Showing 12001 words to 15000 words out of 92582 words
bani English Education a BUK.'
'Kai ma sha Allah, nayi miki murna sosai kuwa. Sai ki dage ki maida hankali ki fita da points mai kyau, Allah ya sa albarka.'
'Amin Yaya, nagode. Bari na kirawo Yaya Hajiyayyaye.'
Kafin tace wani abu ta katse wayar saboda tsabar doki.
Dariya kawai tayi ta ajiye wayar a kan kujera, ba karamin dadi taji ba da Hamida ta sami damar yin degree. Da ita da Yaya Hajiyayyaye duka diploma ce da su, Yaya Habibu ne kawai me degree. Ita Yaya Hajiyayyaye ko JAMB batayi ba ma SSCE tana fitowa Abbansu ya nema mata diploma a Polytechnic ta Kano. Ita Kuma Safiyyan tayi JAMB har sai biyu ma mma makinta bai kai ba, ta tafi Kaduna gidan Baba Shehu kanin Abbansu kawai sai ya hadata da Sajida yarinyarsa ya samar musu admission a KADPOLY. Don haka a can ta zauna gidan Baba Shehu har ta gama diploma wato ND kuma tayi HND a fannin computer science. A can Kadunan suka hadu da Mukhtar ya je daurin aure ita kuma ta taso daga makaranta.
A da tana da niyyar ta koma tayi degree a nan BUK amma tana gama jarrabawar karshe aka yi bikinsu da Mukhtar, ita kuma bata sake tada zancen ba.
Babu wanda ya hanata haka kawai ta zabarwa kanta hakura da karatun domin tana ganin da ta gayawa Mukhtar din zai barta ta cigaba. Yanzu ma kuma tana ji a ranta idan ta sami dama zata yi masa zancen ko Allah zai sa tana da rabo ta koma tayi degree din.
Sai wajen karfe tara ya dawo lokacin yara sunyi bacci, tana zaune a falo tana kallon wani fim a MBC 2. Tayi masa sannu da zuwa ta karbi ledar hannunsa wadda ya siyo musu burodin safe yayinda shi kuma ya wuce dakin, da kyar ta dauke kanta daga kallon da takeyi ta dauki ruwa ta kai masa dakin.
Ajiyewa tayi ta fito tana kallo tana jera masa abincin dare, tana gamawa ta koma ta zauna ta cigaba da kallon. Tana jiyo fitowarsa ta hakura da kallon film din ta mayar tashar Aljazeera, ta riga ta saba indai yana zaune to ba a kallon fim saboda shi baya son fim daga labarai sai ball ko kuma wrestling. Idan ma ya zauna bata canza ba da kanshi zai dau remote din ya canza yana fadin
'Ana nan ana ta kallon shirme.'
Don haka ma ta riga ta hakura da kallon TV, da rana ta kunnawa yara da daddare kuma shi yayi nasa kallon.
Yana zama ta tashi ta zuba masa abinci, yana ci suna dan taba hira har ya gama.
Yana kwance a kan gadonsa da waya a hannunsa ta shiga dakin da sallama, bayan ya amsa sallamar tace
'Baka kwanta ba.'
Ya dubeta yace
'Sai dai niyya.'
Ta wuce daya gefen gadon ta kwanta tana fuskantarsa, jim kadan ya ajiye wayar ya kalleta yayi murmushi yace
'Kema ba baccin zakiyi ba ai kallo-kallo kika mayar da ni.'
Tayi dariya ta cigaba da kallon nasa, ya lakace mata hanci yace
'Gobe zamuje mu kai kudin auren Saifullahi.'
Murmushinta ya karu tace
'Kai ma sha Allahu, Allah ya sa albarka, Allah ya sa ayi damu. Saura Aminin Hajiya.'
'Wannan ai da saura, kin san Baba ba zai barshi ya yi aure ba sai ya gama bautar kasa ya sami aiki ya shekara yana yi tukunna.
'To Allah ya nuna mana ai kamar yau ne.'
Sukayi shiru shi ya cigaba da abinda yakeyi a wayarsa ita kuma tana kwance kawai tana tunani kala-kala. Jimawa kadan tace
'Habibi.'
Ya kalleta yace
'Ga ni.'
Tayi dariya tace
'Nima ga ni.'
Shima dariyar yayi yace
'Ina sauraronki.'
Ta mika kafarta ta fara sosa masa tafin kafa sannan tace
'Kaima da auren ka kara kawai.'
Maganar ta shammaceshi matuka har saida ya dan razana. Ya dubeta da tsananin mamaki ya ga hankalinta a kwance yake murmushi ma takeyi, ya jijjiga kai sannan yace
'Um! Haka nace miki ina bukatar karin wata matar?'
'A'a, haka dai na gani.'
Ya bata rai sannan yace
'To baki ga dai-dai ba.'
Tayi shiru kamar baza tace komai ba, jim kadan sai ta daure tace
'Wannan yarinyar da kayiwa birthday last week ai ko itama da ka aura ku huta.'
A fusace ya ajiye wayar dake hannunsa a kan durowar gado, ya tashi daga kashingidar da yayi ya zauna don haka itama ta mike daga kwance ta zauna tana kallonsa tana mamakin yanda ya fusata daga magana. Harararta yake yi yana magana a fusace
'Dole ki tsara min rayuwa tunda ke kika haifeni, shi yasa kika tura ana bibiyata saboda ki samu abinda za ki kafa min hujja da shi ko?'
'Ni ban tura a bibiyeka ba, ina gida aka turo min video din, kuma naga yarinyar itace wadda take turo maka hotunanta tsirara shi yasa nace kuyi aure ku huta da buya kuna sabon Allah.'
Ya kara fusata
'Shi yasa kika sakani a gaba zakiyi min rashin kunya ko? Kin..'
Ta katse shi a marairaice tana fadin
'Ba haka bane Abban Nurain, kaida Allah ya bawa damar auren mace hudu idan ka kara daya ai ba zai zama matsala ba. Aure ai shine cikar burin masoya, tunda kuna son juna ku cika burinku mana kuyi aure ku huta.'
'To tunda ke kika haifeni kiyi min auren dole mana?'
Ya fada a fusace. Ta sunkuyar da kanta sannan ta dago a hankali tace
'Allah ya baka hakuri, dama gani nayi...'
Da hanzari ya katseta a fusace
'Bana son jin abinda kika gani ki tashi ki fice min daga daki kafin ranki ya baci.'
Ta kalleshi taga yanda ya sha kuna yana nuna mata kofa, ta sunkuyar da kai ta share kwalla cikin sanyin murya ta fara kokarin mikewa tana fadin
'Allah ya baka hakuri.'
Ta fice ta barshi a dakin yana huci. Tana shiga dakinta ta turo kofar ta zube a bayan kofar, kafafuwanta sun kasa karasawa da ita kan gadonta.
'Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun.'
Bata taba tsammanin wannan maganar zata bata ran Abban Nurain ba domin ita ta zata son yarinyar nan yakeyi tsakani da Allah, kuma ta zata zai yi farin ciki da ta kawo wannan shawarar amma ya rufe ido yana mata fada. Itama bata so ayi mata kishiya amma da ya dinga bin mata a waje gara ya auro uku su hadu suyi zamansu.
Ta gyara zama a nan bayan kofar ta tankwashe kafa ta ja zanin jikinta ta goge hawaye, tayi ajiyar zuciya. Ta daga hannuwanta tana kai kallonta sama
'Allah Kai ne Allah, bani da wata dabara Ya Hayyu ya Qayyum Allah Ka kawo min mafita.'
Ta sauke hannuwanta ta share hawaye zuciyarta tana mata kuna saboda takaici. Jimawa kadan ta mike ta yiwa alwala ta zo ta tayarda Sallah, tun tana yi ba tare da ta san me take karantawa a sallar ba har ta fara samun nutsuwa. Kafin ta idar zuciyarta ta dan yi sanyi, tayi addu'ointa sosai, ta tashi ta sa yara a fitsari sannan ta kwanta.
.......
Ko da gari ya waye ma haka ya tashi yana fushi da ita don ko abincin safe bai ci ba duk da ta dafa, haka ya shirya ya fice suka tafi kai kudin auren. Sai dare ya dawo gidan, bayan tayi masa sannu da zuwa ta saka masa abincin dare, ya dai ci abincin amma har a lokacin fushi yakeyi da ita. Sai da suka kwashe wajen kwana biyar a haka, duk yanda ta kai ga kokarin kyautata masa ya ki ya daina fushi da ita. So takeyi ma ta je ta yiwa Hajiya Allah ya sanya alkhairi na kai kudin auren Saifullahi amma ta kasa tambaya saboda yanda yake fama daure fuska yana fizge-fizge.
Sai da aka yi wajen sati daya sannan taga kamar ya fara saukowa tunda yana dan tsayawa suyi hira.
Dawowarsa kenan daga office ya gama cin abincin da ta saka masa ya tashi daga falon ya shige daki ya barta ita kadai a falon, chatting takeyi a WhatsApp don haka bata bishi ba tayi zamanta. Bai dade da shiga ba aka buga gate, ta tashi ta fito ta tsaya daga ciki ba tare da ta bude gate din ba tace
'Waye?'
Daga wajen aka amsa
'Musa me wanki ne.'
'Ana zuwa.'
Ta juyo ta dawo ciki ta wuce daki don ta kirawo Abban Nuraina yazo ya karba, haka ya sanar mata idan yana gidan aka buga kofa indai namiji ne ya fi so ta kirawo shi ya bude.
Babu takalmi a kafarta watakila shi yasa bai ji takun tahowarta ba har ta tura kofar corridor din da dakin yake ciki ta shiga, tana jiyo sautin muryarsa yana waya wanda ko ba'a gaya mata ba ta san da mace yake wayar saboda yanda yake ta kwantar da murya kamar me waka. Da sallama ta shiga dakin da yake kofar dakin a bude take ta jiyo kalmar karshe da yake fada
'Kada ki damu Baby na yanzu zan zo.'
Ta karasa ciki yayinda shi kuma yayi sallama da wadda yake wayar da ita ya ajiye wayar ya dago yana dubanta ya amsa sallamarta. Tayi kamar bata ji me ya fada a wayar ba tace
'Musa me wanki yana kiranka a bakin gate.'
Ya mike ya fara kokarin fita
'Yauwa bari naje wankina ya kawo min.'
Yana wucewa ta juyo ta biyo bayansa ta dawo falon. Danne zuciyarta take tana ambaton Allah don bata so ta nuna masa ta ji wayar da yakeyi, to idan ta nuna masa ta ji ma babu yanda zata yi tunda dai duk alamu sun nuna ba zai iya dainawa ba. Ko wacece kuma Babynsa oho? Kullum addu'a take Allah ya yaye masa amma kullum canza salon kawai yakeyi, ko da yake shi a karan kansa baya so ya daina don haka zai yi wahala ya daina.
Ya shigo da kayan wanki a hannunsa ya wuce daki, Nurain da Nana suka bi shi a baya da gudu. Tana nan zaune ya fito a shirye tsaf yana baza kamshi su Nana suna biye da shi, ya dubeta yace
'Zan dan je wata unguwa ne daga can kuma zan wuce gidan Hajiya.'
Ta dubeshi da fara'arta
'A dawo lafiya, don Allah ka gaishe min da hajiya. Muma dai in sha Allahu gobe ma je da yara mu gaida Hajiya.'
'To Allah ya kaimu goben.'
Ya fice ya barmata kamshin tuararensa wanda babu abinda yake kara mata banda takaici.
Tana ji tana gani ya fice ya tafi wajen wata wadda shi kanshi ya tabbatar ba auren ta zai yi ba.
Haka ta zauna a gidan nan ranta babu dadi tana ta tunanin mafita amma ta rasa.
Sai wajen karfe tara da rabi na dare ya dawo, tana rabarsa ta ji kamshi na daban a jikinsa. Bata san kamshin ba don tabbas ba kamshin turarensa bane kuma ba na Sucre bane don tun tuni ta gane kamshin turaren Sucre. Ya wuceta a falo ya shige daki zai canzo kaya, ta bi bayansa da kallo tace
'Ikon Allah! An yi sabuwa kenan, Allah ya raba bawa da wahala.'
Haka ta kwana tana tunanin mafita bata samu ba, mafita daya ta rage mata shine ta kai kararsa wajen Hajiya in ya so ko auren ne su saka shi yayi. Amma gaskiya tana matukar jin kunyar Hajiya kuma tana ganin rashin dacewar kai karar da wajen mahaifiyarsa, amma kawo yanzu bata da wani zabi. Ta dai bari zuwa gobe taje wajen Hajiya taga idan zata iya dagewa ta fada mata don tana kyautata zaton Hajiyar zata samar mata da mafita.
KARSHEN BABI NA TAKWAS
MATAR MUKHTAR
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
FIKRA WRITERS ASSOCIATION
BABI NA TARA
09
Tunda zai fita office ya bata kudin motar zuwa gidan Hajiya, ya sanar da ita idan ta shirya su tafi in ya dawo daga aiki zai samesu a can sai su dawo tare. Sai da tayi sallar la'asar sannan ta shirya su suka kama hanya.
Suna isa suka tarar da Inna a tsakar gida ita da masu aikin gidan saboda a ranar itace da girki. Inna kishiyar mahaifiyar su Mukhtar ce wadda itace amarya, tana da yara uku; Amina, Maryam da Habiba dukanninsu kuma kannen Mukhtar din ne. Nan ta zauna ita da yaran suka gaisa sosai da Inna sannan ta shige wajen Hajiya ta bar yaran a nan, wadanda tana wucewa suka bita da gudu.
A falo suka sami Hajiya tana zaune tana kallon TV yayinda Bahijja 'yar danuwanta wadda take riko take ta 'yan gyare-gyare a wajen.
Nan da nan aka hau hidima da su ita da yaran, Bahijja ta kawo musu ruwa da kuma cin-cin. Basu dade da zama ba Ummahani da Maryam suka dawo daga makaranta; Ummahani itace autar Hajiya da yake mata biyu ne da ita ita kadai ce ta rage batayi aure ba ita kuma Maryam 'yar wajen Inna ce. Suna ajiye jaka suka dawo wajen Safiyya aka yi ta hira.
Sai can daf da Magriba sannan duk suka fice, ya zama babu kowa a falon sai Hajiya da Safiyya. Ta yi dan gyaran murya tace
'Ashe kuma an kai kudin Saifullahi.'
Take fara'ar Hajiya ta karu tace
'I, saifu girma ya zo in sha Allahu.'
'Allah ya sa albarka, Allah ya sa muna raye kuma Allah ta nuna mana na
'yan baya.'
'Amin ya Allah.'
Suka yi shiru na dan lokaci.
Tun bata fadi komai ba ta fara neman birkicewa, da kyar ta tattaro nutsuwarta ta dan yi gyaran murya tana ta faman murza 'yan yatsu kamar mara gaskiya
'Umm, Hajiya shima Yayan da aure aka ce ya kara da ya fi.'
Maganar ta zo mata a ba zata, tayi firgigit tana dan zare ido
'Me kika ce Safiyya, wanne Yayan ne zai kara aure Safiyya?'
Nan da nan ta birkice ta fara nadamar abinda ta fada, duk kunya ta kamata, ta kasa cewa komai saboda yanda Hajiyan ta tsattsareta da ido.
'Mukhtar din ne shine zai yi auren amma sai yanzu nake ji.'
Ta daure a kunyace tace
'A'a Hajiya, nice nace dama shima zai kara.'
Mamakin hajiya ya karu sosai, tace
'Ke Safiyya wace mace kika gani tana cewa miji yayi aure, abinda sai idan babu yanda zaka yi. Ko dai akwai wata matsala ne ki gaya min sai a san abun yi.'
Ta muskuta cike da nadamar fara wannan zancen saboda yanda kunya duk ta lullubeta, da kyar ta lalubi muryarta tace
'Hajiya dama wata yarinya ce da yake nema,suna tare kullum sai dai suyi ta waya ko kuma su fita tare. Na ce ya aureta mu zauna tare ya kama fada kuma yace ba zai aureta ba, amma kuma har yanzun suna tare. Shine nace ko za kiyi masa magana.'
'Ikon Allah, Mukhtar din dai?'
Kai kawai ta gyada mata
'To ai kuwa gara ya aureta idan ba haka meye manufar kana da matarka kuma ka bal-balce a wajen wata, kuma kai da ma ta gidan da kanta tace ka auro waccan.'
Suka yi shiru na dan lokaci. Sosai hajiya ta fahimci inda zancen ya dosa, duk da ta ga kokarin Safiyyan da ta tunkareta da wannan zancen. Sai dai kuma ta ji dadi da ba wani wajen take ba tazo nan wajenta, in sha Allahu zata yiwa tufkar hanci. Ta san tunda Safiyya tayi wannan maganar lallai ta rasa yanda zata yi da Mukhtar din ne domin kuwa shi mutum ne mai saukin kai sosai amma kuma idan yana son yin wani abu to hanashi sai dai wani ikon na Allah ga kafiyar tsiya. Tayi gyaran Murya tace
'Kada ki damu Safiyya, barni da shi kinji zai zo ya sameni. Ai musulmi muke ba arna ba dole yayi abinda Allah yace.'
Tayi ajiyar zuciya saboda yanda Hajiyan ta fahimceta ba tare da ta nuna mata wani abu ba.
Nan suka zauna Hajiya tana kara kwantar mata da hankali da bata shawarwari. Ana yin sallar Magriba ya shigo gidan, tana ta rokon Allah kada Hajiya tayi masa magana a gabanta sai taji shiru. Ya gaida Hajiya suka dan yi hirarsu sannan ya dubi Hajiyan yace
'Bari naje wajen Baba, yanzu zan sauko sai mu tafi.'
Tace
'Kada ma ka sauko yanzu, Inna ta dora abincin dare da su idan kunci gaba daya kwa tafi.'
'To Hajiya.'
Ya amsa ya wuce falon sama inda nan ne bangaren Baban nasu.
_
Duk yanda Fatima ta so ta boye damuwarta a kan halin da alakarsu da Mukhtar take ciki ya gagara, tayi wani zuru-zuru ga rama. Da Mommy ta matsa mata da tambaya sai tace zazzabine yake damunta, don haka Mommy da kanta ta kai ta asibiti. Gwajin zazzabin malaria aka yi mata kuma aka samu akwai shi a jinkinta duk da likita yace ba mai yawa bane. Aka bata magungunan harda na karin kuzari, bata son shan magani don haka Mommy ce ta ajiye magungunan a wajenta. Idan lokacin sha yayi da kanta zata kirawo Fatiman ta sata a gaba ta sha sannan ta kyaleta, don haka tana ji tana gani ta dinga hadiyar magungunan nan har ta shanye.
Ta gaji da kiran wayar Mukhtar baya dauka, kuma baya biyo baya. Ta kirawo abokinshi ma Suraj da yake tana da lamabrsa yace mata abokinsa yana nan lafiya aiyuka ne kawai suka yi masa yawa saboda an bashi deadline din gamawa, amma ya bata tabbacin zai sa yayi mata waya amma shiru har yau. Tun karshen wata take sa ran zuwanshi ko kuma 'yan aikensa amma gashi yanzu har an shiga sati na biyu a wani watan shiru.
Tana idar da sallar azahar ta fito farfajiyar gidansu ta zauna a kasan bishiyar mangoro da waya a hannunta, Mukhatra din dai take son kira. Tana matukar son Mukhtar har bata jin zata iya rabuwa da shi, gara idan wani abu tayi masa ta bashi hakuri ya zo ayi auren nan a huta. Tun shekaran jiya rabon da ta kirawo shi duk da shekaran jiya ma bai dauka ba, ta rasa haushinsa take ji ko kuwa kewarsa take yi, gashi kullum dare da tunaninsa take kwana don wata ran idan ta tashi da suba sai
08, January 2025
Nafisa
I cant download the book