Showing 57001 words to 60000 words out of 92582 words

Chapter 20 - MATAR MUKHTAR COMPLT

SAKINA   

16 Aug 2024

7152

nake tambayarta tana jina taki magana.'

Inna ta harareta

'Ikon Allah kefa kika ce likitan yace sai an bata na sati biyu, idan ma da wani abun ba sai ki bashi maganin ba in ya so sai ki cigaba da fushin naki tunda ke bakya jin magana.'

Tuni hawaye suka wanke mata fuska saboda takaicin maganar Inna, bata so Inna tayi wannan maganar ba don ba tayi niyyar bada maganin ba. Saboda yanda Nana take hanata bacci shi yasa tun cikinta yana da wata uku da ta kaisu asibiti suna mura aka basu Benelyn taga ya sa Nana bacci don haka tun lokacin kullum da rana sai ta bata don tayi bacci ta barta ta huta.

Muryar Inna ce ta katse mata tunanin

'Inaga dai tafiya zanyi na bar miki gidan nan Jamila tunda ba mijinki ba nima ban isa nayi magana ki ji ba. Kwana nawa da yin abun nan na baki hakuri, kince kin hakura da sunan amma baki daina wulakanci ba?'

Ta dubi Mukhtar tace

'Muje Abban Nurain na duba maka maganin ina ga yana kicin ai.'

Ta wuce gaba Mukhtar da Aminu suka bita a baya. Suna fita Jamila ta tashi ta dora hannunta a ka ta fasa kuka me gunji saboda takaici, ji take kamar zuciyarta zata fito ta bakinta. Ya akayi aka san tana bawa Nana magani? Ina yaran ma suke?

Sukuwa su Mukhtar suna shiga kicin Inna ta hau bude durowoyin jikin bango na sama don a nan ne take tunanin zata sami maganin duk da bata da tabbas, ta dai kula kamar daga kicin Jamila take dauko maganin. Sai da ta bude durowa uku, a ta hudun ta samu. Durowar ma gaba daya a cike take da kwalaben magani.

'Yauwa gashi nan.'

Kafin ta dauko Aminu ya wucesu ya mika hannu ya dauko kwalabe biyu da suke gaba, ya duba yaga Benilyn syrup for children, kwalba daya an sha kamar Rabi dayar kuma sabo ne ko budewa ba ayi ba amma an cire kwalin. Ya zura hannu yana juya ragowar kwalaben wadanda zasu kai kamar guda goma, suma duka na Benilyn din ne sai dai duka babu komai komai a ciki an shanye. Ba tare da yace komai ba ya zaro wayarsa ya dauki hoton durowar ya wuce ta tsakanin Inna da Mukhtar din ya fice ya barsu a nan.

Inna ta bi bayansa da kallo sannan ta juyo ta dubi Mukhtar din tace

'Wai me yake faruwa ne?'

Ya shafa kansa ya fesar da iska ya kalleta da idanuwansa wadanda suka kara ja da kyar ya nemo muryarsa yace

'Maganin da yan kwaya suke sha shi take bawa Nana, gashi nan duk wadannan kwalaben a cikin Nana ya kare.'

Ya share kwallar da ta taru a kwarmin idonasa; ya akayi bai gane ba? Yana kallo Nana tana yawan bacci yanzu amma bai kawo komai, idan yacewa Jamila Nana fa da bata bacci sai tace 'kyaleta aka yi.'

Gaba daya kansa ya cushe , zuciyarsa nema take ta daina aiki, tausayin Nana yake ji yana tunanin tashin hankalin da Baba zai yi masa.

Inna ta katse masa tunani

'Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun. Wannan wane irin rashin hankali ne?'

Ya raba ta gefenta ya wuce ya nufi corridor din da zata kai shi saman gidan, yana taka matattakala ta daya yaji sallamar Mustafa don haka dole ya dawo ya san daga office ne.

Sai a lokacin ya tuna da report din da ya kamata ya kai office, ya bar computer din da karamar wayar tasa a mota don haka ya san jinsa akayi shiru aka turo Mustafan.

Kafin ya karasa cikin falon Mustafan yace

'Mutumina ya haka ne DG sai neman ka yake, wayarka a kashe dayar kuma baka dauka?'

Ya sa tafukan hannunsa ya rufe fuskarsa ya ce

'Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun!'

Mustafa ya karaso ya dafa kafadarsa

'Lafiya dai, ya naganka duk a firgice.'

Ya kama hannun Mustafan ya sauke daga kafadarsa yana fadin

'Muje mota, aikin yana can.'

Suka fice suka bar Inna wadda take tsaye a kofar kicin ta kasa motsi saboda tsoron abinda Jamilan ta aikata.

KARSHEN BABI NA ASHIRIN DA BIYAR

MATAR MUKHTAR

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA ASHIRIN DA SHIDA

26
Suna fita Inna ta wuce sama wajen Jamila, tana nan a kwance a inda suka barta tana faman share hawaye. Ta karasa ta zauna a gefen gadon dai-dai inda kafar Jamilan take ta dubeta duba na takaici tace

'Don Allah Jamila wacce irin barna kika aikata haka? Hauka kike so ki saka yarinyar ko kuwa so kike ki mayar da ita 'yar maye?'

Ta tashi zaune ta dora hannu a ka

'Ni wallahi Inna ban sani ba, ki na kallon dai yanda yarinyar nan take da sa mutum wahala. Kuma likita ne ya basu maganin, da naga in ta sha tana yin bacci shine na cigaba da bata.'

Takaicin Inna ya karu

'Ikon Allah! Yanzu ke har kina da bakin magana? To gara ma na gaya miki tun wuri yaro duka ko wanne da irin wahalarsa sai dai idan ba zaki haifa ba. Kika kasa cewa ubansu ya dauke yaransa amma?'

'Inna wallahi na gaya masa sai dai kawai yace na yi hakuri, to ya zan yi?'

'Ai kin yi yanda yayi miki dadi a rai. Bari na jira ya zo naga matakin da zai dauka don ba lallai ya iya zama dake ba. In ya so sai mu wuce na mika ki hannun iyayenki kya yi musu bayani.'

Ta kara rushewa da kuka yayinda Inna ta fito ta barta a dakin. Kanta sai sarawa kawai yakeyi gashi ta kasa daina hawaye, ya hanata suna ya turawa budurwa kudin taron kuma yanzu ga wannan maganar ta fito.

Haka tayi ta kwance har sai da Baby Halima ta gaji da kwanciya ta sa kuka sannan ta tashi ta dauki baby.
.......

Inda Aminu ya bar Baba da Hajiya a nan ya samesu. Yana shiga ya karasa ya mikawa Baba kwalaben maganin, itama Hajiya ta matso don ta gani. Bude baki Baba yayi yabi kwalaben da kallo yana fadin

'Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun.'

Aminu ya zaro wayarsa ya budo hoton da ya dauka ya mikawa Baba yana fadin

'Ka ga durowar da take ajiye maganin Baba, wadannan kwalaben duk na benilyn din ne. Allah ne kawai ya san tun yaushe take bawa Nana wannan maganin mayen.'

Tuni hawaye suka wanke fuskar Hajiya yayinda Baba ya dubi Aminun yace

'Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, ai yanzu dole a nema mata taimako.'

Hajiya tace

'Yarinyar nan bata yi mana adalci ba, da ita da Mukhtar din da sun sani sun dawo min da yaran gaba daya.'

A nan baba ya dauki wayarsa ya kirawo Dr. Jibrin wanda da ne a wajen kanin Baban kuma likitan yara ne a asibitin Murtala. A take ya ce zai iso gidan nan da minti talatin.

Yana isowa bayan yaji bayanin Baba yace babu wani abu tunda shekarunta hudu kawai, amma dai sai kunyi hakuri da ita saboda zata yi rigima da yawa. Kuma yace a dinga yawan bata ruwa ana bata abubuwa masu zaki wadanda zasu sa ta sami karfi a jikinta. Sannan yace akwai allura da zai yi mata ta kwana uku, kullum da daddare zai dinga zuwa yana yi mata. Ya kwantar musu da hankali ya nuna musu ba wani abu bane tunda an gane da wuri.

Haka Hajiya daga baya sai da ta saka aka samo ruwan zamzam wanda kullum take tofa mata fatiha kafa bakwai tana bata tana sha.
.......

Bayan sun fito da Mustafa haka ya dan jirashi ya karasa aikin ya tura computer din Mustafan, yayi masa bayanin idan ya koma office din ya gaya musu an samu accident ne a gidansa. Mustafan ya dubeshi yace

'Amman dai kada ka koma gidan yanzu don kar kuyi bataciyya, gara a bi abun a hankali. Gara ma kawai ka wuce gidan Baba, nima da na kai takardun nan zan zo na sameka please, just calm down small.'

'Kada ka damu abokina, ai dole na wuce can din don dole naje na bawa Baba da Hajiya hakuri.'

Haka suka yi sallama Mustafa ya tura motarsa ya tafi ya bar Mukhtar din a cikin tasa motar da dama a waje ya ajiyeta lokacin da suka dawo karbar magani.

Kansa ya kulle, ya shiga matsananciyar damuwa. To yanzu ma ina za shi? Gidansa dai baya son shiga don yana ji kamar idan ya shiga komai zai iya faruwa tsakaninsa da Jamila. Baya son kuma yaje gidan Baba don bai san ma da don idon da zai kalli Baban ba, ya san ma Baba ba zai saurareshi ba a halin ya zu.

Da ya rasa mafita sai kawai ya kifa kansa a kan steering din motar ya rufe idanuwansa. Bai san tsawon lokacin da ya dauka a haka ba, har sai da ya gaji ya daga kansa ya lalubi karamar wayarsa ya duba lokaci.

Karfe uku da minti goma ya gani, da mamaki yace

'Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun!'

Nan take ya tuna baiyi sallar azahar ba, kafin ya yanke shawara kuma cikinsa ya bada kugi alamar yunwa yake ji.

Baya son kula kowa a cikin gidan don haka sai kawai ya tayar da mota ya zagaya bayan layinsu wani restaurant ya sayi abinci ya ci. Kafin ya gama uku da Rabi ta gota don haka masallacin layinsu ya dawo yayi sallar azahar ya jira aka yi la'asar sannan ya fito da niyyar tafiya gida.

Tun kafin a sallame sallar la'asar ya tuna Fatima tana can tana jiransa a Zariya ko waya bai samu yayi mata ba. Yana idar da Sallah ya sake duba lokaci karfe hudu da minti biyar; ya jijjiga kai don ya san babu yanda za ayi ya tafi Zariya yanzu. Gashi wayar ma da yayi saving lambarta Jamila ta fasa, duk lambobin da suke kan karamar wayarsa babu suna yayi saving.

Da kyar ya lalubo lambar Fatima ya kirawo ta, tana dauka tace

'Ka bar ni da zulumi, Allah ya sa dai ba accident kayi ba don tun dazu ma nake kiran layinka a kashe.'

A hankali yake magana yace

'Ban ma taho ba, ina gida matsala aka samu Nana ta gamu da minor accident. Gashi an sace wayar tawa garin na kaita asibiti, sai yanzu na sami kaina.'

Ta yatsina fuska tace

'Allah sarki, Allah ya sauwake.'

Suka dan taba hira har zasuyi sallama yace

'Gobe in sha Allah da wuri zan fito zaki ganni.'

'Allah ya kai mu. Allah ya sa dai ba gidan jiya za a koma ba!'

Ya jijjiga kai cikin damuwa, baya son damuwar Fatima don yanzu in ya bata mata rai sai kawai ya ji zuciyarsa tayi kunci. Kwana biyun nan da bai je ya ganta ba ji yake kamar a wuta yake kwana. Yace

'Haba Baby, kema kin san ba za ayi haka ba. Da kin barni ma ai da yanzu kina gida na ko?'

'To babu damuwa, goben mayi magana.'

Sukayi sallama, ya ajiye waya ya sake kifa kansa a kan sitiyari. Mintuna kadan ya tuna a bakin masallaci yake don haka ya san yanzu za a fara tambayarsa ko lafiya. Don haka ya kunna motar ya nufi gidan.

A falon kasa ya sami Inna da goyon baby a bayanta, sallama kawai yayi mata ya wuce ya nufi hawa sama ba tare da ya ce mata komai ba. Ta riga ta san ransa a bace yake don haka itama din ta kyaleshi.

Yana shiga dakinsa ya fada wanka, bayan ya fito ya tsaya a gaban wardrobe domin ya dauki kayan sawa. Ya zaro kayan a hankali, kafin ya ajiye kayan a kan gadon ya tuna ai harda kayan su Nurain Baba yace a kai kuma ba'a kai ba. Don haka yana saka kayansa ya wuce daki Jamila.

Kofar a bude take don haka ya tura kofar ya shiga ba tare da sallama ba. Tana nan kwance a gefen gadon kamar mara lafiya, bai ko kalli inda take ba ya wuce ya nufi wardrobe. Akwai akwatinsu wanda suka zo dashi daga gidan Hajiya shi ya sauke a saman wardrobe din ya kwashe duka kayansu, ya tura akwatin ya fice.
Yana ficewa ta gyara kwanciya ta kara fashewa da kuka; saboda yanda ta ji babu dadi da ta gane ya kwashe yaransa.

Yana fita ya wuce gidansu, abinda ya zata shine ya faru. Domin yana shiga tun kafin ma ya hau saman Baba Baban ya aiko a kirawo shi. Tun kafin ya tsuguna a gaban Baban ya fara fada, sosai ya kare masa fada yace

'Ka kori uwarsu kuma ka kasa kula da amanarsu, kana cikin gidan amma sama da wata shida ana bawa yarinyar kayan maye wai baka sani ba saboda sakarci.'

Yana gama fadan kuma yace ya tashi ya fice masa daga gida. Haka ya fito ya kama tuki yana tafiya kamar ba zai je ba, domin maganganun baba sun sa shima ya fara zargin kansa.

Bai taba jin takaicin rabuwa da Safiyya ba sai yau, lallai ya san da tana nan da haka bata faru ba.

Haka har ya isa gidan ya shige dakinsa ya kwanta domin yanzu idan ba kwanciyar na bai san me zai yi ba. Duk wani abu da zai debe masa kewa a kan wayarsa ne kuma ga shi Jamila ta fasa wayar, a halin yanzu ma kuma bashi da kudin da zai sake sayen wata wayar sai dai ko zuwa ayi albashi sai ya sayi wata Yar matsakaiciya kafin ya sami kudin.

KARSHEN BABI NA ASHIRIN DA SHIDA
MATAR MUKHTAR

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI

27
Zuwa yanzu kitso ya kankama sosai a wajen Safiyya, domin yanzu kusan duk sati sai ta sami masu son kitso; ko su zo ko taje tayi musu.

Tunda ta bude account sai ya zama da zarar ta gama kitso take ware dan wani abu ta bawa Umma sannan ta dauki na kashewa ta bawa Sabir sauran ya kai mata banki. Duk lokacin da ya kai mata kudi idan taga alert sai ta ji kamar ta shide saboda dadi. Ranar da kudin nan suka kai dubu ashirin Allah ne kadai ya san dadin da ta ji.

Washegarin ranar kuwa ta saka Sabir a gaba ya rakata kasuwar Sabon Gari ta siyo hair dryer da kayan wankin kai; saboda ta riga ta yanke shawara duk inda take kitso musamman da yake ana kiranta ne don yara to zata gaya musu har wankin kan yaran zata dinga yi sai mutum ya biya kudi. Sai ta mayar da shi kitso da wankin Kai N800, kitso kawai Kuma N400, na manya kuma N500. Haka ta cigaba da sana'arta tana tara kudin ta.

Sosai Umma ta rage duk wasu abubuwa da take yi mata, duk da har yanzu tana yawan yi mata maganar aure. Tana nuna mata ba zata zauna mata a gida ta ki aure ba saboda tana samun kudi. Haka dai ta cigaba da lallaba Umma don a zauna lafiya, domin a halin yanzu bata da wani manemi ma a kasa.

Mazan ma gaba daya tsoronsu takeyi; tun farkon da ta fara kitso sau biyu tana haduwa da masu sonta.

Kowannensu kamar mutumin kirki amma duka suna zuwa suka nuna mata ba aure zasuyi ba lalata ce ta kawo su, shi dayan ma har bayani yayi mata wai tunda ta taba aure ba wani abu bane don babu wanda zai gane. Haka ta sallamesu duka kuma ta yiwa kanta alkawarin ba zata sake kula wani namiji ba.

Shi kuwa Mukhtar a yanzu ma ji take ko ya dawo ba zata saurare shi ba. Damuwarta daya yaranta wadanda har yanzu duk lokacin da ta tuna su sai tayi kuka, ana kawo su wajenta lokaci zuwa lokaci tunda yanzu gashi an gaya mata sun koma wajen Hajiya. Tana da damar zuwa ta gansu amma tayi wa kanta alkawarin ba zata sake zuwa gidan ba don kada ma su zata ko zawarcin Mukhtar takeyi.
........

Ita da Sabir, da Hamida ne kawai a gidan don Umma ta tafi biki gidan kawarta. Suna nan zaune suka ji sallama, nan yaran suka shigo da gudu. Yaran Yaya Habibu ne kananan wato Ummi da Halifa wadanda amaryarsa ta haifa masa tare da uwarsu Anti Farida; Yaya Habibu matansa biyu Anti Salma Uwargida mai yara biyar sai kuma ita Anti Farida wadda dai-dai lokacin auren Safiyya ya aureta. Uwargida Anti Salam bata da son mutane kuma bata so a rabi mijinta don haka dole danginsa suke baya-baya da shi babu mai son zuwa gidansa, ita ma kuma sai yayi da gaske take shiga danginsa, don ko yaranta bata bari su je yanda ya kamata. Sai da ya auro Anti Farida wadda ita kuma mace ce mai son mutane sannan danginsa suka fara sakewa a gidansa. Ko yanzu ma ita da yaran zuwa suka yi su gaida Hajiya da yake Alhamis ce babu islamiyya, kuma kamar yanda ta saba sai da ta rikowa Hajiya sabulu da turare; tunda tana koyarwa a makarantar kudi da albashinta take wannan hidimar.

Suna shiga suka zauna wajen su Safiyya aka hau hira. Daga baya kuma Safiyya ta yi musu kitso ita da Ummi. Suna cikin hira Anti Farida tace

'Ni Safiyya ki dauko kwalinki na diploma mana, ko yayanki ai sai ya samo miki aiki ko da a private school ne. Albashin dai babu yawa tunda kinga nima dubu goma sha tara suke bani inda nake koyarwa amma Ina laifi.'

Hamida tace

'Kuma wallahi hakane Yaya Safiyya, ga unguwar nan da makarnatun kala kala.'

Safiyyan ta dubi Anti Farida tace

'To matar Yaya ki wuce min gaba, Allah ya sa Umma ta bari don kin ga yanzu ma gani take kamar kudin kitson nan ne yake hana ni aure.'

'Bari na sami Yayan naki shi zance yayiwa Umman magana, ai aure nufin Allah ne idan bai zo ba kuma a haka ake so mutum ya kare yana rabe-rabe.'

Haka suka karasa hirarrakinsu sai wajen magriba da Umman ta dawo su Farida sukayi sallama suka kama hanya.

Sai da Farida tayi magana sannan ma Safiyya ta tuna da cewa tayi diploma, a da kuma gani take

08, January 2025
Nafisa

I cant download the book

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login