Showing 39001 words to 42000 words out of 92582 words

Chapter 14 - MATAR MUKHTAR COMPLT

SAKINA   

16 Aug 2024

7148

kalleta ta jijjiga kai tana mamakin yanda ta bari bacci ya kwasheta a haka. Ta karasa ta tabata

'Fatima ki gyara kwanciyar ki kiyi azkar.'

Ta juya daga rub da cikin ta bata amsa cikin magagin bacci

'Na yi.'

Ta janyo abun rufar ta ta lullube mata kafafu, ta kashe fitilar sannan ta ja mata kofa ta fice.
Tana son Fatima sosai, amma a dai-dai wannan lokacin bata da burin da ya wuce ace Fatima tayi aure. A halin ya zu ma gani take kamar tana kin kula samarin ne da gan-gan saboda wani abu da ta saka a ranta, amma duk da haka tana yi mata addu'a Allah ya bata miji na gari.
........

Ranar asabar tun asuba Fatima ta shiga kichin, kafin karfe takwas ta gasa cake mai dadi sannan ta hada zobo ta cewa Baba Habi a yi abincin safe da kawarta; wanda ta san kunun gyada za a dama da kosai. Wajen karfe tara da Rabi Janan ta iso, zuwa lokacin Mommy ta jima da fita. Tana tsayawa a gate tayiwa Fatima waya don haka tun daga mota ta tarota, bayan sun gaisa da Adnan suka shigo gidan tayi mata masauki a dakinta.

Sai da ta jere mata abincin safe sannan suka gaisa yayinda Fatima ta bude kwanon kosai ta tura mata tare da zuba mata kunu a kofi sannan ta koma kusa da ita a kan kafet din da yake dakin ta zauna.

Bayan Janan ta kurbe kunun da ta cika baki da shi ta dubi Fatima ta ce

'Kawata duk kin wani rame sai kace dake Mommy take tsomen shayi.'

Tayi 'yar gajeriyar dariya tare da kawar da kai

'Ba zaki gane ba kawata, sai a hankali.'

Bayan ta gama cin abincin Fatima ta kwashe kwanukan ta mayar kicin ta debo cake din da zobo ta ajiye a kan mudubin tace

'Ga wannan kuma na anjima ne.'

Suka koma kan gado suka baje. Janan ta dubi Fatima tace

'Kawata kin san kuwa tun yaushe nake nemanki? Na shako gulma kuma bazata yiwu ta waya ba shi yasa na tsaro shi ya kawo ni. Tukunnama wai ni ina mutuminki Mukhtar ne?'

Tayi tsaki ta kawar da kai

'Hm! Ki bari kawai kawata. Kin san wulakancin da mutumin nan yayi min kuwa? Na zo na gama bazawa zai aiko a saka rana amma kawai sai ya dauke wuta ya daina kulani, ke daga karshe dai blocking dina yayi.'

Ta zaro ido tare da cije lebe

'Kutumar Uba! Lallai wannan ya cika mara mutunci, yana so yace ya bata miki lokaci a banza kenan? Shi bai barki kin kula mutanen arziki kin sami miji ba shi kuma don ubanshi har ke zai yi blocking?'

Ta kawar da kai ta share kwalla, wannan hirara ta fama mata ciwo. Janan ta sa hannu ta sake share mata kwallar yayinda ita kuma ta cije lebe ta rike hannun Janan din tace

'Janan ba zaki gane irin cutar da Mukhtar yayi min ba, kin san haka ya mayar da ni kamar matarsa duk lokacin da muka fita hotel muke zuwa ya gama bukatarsa sannan ya dawo da ni a kan alkawarin zai aureni.'

Tuni ta fizge hannunta ta dora a ka tare da bude baki, takaici ya sa itama ta saki kwalla

'Fatima garin yaya? Ke me yayi miki zafi? Ya za ayi ki amince da shi har haka? Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun.'

Zuwa yanzu gaba dayansu kowa hawaye takeyi. Mamakine ya cika Fatima, kenan su su Janan da sauran kawayensu da take gani suna rungume-rungume da samari su basa bada kansu kenan; iya rungumar suke tsayawa? Ta bude baki cikin rawar murya

'To ya yi min alkawarin aure kuma naga wadda ba ayiwa alkawarin aure ba ma haka za ki ga saurayin ya tsotseta a mota kuma ki ji sun fita shan ice cream da daddare.'

Ta sauke hannun daga ka ta kama hannun Fatima

'To ai kawata iya nan ake tsayawa baka bada kai tunda ba karuwanci muka zo yi ba, kai da kake so ko waye ya aureka ka je a cikakkiyar budurwa? Ai dole ma ya guje ki kawata to me zai yiwa doki idan ya aurenki?'

Ta fada jikin Janan ta saki kuka gaba daya Janan tana tayata, sai da sukayi mai isarsu sannan suka bari. Janan tace

'Bana son saki kuka kawata amma kin san gulmar me na shako nake nemanki?'

Ta jijjiga kai alamar a'a, don haka Janan ta cigaba

'Ya gaya miki dalilin da yasa bazai aureki ba.'

'Hmm! Kafin dai ya daina kula ni cewa yake wai Hajiya ce bata yarda a yiwa Safiyya kishiya ba saboda 'yar kanwarta ce amma zai tsara Hajiyan. Har wayar mu ta karshe da yana borin kunya haka ya gaya min. Sai daga baya na gane duk ni yake rainawa hankali Bai taba niyyar aure na ba.'

'Tabbas! Bai taba niyyar aurenki ba.'

Ta zaro wayarta daga jaka ta budo wani hoto ta mikawa Fatima, screenshot akayi na hoton don haka da rubutu a kai "New love story". Tana ganin hoton ta saka hannunta daya ta dafe kirji saboda yanda takeji kamar zuciyarta zata faso kirjinta ta fito; Mukhtar ne da wata farar yarinya kyakkyawa, ya rungumota suna kallon fuskar juna suna murmushi. Daga ganin hotunan ka san pre wedding ne. Ta tuno lokacin birthday dinta da suka je Minjibir park, kwalla ta kara cicciko mata ido. Ta turawa Janan wayarta tana fadin

'Aure zai yi ko Janan?'

Ta kawar da kai

'Um, harda ma katin bikin ya saka a status ban san yanda akayi ban sauke katin ba.'

Ta sake dafe kirji tace

'Allah ya isa na, duk sanda na tuna mutumin nan sai na yi masa Allah ya isa. Shi ya fara sanina a mace kuna shi kadai na sani duk a kan yana cewa zai aure ni, hotunana da yake da su wanda nake tsirara sun isheni takaici. Ya cuceni kawai, gashi har yanzu ba wani labari ban san ma da wanne idon zan kalli mijin da zan aura ba; idan ma ina da rabon auren kenan.'

Janan ta share mata hawaye ta rungumeta, suka dauki lokaci a haka, kamar wadda aka tsikara Janan din tace

'Ke daina kuka kawata, wallahi bai isa ya ci bulus ba ko da wa yake yawo a garin nan sai munyi maganinsa daga shi har wannan kazar da zai aura.'

Ta kalleta da mamaki, Janan din ta dafa kafadarta

'Ki zo na kaiki inda za a saka miki dan iska a kwalba, wallahi sai yanda kika yi da shi. Ko uwarshi ba zata fiki iko da shi ba; ki ja shi a kasa in kin ga dama ki aureshi ki sa ya saki waccan idan kuma kin sami wanda ya fishi ki fasa kwalbar kiyi aurenki ai dai kema kin rama.'

Ta kalleta da mamaki

'Kai kawata!'

Ta harareta

'To ki zauna a nan kiyita kuka, ya fafe ki yaje ya auri wata wai shi mai wayo ke kuma ya ci bulus kenan.'

Tayi tunani na dan lokaci ta yi murmushi ta dubi Janan din tace

'To ya za ayi kawata, don sai yanzu ma da naga aure zai yi na gane ni ya rainawa wayo.'

Ta Mika mata hannu suka tafa

'Yauwa 'yar gari, sai ya dawo hannunki kema ki ja banza a kasa.'

Tayi murmushi kawai don ko bazata aureshi zata so ta tarwatsa masa gida kamar yanda ya tarwatsa mata rayuwa. Janan tace

'Adnan zai je Umra da azumi kuma sai bayan sallah zai dawo don haka da an fara azumi zan tafi gida, bayan Sallah zan koma Minna sai ki san yanda za kiyi ki tsara Mommy, a Minna malamin yake sai kizo muje kawata. Aikinsa kamar yankan wuka ne, ke dai ki tanadi kudi kamar wata dubu dari haka.'

'Kada ki damu kawata, zan sami kudi ko da a wajen Yaya Ibrahim ma kuma ga 'yan canjin alwee dina; don ma Umma tana karbewa.'

Nan suka karasa hirarrakinsu har sai wajen sha biyu na rana sannan Adnan ya zo ya dauki Janan, suka yi sallama a kan sai bayan Sallah fatiman zata sameta a Minna suje wajen malam.

KARSHEN BABI NA GOMA SHA TAKWAS
MATAR MUKHTAR

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA GOMA SHA TARA

19
Bai taba murnar rabuwa da Safiyya ba sai da yaga Jamila a gidansa, tabbas ya godewa Allah da ya rabashi da Safiyya domin da bai rabu da ita ba da yanzu bai auri Jamila ba. Tana da matukar natsuwa bayan kyau da haduwa, gashi kuma tana da ilimin addini. Itama Safiyyan ba baya bace amma a halin yanzu baya ganin kowa sai Jamila. 'Yan uwanshi duk sun ziyarci gidan amarya yayinda itama amarya taje gidansu ta gaida Hajiya da sauran mutanen gidan.

Tun kafin ya aureta ya riga yayi mata maganar zata rike masa Nana da Nurain kuma ta amince. Duk da a gidansu daga ita sai auta amma bata da matsala da yara, musamman da yake kanana ne kuma yayarta ta nuna mata yadda ta tarbiyyantar dasu haka zasu taso; don haka da shirinsu ta shigo gidan. Sai dai ya sanar da ita sai bayan karamar sallah zai dauko su, saboda yana so ya gama amarcinsa kafin su dawo.

A can gidan ma tun kafin ya fara maganar aure Hajiya take gaya masa ya dawo da matarsa ko kuma yayi aure don ya kwashi yaransa.

Ranar da aka fara azumi bayan an sha ruwa ya dauketa suka je yiwa hajiya barka da shan ruwa. Nan falon Hajiyan ya barta da Bahijja, ta ja su Nana da hira don tana so su dan sake da ita kafin su dawo hannunta.

A falo ya sami Baba suna hira da Anti, amaryar Hajiya, bayan ya gaishesu Anti ta tashi ta basu wajen. Sun dan taba hira a nan Saifullahi da Aminu suka shigo suka samesu duka suka yita hira da Baban, jimawa kadan ya dubi Baba yace

'Bari naje mu tafi Baba.'

Ya kalleshi

'Yaushe zaka dauki 'yayanka?'

'Bayan sallah in sha Allah Baba.'

'Ina fatan ka gaya mata zata zauna da su, ko wajen uwarsu zaka mayar da su? Don dai kaga Hajiya yanzu ma lallabawa take kada kafarta ta dameta da ciwo.'

'Eh na gaya mata Baba, zata zauna min da su.'

'To Allah ya bada zaman lafiya.'

Ya amsa sannan yayi sallama da su Saifullahi ya fito suka koma gida.
_

Tunda Safiyya take bata taba yin azumin da bata ji dadinsa ba kamar wannan; tana jin dadin ibadarta matuka gashi kullum sai ta raba dare tana sallah don haka wannan yana sa mata nutsuwa ta zuciya. Amma kuma tana shan aiki don kullum a tsaye take wuni, Umma da kanta take kare Hamida idan ta dawo daga makaranta sai tace ta gaji. Zuwa yanzu abun ya daina damunta kuma ya daina bata mamaki don haka hidimarta kawai take yi.

Ta san bata ajiye ko sisi ba don haka bata sa rai da kayan sallah ba, tana kallo dai Umma ta siyawa Hamida leshi da mayafi. Bayan da aka kawo kayan da yake duk suna zaune a falo aka kawo sai Umman ta dubi Safiyya tace

'To ke kuma idan na kara samun kudi na ga abinda zan iya yi miki na sallar ki sabunta.'

Murmushin kawai tayi tace

'Allah ya hore.'

Bayan kwana biyu kuma tana ji aka sayi takalmi da jaka na Hamida. Sai da akayi azumi goma sha biyar Yaya Hajiyayyaye ta zo gaisuwar azumi ta kawowa Umma atamfa da takalmi wanda daman duk shekara maigidanta ya saba bawa Umman atamfa. Hamida kuma ta tambayeta kudin dinki tace ta kai zata biya. Ita kuwa Safiyya ko maganarta ba'a yi saboda kada tace ma ayi mata, ita kuwa ta ja bakinta tayi shiru tana harkar gabanta.

Sallah saura kwana goma sha biyu Yaya Habibu yazo da nashi kayan; ya kawowa Umma leshi, Hamida atamfa yayinda ya bawa Safiyya atamfa itama. Da zai tafi kuma yace Sabir ya raka Safiyya da Hamida shagon abokinsa a kantin kwari su zabi takalmi da mayafi. Har ya tashi zai tafi ya kawo naira dubu biyar ya bawa Safiyya yace ta kai dinki, don haka yana fita ta wuce ta kai dinkin ta.
..........

Ta gaji da wannan zaman na jira wanda bata san me take jira ba; kullum kara shiga damuwa takeyi. Sai ta fara kokarin tursasawa kanta walwala sai wani abu ya faru wanda zai sake mayar da ita damuwa; ko kuma Umma ko 'yanuwanta su gaya mata wata magana da zata mayar da ita damuwa. Wani lokacin har ji take kamar an saka zuciyarta a keji kirjinta yayi kunci, wani lokacin kuma sai ta ji da kyar take numfashi.
Kullum sai tayi sallar dare tayi addu'a amma kuma kullum damuwarta karuwa takeyi; duk da haka kullum tana addu'a Allah ya yaye mata kuma tana sa rai Allah ya amsa.

Ta yanke shawarar bayan sallah islamiyya zata koma, sai dai kuma tana tsoron gayawa Umma kada ta hana; ba wai tana da tabbas din hakan bane amma ta san kadan da aikin Umma tace babu inda zata. Don haka ta kirawo Yaya Habibu ta sanar dashi a kan yayiwa Umman magana; yaji dadi sosai don haka yace ta bari bayan sallah zai siyo form ya zo mata da shi sai ya kaita da kansa.

Ranar Sallah da wuri suka gama aikinsu da yake kowa ya sa hannu, nan da nan kowa ya shirya cikin kwalliyar Sallah. Can bayan azahar tana zaune a daki ta jiyo shigowar Nana da Nurain, Aliyu ne ya kawo su ya gaida Umma a tsakar gida ya sanar da ita bayan magriba zai zo ya daukesu.

'Umma ina Mamanmu?'

Nurain ya tambaya bayan ya gaida Umma da Hamida dake tsakar gida, Umma tayi dariya tace

'Ai nice mamanku.'

Shima dariyar yayi ya nufi daki da gudu yana fadin
'Ai na san tana cikin nan.'

A take Nana ta bi bayansa, suna shiga dakin suka fada jikinta da gudu sunata dariya. Ta rungumesu gaba daya itama tana dariyar domin tayi kewarsu sosai. Ta dago su ta shafa kan Nana wanda ya sha ribbons sai dai babu kitso tace

'Nana kin bari kikayi a yi miki kitso ko?'

Ta noke kai, Nurain yace

'Eh Mama, kuka takeyi Baba yace a kyaleta.'

Ta shafa kanta

'Ki dinga tsayawa ana yi miki kitso kinji Nanan Mama, in ba haka ba ba zaki zama yar gayu ba.'

Kafin ta bada amsa Nurain yace

'Mama Abbanmu yayi wata amarya, sunanta Anti Jamila amma yace Mommy zamu dinga ce mata. Mun je ma gidan wani babban sabon gida ne, Abba yace ni da Nana bayan sallah zamu koma muma mu koma wajenta.'

Nana da take kan cinyarta ta tallafo habarta tana kallon idonta tace

'Mama kema ai zaki dawo sabon gidan ko?'

Kafin ta amsa Nurain ya dubi fuskar Nanan yace

'Ke Abbanmu ya saketa ba zata dawo ba, sun rabu.'

Ya dubi Safiyyan yace

'Ko Mama.'

Ta kalleshi tayi murmushi tana kokarin neman amsar da zata bashi, taga dai babu abinda yayi saura da zata boye tunda su can sun gaya masa don haka ta daga kai alamar eh tace

'Umm.'

Nana ta kwabe fuska tana duban Safiyyan tace

'To nima gidan Umma zan dawo na dinga bacci a wajenki kinji Mama.'

Ta shafa kanta tana murmushi, ta rasa amsar da zata bata don haka ta canza hirar ta hanyar tambayar Nana ko Abba ya sakata a makaranta.

Haka suka wuni sunata wasa da surutu a gidan, kafin magriba ta lallaba Nana ta yi mata kitso mai kyau; da yake ta iya kitso sosai kukan tane yasa bata yi mata sai ta bayar a kaita inda bazata ji kukan ba.

Sai bayan magriba Aliyu yazo daukarsu. Yana shiga gidan Nana ta sa kuka ita bazata bishi ba, da kyar da lallashi ya dauketa suka wuce.
Itama Safiyyan haka ta kwana ranta babu dadi, ta rasa binda yake damunta; kishin labarin amaryar da suka zo mata dashi ko kuma kewarsu. Ta ji tausayinsu sosai kuma taji tausayin kanta, a haka bacci ya kwasheta.
_

Tunda Aliyu ya mayar da su Nurain gidan Hajiya ake ta fama da Nana, ta dai hakura ta daina kuka amma ta ki kula kowa; da anyi magana sai tace ita wajen Mamanta zata. Haka dai aka rabu da ita aka cigaba da hada musu kayansu domin babansu ya ce a shiryasu, washegari za su zo da Jamila kuma idan sun zo da su zasu tafi shikenan sun koma gidansu.

Sai bayan la'asar suka iso gidan, bayan an gaggaisa ya bar Jamila wajen Bahijja ya fice. Sun dan taba hira kadan amma da yake ita din ba mai yawan surutu bace haka suka zauna kowa hankalinsa yana kan wayarsa. Sai bayan isha'i ya dawo, nan da nan aka saka kayansu a mota Nurain yana ta murna zai koma sabon gida yayinda Nana take ta fushi; ta ki kula kowa har Abban nata sai dai kawai duk abinda aka ce tayi zata yi. Haka suka kama hanya har gida.

Sai wajen karfe tara suka shiga gidan, gaba dayansu sun riga sun ci abinci don haka nan da nan aka hau shirin bacci.
Ya riga ya sanar da Jamila a dakinta zasu kwana duk da akwai dakinsu a sama amma ya sanar da ita sunyi kankanta a barsu su kwana su kadai; don haka ma babu komai a dakin nasu sai tarkacenta da ta ajiye. A kasa ma suna da daki wanda shi na wasa ne da karatu.
Tsaf ta shiryasu ta saka su sukayi fitsari sannan ta raka su daki ta kwantar dasu a kan gadonta. Ta dubesu tace

'Kada wanda yayi min fitsarin kwance kun ji ko? Idan za kuyi fitsari ku tasheni.'

Ta dubi Nurain tana nuna masa bandakinta tace

'Kai Nurain ga bandaki nan ka ji?'

Ya daga kai alamar toh. Ta kwantar da Nana wadda take zaune tana kallonta kawai, ta gyara musu rufa ta tofa musu addua sanna tace

'To kowa ya rufe ido yayi bacci.'

Take suka rufe ido kamar yanda tace don haka ta tashi ta fice ta bar musu fitila a kunne kuma kofar

08, January 2025
Nafisa

I cant download the book

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login