi ajiyar zuciya

'Kai! Allah ya kiyaye gaba, amma fa kin daga min hankali Sweetheart.'

Tayi 'yar dariya

'Nima ba da son raina ba Honey.'

Suka dan taba hira tana tambayar masu jego, ba jimawa tace

'Bari na mayarwa da Baba Habi wayarta na zo na kwanta.'

Cikin damuwa yace

'To yanzu ya za ayi kenan na dinga jinki.'

'Hm! Ka san dai bani da kudi ko? Mommy ma kam yanzu ko saurarona ba zata yi ba, sai dai kawai lokacin da na sami aron waya ka jini.'

Ya sake shiga damuwa don ba zai iya jure rashin jin Fatima ba a yanzu. Yace

'Ina ga ba haka za ayi ba, nawane kudin wayar sai na turo miki kawai gobe sai ki saya a nan ko?'

'Ai kuwa da naji dadi Honey, akwai wani dan uwanmu yana sayarwa yanzu zan mishi magana gobe da safe ya kawo min sai na turo maka account din shi ka saka masa kudin.'

'Ok, to hakan yayi.'

Suka yi sallama suka ajiye waya.

Ya gyara filo ya kwanta. Sai a lokacin sannan ya tuna hidimar haihuwa ce a gabansa kuma ko yanzu ma ya kashe kudi da yawa bai san wayar nawa Fatiman zata kawo ba. Ya san dai ko ta nawa ta kawo dole ya siya shi yasa ma yake fatan ta kawo wadda bata haura dubu hamsin ba.

Haka ya kwanta yana ta faman lissafin kudi saboda yanda hidima take kansa , sai dai da yake bacci barawo ne sai da ya sace shi.
..........

Bai dade da shiga office ba Fatima ta kirawo shi a waya, kai daga jin muryarta ka san tana cikin walwala. Bayan sun gaisa tace

'Honey ga wayar fa an kawo min, don itace ma na saka sim dina ciki nake kiranka.'

Ya yi murmushi wanda har saida ta jiyo sautinsa a cikin wayar

'Ah, good. Yanzu dama nake tunaninki ashe ya kawo. To nawa ne kudin?'

Kai tsaye tace

'Dubu dari da talatin.'

Gumi ya karyo masa don bai zata za ta sayi mai tsada haka ba

'Har 130k? Wace iri ce ne wayar?'

Ta fuskanci yanda ya canza don haka itama tayi muryar tausayi

'Umm! iPhone ce. To ko mayar masa za ayi na hakura don gaskiya sai dai na hakura tunda ai ba zan yi ta zama da karamar waya ba ko.'

'No! Ba wata damuwa fa, ki turo account number din ta whatsapp yanzu zan saka masa. Kin san Jamila ta haihu ne gashi next week suna shi yasa babu kudi sosai.'

'Au haka ne fa, ka san na manta da ba zan yi maganar wayar ba ma. Don Allah ka turo min hoton Baby.'

'Ok. Bari na tura masa kudin yanzu idan na tura mayi waya.'

Suka yi sallama ya ajiye waya. Take ya bude Whatsapp wanda yana budewa sakonta ya shigo ta turo da account number. Sunan namiji ne da account din don haka bai kawo wani abu ba, kafin ya gama kwafar account number din wani sakon

08, January 2025
Nafisa

I cant download the book

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login