Showing 69001 words to 72000 words out of 92582 words

Chapter 24 - MATAR MUKHTAR COMPLT

SAKINA   

16 Aug 2024

7156

ke kan teburin

'Don Allah kayi hakuri Suraj, ko dai tasowa zan yi muje?'

'Tunda tce kada ka zo to ka barshi kawai, za kaji yanda mukayi.'

Suraj din yayi masa sallama ya fice yana jan kafa saboda takaici.

Ya koma ya zauna a kan kujerar kamar wanda aka tunkuda, ya dafe kansa wanda yake sarawa da karfi kamar zai fashe yana fitar da gumi ko ta ina. Ya rufe jajayen idanuwansa ya kifa kai a kan teburin yana fitar da iska mai zafi.


KARSHEN BABI NA TALATIN
MATAR MUKHTAR

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA TALATIN DA DAYA

31
Nan ya zauna da kansa kife a kan tebur har mutane suka fara fita daga office din, don haka masinjansa ya tura kofar ya shiga da sallama, sallamarsa ce ta sa Mukhtar din ya dago kai.

'Yallabai lafiya dai ko? Na ga baka fito ba.'

Ya dan mutssike ido

'Bacci ne ya dan kwasheni, yanzu zan fito.'

Nan da nan ya tashi ya hada kayansa ya fice daga office din, a lokacin ana ta kiraye-kirayen sallar Magriba.

Har ya kama hanyar gida ya tuna a yanda zuciyarsa take tafasa zai iya jiwa Jamila ciwo, sannan gashi Baba ya ce masa kada ya sake ya kara taba ta da sunan duka, don haka sai ya karkata motar ya nufi Bristol Hotel. Yana shiga ya kama daki; wanka ya fara yi don ya rage zafin da kirjinsa yake yi. Nan yayi sallar Magriba, ya yi order din abinci ya ci ya koshi sannan ya haye gado ya kwanta. Nan da nan bacci ya kwasheshi, bai farka ba sai sha biyu saura, yana farkawa yayi sallar isha'i ya dauko mukullin motarsa ya kama hanyar gida.

Tana zaune a falo zuciyarta sai suya take saboda takaici, tun wajen goman dare take kiransa ya ki ya dauka. Babu wanda take zargi sai karuwarsa da ta kirawo dazu; tabbasa itace ta rike Mukhtar don tayi mata wulakanci kuma ita ta hanshi daukan wayar. Don haka ta ci alwashi duk inda matar nan take gobe zata sa a nemo mata ita don taje ta sameta. Tana zaune tana jiran taga ta inda zai shigo gidan, wajen sha biyu da kwata ta ji motsinsa maigadi ya bude masa get.

Bata ji sallamarsa ba don haka itama bata amsa ba, tana zaune a kan kujera tana jijjiga kafa tana yi masa kallon raini mai cike da alamomin tambaya kala-kala.
Yana shigowa falon ya sa mukulli ya rufe kofar, ya nufo inda take zaune yana goye da jakar computer dinsa, a hannunsa kuma yana rike da shafin wata mujalla. Kafin ya karaso ta mike tsaye

'Wannan wane irin sabon wulakanci ne Mukhtar, sha biyun dare kake shigowa gidan matarka ta sunna kana can wajen matan banza don tsabar wulakanci.'

Kallon takaici kawai yake mata yana jijjiga kai, ya mika mata shafin mujallar da yake hannunsa wanda rubutu ne akayi a kan rayuwar Prof Hajara sai hotonta a tsakiyar shafin daga kasa kuma ga wani hoton nata ita da mijinta Senator Aliyu A. Minjibir.

Ta karba a wulakance, ya nuna hoton senator yace

'Wannan matar kika kirawo kika ce mata karuwa, ga mijinta sune masu rike da kasar. Suraj ne ya hadani da ita ta sayi computers guda biyu wadanda na san kin gansu, bayan nan kuma tayi order din wasu computers din guda 40 zata zuba a makarantarta Alheri Model Academy, na san kin san makarantar. Duk zagin da kika yi mata tayi recording yana nan na turo miki ta Whatsapp. Ta janye kwangilar computers din da ta bani guda arba'in nayi asarar ribar sama da naira miliyan daya, abinda kika yi mata kuma ban sani ba ko ta hakura ko bata hakura ba amma dai na bata hakuri kuma na gaya mata ba ni na saka ki ba don haka duk wani hukunci da zata dauka a kanki zata dauka. Ai kema babanki mai shari'a ne ne ko? To ki gaya masa abinda kika yi ku zama cikin shiri.'

Ya ja kafarsa da kyar ya wuce ya nufi hawa benen da zai kaishi dakinsa , ya barta a nan tsaye da takardar a hannunta da bakinta a bude.

Ta koma ta zauna a kan kujerar kamar an tura ta, ta dora hannu a ka. Ta sake kallon shafin da ke kan cinyarta; yanzu matar senator ta zaga, Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Tabbas ta san Abbanta mai shari'a ne amma na jihar Kano, kuma ma yayi retire. Wannan zancen ma idan Abban ya ji ai ta shiga uku, ba ita ba ko Ummanta ma ba zai kyale ba.

Yanda ya kwanta ya kasa bacci itama haka ta kwanta. Saura kadan ta turawa kaninta lambar matar ya nemo mata inda take Allah ya takaita mata wahala ta kirawo shi wayarsa a kashe; tabbas da ta shiga Babbar matsala. Haka ta kwana tana fatan Allah yasa matar nan ta hakura.
Received at Sakina
-----

Gaba daya gidan ya kacame ana ta shirin biki, Bahijja wadda 'yar kanwar Hajiya ce Hajiyan take riko ita Aminu zai aura, ita kuma Habiba wadda suke kira Biba 'yar wajen kishiyar Hajiya nata mijin da ban ba dan uwa bane. Gaba dayansu Baba ne zai aura da su don haka ya saka rana lokaci daya. Saura sati biyu bikin don haka Biba da Bahijja sai rabon kati suke.

Biba ce ta leko dakin Hajiya bayan ta gaida Hajiya ta kwalawa Bahijja dake daki kira

'Anti Ba kin shirya mu tafi?'

Ta fito daga dakin a shirye da jaka a hannu, ta zauna a kusa da Hajiya ta langabe kai tace

'Hajiya don Allah mu kaiwa Anti Safiyya?'

Biba tace

'E wallahi Hajiya.'

Hajiya ta bisu da kallon mamaki tace

'Yanzu har sai an rokeni a kaiwa Safiyya kati, ai ko baku kai mata ba ma ni zan baku na Ummanta ku kai tunda na bikin Saifullahi ma ku na aika kuka kai.'

'Yauwa Hajiya.'

Suka amsa gaba daya. Hajiya tace

'Ku hada da na manya ku bawa Ummanta, ga cingam can a kan mudubina Bahijja ki dauko ku hada.'

Har sun fita Hajiya ta sake kiransu tace

'Wancan leshin da kika ce kawarki ta fasa siya ki dauka na siya a kaiwa Safiyya ace in ji ni don itama ta saka anko.'

Nan da nan da murnarsu suka dauka suka wuce.
Hajiya ta bi bayansa da murmushi tana fatan Allah ya sa Safiyyan ta zo bikin su hadu da Mukhtar, don ita a yanzu babu abinda take so kamar taga Mukhtar ya dawo da Safiyya. Ko ba don yaran ba shi kansa kullum ganinsa take bashi da nutsuwa, gani take kamar zaman lalura kawai yake da Jamila.

Da yake Aminu ne ya kaisu haka suka hadu suka saka Safiyya a gaba sai da tayi musu alkawarin zata zo launching din; wanda biki ne da gaba daya 'yan gidan suke haduwa. Don har dinki ma Aminu yace ta kawo su kai mata tace su barshi zata kai.
Haka Umma ta saka ta a gaba a kan lallai sai ta cika alkawi domin itama idan dai kalau take; da yake yanzu tana fama da ciwon gwiwa; tana son ta jewa Hajiya don bata je na Saifullahi ba lokacin tana jin zafin sakin da aka yiwa Safiyya.
------

Tun bayan da ya bata wannan shafin mujallar bai sake shiga harkarta ba, haka yayi banza da ita. Tana ta addua kada a zo nemanta kuma tana jin Allah ya amsa don gashi yau kwana biyar shiru.

Abu daya ne yake damunta yanda Mukhtar ya daina shiga harkarta kuma ya daina fita daga gidan, don ko aiki ma tun ranar da ya shigo sha biyun dare bai sake zuwa ba.

Yana kulle a dakinsa, idan lokacin abinci yayi sai dai taga ya fita ya shigo da abinci a leda ya wuce dakin, in ya gama ya fito da su ya sa a shara. Kwanansa biyar a haka yau, abun ya isheta kada ma taje matar sawa tayi aka koreshi daga aiki daga dan wannan abun.

Don haka yau tayi niyyar idan ya fito karbar abincin sa a waje ta tare shi sai ya gaya mata abinda yake ciki.

Tana sallah ya fito ya karbo abincin rana don haka tana idarwa ta zauna tana jiransa ya sauko zubar da ledojin.
Jimawa kadan ya sauko ya kai sharar waje ya dawo.

Sai da ya zo tsakiyar falon sannan ta mike ta sha gabansa, ya kalleta ba tare da ya ce komai ba don haka tace

'Mukhtar don girman Allah ka zauna muyi magana.'

Ba tare da yace komai ba ya matsa ya zauna akan kujera ya zuba mata ido, ta biyo bayansa itama ta zauna. Suka hada ido ta sunkuyar da kai, ta sa hannu ta share kwallar da ta taru a gefen idonta tace

'Don Allah ko ma me nayi kayi hakuri, idan ma so kake naje na bawa matar nan hakuri to ni ka kaini inda take.'

Ya kawar da kai kamar ba zai yi magana ba, jimawa kadan kuma yace

'Ni kam tace bata son ta sake gani na, ke kuma idan tana son ganinki ta san yanda za ayi ta sameki ke dai kawai ki zama cikin shiri.'

Ta sunkuyar da kai ta goge hawaye, jim kadan yace

'Idan babu wani abun kuma zan wuce daki.'

Ta kai hannu ta dafa cinyarsa

'To don Allah ka daina zaman daki, ina girka abinci kuma sai ka dinga siyowa? Naga har aiki ma ka daina zuwa, ko hutu aka yi?'
Ya tabe baki

'Ai na hakura, shi yasa na zauna a dakin, aikin ma na hakura dashi resignation letter zan rubuta na bayar sai na dawo na zauna a gida. Kinga idan kina kallona kina kula dani babu wadda zan kula balle ki dinga bin matan mutane kina zagi. Yan kudin da suka yi min saura da abincin dake gidan idan suka kare na san ko a gidanku ba zaki kasa karbo mana tallafi ba ko?'

Ta sake fashewa da kuka, ta sauka daga kan kujerar ta durkusa a kafarsa tana rusa kuka
'Don Allah kayi hakuri, ai nace ba zan kuma ba, wallahi kuma da gaske nake.'

'Mtseewww!'

Ya mike ya kewayeta ya koma dakin.

Haka ya cigaba da shareta, sai dai kawai yana fita yamma yaje gidan Baba.

Ana ta Shirin biki don haka ya san dole za a nemeshi.

Ko da yaje gidan ma sai da Baban ya tambayeshi ko lafiya ya kwana biyu bai zo ba, haka ya shirga karya yace aikine yayi masa yawa gashi kuma yayi zazzabi.

Saura kwana uku bikin ya kawo mata kati tunda dama ya riga yayi mata anko kuma ta riga ta dinka. Bayan ya bata katin tace

'Ma Sha Allah, Allah ya sanya alkhairi.'

'Amin. Duk wanda ba zaki je ba sai ki tanadi uzirin da zaki bawa Hajiya don na gaya musu ke da Halimatu lafiyarku kalau.'

Ya wuce ya barta a wajen.

Ko lafiya kalau ake zaune ita din ba mace ce mai son shiga mutane ba, kuma bata fiya kula mutane ba. Tunda ya dauke su Nana bata je gidan ba, domin ko yawon arba'in bata je ba saboda kunyar abinda ta aikata. Ko Hajiya rabonta da ganin Halimatu tun tana kwana biyu da haihuwa, har saida ta iya zama ta fara cin abinci sannan yake daukanta ya tafi da ita idan zai je da yamma.
........

Kamu aka fara yi ranar Alhamis, bayan ya dawo daga aiki yaci abinci ya shirya zai fice. A shirye ta sauko dauke da Halimatu tace

'Mun shirya, bari mu fito ka kai mu wajen kamun.'

A gida suke yin kamunsu don haka gidan Hajiya ya wuce dasu. Gidan ya cika makil da dangi, yanda ta zata za a ki kulata ba haka bane domin duk an gaggaisa. Hajiya ma tana ta haba-haba da su tana nunawa dangi amaryar Mukhtar da Halimatu. Dama duk mutan gidan basu saba hira da ita ba saboda ita din ba mai hira sosai bace, don haka dai ta nemi waje a falon Anti ta zauna. Sai bayan isha'i ya daukota suka dawo gida.

Washegari ranar Juma'a itace ranar launching wanda ake yi a event center. Babban waje ne aka kama wanda aka cikashi da kujeru ga kwalliya sai kyalli wajen yakeyi. Yanda 'yan mata sukayi ankon shudin leshi haka 'yan mazan gidan suka sha farar shadda, wajen zaman mata da ban da inda maza suka zauna.

Kusa da matar Saifullahi Jamila ta zauna inda suke tare da wasu 'yayan wan Baba.

Sai bayan Amare da angwaye sun shigo sannan 'yan mazan gidan suka shigo. Daga inda su Jamila suka zauna tana hangen Mukhtar, duk da bata jin zai kula 'yan mata a bikin gidansu amma dai ta san maza suna da dabara kala-kala ta yanda zasu sami lambar 'yan mata don haka duk abinda ake yi hankalinta yana kansa.

Har ya kau da kai ya tuna kamar Safiyya fa ya gani a cikin mutanen da suke shigowa, ba tare da bata lokaci ba ya sake kallon wajen. Ya kasa dauke idonsa daga kanta, tare suka shigo wajen ita da Hamida.

Siket ne ta dinka da leshin six-pieces da riga fitted, ga mayafinta Mai ruwan gwal ya sha duwatsu sai kyalli yake, takalmin da ta saka ya dan kara mata tsawo ga 'yar karamar jakarta wadda ta rike a hannunta da yasha agog da zobba masu kyau. Babu make-up a fuskarta don dama ita bata saba yin makeup din ba, amma ta gyara fuskar fes, tayi haske ga fatarta har wani kyalli take.

Teburin da yake zaune yana daga gefe a cikin hall din, a hankali suke tafiya suna waige-waige kamar masu neman wani. Da gudu Nana ta bullo daga cikin mutane ta fada jikin Safiyya. Tayi murmushin da shi kansa sai da ya saka shi murmushi; yayi kewar Safiyya shi kanshi bai san me ya hanashi komawa su mayar da aurensu ba amma in sha Allah yana ganin yanzu lokaci yayi.
Received at Sakina

Idonsa yana kanta. Nana ta ja hannunsu ita da Hamida suka shiga cikin hall din. Da wuri Hamida ta zauna da ta sami teburi a wajen 'yan mata. Ita kuwa Safiyya ko ta zauna sai wasu 'yan uwan nasa su hangota a daga mata hannu ta tashi taje su gaisa. Haka ta karasa teburin su Anti da kannen Hajiya ta zube har kasa ta gaishe su.

Sai yanzu ya gane ba wai kansa kawai ya cuta da ya rabu da Safiyya ba harda danginsa, yanda suke haba-haba da ita bai taba ganin suna yi da Jamila ba; duk da ita Jamila a dabi'arta dama ba mace ce mai son shiga mutane ba kuma bata kai Safiyya fara'a ba.

Sai da ya san yanda yayi ya kirawo Nurain ya rada masa idan Mama zata tafi ya zo ya gaya masa.

Can wajen karfe bakwai da rabi suka mike ita da Hamida, sukayi sallama da amare sannan suka dawo Safiyyan ta tsuguna tayiwa su Anti sallama. Suka kamo hanyar fita tana rike da Nana yayinda su Na'ima 'yan gidan su Bahijja suka mike don yi musu rakiya.

Suka fito suna hira har suka fito bakin kofar hall din, Safiyya ta mikawa Na'ima hannun Nana tace

'Ga 'yarki nan Anti Na'ima ku koma mu mu wuce.'

A daidai nan Mukhtar ya fito yana rike da hannun Nurain wanda yayi wa Safiyya sallama ya koma da su Na'ima, suka wuce suna yiwa Mukhtar dariya.

Kafin ya gama tsayawa gaban Safiyya Hamida ta bar wajen saboda takaici. Ita kuwa Safiyya da murmushinta suka gaisa, bayan sun gaisa yace

'Kina nan Safiyya? Kin buya?'

Tayi murmushi

'Yanzu da dalili yazo ai na fito. Ya aiki ya family? Na ga Halimatu ta zama budurwa, Allah ya raya mana.'

'Amin ya Allah, bari na samo yaro sai a kaiku gida.'

'Ah, ai Sabir ne ya kawo mu a motar Yaya Habibu gashi can ma ni suke jira.'

Ta fada tana nuna masa inda Sabir din yake.

Ya dan taka mata, kafin su karasa motar sukayi sallama ya koma ciki ita kuma ta shiga mota.

Tana zama a motar Sabir ya fara mita

'Yaya Safiyya don Allah ki daina yiwa mutumin nan dariya, Haba mana. Idan Baban Muhammad ya gani ai ba zai ji dadi ba.'

Kafin ta bashi amsa Hamida tace

'Eh wallahi Yaya Safiyya, dan rainin hankali kawai. Sai wani faman yagewa mutane baki yake babu kyan gani.'

Tace

'Ikon Allah, shikenan kuma ba fada sai na hau gaba da mutum?'

Sabir yace

'Ki dai daina kulashi Yaya Safiyya, wannan yawan fara'ar taki dole ma ki koyi shan kunu.'

Ta kyalkyale da dariya, ya ja mota suka fice daga wajen. Suna tsayawa a danja almajira ta taso tana masa bara, ya mikawa Hamida hannu yace

'Hamee bani Murtala in yi sadaka Allah ya raba mu da mugun ji da mugun gani kin ji.'

Ya saka mishi nera hamsin Safiyya na masa dariya, ya mika sadakar suka wuce gida.

KARSHEN BABI NA TALATIN DA DAYA

MATAR MUKHTAR

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA TALATIN DA BIYU

32
Duk wani motsin Mukhtar a wajen bikin nan Jamila tana kallonsa, tana kallon yanda ya dinga bin duk wani motsi na Safiyya da ido haka kuma tana kallon lokacin da ya ja Nurain suka bi bayan Safiyya. Don haka ranta ya gama baci kafin a tashi daga wannan taron. Bata sani ba itama Safiyyan nemanta yakeyi ko kuwa dawo da ita zai yi. Ko ma dai menene dole ta kora masa jawabi domin ko dawo da Safiyyan zai yi bazata yarda ta zauna da ita a wannan gidan ba sai dai ya nemi wani gidan ya ajiyeta a can.

Sai wajen tara da rabi na dare aka tashi daga taron, kafin ma ya fito Jamila tana jiransa a bakin mota tana dauke da Halimatu. Sai da kannen Hajiya suka fito su hudu suka shiga bayan motar sannan ita ta shiga gaba suka kama hanya.

Har suka isa kofar gidan Hajiya bata ce komai ba, shi kadai yake hirarsa da 'yanuwansa. Bayan sun sauka daga motar

08, January 2025
Nafisa

I cant download the book

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login