Showing 54001 words to 57000 words out of 92582 words

Chapter 19 - MATAR MUKHTAR COMPLT

SAKINA   

16 Aug 2024

7164

nata ya shigo

"Honey please 135k zaka tura masa coz yaron shago ne ko don shima ya sami wani abu."

Yana yatsina fuska ya rubuta amsa ya tura

"Yes my love."

Haka ya gama lissafinsa ya tura 135k wannan account, sannan ya tura mata rasit. Tana budewa ta kyalkyale da wata dariyar mugunta ta fada a fili kamar mai magana da wani

"Hoo, ai ko zaku tafi tsirara sai ka yi min yanda nake so dan rainin hankali."

Sannan ta kirawo shi ta yi masa godiya. Ta yiwa wanda ta turawa kudin waya don ya kawo mata waya wadda kudinta 102k ne ya hado mata da canjin kuma ya karbi wayarta wadda babu abinda tayi ya sayar mata.

Haka ya wuni a office yana tufka da warwara domin gobe Juma'a kuma goben ya kamata ya je Zariya amma baya son batawa Fatima rai yace ya fasa, sai faman bitar kalmomin da zai lallasheta da su yake yi saboda yanzu har wani tsoron bacin ranta yake yi. Idan yace zai je gobe to gaskiya bashi da isassun kudi gara ya bari watakila zuwa Lahadi ya samu.

Ga Jamila kuma da yake ta tunanin yanda zai yi ya gaya mata ba zai iya bata kudin event center ba, domin itama gobene tace za a tura musu kudin.

Sai bayan la'asar ya shirya zai fito daga office ya tafi gida, har ya dauko jakarsa ya tuna gara ya kirawo Fatima ya tsarata tun yanzu don ta san ba zai zo gobe ba. Domin idan ya je gida so yake ya mayar da hankalinsa wajen lallaba Jamila, tunda duk inda yake jin zai sami kudi ya buga amma bai samu ba.

Ba tare da wata damuwa ba Fatima ta yarda yayi zamansa gobe, in ya so kamar yanda ya fada ranar Lahadi ya zo. Don haka abubuwa sun masa sauki, ya nufi gida yana tunanin yanda zai yi da Jamila.
__

Sai da ya gama cin abincin dare sannan ta sameshi a falon sama, yana zaune a kan kujerar zaman mutum uku rike da remote yana kallo. Ta karasa ta zauna a jikinsa tana murmushi

'Sannu da zuwa.'

Ya amsa yana dubanta

'Yauwa.'

Ta mika masa 'yar karamar takardar dake hannunta tana fadin

'Ga account din me event center sai ka tura mata 120k din yau zuwa gobe.'

Ya sa hannu ya karbi takardar yana yake

'Ummm! Kin san ma duk na kashe kudin.'

Tayi gajeran murmushi

'Ai kuwa dai kai ake jira.'

Ya dan kawar da kai yayinda ya ajiye takardar a gafensa, tayi shiru tana binsa da kallo tana sauraron abinda zai ce. Ya kalleta suka hada ido ya kawar da kansa ya sake bata rai sannan yace

'Kin gane ko? Gaskiya hakura za ayi da event center din nan, kuyi taron nan a gida don gaskiya yanzu ko dubu ashirin babu a hannuna.'

Nan da nan ta tsuke fuska, ta muskuta ta gyara zama ta yanda zata dinga kallon fuskarsa ta dafe kirji tace

'Ban gane me kake nufi ba kayi min bayani.'

Cikin yanayin na ko-in-kula yace

'Kina dai kallon yanda na kashe kudi, tun kafin ki haihu ake abu daya. Dama wasu kudi na sa rai zan samu kuma zuwa yanzu basu shigo ba, wanda zai turo min kudin ma baya kasar.'

Ta sake gyara zama ta galla masa harara, cikin dacin rai tace

'Amma dai wulakanci ka shirya yi min ko? Ya za ayi don tsabar wulakanci saboda ka nunawa duniya ban isa ba shine zakace baka da kudi. Da can ka san baka da kudin ka sa nayi magana da mutane ana son ayi booking hall sun hana saboda ni kuma yanzu kace baka da kudi.'

Shima ya fara hasala ya dubeta ta gefen ido yace

'To bani da shi satowa zanyi na baki, shi sunan ce miki akayi idan ba a yi a event center ba an sabi Allah ne?'

Hawaye ya fara bin idonta saboda bacin rai, har wani hayaki take ji yana tasowa daga kirjinta, tace

'Bana son wulakanci Mukhtar, bana son wulakanci! Ka bani kudin nan na sallami mutane. Na riga na gama gayawa mutane za ayi taro a event center amma kace min ga zance ga magana?'

'To yanzu ya kike so nayi miki? Na gaya miki bani da kudi. Duk ma wanda kika gayawa ki koma ki gaya musu a nan za ayi, ba shi ke nan ba ai dai an yi suna ko?'

Ta share hawaye tare da zuke majinar da take neman fito mata daga hanci yayinda shi kuma ya mayar da hankali a kan kallon TV din da yake yi. Kallonsa kawai take tana hawaye ta ma rasa me zata ce. Da kyar ta bude baki cikin shesshekar kuka tace

'Da can me yasa ka sa min rai ka san ba zaka biya min ba, idan kana so ai ko bashi zaka ciyo ka bayar amma don wulakanci kake wannan maganar.'

Da mamaki ya juyo ya kalleta

'Bashi? Saboda sunan zan ciwo bashi? Lallai baki da hankali.'

Ta dan ja baya da mamaki tace

'Oh! Bani ma da hankali ashe ko? Da yake nice nayi alkawarin na saba ai dole kace bani da hankali.'

Tayi kwafa ta tashi ta fice daga falon cikin sauri tana tafiya kamar zata kifa. Dakin kasa ta dawo inda a nan take kwana tunda ta haihu, ta fada kan gadon ta rushe da kuka. Bata jima da shiga ba Inna ta shigo da goyon baby a bayanta ta karasa ta taba kafar Jamilan tace

'Ki tashi ki ci abinci Jamila , ga tuwo can na sauke kije ki kai masa nasa kema na kawo miki ki ci dare yana yi.'

Tana juyowa suka hada ido da Inna ta sake rushewa da Kuka, da hanzari Inna ta matsa ta zauna a kusa da ita ta dafata

'Subhanallah! Me ya faru kuma wannan kuka haka kamar wadda aka yiwa mutuwa.'

Nan ta gayawa Inna abinda ya faru. Tana rufe bakinta Inna ta dauke hannunta da ta dafata dashi tana mata kallon mamaki tace

'Au! Yanzu wannan shine dalilin da yasa kike wannan kukan. Naga dai ba sunan aka fasa ba, gidanki ma gashinan ai ya fi event center din kyau.'

Cikin shasshekar kuka tace

'Inna Wannan ai wulakanci ne yanzu me yake so na gaya mutanen da na cewa za ayi suna a event center?'

'Sai kice musu an fasa su taho gidanki, idan ba zaki iya ba ki bani ni na gaya musu.'

Haka Inna tayi ta lallabata tana bata hakuri sannan daga baya taci tuwon, amma na Mukhtar cewa tayi bazata kai masa ba. Dole Inna ta tura Nurain ya kai flask din tuwo ya dawo ya dauki na miya sannan ta bashi plate da cokali ya kai.

KARSHEN BABI NA ASHIRIN DA HUDU.

MATAR MUKHTAR

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA ASHIRIN DA BIYAR

25
Tun daga wannan lokacin Jamila ta daina kula Mukhtar, hasali ma tun ranar alhamis din da ya sanar da ita ba zai biya kudin event center ba har kawo yau ranar Lahadi bai sake ganinta ba. Saboda Inna tana gida ya daina shiga inda take don mafi yawan in lokuta suna tare, ita kuma bata sake nemansa ba.

Tun safe da ya tashi yake shirin tafiya Zariya wajen Fatima, domin a yanda yake ji ba zai iya wuce yau bai je ya ganta ba. Sai da ya gama shiryawa tsaf ya sa kayansa sannan aka kirawo shi daga office, akwai report na wani aiki da office din suka yi ana so ya je yanzu da report din a kai gidan gwamnati.

Babu yanda ya iya don haka ya dauko computer dinsa ya kunna, akwai teburinsa na karatu a falon saman wanda yake daidai kusa da kofar dakinsa. Nan kan teburin ya zauna ya fara aiki don bai ma gama rubuta Report din ba.

Ita kuwa Jamila tana dakinta na sama, zuwa yanzu duk wanda ta gayawa suna ta kirawo su ta sanar da su an fasa don haka babu taro. Ta kudire a ranta ta fasa yin taron tunda yayi mata haka.

A kwance take yayinda baby Halimatu take bacci a gefenta wayarta tayi kara, tana dagawa taga Aminu, wato kanin Mukhtar. Bayan sun gaisa yace

'Ina falon kasa, megadi yace min kuna nan amma naji gidan shiru shi kuma Yaya na kirawo shi wayarsa busy. Kice masa Baba ne ya aikoni.'

'Ayya, duka muna sama. Inna ma yanzu ta fita ni da baby ka ganmu bacci muke. Bari na turo maka shi.'

Ta ajiye wayar ya tashi domin ta kirawo shi, ta san dai ba zai wuce dakinsa ba tunda bata ji fitar motarsa ba. Akwai kofa a cikin dakinta wadda zata kaita dakinsa don haka ta nan ta bi, babu kowa a dakin sai dai ta jiyo motsinsa a teburin karatunsa da alama waya yake ko kuma wani abun ya kunna a computer yake saurara.

A hankali ta karasa bakin kofar ta riga ta saita fuskarta a fushi don sakon kawai zata gaya masa ta fita ba wai ta huce bane. Tana matsowa zata tura kofar wadda take a bude kadan ta jiyo maganganunsa a waya yana yi cikin nishadi

"Haba Baby na, ai kin san dole ne nazo na ganki tunda ranar Juma'a ban zo ba. Ba zan iya jure rashin jinki da ganinki ba shi yasa na turo miki kudi kika sayi wayar nan da gaggawawa."

Ya dan yi shiru yana sauraro

"Eh mana, ai yau dole na zo idan ba so kike zuciyata ta daina aiki ba."

"Ah ke da kike jira nazo muyi selfie a sabuwar waya?"

Bata san me aka gaya masa ba ya kyalkyale da dariya

"Kina ji ko Baby, bari nayi sauri na gama aikin nan ko na samu na taho, kin san fa Zariya da nisa duk da dai garin masoyi baya nisa."

Cikin zafin nama ta banko kofar ta shigo ta tsaya a gafen teburin wanda yake manne da jikin bango, hannunta yana kan kwankwasonta tana jijjiga kafa tana masa kallo me cike da masifa.

Yayi wuf ya katse wayar, bai zata zata shigo ta nan a yanzu ba musamman da yake ta kwana biyu rabonta da sashin nasa.

A tsiwace tace

'Wace 'yar iskar karuwar kake magana da ita? Wato dama ba kudine baka da shi ba kwashewa kayi ka bawa karuwa kawai saboda ta buda maka tsakanin cinyoyinta ko? Shi yasa ka kashe min...'

Ya mike tsaye a fusace ya nunata da wayar da take hannunsa kirar Samsung mai tsadar yace

'Ke wai me yake damun kanki ne? S...'

A fusace ta fizge wayar hannunsa ta maka ta da bangon da yake bayanta iya karfinta, ya dora hannusa a ka ya bude baki a dai-dai lokacin da wayar wadda ko batirinta ba a cirewa ta tarwatse tayi dai-dai. Cikin zafin nama ta cakuma kwalar rigarsa tana magana tana huci

'Ni zaka kawowa bariki har cikin gida? To wallahi baka is....'

Ya fizge hannunta daga wuyansa wanda yayi sanadiyyar zubewar maballan rigarsa a kasa, ya daga hannu ya kwada mata mari . Ta saki kara tare da dafe kuncinta, yayinda Nana wadda take bacci a kan kafet din falon ta farka da kuka a gigice. Nan da nan Nurain wanda ya buya a bayan kujera tunda suka fara fadan ya fito ya rungumeta yana kokarin toshe mata baki.
Mukhtar ya juya da sauri ya nufi su Nana. Iya karfinta ta sa hannu ta fincikoshi har ya doke kujerar da ya tashi

'Ni zaka bari a tsaye, ka cuceni ka mareni sannan ka barni a tsaye? Wallahi baka isa ba Mukhtar kayi kadan. Mazinaci, macuci algungumi kawai.'

Ya daga hannu zai sake marinta cikin zafin mama ta rage tsawo ta sa karfi ta bangajeshi yayi baya kamar zai fadi, cikin karaji tace

'Kai ka isa ka sake marina? Wallahi wanda kayi ma ka ci bashi kuma da kai da duk wata karuwa da kake nema sai na mayar daku kalar kwatance a garin nan.'

Ya rasa ma me zai ce mata, da kyar ya samu ya tsaya. Ta juya a fusace zata fice daga dakin sai kuma ta yiwo taku biyu baya ta kaiwa computer dinsa cafka, cikin zafin nama ya tureta gefe ta tafi ta fadi a kusa da kujerar zaman mutum biyu tana huci.

A dai-dai lokacin Aminu ya shigo Nuraini yana biye da shi yana buya a bayansa; wanda Nurain ne yaja Nanan suka fice don su kirawo Inna suna saukowa suka ci karo da Aminu don haka Nurain ya ja shi sama yayinda Nana ta buya a bayan kujera tace ita ba zata koma ba.

Ta taso da hanzari daga inda take zube ta nufo Mukhtar din da sauri, Aminu ya kara hanzari ya riketa domin ya ga lokacin da Mukhtar din ya tureta. Yayi wuf ya cafke hannunta yace

'Haba Anti yi hakuri mana.'

Sai a lokacin ta gane an shigo wajen, tana hada ido da Aminun kuma ta fisge hannunta ta hada duka hannuwa biyun ta dora a ka ta zube kasa tana faman rusar kuka.

Ya karasa kusa da Mukhtar din yana fadin

'Yaya lafiya kuwa? Kun firgita yara kuna ta hayaniya. Kayi hakuri mana Yaya.'

Ya kalli Aminun da jajayen idonsa yayi kwafa sannan yace

'Menene?'

'Baba ne ya aiko ni na kawo rago, gashi can har maigadi ya daureshi.'

Dama haka Baba yake musu, idan an yi maka haihuwa ko ka sayi rago to shima sai ya bada nashi saboda yana da dabbobi da ake masa kiwo a kauye.

Bai ce komai ba ya wuce Aminun ya tsuguna a gaban wayarsa wadda ta fashe, ya bi wajen da kallon takaici. Aminu ya karaso ya tsaya a kansa ya leka abinda yake dubawa.

'Subhanallah. Fashewa wayar tayi Yaya.'

Ya mike tsaye ba tare da ya dauki komai a wayar ba ya bi ta gefen Aminun yana fadin

'Ka cewa Baba nagode, zan zo da daddare.'

Ya tattara computer dinsa da karamar wayarsa ya shige dakin, yana shiga ya sakawa kofar mukulli ya karasa ya kulle wadda ta shigo daga dakin Jamilan ya ajiye computer a kan gado ya zauna ya saka tafukan hannuwansa ya rufe fuskarsa zuciyarsa tana suya. Gaba daya kwakwalwarsa nema take ta daina aiki, kansa ya cunkushe ya ma manta da cewa ana jiransa me ya kai report office za a kaiwa gwamna.

Shi kuwa Aminu yana saukowa Nana ta makale a jikinsa ta sa kuka sai ya kaita wajen hajiya, ya dauketa ya sakata a kafada. A dai-dai nan Inna ta shigo da sallamarta bayan ya gaisheta ya gaya mata daga gidan su Mukhtar yake sako ya kawo. Ta miko hannu zata karbi Nana tana fadin

'Yaki nan gotai gotai dake Uwar masu gida ake daukanki.'

Ta kara kankameshi, ya dubi Inna yace

'Rigima take ji wajen Hajiya zan kaisu.'

Yayi mata sallama ya fice da yaran.

Inna Bata hawa dakin Jamila na sama don haka da bata ganta a kasa ba sai ta cigaba da harkonkinta ta san itama idan ta gama abinda takeyi zata sauki.
...

Aminu yana shiga gida ya wuce falon Baba inda yayi sa'a ya tarar da Hajiyan ma a can. Ya mika mata Nana wadda ta riga ta fara bacci, ta rugumeta yayinda ita kuma Nanan ta bude kumburarrun idanuwanta ta kalli fuskar hajiya tace

'Hajiya.'

'Na'am kawata, kuka kika yi ko?'

Ta daga kai alamar e sannan tace

'Bazan koma gun Mommy ba a wajenki zan dinga kwana ko Baba Aminu ya kai ni wajen Mama.'

Hajiya ta kula da baccin da yake fizgar Nanan don haka ta rungumeta tana fadin

'Shikenan a nan zamuyi zaman mu kawata.'

Baba ya dubi Amin wanda yake zaune a gaba Baban yana ta muzurai yace

'Ina Jamilan?'

'Tana sama ai inaga dai bacci sukeyi don tun fitarka basu sauko ba.'

Kafin ta rufe bakinta ya shige cikin corridor din da zai kaishi saman. Ta karasa ta zauna a kujerar da take kusa da wadda Aminu ya zauna tana dubansa tace

'Lafiya dai ko? Na ga kamar da matsala.'

Yayi murmushin yake yace

'Lafiya kalau in sha Allah. Maganin da ake bawa Nana aka ce a karbo don a cigaba da bata.'

Ta yamutsa fuska ta jingina da bayan kujerar da take kai

'Ni dai wallahi da ma zaku kyaleta da maganin nan, maganin mura ne kuma ta daina murar yarinyarda kullum hancinta yake a bushe. Tunda na zo gidan nan nace a daina bata ta warke uwar tace min wai haka likita yace a bata na sati biyu don haka dole sai an bata. Murar yaro wallahi ba wani abu bace idan an barta kwana biyu warkewa takeyi gara ma ka bawa yaro zuma kawai. Don Allah ku barta da maganin nan wallahi ba wata mura.'

Cikin yanayi na mamaki Aminu ya jijjiga kai yace

'In Sha Allah zan gayawa Hajiyan don ita bata ma san na mura bane ta zata na zazzabi ne, na san ita ma bazata bata ba.'

'Yauwa ko kai fa.'

Kafin suce wani abu suka jiyo amon muryar Mukhtar daga sama ga dukkan alamu fada yakeyi. Suka dan kasa kunne, har yanzu hayaniyarsa suke jiyowa domin da ya hau a kwance ya sameta a kan gadon kuma tunda ya shiga dakin yake tambayarta ina maganin da take bawa Nana tayi masa shiru, duk wannan hayaniyar da yakeyi sau daya ta kalleshi ta koma ta cigaba da kwanciyarta taki ce masa komai.

Da gudu Aminu ya mike ya haye saman yana tsoron kada ya sake kai mata duka, a take Inna tabi bayansa don duk wanda yaji muryar Mukhtar din ya san fada yake.

A tsaye yake a gaban gadon da take kwance, yana jin shigarsu ya juyo ya dube su idanunsa sunyi ja wur ya hada hannuwansa biyu ya shafi kansa da su yana fesar da iska. Inna ta ture Aminu ta karasa cikin dakin ta doki kafar Jamilan ranta a bace tace

'Wai wane irin iskanci ne wannan ba dake yake magana ba kina kwance kina ji.'

Ta mayar da dubanta ga Mukhtar din tace

'Me yake faruwa ne?'

'Magani zata bani wanda take bawa Nana shine

08, January 2025
Nafisa

I cant download the book

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login