Showing 30001 words to 33000 words out of 92582 words

Chapter 11 - MATAR MUKHTAR COMPLT

SAKINA   

16 Aug 2024

7145

Umma bandaki sanna ta shirya. A falo ta sami Umma tare da Hamida da Sabir suna zaune a falo, Sabir ya dubeta yace

'Ya Safiyya ina zaki je?'

'Gidan Baban Hotoro.'

'Kai ai kuwa nima na dade ban je gidan ba, ko na zo mu tafi?'

Da fara'arta ta amsa shi

'Eh mana, taso mu je.'

Ta dubi Hamida

'Ko zaki je kema sai mu jira ki ki shirya mu tafi?'

Ta girgiza kai

'A'a, ina da test ranar Monday gara nayi karatu wataran naje.'

Umma ta harareta tace

'Ko baki da test ma daman ba zuwa kike son yi ba, daddawar daka. Ayi mutum shi dai ba zai shiga mutane ba sai kace wata mujiya.'

Sukayi dariya ita kuma Hamida tana ta zumbura baki. Safiyya da Sabir suka yiwa Umma sallama suka kama hanya.
...........

Matan Baban Hotoro biyu da kuma 'yaya goma sha biyu, biyar na uwar gida wadda ake kira Mama bakwai kuma na amarya wadda ake kira Anti. Matsaikaici gidane me bene hawa daya, wajen Mama ne a kasa yayinda wajen Anti yake a sama shi kuma Baba nasa wajen a kasa yake daga gefe.

Wajen karfe sha daya da rabi suka isa gidan, suna shiga suka sauka a wajen Mama. Yaranta duka sunyi aure don haka babu kowa a wajen sai mai aikinta sai Aisha da Zahra jikokinta na wajen Babbar yarinyarta Afiya da suka zo mata hutun karshen mako. Nan suka zauna suka gaisa suka dan taba hira, suna cikin hirar ne Sabir ya jiyo su Aliyu a farfajiyar gidan don haka shima ya tashi ya fita.

Aliyu da Yasir sune kananan yaran Anti kuma sa'anni ne da Sabir sai dai Yasir ya girme masa da shekara daya da rabi. Da yake yaran Anti mutum biyu kawai aka aurar akwai 'yan mata biyu Saliha da Rukayya wadanda suke karatu a jami'a, don haka ba jimawa Safiyya ta dubi Mama tace

'Bari naje sama mu gaisa da su Saliha, kafin na sauko Baban ya fito sai na gaisheshi mu wuce.'

'Au na zata wuni kuka zo mana Safiyya?'

Tayi murmushi

'A'a Mama, ai in sha Allahu da bikin su Saliha kwana ma zanzo nayi tunda an kusa, yau din akwai inda za mu je shi yasa.'

Ta haye sama wajen su Saliha, sun dan jima suna hira duk da su din ba sa'anninta bane tunda ta basu wajen shekaru hudu amma akwai shakuwa ta zumunci tsakaninsu.

Ta mike tayi musu sallama ta sauko don ta gaida Baba su wuce, tana karasowa cikin falon Mama ta tarar da Auwalu yana zuane suna hira da Mama. Auwalu dan wan mahaifinsu ne wanda a nan wajen Maman ya girma, yana da aure da yara hudu kuma suna zama ne a Jigawa saboda a can yake aiki; ya zo hutun karshen mako ne da yake nan ne gidansu ya zo ya gaida Mama da Baba.

Ta dan zauna suka gaisa da shi tana saka baki a hirar tasu, a haka Baba ya fito ya samesu. Ya zauna a kan kujerar zaman mutum uku su kuma suka koma kan kafet suka kwashi gaisuwa. Ya dubi Safiyya yace

'Safiyya, ya gidan ya Umma da kannenki?'

'Lafiya kalau Baba.'

'To ya naki yaran? Kina dan tuntubarsu ko?'

'Eh Baba, an kawo su ma sun yi mana wuni.'

'To ma sha Allahu, in sha Allahu komai zai warware kinji. Ki ci gaba da rayuwarki kina walwala kada ki sa wata damuwa a ranki, Allah yana sane da bawa kuma Allah mai jin kai ne. Allah ya baki mini na gari.'

'Amin.'
Ta amsa da murya kasa-kasa.

Baba ya juya ya dubi Auwalu wanda fuskarsa ta nuna alamun sun sakashi a duhu yace

'Ka san aurenta ya mutu, harma ta gama idda.'

Mamakinsa ya kara yawa

'Subhanallahi, ai ban sani ba. Allah ya sa haka ne ya fi alkhairi.'

Ta amsa da murya kasa-kasa
'Amin.'

Ta yiwa Baba sallama ya mike ya zaro kudi a aljihunsa naira dubu biyu ya mika mata

'Ungo wannan ku hau mota, canjin kya sayi wani abun.'

Ta tsuguna tana godiya kafin ta rufe bakinta Auwalu ya zaro naira dubu biyar yana ta wani murmushi ya mika mata yana

'Ga wannan ma kya kara.'

Ta dan ja baya tace

'Yaya Auwalu ka b...'

Ya harareta ya dubi Baba

'Ka gani ko Baba ni bata kawai nayi amma ba zata karbi nawa ba.'

Baba yayi dariya

'Ai yayanku ne Safiyya, to in bakwa so duk ku bani na sayi goro.'

Ta karba tayi godiya, ta wuce kicin domin tayiwa Mama sallama tana tunanin abinda ya sa Auwalun yake kallonta kamar wani mayunwacin maye; Allah ya sa dai ba cewa zai yi yana sonta ba don bazata aureshi ba, ba don komai ba sai don kawai baya cikin tsarin mazan da take sha'awar aure. Amma shi din ta san mutumin kirki ne kuma yana da dan abun hannunsa.

Bayan ta fito ta sami Sabir a kofar gida da su Aliyu, sai da ya koma ciki yayi sallama da mutanen gidan sannan ya fito suka kama hanya.
Tasi suka hau zuwa court road inda zasu sauka su karasa karkasara gidan Karima kamar yanda tayi mata alkawari. Suna zama a tasi din ta dauko wayarta don kiran Karima, sai ji tayi ance babu kudi; wanda taci bashi ta kirata jiya ma ashe ya kare. Ta kalli Sabir tace

'Da kudi a wayarka na kira Karima, za mu dan tsaya a gidanta idan muka gaisa sai mu wuce.'

Ya zaro wayar ya mika mata, tana saka lamabr ta kira, bugu daya Kariman ta dauka

'Hello, Salamu alaikum.'

'Wa alaikumussalam, Karima Safiyya ce kin ganmu a tasi mun kusa karasowa AKTH din ta wajen ina za mu sauka in zan zo gidan naki.'

A ka dan yi shiru don haka tace

'Hello kawata.'

Shiru dai har yanzu, sai dai kamar tana jin alamar numfashin mutum da 'yan surutan da suke can wajen kamar na TV kadan-kadan. Ta sake cewa

'Hello.'

Har yanzu shiru, ta cire wayar daga kunnenta tana kalla

'Ikon Allah inaga dai bata ji na.'

Ta katse kiran ta sake kira nan take, haka wayar tayi ta ringing ba a dauka ba. Har suka zo Aminu Kano ba a dauka ba don haka tacewa direban tasi tunda BUK zai je ya wuce da su sai su sauka a unguwarsu wato kofar fanfo.

Har suka zo gida tana mamaki don kuwa ta tabbatar kariman taji lokacin da tace itace Safiyya, amma sai ta basar da yake ta san halin network. Suna sauka daga tasi bayan ta sallami direba ta zaro kudi a jakarta ta cewa Sabir

'Ka ga ma har dubu biyu Baba ya bamu mu hau mota.'

'Ai kuwa mun gode, ki barshi kawai a wajenki kya kashe ba ma sai kin gayawa Umma ba.'

Tayi 'yar dariya

'Gara dai na gaya mata kada shi ya gaya mata zancen ya zama wani abu da ban. Ungo dari biyar dai ka siyo min katin dari uku ka siyo na dari biyu idan munje sai mu bata canjin mu gaya mata haka.'

Ya karba ya tsallaka titi don ya siyo musu katin, ta cigaba da tafiya tana tunanin idan ta saka sai ta kirawo Karima da wayarta watakila don bata san lambar Sabir ba shi yasa ta ki dauka kuma taki biyowa.
...........

Zuwa yanzu Safiyya ta riga ta saba da zama a dakinsu ita da Hamida idan dai ba wani abu zata yi a tsakar gida ko falo ba. Umma tana yawan zama a falo ko ita kadai ko ita da Hamida da Sabir, itama Safiyyan tana son zama da su sai dai yanzu da Umma ta ga tana walwala zata yi mata gorin aure:

'da yanzu kema ai kina dakinki cikin sakewa.'
'duk matar da kika gani a daki hakuri take wanda ke kika kasa.'
'Allah ya baki miji mai kula dake baki sami natsuwa ba sai da kika kashe auren, ai kinwa kanki.'
'ki lallabo Abban Nurain ku mayar da aurenku don yanzu ba son auren zawarawa ake ba, shine ya sanka shine kawai zai iya zama dake.'

Wadannan sune kalaman da Umma take yawan gaya mata wadanda suke bata mata rai. Kawo yanzu idan aka ce mata ba Umma ce ta haifeta ba to tabbas ba zata yi musu ba. Don haka kusan kullum tana daki ita kadai kamar wata mai laifi.

A kashingide take a gefen gado ta gama saka katin wayar da Sabir ya siyo mata; a cikin kudin
da Yaya Auwalu ya bata da suka je gidan Baban Hotoro ta bayar ya siyo mata tunda bata nunawa Umma su ba. Ta gama shigar da katin wayar ta sayi data ta yin Whatsapp, nan da nan ta kunna ta fara duba sakonnin. Tana cikin dubawa ta tuna tun wancan satin da suka je gidan Baban Hotoro tace zata kirawo Karima bata kirawota ba, don haka nan da nan ta danna mata kira ta san yanzu zata dauka tunda da wayarta me. Haka wayar tayi ta ringing ba tare da an dauka ba har ta tsinke, sai da ta buga Sau uku sannan ta hakura; watakil Kariman bata kusa da wayar. Ta hakura da kiran ta koma Whatsapp ta cigaba da duba sakonnin groups dinta, wani kira ne ya shigo wayar da wata lamba da bata sani ba, tayi tunanin Karima ce don haka tayi sauri ta dauka.

'Salam alaikum.'

'Wa alaikum salam.'

Sai kuma taji muryar namiji, wadda ba tare da bata lokaci ba ta gane Yaya Auwalu ne. Cikin fara'a suka gaisa duk da tana mamakin kiranta da yakeyi tunda bai taba kiranta ba sai dai su gaisa a WhatsApp ko a group dinsu ma family. Tace

'Banibda wannan lamabar taka ai, shi ya sa da ban gane ba.'

'Eh, ai ba itace ta Whatsapp din ba.'

'Allah sarki.'

'To ya kike Safiyya? Ya kuka je gida rannan?'

'Lafiya kalau.'

Ta amsa da sanyin murya tana mamakin dalilin da yasa yake kiranta; Allah ya sa dai kada yace yana sonta don ba zata aureshi ba, ko babu komai suna mutunci da matarsa sannan kuma baya cikin irin mazajen da take fatan aure. Ya katse mata tunani daga daya bangaren

'Kina jina ko Safiyya, wata magana ce dama nake so muyi dake, Allah ya sa dai ki fahimceni mu samu mu fahimci juna.'

'Um to ina jinka Yaya Auwalu.'

'Yauwa kin gane ko? Akwai wani waje da nake dan zama idan na shigo Kano can a farm center, da zaki zo ki sameni da sai muyi maganar a nutse.'

Taji wani banbarakwai amma dai ta daure tace

'Gaskiya Umma bata barina fita zai ma fi sauki muyi maganar ta waya.'

Bata so tace ya zo gidan don kada Umma ta ganshi ta ce sai ta aureshi. Ya katse mata tunani

'Umm kin gane ko, ai za ki san dabarar da zakiyi wa Umma ki fara fita tunda ni ma din maganar da nazo da ita sai an fitan in dai kin amince.'

'Ai idan na san menene sai na san abinda zan gaya mata watakila idan taga abun yana da mahimmanci sai ta barni na fito.'

Tana jiyo sautin murmushinsa ta cikin wayar sannan yace

'Yauwa 'yar gari. Kin gane ko? Zuwa za ki dinga yi mu amfana da juna, ki dan taya ni hira ni kuma duk wata bukata taki ta kudi nayi miki ita komai yawansu.'

Ta so ta fahimci wani abu amma kuma bata son ta munana zato.

'Ban gane ba fa Yaya Auwalu.'

'Kin gane ko? Akwai hotel da nake sauka a nan din, yana can nesa da gari don haka kada ma kiji komai babu wanda zai ganki. Idan na shigo gari sai na kiraki kizo mu dan abun nan ni kuma sai na cika miki jakarki.'

Abin da bata son ta yarda dashi shi yake son ya gaya mata, bugun zuciyarta ya kara sauri domin ba a taba yi mata cin mutunci mai kama da wannan ba. Cikin dacin rai ta bashi amsa tana murmushin takaici

'Hotel Yaya Auwalu? Zina kenan zan zo muyi? Lall...'

Da hanzari ya katseta

'Ba haka bane, kada ki zama bagidajiya mana Safiyya. Kina bukatar kudi ni kuma ina bukarki ki zo ki debe min kewa, abu ne fa da za a yi a sirri. Ko baki gane bane?'

Zuciyarta ta gama harzuka har daci take ji a bakinta, yanzu har ta fara kama mazinaciya ne bata sani ba da yake mata wannan maganar.

'Ni bana bukatar komai daga gareka, abunda kake bukata daga gareni kuma ba zaka samu ba. Ina maka addu'ar Allah ya shiryeka ko don saboda mutuncin iyalanka kuma zan cigaba da rokon Allah ya saka min wannan cin zarafin da kayi min. Allah ya isa ban yafe maka ba don ni ba mazinaciya bace.'

'Ke S..'

Tayi sauri ta katse wayar, tuni kwalla ta cicciko mata ido ta sa bayan hannunta ta goge. Ta daga wayar ta lalubo lambar da ya kirata da ita tayi blocking, ta lalubo daya lambar ma da yake Whatsapp da ita itama tayi blocking.
Ta jefe wayar kan gado cike da takaici yayinda hawaye ya wanke mata fuska, bata son Hamida ta shigo ta ganta tana kuka don bata san me zata ce ya sakata kukan ba don haka ta tashi ta fada bandaki ta turo kofar.

Tunda take a rayuwarta ba a taba yi mata cin mutunci irin wannan ba; bata taba sanin Yaya Auwalu yana neman mata ba. Ko kuma itace tayi masa arha da yawa yake so ya fara ta kanta tunda ta zama bazawara? Abinda mijinta yayi da wasu matan ya haifar mata da fitna shine itama ake gaiyatarta ta aikata? Ba zata taba yafewa Auwalu wannan wulakanci da yayi mata ba. Ta share hawayenta ta matsa ta kunna fanfo saboda bata so a jiyo motsinta a bandakin. Sai da tayi kuka ya isheta har kanta ya nemi fara ciwo sannan ta wanke fuskarta tayiwo alwala ta fito daga bandakin, ta zauna a kan dadduma ta fara karatun kur'ani; wanda duk lokacin da ta ji tana shirin shiga damuwa shi take yi.

KARSHEN BABI NA GOMA SHA BIYAR
MATAR MUKHTAR

Written by:
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA SHA SHIDA

16
Yayi kewar Safiyya sosai, musamman idan yaje gidan Hajiya Nana ta sa masa rigima sai ya kaita wajen Mamanta. A hankali yaran suka fara sabawa shima kuma ya saba, kuma da yake babu wanda ya sake yi masa maganar Safiyyan a gidan sai shima ya bar maganar. Yana son Safiyya kuma yana son su dawo suyi zamansu, amma shi jira yake ita ta nemeshi ta bashi hakuri, ya saba a rayuwarsa 'yan matansa da yake lalata da su suna lallabashi don haka itama Safiyya ya san idan ta gama gwaruwa zata nemeshi; a lokacin ne shi kuma zai samu damar kafa mata sharuddan da ya tanada kafin ya mayar da aurensu.

Don haka ya cigaba da rayuwarsa yana cigaba da ginin gidansa yayinda mafi yawancin lokuta a hotel yake kwana da 'yan matansa wadanda yanzu suka kara yawa. Tun tuni ya rufe shafin Fatima don kawo yanzu ma ko tunawa baya yi da ita kwata-kwata.
..........

Sani Bashir abokinsa ne sosai wanda tare suka yi jami'a gaba daya da su Suraj, sai dai suna gama jami'a shi sani ya sami gurbin karatu a UK yayi tafiyarsa. Tunda ya tafi bai dawo ba yana cigaba da karatunsa a can yana aiki har sai yanzu ya dawo, kuma a dai-dai lokacin ne satin bikinsa ya shigo.

Tunda aka fara hidimar bikin aka nemi amarya Rukayya da ta hada abokan ango da babbar kawarta don shirye shiryen bikin amma tace bata da kawa, don haka sai ta hada su da kanwarta wato Jamila A. K. Tanko. Tunda aka hada Jamila da Mukhtar babban abokin ango su tsara yanda za a yi biki suka dinke, duk da a lokacin Mukhtar bai san me yake so daga gareta ba.

Kyakkyawace kwarai da gaske, ga farar fata, gashinta har gadon baya irin na buzaye saboda mahaifiyarta buzuwa ce. Baya gajiya da kallonta kuma baya gajiya da sauraranta musamman da yake ta iya hira ta daukan hankali ga murya kamar sarewa. Saura sati biyu bikin suka hadu amma sun sami shakuwa kai kace sun yi watanni da sanin juna. Sau da aka gama biki sannan ya tabbatar mata da soyayyasa, itama da yake bata da wani saurayi a kasa sai ta nuna masa a shirye take tunda ya amince zata cigaba da karatu a gidansa wanda yanzu haka a level 2 take.

Da farko ya so ya rudeta ya samu biyan bukatarsa amma kuma da yaji waye mahaifinta ya san gidansu ba inda zai je yayi wannan wargin ya tashi lafiya bane. Ba wai kudi mahaifinta ya tara ba, amma fitacce ne a garin Kano kasancewar ya rike mukamin Chief Judge na kotun jiha. Da yake kuma Jamilan tayi yanda yake jin ta kai a nuna ta a taro sai kawai ya yanke shawarar aurenta tunda ma Safiyyan bata nemeshi ba.

Ana gama bikin yayarta da Sani su kuma suka cigaba da soyayyarsu.
Basu fi wata daya ba mahaifinta ya nemeshi ya sanar da shi idan aure zai yi ya turo magabatansa, idan kuma ba haka ba ya daina zuwa; inda shi kuma yayi alkawarin turo iyayensa nan da sati mai zuwa.
.......

A falo ya sami Hajiya tana zaune tana cin gyada me gishiri, su Nana suna ta kaiwa da kawowarsu tsakanin wajen Bahijjan wadda a dole suka mayar mata da suna Anti Ba da kuma da wajen Anti Habiba. Bayan ya gaisheta ta amsa da fara'arta, ya gyara zama ba tare da yace komai ba. Ta debi gyadar da take gabanta ta mika masa tana fadin

'Kaima in sam maka gyadar ko in cinye kayata?.'

Yayai dan murmushi

'Hajiya ai ledar kawai za ki turo min.'

'Ba zan baka ba tamu ce ni da yara, in dai kana so ga kwaya goma.'

Ya mika hannu ya karbi wadda ta debo a hannunta, suka yi shiru kowa yana cin gyada. Jimawa kadan yayi gyaran murya yace

'Hajiya dama akwai yarinyar da nake neman aurenta mahaifinta yace na turo, shine

08, January 2025
Nafisa

I cant download the book

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login