Showing 72001 words to 75000 words out of 92582 words

Chapter 25 - MATAR MUKHTAR COMPLT

SAKINA   

16 Aug 2024

7149

tayi musu sai da safe ya juya motar suka kama hanyar gida.

Yanda yake ta faman walwala yana yiwa Halimatu wasa shine abinda ya kara bata haushi, ta manta rabon da taganshi cikin walwala haka. Tun da ta kirawo matar nan rabon da ya kulata, ko Halimatu ma bai fiye yi mata wasa sosai ba. Amma gashi yanzu daga yaga tsohuwar matarsa ya fara walwala harda wasa.

Yanda ta maka masa kofar motar bayan ta sauka ya isa ya sa ya fahimci akwai matsala, amma da yake hankalinsa baya wajen bai ma san tana yi ba.

Sai da ta samu Halimatu tayi bacci sannan ta wuce dakinsa. Yana zaune a gefen gado yana ta faman latsa waya ta shiga, tana shiga ta zauna a kan kujerar zaman mutum daya da take dakin. Bata ce masa komai ba, shima kuma da yake batayi sallama ba ta shiga bai ce mata komai ba kawai ya cigaba da abinda yake yi.

Sai da ta numfasa tace

'Mukhtar.'

Ya dago ya kalleta.

Cikin izgili tace

'Meye na ga kana ta wani bin Safiyya a wajen biki, naga dai yanzu babu aurenka a kanta ko?'

Yayi 'yar dariya

'Kwarai babu aure amma ina fatan kin san ina da damar na sake aurota ko? Ina kuma fatan kin san itace uwar 'yayana don haka kin ga dole na bita ko?'

'Ni da ba uwar 'yaya ba! Ina fatan dai idan ka sake aurotan ba nan zaka ajiye min ita ba don babu matar da zan zauna da ita a wannan gidan, kuma Allah ya sa kada a bige da aure a shiga lalacewa kuma.'

Ta fada tana mikewa don ta fice ta bar masa dakin.

Nan take ya hade fuska ya mike ya sha gabanta yana nuna ta da yatsa yace

'Kada ki sake ki taba mutuncin Safiyya idan kina son zaman lafiya kin ji na gaya miki, kuma in na kawota gidan nan kina iya ficewa tunda dama ban taba rufe miki kofa na hanaki fita ba.'

'mtsewwww!'

Ta ja tsaki, ta juya ta fice ta bar masa dakin.

Ya koma ya zauna a kan gadon; ya za ayi ma ya hada Safiyya da Jamila a gida daya, ai ba zai ma yiwu ba. Yanda Safiyya take girmamashi tana kula dashi ba zai hada ta da Jamila ba ta ga yanda ake wa miji wulakanci itama ta koya. Dole ma ya nemi gida ya siya a nesa da wannan unguwar, ko babu komai ya sami inda zai dinga nutsuwa tayi ta fitnarta ita kadai.

Ya dauki lokaci yana kokarin samun Safiyyan a WhatsApp amma ya gagara, sai daga baya ya gane tayi blocking dinsa. Har ya dauki layinsa wanda bata sani ba zai kirata sai kuma ya fasa, gara ya bari kawai tunda in sha Allahu jibi Lahadi idan aka gama biki zai je ya sameta a gidansu.
........

Tunda gari ya waye yake Allah-Allah dare yayi domin yaje ya sami Safiyya, yanda ya ganta ya san ba zata bashi matsala ba in sha Allahu. Dama ya san Safiyya bata da fushi da yawa.

Yana idar da sallar la'asar kuma ya canza shawara; yasan yanzu haka tana da zawarawanta da suke zuwa zance da daddare don haka gara ya je bayan sallar la'asar ya sameta a nutse.

Nan da nan ya dauki mota ya fice, ya cewa Jamila ya tafi gidan Hajiya. Gidan Hajiyan ya fara tsayawa don haka sai wajen biyar sannan ya wuce gidansu Safiyya.
.........

Kamar yanda ya sabarwa kansa in dai zai wuce Abuja yana tsayawa yayiwa Safiyya sallama, kuma shi dama baya zuwa zance da daddare. Ya gaya mata in dai yana gari toh baya son fita da daddare ya fi son ya zauna a gidansa tunda yana dadewa bai hadu da yaransa ba, wannan shine lokacin hirarsu.

Jirgin karfe takwas na dare zai bi don haka yana idar da sallar la'asar ya sa direbanshi ya tukoshi suka taho wajen Safiyya; don in ya gama ya koma gida kafin dare yayi maman Muhammad ta kaishi airport ita da yara.

Inda suka saba zama nan suka zauna, sai da biyar ta gota sannan yace mata zai tafi, don haka ta mike domin ta rakashi bakin get kamar yanda ta saba.

Shine ya fara fitowa ta karamin gate din tana biye da shi suna ta hirarrakinsu cikin fara'a. A dai-dai wannan lokacin kuma Mukhtar ya karyo kwanar gidan, idonsa a kan get din. Ko ba a gaya masa ba ya san Safiyya ce waccan dan fes yake hangosu, ya sauka daga kan titi ya tsaya a gefen hanya yana mamaki don duk wanda ya hangesu ya san soyayya suke yi.

Tana sanye da abaya ta yane kanta da karamin mayafi mai ruwan omo sai kallon mutumin take tana masa murmushi; irin murmushin da bai taba zaton Safiyya zata iya yiwa wani ba idan ba shi ba.

Safiyya ta dubi Baban Muhammad tace

'Toh mijin barrister sai yaushe kenan za a sake zagayo mu?'

Ya kyalkyale da dariya yace

'Ni 'da su! Yau kuma mijin barrister na koma?'

'To ai dolene ace da mijin iya Baba.'

'Shikenan kuma za a kashe ni da Hausa.'

Itama tayi dariyar.

Suka jero tare suka nufo dalleliyar motar da take ajiye daga gefe wadda direban yake zaune a kan booth din baya.

Kafin su karaso direban ya sauka ya zagaya ya tsaya a gaban Baban Muhammad ya sara irin yanda sojoji sukeyi, ya mika hannu ya bude masa kofa. Yayi sallama da Safiyya ya shiga mota. Ba a ja motar ba har saida Safiyyan ta shiga gida ta rufe get din.

Tana rufe get din ya kifa kansa a kan sitiyari motar, ji yake kamar wani abu ya tokare masa zuciya. Bai taba sanin yana da kishi haka ba sai yanzu, domin ko da Safiyya tana budurwa bai taba ganinta da wani ba. A yanayin da yake ciki ba zai iya tunkararta a haka ba don haka ya gwammace ya tafi ya sake dawowa wata ranar.

Don haka ya karya kan motarsa ya juya ya nufi gida. Duk da bai ga fuskar mutumin sosai ba amma ya san ba wani girmansa yayi ba a shekaru,sai dai ko ya nuna masa kudi don ya ga ma kamar soja ne. Kuma da alama Safiyyan tana sonshi; lallai akwai aiki.
........

Tunda Fatima suka daidaita da Ahmad sai kuma ta shiga fargaba da adduar Allah ya sa kada ya gane ita din ba budurwa bace. Duk sati sai ya zo daga Abuja, duk dangin su Fatima an san shi domin bai fi sati hudu da fara zuwa ba ya sa Ibrahim ya hadashi da dan rakiya suka je ya gaida 'yan uwan mahaifinsu dake nan Zariyan.

Nan da nan ta manta da maganar Mukhtar domin sosai take son Ahmad. Kuma da yake duk wani bincike da za ayi an gama yi gaba daya an yi na'am da shi.

Yau Asabar, tun safe take shirin tarbarsa; duk da baya yarda yaci abinci a gidan toh takan yi masa wani snack wanda ko bai ci ba sai ta juye masa a container ya tafi da shi. Yau din ma cake tayi masa ga kuma kunun aya mai sanyi.

Sai wajen sha daya ya karaso, suka zauna a falon da suka saba zama. Sun dan taba hira kadan ya dubeta ya cika bakinshi da cake yana shafa ciki yace

'Kina bani kayan dadi da yawa fa, zaki sa tumbin kudina ya kara tsini.'

Ta kyalkyale da dariya

'Babu komai kudin ma sai su karu.'

Jimawa kadan yace

'Zamu je Dubai next week daga office, zamu je wani conference daga nan kuma zamu yi wani short course. Sai bayan sati hudu zamu dawo. Amma na gayawa Ibrahim kafin na tafi za a kawo kudin aure in ya so da na dawo sai a fara shirin biki.'

Ta dago ta kalleshi suka hada ido sai kuma ta sunkuyar da kai. Yace

'Ko baki shirya bane tayi Daria

'In dai ka shirya nima na shirya.'

'Yauwa, ranar Laraba za a kawo don ranar Alhamis zamu wuce.'

Suka karasa hirarrakinsu yayi mata sallama a kan sai ya dawo zasu hadu.
............

Kamar yanda ya gaya mata kuwa ranar Laraba iyayen Ahmad suka zo da kudin aurenta, gidan kanin Babanta wanda shine waliyyinsu a nan aka karba duk da Ibrahim ma yana wajen.

Cikin karamci da mutunci akayi aka gama, suka bayar da kudin aure naira dubu dari biyu. Da kyar suka karbi tukwicin da aka basu suna cewa

'Su ai an gama yi musu tukwici tunda aka basu Fatima.'

Suka tafi a kan da ya dawo za su kawo kayan aure a sa rana.

Haka suka rabu ana son barka.
........
Tunda Yaya Ibrahim ya dawo da kudin auren Fatima ya kuma ya tabbatar mata za a sa rana da zarar Ahmad ya dawo ta sake shiga damuwa. Duk wani abu da akeyi na shirya amarya ta san Mommy zata yi mata sai dai ta san Mommy bata san ta rabu da budurcinta ba don haka shirin budurwa zata yi mata.

Sai a lokacin ta kara nadamar sakarwa Mukhtar kanta, gashi ko ba a gaya mata ba ta san tana dauke da ciwon sanyi don lokaci zuwa lokaci tana ganin alamomin a jikinta.

Ko ba zata nemi na gyaran ba ta san ko a boye dole ta nemi maganin da zai rabata da wannan sanyi, domin idan taje da shi ya zama wanda ake iya dauka ne ta sawa Ahmad bata yi masa adalci ba.

Nan da nan ta sake shiga damuwa. Sai bayan kwana biyu dabara ta fado mata; makarantar da take koyarwa akwai wata malama maman Haidar; wadda bata fi shekarunta ba duk da ita tana da aure, don haka ta yanke ita zata tambaya tunda suna shiri sosai.

Ranar Juma'a tana shiga makaranta ta ja Maman Haidar, bayan tayi mata bayanin abinda take so ta dubeta tace

'Ke kuma me ya hada ki da maganin sanyi?'

'Uhm, kin san zaman hostel nayi, kuma nan da 'yan watanni za a yi bikina. Kin san duk wanda yake shiga bandakin nan na hostel baya rabuwa da cututtuka.'

'Hakane kawata, ai kuwa da gaskiyarki. Zan kuma hadaki da wadda zata baki maganin sanyin dan gaske don in dai kin yi amfani dashi yadda tace to babu ke ba sanyi in sha Allah don na gwada maganinta kuma na ga aikinsa.'

Ta yagi takarda ta rubuta mata lambar waya 07039080978, 09077591726. Ta mika mata takardar tana fadin

'Farida Abdallah kenan, tana nan a Kaduna. Ki kirawota duk wani bayani zata yi miki muma kina tura mata kudi zata aiko miki da kayanki har nan Zazzau.'

Ta karba tayi mata godiya.

Kasa daurewa tayi taje gida don haka ana yin break ta kirawo ta. Kafin a tashi sun gama ciniki ta tura kudi. Don haka kafin magriba sakonta ya iso wanda tace a kirawo Maman Haidar ta karbar mata.
.......

Bata fi kwana biyar da fara amfani da kayan Farida ba taji sauyi a jikinta don haka ta kara dagewa. Na gyara kuma ta bari a kan sai ta gama da na sanyin sai ta nemi na matsi wanda zai matseta tsam.
.......

Duk yanda Mukhtar yake jin ganin Safiyya zai yi masa sauki abun ya ci tura, ya koma ranar litinin da yamma aka ce masa bata nan wanda kitso taje wani gida a hotoro daga nan kuma ta tsaya a gidan Baban hotoro har sai dare ta dawo.

Har ciki ya shiga ya gaida Umma, suka gaisa itama tana haba-haba. Bayan ya tafi Hamida take fadan yanda Umman ta sakar masa fuska, Umma tace

'Yarinta ke damunki, ai kuma baku isa kuyi fada dashi ba tunda dai shine uban 'yayanku Nana da Nurain. Kuma ko don kuyi musu kara ai kwa girmamashi ko da baya auren Safiyya.'

Ranar Talata ma haka ya koma, nan kuma tun kafin ya karasa kofar gidan ya hango wata dalleliyar mota a bakin gate, wadda saurayin Hamida ne wanda zai aureta ya zo da ita.

Duk da ba itace motar da yaga bazawarin Safiyya a ciki ba amma sai ya dauka shi ya zo da ita, don haka nan da nan ranshi yayi matukar baci. Ya karya kan motar ya koma zuciyarsa tana ta turiri.

Gaba daya a cikin damuwa ya kare satin, yana tsananin son ganin Safiyya gashi tayi blocking layinsa ko ya kirata bata shiga. baya jin zai iya barinta wani ya aureta a halin yanzu; Safiyya tashi ce shi kadai in sha Allahu.


Sai ranar Juma'ah bayan ya dawo daga masallaci, yana tsaye a mota a bakin gate kafin ya shiga gidan ya dauki karamar wayarsa ya kirawota da layinsa wanda yake jin batayi blocking ba. Ai kuwa yana kira ta shiga, sai da ta kusa tsinkewa sannan ta daga. Tana yin sallama ya saki murmushi saboda jin dadi, bayan sun gaisa yace

'Safiyya ina kika shiga ne nake ta nemanki, tun ranar Lahadi sai yanzu na sameki.'

Tayi 'yar dariya

'Ni din wai? Ina nan a gida watakila baka nemeni bane.'

'Hmm! To yanzu ya za ayi Safee? Ina son ganinki.'

'Ai gani ko? Ina sauraronka? Ya yaran dai?'

'Suna nan lafiya kalau, ai kin gansu ranar Juma'ah ko?'

'Eh haka ne kam.'

'To yanzu yaushe zan zo?'

'Au wai ta wayar ma haka bai isa ba? Inaga ai zaka iya zuwa duk lokacin da ka shirya.'

'A'a, ki dai gaya min ranar da idan na zo zan sameki ko? Don maganar da nake son mu tattauna da ke mai mahimmanci ce sosai.'

'Ok, to kazo gobe.'

'Karfe nawa?'

Cikin kosawa da mamaki tace

'Daga bayan azhar har dare ina nan.'

Har sun yi sallama yace

'Safiyya.'

'Na'am.'

'Zunubin da nayi kika yi blocking din main layina na tuba please ki bude ni.'

Tayi dariya

'To in sha Allah.'

Sukayi sallama suka ajiye waya yana ce mata sai goben.

Ta ajiye wayar a gefenta tana dariya a ranta tace; ko menene ake nemana oho. Bata yi tunanin zai zo yace yana sonta ba ko daya don yanda taga ya banzatar da ita bayan rabuwarsu ta zata ya gama da ita. Duk da dai da suka hadu a wajen biki ta kula da wata rawar jiki da yake. Ko ma dai menene tana jiranshi ya zo taji.

KARSHEN BABI NA TALATIN DA BIYU.

Talla:
Idan kina son maganin sanyi Mai kyau da inganci ki nemi Farida Abdallah, tana Kaduna Kuma tana aikawa ko Ina. 07039080978, 09077591726.

MATAR MUKHTAR

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA TALATIN DA UKU

33
Tun safe yake shirin zuwa wajen Safiyya yana bitar kalaman da zai tsarata da su, la'asar tana yi ya shirya ya kama hanya. Yana tsayawa a kofar gidan ya gwada kiranta inda ya samu har yanzu bata bude layinsa da ta toshe ba, yayi murmushi ya dauki karamar wayar ya kirawota. Kafin su gaisa ya ce mata yana kofar gida amma yana so ya shigo ya gaida Umma, Sabir baya nan don haka Hamida aka tura tana ta faman zumbura baki ta shigo da shi. Bayan ya gaida Umman ya koma waje, Safiyya ta fito ta bi bayansa.

Tana zama ya dubeta yace

'Kin ki ki bude layina da kika yi blocking, yanzu ma sai da na kira shiru.'

'La! Ka san mantawa nayi, bari na shiga gidan don wayar tana ciki.'

Yayi murmushi sannan suka gaisa, suka dan yi jim tana sauraronsa, ya dan yi gyaran murya yace

'Safiyya, ya kwana biyu?'

Da murmushi ta amsa, murmushin da yake kara masa karsashi yana ganin kamar Safiyya tasa ce shi kadai

'Alhamdulillah.'

Suka sake yin shiru na dan lokaci, jim kadan yace

'Abubuwa da dama sun faru Safiyya, wanda na san nine mai laifi shi ya sa ma na zo na baki hakuri kuma na nemi yafiyarki.'

Ta dan kau da kai sannan ta dube shi

'Ni dama ban rike da komai ba, idan kuma da hakkina a ciki ma tun tuni na yafe. Allah ya yafe mana baki daya amma ni in dai nice komai ya wuce.'

Sosai ya ji dadin maganganunta musamman da yake har yanzu cikin fara'a take zancen. Jimawa kadan kuma yace

'Alhamdulillah, nagode. Kinga kenan ba zamu sami wata matsala ba wajen mayarda aurenmu ko?'

Ta kalleshi da mamaki a fuskarta, ta yi 'yar gajeriyar dariya

'Wane aure Kuma? Wanda aka gama tun shekaru uku ko fiye? Ai ina ga mun gama aure ni da kai ko?'

A take yanayinsa ya canza, da muryar lallashi yace

'Kada kice haka Safiyya, idan baki manta ba tun a lokacin na gaya miki zan dawo mu mayar da aurenmu ko? Ai k...'

'Ikon Allah, to da ni din ka zata riga ce da ka rataye wadda kake da damar ka dauka ka mayar a lokacin da ka ga dama?'

Ya kalleta na dan lokaci ya jijjiga kai

'Me yayi zafi haka? Ai kin fi karfin haka a wajena. Na san na yi kuskure kuma ban kyauta ba, shi yasa ma na fara da baki hakuri. Inaga kamar ni nafi dacewa dake kamar yanda ke kika fi dacewa da ni, ko don yara ai kya tausaya mana.'

'Mukhtar kenan, kai ma ka kasa tausayawa yaran balle ni da dama tun kafin nayi aire na san duka binda zan haifa na ubane, haihuwarce kawai tawa?'

'Kada ki ce haka Safee, don Allah ki yarda ki dawo dakinki. Duk ma wani abu da nake yake sosa miki rai na bari kuma nayi miki alkawarin ba zan sake ba. Kum.....'

Ya fara bata haushi don haka ta daga masa hannu tace

'Bari kaji Mukhtar, in dai aure ne da ni kai in sha Allahu ya kare. Wato lokacin da ka koroni kace na fice maka gida tabbas na shiga damuwa ba kadan ba, don ban taba zaton zan iya rayuwa babu kai ba. Kusan shekara daya zuwa biyu bayan ka sakeni tabbas da ka dawo a shirye nake da na koma gidanka ko da kuwa nice zan baka sadaki. Amma a halin yanzu na gane soyayya ta fi zuciyarka yalwa haka kuma duniya

08, January 2025
Nafisa

I cant download the book

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login