Showing 42001 words to 45000 words out of 92582 words
a bude, ta fito falo ta sami Mukhtar yana kwance rigingine a kan kujera yana kallon Nigerian film. Kai tsaye kan ruwan cikinsa ta kwanta tana fadin
'Honey na...'
Katseta yayi yana kokarin tureta yana fadin
'Tashi mana, da yara fa a gidan ba lallai sunyi bacci ba wani zai iya fitowa fa.'
Ta kalleshi da alamar tambaya a idonta, sai kuma ta basar. Ta mike ta koma kan wata kujerar ta zauna tana fadin
'Ai inaga sunyi bacci ma.'
Suka cigaba da kallon suna hira jefi-jefi; tana fatan Allah yasa kada yaran nan su zamar mata matsala don ta ga sauyi daga wajen Mukhtar yanzu-yanzun nan. A haka har lokacin bacci yayi suka tashi suka shige daki. A hankali ta leka dakin ta hangosu ta cikin gidan sauro suna ta baccinsu, sai kawai ta janyo kofa ta rufe musu ta wuce dakin Mukhtar suka kwanta.
Sun riga sun saba basa kula juna lokacin kwanciyar bacci sai sunyi bacci ya ishesu idan akayi sallar asuba sannan yake nutsuwa da ita, don haka yau din ma baccinsu suka yi. Ana yin assalatu Mukhtar ya shirya bayan ya tasheta ya wuce masallaci don yayi sallah. Kamar yanda ta saba tana idar da sallah ta kara gayar jikinta ta fesa turarukanta sannan ta koma gado ta kwanta, yana dawowa shima ya bi bayanta ya kwanta. Kafin ya gama gyara kwanciyarsa ta juyo ta matso jikinsa tana masa sannu da zuwa. Bayan ya amsa yace
'Kin dubo yaran naki kuwa.'
Ta gyara kanta da ta kwantar a kan kirjinsa sannan tace
'Umm, duka bacci sukeyi.'
Ta cigaba da lalubarsa duk da ya rage mata kuzari da ya kawo maganar yara, haka kawai da asubar fari zai wani ce ta duba su kamar wata shanya. Dole shima ya fara biye mata, kafin suyi nisa suka jiyo ihun Nana tana kuka tana kiran Bahijja
'Anti Ba.'
Ya daga kanta daga jikinsa yace
'Kin ji Nana can ta tashi.'
Ta dauke wuta na dan lokaci; wannan kuma wace irin musiba ce ace sai yanzune zasu farka su basu san asuba ba kenan. Ta riga ta gama laushi amma haka ta janye jikinta ta dauki zaninta a saman wardrobe ta daura a kan rigar bacci ta fito don zuwa wajensu.
A tsakiyar gadon ta sami Nana tana zaune tana faman rusa kuka, kafin ta karasa kan gadon tace
'Nana, me ya sameki?'
Ta juyo ta kalleta tana share hawaye tana fadin
'Na tashi, Anti Ba nake nema ta zuba min shayi.'
Mamaki ya kamata, ta danna wayarta dake hannunta don ganin lokaci taga karfe shida ma bata karasa ba. Ta fara kokarin cire net din tana fadin
'Nana shayi zaki sha yanzu, ai safiya batayi ba.'
Ta rataye net din a saman gadon ta karaso ta zauna a gefen, kafin ta karasa mika hannunta ta kamo Nanan taji danshi a inda ta ajiye hannunta. Ta dago kai ta dubi Nana tana kokarin hadiye takaicin da ya taso mata
'Nana fitsari kikayi?'
Tayi narai-narai da ido tana shirin fashewa da kuka, bata son jin kukan don haka ta daga mata hannu tana fadin
'Ya isa!'
A nan Nurain ya farka, yana mika yana kallon dakin
'Nurain me ka tashi yi kaima safiya batayi ba fa.'
Ya kalli wajen da yake zaune a kan bargonta da ta ture gefe suka kwanta, ya kalleta ya koma ya sunkuyar da kai kamar mara gaskiya. Cikin yanayi na jin kunya yace
'Na manta nayi fitsari.'
Ta kalleshi cike da takaici ta kalli wajen da yake zaune, ga fitsarin nan ma yana naso don wannan ma bai wuce ace yanzu yayi shi ba. Takaici ya sake kuleta, wannan wacce irin musiba ce, duka su biyun sun yi mata fitsari a kwance. Ta manta gaba daya Hajiya tace mata ana saka su fitsari bayan sun kwanta; Nurain sau daya ita kuma Nana sau biyu. Ta rufe fuskarta da tafukan hannunta cike da takaici; kenan ba zata dinga bacci ba saboda wadannan yaran; lallai tana da aiki. Ta sa su suka sauka gaba daya, Allah ya so lokacin zafi ne don haka ta wanke musu jiki da ruwan fanfo ta canza musu kaya tana tunanin yanda zata yi da katifar bayan ta yayyafa mata ruwa. Ta kallesu suna zaune a kafet din dake tsakiyar dakin tace
'Ku kwanta a nan sai an jima zamu tashi.'
Nan da nan Nurain ya kwanta, ita kuwa Nana ta dubeta da murya kasa-kasa tace
'Shayi zan sha.'
Ta zabga mata harara wadda ta sa Nanan ta sunkuyar da kanta, ta fara kuka a hankali yayi da ita kuma Jamilan take tsaye tana tunanin abun yi. Wajen mijinta take so ta koma su karasa abinda suka fara amma yarinyar nan tana maganar shayi. Ihun Nanan ne ya katse mata tunani, inda ta sa kuka iya karfinta. Ta dubeta cike da takaici
'Idan baki rufe min baki kin kwanta ba ko na tashi ba zan baki shayin ba.'
Nanan ta fara kokarin hadiye kukanta tana shirin kwanciya Abbanta ya turo kofa ya shigo, ya fara dubansu daya bayan daya
'Ya hakane, me ke faruwa? Ya na gansu a kasa gadon fa?'
Ta kawar da kai sannan ta bashi amsa
'Fitsarin kwance sukayi duka su biyun.'
'Subhanallah, baki farka kin sakasu ba ko? Ai sai ana sakasu cikin dare.'
Tayi murmushin yake tace
'Ai baka tashe ni ka tuna min ba.'
Ya kalleta shekeke
'Au nine ma zan dinga tashinki kenan? Ki dai saka alarm a wayarki kawai.'
Ya karasa ya tsuguna gaban Nana yana mata magana
'Nana kukan me kikeyi.'
Cikin shessheka ta bashi amsa
'Ssshayi zan sha kuma ka kaini wajen Hajiya da Anti Ba.'
Ya dauketa ya dora a kan cinyarsa ya fara share mata hawaye
'Kiyi hakuri in an kwana biyu zamu je wajen Hajiya. Nan ma ai akwai shayi, bari Mommy ta hada miki mai dadi ki sha.'
Ya kalli Jamila dake tsaye tana kallonsu yace
'Ki hada musu shayi.'
A ciki ta amsa ta fice daga dakin jikinta babu kwari; lallai za ayi rigima. Daga farawa yaran har sun isheta, bata san raino ba domin kaninta daya kuma shekara daya ta bashi. Sauran kannen nata da yake ba dakinsu daya ba duk bata san yanda ake rainonsu ba. Wai harda wani hada musu shayi, ita tana sauri ta koma ta biya masa bukata ashe shi yaransa ne a gabansa. Gaskiya da sake!
Ta fito daga kicin da kofunan roba guda biyu a hannuwanta kowanne da shayi rabin kofin, ya riga ya fito dasu falo don haka nan ta samesu ta ajiye musu shayin. Sai da ta ajiye musu shayin tana shirin tashi Nurain ya kalli babansa yace
'Abba babu burodi?'
Ya dubeta
'Ki duko masa burodi.'
Haka ya zauna da yaran har gari ya karasa wayewa ko dakin bai koma ba, daga baya ta fito ta koma kichin ta hada musu abincin safe. Bayan ya gama shiryawa zai fita ne ya sameta a dakinta tana zaune a kan kujerar gaban mudubi, ya karasa ya tsuguna a gabanta
'Jam-jam.'
Ta kalleshi tana wani gajeran murmushi.
'Ni zan fita. Don Allah ki dinga hakuri da yaran nan kin san yanzu suke kokarin adjusting amma in sha Allah idan suka saba shikenan. Nana tana da rigima amma itama da ta saba shikenan, kiyi hakuri da su.'
Tayi murmushi tana kallonsa tace
'To kuma me akayi kake wani bani hakuri?'
Yayi dariya
'Babu komai, kawai dai na san zama da yara sai hakuri.'
Itama dariyar tayi tace
'To na hakura.'
Ya mike itama ta mike, ta dan matso jikinsa kadan suka hada ido. Ya lakace mata hanci yace
'Akwai bashi na a kanki, yau da magaribar fari zaki biya bashi.'
Tayi dariya tace
'Kai dai zaka biya bashi.'
Sai da ya kamo mata katifarta ta fito da ita ta jingine a tsakar gida sannan yayi musu sallama ya fice.
.....
Duk yanda ta dauki zama da yaran nan ya wuce haka, hidimarsu tana isarta. Gashi wani lokacin suyi ta fada suna kawo kara, haka dai take hakuri tana kawar da kai, amma kullum kafin dare sun gajiyar da ita. Shi kansa Mukhtar din sai da yaga alamar hakan a mu'amalarta.
KARSHEN BABI NA GOMA SHA TARA
MATAR MUKHTAR
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
BABI NA ASHIRI
20
Hamida ce a falo tana kallo yayinda Safiyya take kwance a daki, Umma ta shiga makota gaisuwar sallah da yake ranar uku ga sallah ne. Da sallama Sabir ya shigo falon bayan Hamida ta amsa ya zauna a kusa da ita, jimawa kadan yace
'Ina Yaya Safiyya?'
'Tana daki mana.'
Take ya mike ya shige dakin da sallama, tana kwance a kan gado idonta a rufe amma shi ya san ba bacci takeyi ba. Ya kula da yanda damuwarta take kara yawa tun cikin azumi, duk da ba tare suke kwana ba amm da safe yawanci da ya kalli idonta ya san tayi kuka da daddare. Idan yace ta daina damuwa sai tace ya daina sa ido ita bata da wata damuwa, ya gayawa Hamida amma ya ga ita abun bai dameta sosai ba. Itama Umma da ya gaya mata cewa tayi
"To wa yace maka zawarci yana da dadi, ai dole ta damu, aurenta ne fa ya mutu."
Ya kula dai babu wanda yake son ya fahimceshi, amma dai yana tsoron ta shiga depression. Shi ma bai san depression din ba sai kwanannan da yake suna SS 3 a makaranta aka shirya musu lakca aka gayyato masana sukayi musu bayani a kan shaye-shaye; a cikin bayanan ne akayi musu bayanin ciwon damuwa da yanda ake gane idan mutum yana cikin damuwa da yanda za a taimaka masa. Shi yasa yake ganin kamar Yaya Safiyya tana cikin damuwa.
Har ya karasa gaban gadon bata bude ido ba kuma bata amsa sallamarsa ba, ya dan doki tafin kafarta yace
'Ya Safiyya bacci kikeyi?'
Ta bude ido ta tashi daga kwance
'Idona biyu Sabir, me ka kawo min?'
Ya zauna a gefen gadon inda ta janye kafafunta
'Yau fa Yaya Habibu zaizo kunyi zancen islamiyyar kuwa?'
Tace
'Eh, na san in sha Allah yau zai wa Umma magana duk da suna hutun sallah ma.'
Ya zaro katin MTN na naira dari ya dauki wayarta ya fara sakawa, tace
'Kai Sabir nace ka daina sayamin kati da kudin makarantarka fa.'
Ya gyara zama ya ci gaba da saka katin
'Haba Ya Safiyya kamar ni babban yaro zaki ce na dogara da kudin makaranta, haba dai ai akwai resources.'
Tayi dariya tana harararsa tace
'Sannu minister of petroleum resources.'
Ya mika mata wayar yana dariya
'Kin san wani abu ma Yaya Safiyya, rannan ba muna maganar ki fara sana'a ba kika ce min baki iya komai na siyarwa ba kuma ba kya jin zaki iya koyon wani abu a yanzu.'
Ta daga masa kai alamar eh, ya cigaba
'To ai kin iya kitso, wanda kika yiwa Nana jiya bakiga yanda yayi kyau ba. Gashi dama su Faridan Yaya Hajiyayyaye ma nan take zube su kiyi musu. Wallahi a sa haraji, kowa yazo ya taho da kudin kitso.'
Tayi dariya
'Lallai Sabir, ka san kuwa nawa ake biya kudin kitson, hamsin ce fa da dari. Yaushe zan iya wahalar banza?'
Ya gyara zama ya koro bayani
'Ina laifi Ya Safiyya? A kan yanda yanzu zaki kwana nawa baki da ko sisi gashi wanda Yaya zai baki duk ki bawa Umma ai gara ki fara kitson, a kalla sai ki dinga boyewa ko nima zan dinga ajiye miki.'
Tayi dariya ta kawar da kai
'Rabani da aikin wahala Sabir.'
Ya marairaice
'Don Allah Yaya Safiyya ki gwada, da wannan zaman ma ai gara kitson ko ba komai ki sami abun da zai debe miki kewa.'
'Hmm! To kai wa yace maka maigidan zata yarda.'
'In dai ke kin yarda ki barni da ita zan tsara miki ita.'
Tayi dariya ta rasa me zata ce masa, bata son gwaleshi saboda yanda ya damu da damuwarta. Amma gani take kitso a matsayin sana'a babu abinda zata samu da shi, kuma ace yanzu shikenan ta zama mai kitso. Ta kalleshi suka hada ido yana jira tace ta amince, ta kawar da kai. Itama bata san ko zata jure ba ko da yake ma ta san unguwar akwai masu kitso don haka ko ma ta fara bazata samu masu zuwa da yawa ba don haka ta kalleshi ta daga kai
'Toh shikenan duk wanda ya shigo gidan nan yace yana son kitso zan yi masa ya kawo kudi.'
Ya tafa hannu yace
'Yesss! Kinga nine
sakatarenki, idan mukayi ciniki ya kai dubu uku za muje mu bude account a banki.'
Tayi dariya ta kalleshi da mamaki
'Wai duk a kan kitson?'
Ya harareta
'Zauna kina kallo.'
Sai bayan isha'i suna zaune a falo suna cin tuwon dare Sabir din ya dubi Umma yace
'Umma Yaya Safiyya fa gobe zata fara yin kitso na kudi nine sakatarenta.'
Umma ta yi dariya sannan ta gatsine fuska
'Kitso kuma? Lallai to ni dai sai da a dinga yi a rumfar kusa da gate saboda bana son gashi a tsakar gidana.'
Safiyya ta kalleshi suka hada ido, ya kalli Umma yace
'Sami'ina wa ada'ana Hajiya Umma, yanda kika ce haka za ayi.'
Ta dubi Safiyya tace
'Ina fatan kin san Saratun gidan Hajiya ma tana kitson tun tuni kuma gida daya ne tsakanin mu da su.'
'Na sani Umma dama nifa ba ma ni na....'
Sabir yayi sauri ya katseta
'Mun sani Umma kowa rabonshi zai ci.'
Ta tabe baki tana duban Safiyyan
'Allah ya bada sa'a, ina dai fatan kin san Yayanku yace islamiyya zai sakaki don dazu ce min yayi nan da sati mai zuwa zaki fara zuwa.'
'Na sani Umma, ya gaya min.'
'To Allah ya bada sa'a.'
Suka karasa hirarrakinsu suka tafi suka kwanta. Ita dai Safiyyan ta san babu wanda zata cewa tana kitso amma kuma kamar yanda ta fadawa Sabir duk wanda ya shigo gidan da sunan kitso zata yi masa.
_
Tunda aka fara bikin sallah Fatima take ta tunanin karyar da zata yiwa Mommy ta barta taje Niger wajen Janan, gaba daya tunaninta ya kare. Ranar hudu ga Sallah aka yiwa su Mommy waya aka sanar dasu rasuwar kanwar mahaifiyarsu a Kafancan, don haka a take suka fara shiri ita da kanwarta wadda itama take aure a nan Zariyan. Mutuwar ta rudasu sosai suna ta kuka, zuwa dare sun gama shiri a kan gobe da sassafe zasu kama hanya. Haka Fatima ta shirya itama domin da ita za a tafi. Da yake sun tafi da wuri kuma direbansu yana da sauri da wuri suka isa, basu dade da isa ba Babbar yayar su Mommy wadda ake kira Inna Amina itama ta shigo da yaranta daga Abuja. Nan da nan suka hade da su Fatima ana ta hirar yaushe gamo, duk da Fatima ta girmi yaranta mata amma sun shaku sosai. Can bayan la'asar Inna ta hada kan yaranta zata tafi, suka hade baki suka kewaye Mommy akan zasu tafi da Yaya Fatima Abuja. Daga baya Inna ta kalli Fatima tace
'Taso mu tafi Fati, ko bazaki bar Mommyn ita kadai ba.'
Sukayi dariya gaba daya, Mommy tace
'Ni a su wa, Allah ya kiyaye hanya.'
Inna ta dubi Fatima tace
'Ko baki dauko kaya ba ki taso muje tunda next week dole mu tafi Zariyan bikin su Hajja sai ki debo kaya.'
Cikin walwala Fatima ta bi su Inna Abuja domin ta san Inna sai tafi saukin tsarawa ta barta taje Minna, idan taci sa'a ma a bata direba duk da ba zata so hakan ba. Nan sukayi sallama da Mommy suka wuce Abuja.
.......
Sai da ta kwana daya tana hutawa a Abuja sannan sukayi waya da Janan suka tsayar da shawara a kan zasu je ranar Asabar don Adnan ranar Asabar din zai dawo amma da daddare. Tun dare ta sami Inna ta gaya mata akwai kawarta a Minna tayi bari tana so taje ta dubo ta gobe, ba tare da wani kai ruwa rana ba Inna ta amince. Tace
'To babu damuwa gobe sai kuje da Malam Musa, dama akwai sakon da zan bashi ya kaiwa wata matar abokin Abbansu a Minnan. In ya ajiyeki sai ya kai sakon ya dawo ya daukeki ku dawo; ammafa ba dadewa zai yi ba don haka sai dai kawai ku gaisa ku dawo.'
Da fara'arta ta amsa
'Babu komai Inna nima dama ba dadewa nake so nayi ba.'
Gari na wayewa Fatima ta shirya, Malam Musa ya kai yaran gidan tahfiz sai su Faisal su uku wadanda dukansu yan jami'a ne. Saida suka fito Faisal din yace zai je shima ya raka Malam Musa don haka gaba daya suka kama hanya. Suna isa Fatima tace Faisal ya fito su shiga su gaisa da kawarta don haka ita da Faisal din suka shiga, bayan sun gaisa yayi musu sallama Janan tace masa za su je nan baya gidan surukanta da Fatima idan sun dawo gidan a rufe suyi waya.
Faisal yana fita Janan ta dubi Fatima tace
'Haba kawata, kin san kuwa yau Adnan zai dawo; ai saura kadan mu makara.
Ta karkata kai tana fadin
'Hmm! Kin san Mommy, Allah ne ma ya sa akai wannan rasuwar na samu hanya na gudo Abuja da ban san yanda za ayi ba.'
'Bari ki gani.'
Da yake a shirye Janan take sai kawai ta dauko mukullin mota da mayafinta suka kama hanya. Suna cikin mota Fatima ta dubeta tace
'Kawata ince ko dai kusa ne, kada fa su dawo bama nan.'
Ta dafa cinyarta tace
'Babu wani nisa fa, cikin gari yake shi ba boka bane ai, yanzu zamu isa. Shi yasa ai na cewa Faisal za mu fita don ma kada su kawo wani abu.'
'Hmmm!'
Sai da suka tsaya a ATM Fatima ta cire duk kudin da yake account dinta wato naira dubu dari sannan suka wuce.
Basu dade suna tafiya ba Janan ta karkata kan motar ta shiga wata unguwa, sun dauki lokaci suna tafiya kafin tayi parking a kofar wani karamin gida. Tabbas a tsakiyar mutane yake don
08, January 2025
Nafisa
I cant download the book