Showing 81001 words to 84000 words out of 92582 words

Chapter 28 - MATAR MUKHTAR COMPLT

SAKINA   

16 Aug 2024

7151

sani ba ta kirawo shi to sai tijara. Don kafin sunan Halimatu ma da taji yana waya da mace a kan ya saya mata wayace ni ko computer wallahi fizge wayar tayi a hannunsa ta buga wayar nan da bango wayar nan ta tarwatse sai sabuwa ya siya.'

Abba ya dubi Jamilan da takaici; wadda kawo yanzu hawaye ya gama wanke mata fuska saboda bata da kalaman da zata kwaci kanta, domin duk abubuwan da Inna take fada ta aikata amma ta san ba za a bata dama ta kare kanta ba; yace

'Wai ko kina hauka ne Jamila? Haka ake zaman auren. Shikenan don yana aurenki ba zai yi hulda da kowacce mace ba? Kin san kuma yana kasuwancinsa?'

Abdallah yace

'So take idan mata sun zo siyan computers yace musu matarsa ta hana maza kawai yake siyarwa.'

Abba ya cigaba

'To ai kuwa ba zai yiwu ba, ki ma gayawa kanki gaskiya. Ga iyayenki nan ki tambayesu, koda yake kema da wayonki kina ganin yanda mata har nan suke zuwa kuma iyayenki su bamu waje mu tattauna saboda yanayin aikina. Baki taba jin wadda ta yi wata fitna ba muma babu wadda ta bincika min waya har na gama aiki lafiya. Wayar mutum kuma ai sirrinshi ce don me zaki bincika masa waya har kina kafa hujja da binciken da kika yi?'

Ya danyi shiru, Inna tace

'Kwarai kuwa, yiwa miji bincike shine silar duk wata matsala idan kuma baki daina ba zaki shiga cikin matsala sosai kuwa.'

Haka dai aka karewa Jamila fada babu ma wanda ya saurareta balle tayi bayani, daga karshe Abba yace idan Mukhtar din ya zo daukanta yana son ganinsa, ita kuma ya gaya mata ta zama cikin shiri idan mijinta ya zo zasu tafi kuma kada ya sake jin wata magana idan ba haka ba ranta zai baci.

Haka ta fito daga falon tana share hawaye, suna komawa dakin Umma tace

'Ki daina kukan haka, kuma kinga ai da baki bincika masa waya ba da kina nan hankalinki a kwance amma kika je kika ganowa kanki abinda zai hanaki zaman lafiya.'

Ta share hawayenta ta dubi Umman

'Umma, yanzu ashe idan mutum yaji ciwo a yatsan kafarsa sai ace ya daina kallon ciwon? Kawai ya rabu da ciwon ba sai ya je asibiti ba ba sai ya sha magani ba ai in bai ga ciwon ba ba zai ji komai ba. Kin san kuwa mutum yana nan zaune ciwon man zaiyi ta cin jikinsa karshe ya ja a yanke kafar ko ma a rasa rai. Wannan fa shine kwatankwacin abinda kuke so nayi. Mijina wani jigo ne a rayuwarta, yana aikata zina ana cewa wai na kauda kaina. A lahira ina son mu shiga Aljannah ni da shi, idan ya mutu yana zina akwai yiwuwar ba zai shiga Aljannah, ba a duniya kuma ya saka ni cikin kunci bayan cututtuka da yake debowa yana shafa min daga wajen matan banza. Meye laifina idan nayi magana Umma? Amma tunda haka kuke so in sha Allahu ba zan sake maganaba, sai dai ki gayawa Abba idan bai saka min cutar da zata kasheni ba to tabbas depression zai kasheni.'

Ta share hawayenta ta kama hannun Umman ta cigaba

'Kiyi min addua Umma, kada Allah ya jarrabi yarana da irin wannan fitnar. Kinga na fara da mace, ki dinga yi min addu'a Allah ya katangeta idan kuma maza Allah ya bani ma to Allah ya hanasu daukan dabi'ar mahaifinsu.'

Ta mike ta shige daki ta bar Umma zaune a falo.

Tana tausayin 'yar tata, tabbas ta san abubuwan da take fada gaskiyane ta yarda Mukhtar din yana neman mata amma bata da yanda zatayi a kai musamman bayan wannan zantuka da Inna da Abdallah suka kawo, wadanda kuma Jamilan bata musa ba.
------

Duk yanda yake tunanin idan yaje Lagos zai huta ya sami nutsuwa ba haka ya kasance ba. Gaba daya ma ya kasa jin dadin taron, dare biyu ne kawai suka kwana da Felicia a dare na uku ya sallameta don baya cikin yanayin da zai iya yi mata wani abu. Haka aka karasa taron nan da shi a daddafe, ana gama taron ranar Alhamis ya biyo jirgin Juma'a da safe ya dawo Kano ba tare da ya kara kwanakin da yayi niyya ba.

Karfe goma na safe jirginsu ya sauka a Kano, daga nan ya dauki shatar tasi zuwa gida. Kayansa kawai ya ajiye ya wuce gidansu, a can ya zauna har lokacin masallaci.

Tare da Baba suka je masallaci suka dawo, ko da suka dawo a falon Hajiya ya zauna inda ya sameta tana cin abinci. Yana zama hajiya ta saka aka kawo masa abinci, yana cikin cin abincin bayan ya hadiye lomar da take bakinsa yace

'Hajiya.'

Ta ajiye kofin da ta sha ruwa tace

'Na'am.'

'Hajiya na je gidansu Safiyya fa.'

'To ma sha Allahu, wani abun ya faru ne a gidan nasu.'

'A'a. Na dai je ne don mu sake aure da ita.'

Nan da nan fara'arta ta karu, ta harareshi tace

'Da kaji wuya ko? To Allah ya sa dai bata sami wani bazawarin ba.'

'To bata dai amsa min ba amma dama na san zai dan dauki lokaci tunda ranta a bace yake. Shima Yayanta na sameshi a office na sanar dashi, yanzu kuma in na tashi zan je gidan Baban Hotoro tunda shine waliyyinta.'

'Ka dai ji kunya wallahi, shekaru kusan uku baka tashi maida auren ba sai yanzu. Allah ya saka su saurareka ita da iyayen nata.'

'In sha Allah zasu saurareni Hajiya, ke dai ki cigaba da addu'a.'

'Hmm! Ka dai ji kunya. Kuma ka gayawa Baba?'

'A'a. Bari nayi sai mun gama dadaitawa tukunna kin san in ya ga dama yanzu zai bata min rai, kwanaki fa cewa yayi Allah ya bata mijin da ya fini.'

'Hm! Ka kaisu idan kaya ne!'

Nan ya zauna har akayi sallar la'asar, yana fitowa daga masallaci ya shiga motarsa ya kama hanya. Safiyyan yake son gani amma gara ya fara zuwa gidan Baban Hotoro ya shigar da gaisuwarsa in ya so idan ya gama sai ya tsaya gidansu Safiyyan; duk da bata san da zuwansa ba tunda ta daina daukan wayarsa.

Cikin nishadi yake tukinsa har Hotoro, ba tare da wata matsala ba aka yi masa iso falon Baban Hotoro inda ya sameshi a zaune yana hutawa. Bayan sun gaisa suka dan yi shiru, shi Baban Hotoro yana sauraron Mukhtar yaji abinda ya kawo shi yayinda shi kuma Mukhtar din yake tunanin ta inda zai fara.

Ya danyi gyaran murya yace

'Dama Baba zuwa nayi na sanar da kai na sami Safiyya munyi magana a kan zamu mayar da aurenmu; duk da dai bata amsa min ba amma in sha Allahu ina sa ran zata amsa. Kuma dama ina so nazo na baka hakuri a kan abubuwan da suka faru, kuskure ne kuma in sha Allahu ba za a sake samun hakan ba.'

Baban Hotoro ya gyara zama yana masa kallon mamaki, yace

'Ikon Allah, Safiyya dai tawa?'

'Eh ita Baba.'

Ya bashi amsa shima yana mamakin tambayar.

Baban Hotoro yayi gyaran murya yace

'Toh ai Safiyya wancan satin aka kawo kudin aurenta.'

Ya nuna jikin bango inda aka ajiye kayan lefen Safiyyan ya cigaba

'Kaga kayan aurenta can gaba daya komai an kawo an sa rana sati sha biyu, kaga yau saura sati goma sha daya kenan. Kuma in dai ba na gamu da makuwa ba to ba kaine kankawo kayan ba.'

Ya daga idonsa ya kalli kayan, ya sunkuyar da kai domin ya kasa hada ido da Baban Hotoro. Kokari yake ya hadiye malolon da ya tokare masa makogoro ya nemo harshensa amma ya kasa. A take gumi ya rufe shi, ya cire hularsa ya ajiye, ya sake kallon kayan ya dubi Baba yace

'Uhmm, ai ban sani ba da yake nima na dan yi tafiya yau na dawo.'

'To ai kuwa an gama maganar Safiyya wannan yaron da ya kawo kaya in sha Allah shi zan aurawa ita idan lokaci yayi. Don haka sai dai nace kayi hakuri a halin yanzu ka rabu da Safiyya tunda kaga musulmi muke kuma addininmu ya hana neman aure cikin nema.'

Ya mayar da hularsa ya bude baki da kyar yace

'Uhm, Nagode.'

Yayiwa Baba sallama ya fice, Baban ya bi bayansa da kallo bayan ya fice yace

'Kaga mutum kamar dan wasan kwaikwayo, shekara uku kana yawonka a gari baka mayar da auren ba sai yanzu rana tsaka kazo wai ayi hakuri.'

Nan takeya dauki waya ya kirawo Safiyyan, bayan sun gaisa ya tambayeta me ke tsakaninta da Mukhtar. Bayan ta gama yi masa bayani yace

'Kina jina ko, kinga wannan mutumin Abdurrahman da ya kawo miki kayan aure? To matukar da ni da ke muna numfashin in sha Allahu babu abinda zai hana na daura miki aure da shi idan ranar tayi, don haka ki fita batun Mukhtar. Kada naji kada na gani ace min kina sauraronsa kin ji na gaya miki.'

'To Baba, dama na gaya masa ai.'

'In banda ma rashin kunya sai yanzu ya tuna damu ya san ya kamata ya zo ya bamu hakuri, to mun bashi auren bamu ji dadi ba don haka ba zamu sake ba. Itama Umman naki zan zo na sameta.'

Sukayi sallama suka ajiye waya.
------

Saida ya dauki lokaci a mota yana kokarin dawo da nutsuwarsa kafin ya tuka motar ya bar kofar gidan Baban Hotoro.

A halin yanzu ba zai iya zuwa wajen Safiyya ba don haka ya karkata motar ya nufi gida, gashi da niyyarsa idan ya gama gidansu Jamila zai wuce ya daukota amma yanzu babu abinda zai iya don haka kawai ya wuce gida.

Bai taba tunanin akwai wanda zai yi masa shigar sauri haka ba, daga tafiya Lagos na kwana biyar har an kawo kayan aure harda sa rana. Yanzu wani ne zai auri Safee?

Ya dafe kansa da yake neman tsagewa saboda ciwo; gaskiya ba zai bari wani aure Safiyya ba, duka yanda za ayi ya janyo ra'ayinta ta aureshi zai yi kafin sati goma sha dayan nan.

KARSHEN BABI NA TALATIN DA BIYAR.

MATAR MUKHTAR

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA TALATIN DA SHIDA

36
Har dare yayi bai ji ya dawo cikin nutsuwarsa ba don haka haka ya hakura ya kwanta ba tare da ya dauko Jamilan ba. Sai da gari ya waye bayan la'asar sannan ya tafi ya daukota.

Saida Abbanta ya sa su a gaba ya dauki lokaci yana yi musu nasiha, ya nunawa Mukhtar din ya daina yin abinda zai kawo zargin tsakaninsa da matarsa.

Sukayi sallama suka kamo hanyar. Har suka iso gida Jamila batace dashi komai ba, sai dai shi da Halimatu yake ta wasa tana masa gwaranci. Suna shiga gidan kafin ya hau saman ya sauko har ta fara kokarin gyara gidan, don haka yana saukowa ya dauki Halimatu yayi mata sallama ya nufi gidan Hajiya da Halimatun.

Tunda ya shiga gidan Hajiya take tambayarsa ya taga yayi zuru-zuru, yace mata babu komai. Sai da ya sameta ita kadai sannan yayi mata bayani har an sawa Safiyya ranar aure, ta dubeshi tace

'Ikon Allah, kayi wasa gashi gar wani zai shiga tsakaninka da ita. Allah ya sa haka ne yafi alkhairi.'

Yayi shiru, jimawa kadan yace

'Hajiya da ma ki sa baki, ai ko ba don ni ba ta dawo don yaran ta ko? Watakila idan kikayi mata magana ko kuma Ummanta za su saurareki.'

'Saboda me zan yi mata magana Mukhtar, kana tausayin yaran ne kai? Ai baka tausayinsu. Babu wanda zan yiwa magana kada ma ka sake min wannan maganar. Idan ita da kanta ta amince shikenan ina murna, amma yadda kayi saki ba tare da ka shawarceni ba haka ma zaka koma ka tsarota kai kadai.'

Nan ta ta shi ta fice ta barshi a falon yana cin abinci.

Haka ya fita ba tare da ya sami abinda yake so ba, don shi ya zata Hajiya zata yarda ta sa baki.
.............

Kamar yanda Jamila tace zata kawar da kai daga abubuwan da Mukhtar yake yi hakan tayi, don tunda ta dawo gidan bata wani shiga harkarsa ba. Sai dai hakan baiyi masa dadi ba. Duk wani abu na hakkin aure tana yi masa kuma tana kwana a dakinsa, amma ta rage hira da shi sosai kuma duk wata kulawa ta musamman ta ja baya. Ya dai kyale haka ne saboda yanzu hankalinshi yana kan fafutukar yanda za ayi Safiyya ta dawo, don haka ya bawa Jamilan lokaci yana jira ya san zata dawo normal.
------

Duk wata hanya da zai bi yaga Safiyya ta gagara gashi yana lissafe da bikinta yanzu saura sati tara. Ya kasa hakura da ita don shi sai yanzu ma ya san yana sonta.

Daga aiki ya dawo ya ci abinci ya dan koma daki ya kwanta, har bacci ya fara daukarsa ya tashi kamar wanda aka tsikari. Ba zai iya hakura da Safiyya ba gara yaje gidan nasu ya gani, watakila zata saurareshi. Don haka ya tashi ya shirya ya fito.

A falo ya sami Jamila tana kallon TV yayinda Halimatu ke wasanta a falon.

'Na fita.'

Cikin halin ko in kula irin wanda take masa tunda ta dawo gidan tace

'A dawo lafiya.'

Ya amsa ya nufi kofa, har ya kusan fita ya dawo, ta bishi da kallo ya tsaya a kusa da kujerar da take K
kai yace

'Wajen Safiyya zan je, na gaya miki zan mayar da aurenta.'

'Allah ya bada sa'a.'

Ya kula da yanda take amsa masa don haka ya sa kai ya fice.

Tun kafin ya isa gidan yake mata waya amma bata dauka ba kamar yanda ta saba. Ba karamin dadi yaji ba da ya hango Sabir a kofar gidan ko ba komai ya sami mai kirawo masa ita.

Yana tsayawa da mota ya ga Sabir din bai taso ba don haka sai ya fito daga motar ya nufi Sabir din wanda yake zaune a kan benci shi da abokinsa. Ya mika musu hannu suka gaisa ya dubi Sabir din yace

'Sabir Safiyya fa, tana nan?'

'No, bata nan ta fita tun dazu.'

'Ikon Allah, gashi ina tayi mata waya bata dauka ba.'

'Eh, inaga tana busy ne.'

Yayi shiru, jim kadan yace

'Umma fa? Tana nan na gaisheta.'

'Itama bata nan.'

Ya sake yin shiru na dan lokaci, sannan yace

'Kuma ba yanzu Safiyyan zata dawo ba?'

'Eh gaskiya ina jin sai dare.'

So yake ya tambayi inda taje don yaji ko zai iya binta, amma ya kula da yanda Sabir din yake ta faman cin magani don haka sai kawai ya karbi lambar wayar Sabir din yana tunanin idan ya kirawota ta ki dagawa sai ya kirawo Sabir din ya hadasu. Yayi masa sallama ya kama hanya.


......

Sai da ya kwana biyu yana kiran Sabir amma shima ya ki dagawa, shi kuma so yake yayi magana da ita don ya tsara kalaman da yake jin zasu lausasa zuciyarta.

Don haka kafin ya shiga office sai da ya sayi sabon layin GLO, yayi rijista ya sa isasshen kati. Yana zama a office ya rufe kofa ya dannawa Safiyya kira da sabon layin.

Bata je makaranta ba saboda Umma tana zazzabi don haka ta dauki hutun kwana biyu don ta zauna da Umman.

Tana zaune a falo yayinda Umman take bacci a dakinta kiran ya shigo, da yake iyayen dalibanta sun saba kiranta idan da wata matsala tana ganin lambar sai ta zata irin haka ne. Da sallama ta amsa wayar, sai dai yana amsa sallamar ta gane wanene don haka ta mike ta koma dakinsu.

Bayan sun gaisa yace

'Safiyya kika ce ba zamu yanke hulda ba amma na fi sati biyu ina kiranki ba kya dagawa.'

Cikin halin ko in kula tace

'Watakila lokacin da kake kira bana kusa. Ya yaran ya su Hajiya?'

'Lafiya kalau Alhamdulillah.'

Suka dan yi jim, sannan ya cigaba

'Safiyya shine baki gaya min an sa miki ranar aure ba?'

'Oh, ai bamu hadu ba tun lokacin amma ai yanzu gashi kaji.'

'Uhm hakane. Yanzu Safee wani zaki aura ba ni ba ina nan da raina da lafiyata.'

Tayi wata 'yar dariya sannan tace

'Naga dai nima da raina da lafiyata ina nan kayi aurenka gashi nan kana morewa, nice bai kamata nayi haka ba saboda ni ban san dadin auren ba ko kuwa?'

'Hakane. To amma yanzu Safiyya kina ganin akwai matar da zan aura ta kula da su Nurain sama dake, ko ba zaki aureni saboda ni ba ai ya kamata ki duba yaran nan ko? Ko yanzu ma da suke wajen Hajiya ke kin san ba Hajiya suke bukata ba ke suke bukata saboda ke ce uwarsu. Kina ganin yanda Jamilan ta yiwa Nana. Don Allah Safiyya ki dawo wajen yaranki, ko ba zaki dawo don ni ba ki duba su mana.'

Maganar ta daki zuciyarta kuma itama abinda yake mata ciwo kenan; rabuwa da yaranta. Idan akwai abinda zai iya mayar da ita gidan Mukhtar din to yaran ne; don lokacin ma da ta ji Jamila tana bawa Nana maganin tari saida tace zata dauko Nana ko kuma ta rokeshi ya mayar da ita, Saida Sabir da Yaya Habibu suka sakata a gaba sannan ta hakura. Cikin sanyin murya tace

'Mukhtar, don Allah lokacin da zaka sakeni duk ba kayi wannan tunanin ba? Ka sakeni ka koroni? Ko ka manta da nace maka yara fa ce min kayi ai ba da su na zo ba ko? Shekarun nan uku Allah ne yake kular min da su ba wani mutum ba kuma na san Allah baya bacci. Amma ka makara, kuma kamar yanda na gaya maka ba zan sake aurenka ba in Sha Allah. Ka cigaba da kula da yaranka kamar yanda kakeyi bayan ka koroni, nima zan cigaba da yi musu addu'a kamar yanda na dinga yi a lokacin da ko kallo ban isheka ba.'

Ta tsinke wayar a take ta danna masa block.

Ta jefa wayar kan gado, hawayen

08, January 2025
Nafisa

I cant download the book

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login