Showing 15001 words to 18000 words out of 92582 words

Chapter 6 - MATAR MUKHTAR COMPLT

SAKINA   

16 Aug 2024

7143

tayi wankan tsarki sannan tayi sallah. Ta lalubo lambarsa zata kirawo sai kuma ta fasa, ta mike ta nufi cikin gida. A kicin ta sami Baba Habi tana shirin dora abincin dare, bayan ta amsa mata sallama tace

'Baba Habi don bani aron wayarki na kira wata lamba, wayata taki kawo network.'

Ta nuna mata karamar wayar da take ajiye a kan tagar kicin din tace

'Gata can 'yar gidan Hajiya sai dai wayar tawa ina jin babu kati fa.'

Ta karasa ta dauki wayar tana fadin

'Yanzu zan saka Baba, sai ma na rage miki.'

Ta juya ta fice ta bar Baba Habi tana ta godiya an ce za a saka mata kati.

Inda ta tashi nan ta dawo ta zauna ta tura kati wayar Baba Habi daga wayarta sannan ta kwafe lamabar Mukhtar a wayar Baba Habi. Yau zata gane wayarta ce Mukhtar baya dagawa ko kuma wayar kowa ma baya dagawa.

Kafin ta gama wannan tunanin wayar ta fara ringing take ta rike numfashinta tana fatan kada ya daga don idan ya daga hakan yana nufin itace baya son magana da ita ya daina daga wayarta yau kusan wata daya.

'Salamu alaikum.'

Fes taji muryarsa daga daya bangaren yana mata sallama. A cikin sanyin murya ta amsa

'Hm! Wa alaikumussalam.'

Da alamun mamaki a muryarsa yace

'Fatima.'

'Mukhtar.'

'Fatima, Lafiya kike naji ki haka?'

'Uhm, Lafiya kalau. Na ji ka shiru ne kuma naga baka daga kirana shi yasa na ari waya na kirawoka, Mommy tana ta magana saboda tun last month nace mata za ku zo ayi magana ban san me zance mata ba. Idan ka fasa aurena ne ai sai ka gaya min na nemi wani ko?'

Ta dan tsagaita shi kuma ya sami damar bata amsa cikin kwantar da murya

'Ba haka bane Fatima kin gane ko? Kin san Hajiya bata so ayiwa Safiyya kishiya har yanzu ban shanyo kanta ba amma in sha Allahu ina sa rai idan Baba ya dawo daga Umra ya sa baki komai zai daidaita. Za mu zo ai kuma na gaya miki yanzu haka kwangilar da na samu ce aiyuka sun min yawa sosai shi yasa ko a waya bakya ji na.'

Tuni hawaye suka wanke mata fuska, ko wanda bai san Mukhtar ba yaji wannan maganar ya san wanda yake fadanta karya yake yi.

Ta cire wayar daga kunnenta ta zubawa madannan wayar ido, babu komai a kanta don ta rasa ma me zata tuna. Ta share hawaye ta danna ta katse kiran, ta saki wayar a kancinyarta tare da tata wayar da take daya hannun ta sa hannuwanta tana share hawayen dake bin fuskarta.
Da kyar ta tattara nutsuwarta ta tashi ta shiga cikin gidan cikin hanzari ta ajiyewa Baba Habi wayarta a kicin din ba tare da ta bari sun hada ido ba ta wuce dakinta.

Tana shiga dakin ta murza mukullin da yake jikin kofar ta ciki ta fada kan gado a rub da ciki. Ta saki kukan da take makalewa gaba daya harda shessheka, saida ta dauki lokaci tana wannan kukan sannan ta dan ji sanyi a ranta ta fara ajiyar zuciya. Ta tashi zaune ta zubo kafafunta kasa, ta saka tafukan hannunta ta rufe fuskarta; Ya za ayi Mukhtar yayi mata haka? Yanzu ba zai aureta ba kenan? Ta cire hannuwan daga fuskarta ta dora a ka, ba zata iya kirga sau nawa suka wuni da shi a hotel yana moreta ba, kenan ya ci bulus? Shi ya fara saninta budurwa kenan ya rabata da budurcinta yanzu duk wanda zai aureta sai dai ya sameta a haka? A yanda Mukhtar ya dinga nuna mata kauna bata taba zaton zai yi mata haka ba. Yanzu me za ta ce da Mommy wadda take jira a zo maganar aurenta? Ta sauke hannuwanta daga kanta, kwakwalwarta tana neman kullewa ta dakatar da tunanin. Ta sa hannuwanta ta dafe kirjinta lokacin da ta tuna cewa Mukhtar yana da hotunanta tsirara babu iyaka.

'Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun.'

Ta fada a fili lokacin da ta tuna har video dinta ya taba dauka tana tsaye a gaban mudubi a hotel din da ya saba kama musu tana ta rawa tana jijjiga jiki shi kuma yana dariya, gashi har fuskarta ya dauka a lokacin. Ko bayan dawowarta daga Kanon ma ta tura masa wasu hotunan nata Kuma duka harda fuska gashi tsirara; don dayan a bandaki ta daukeshi tana wanka jikinta duk kumfa. Ta mike tsaye zumbur kamar wadda aka tsikara ta fara kaiwa da kawowa a dakin. Yanzu idan ya fito da hotunan ya nunawa wani fa? Ko kuma suka fito Yaya ko Mommy suka gani. Ta sake dora hannuwanta a ka tana fadin

'Ka cuceni Mukhtar, ka cuceni? Ni ka mayar karuwa Mukhtar? Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun.'

Ta tsuguna a gaban gadon kamar me yin addua irin ta arna, hawaye yaki ya kare a idonta don haka ta gaji da sharewa. Ta juyo tsayuwar mota a tsakar gida wanda ya tabbatar mata Mommy ta dawo, gaba daya ma ta manta Mommy daga wajen aiki tayiwo mata waya ta sanar da ita sun wuce asibiti da Aisha matar Yaya Ibrahim zata haihu.

Kafin ta gama wannan tunanin ta jiyo takun Mommy ta nufo dakin don haka cikin sauri ta haye kan gadon ta kwanta ta kama goge fuskarta da zanin gadon.

Saida ta ji Mommy tana kokawa da hannun kofar sannan ta tuna ashe ta kulle dakin, ta tashi da sauri don ta san Mommy ta tsani jira kuma bata so ta dinga kulle kofar dakin ta karasa ta bude kofar. Da fara'arta ta shige dakin tana neman ture Fatiman tace

'Kina in .....'

Ta bi fuskarta da kallo tana mamaki

'A'a! Me ya sameki ne haka Fati kukan me kike yi.'

Ta kakalo murmushi ta kawar da jajayen idanuwanta tace

'Ba kuka fa nake ba Mommy, kaina ne yake min ciwo.'

Da matukar mamaki tace

'Ciwon kan ne kikayi kace-kace haka.'

Ta sunkuyar da kai tana kokarin boye kwallar da take shirin fadowa daga idanuwanta. Fitsarin da yake marar Mommy ne ya mintsineta don haka ta dan cije lebe, tun safe rabonta da fitsari gashi ta sha ruwa da yawa. Ta dubi fatiman tace Allah ya sauwake ta juya cikin sauri ta nufi nata dakin.

Tana fita Fatima ta rufe kofar dakin ta jingina da bayan kofar dakin ta daga kai sama tanawa Allah godiya da Mommy ta kyaleta ta tafi. Ta juya ta kalli kofar ta daga hannu sama kamar me addu'a tace

'Allah ya sa kada ta kirawoni.'

Ta share kwalla a idonta ta koma ta kwanta a kan gadon tana fatan Allah yasa mafarki ne abinda yake faruwa. Bata dade da kwanciya ba akayi kiran sallar la'asar, har aka tayar da sallah a masallacin kusa da su tana kwance ta kasa tashi sai gyangyadi da yake kwasarta.

Tana nan kwance Baba Habi ta kwankwasa mata kofa tana fadin

'Fatiti kizo inji Hajiya tana dakinta.'

'To.'

Ta amsa daga ciki. Nan da nan ta mike ta sauko daga kan gadon ta nufi bandaki da niyyar ta fara yin alwala tayi sallah sai kuma ta tuna idan tayi jinkiri da yawa Mommy zata iya biyota har dakin don haka kawai ta fice daga dakin ta nufi dakin Mommy.
MATAR MUKHTAR

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

FIKRA WRITERS ASSOCIATION


BABI NA GOMA

10
Tunda Safiyya tayiwa Hajiya maganar Mukhtar saida sati ya zagayo sannan Hajiyan ta sami damar yi masa maganar. Wajen karfe biyar na yamma ya shiga gidan yayi sa'a babu kowa a wajen Hajiyan sai ita kadai don haka ya zauna suna hira. Tayi gyaran murya tace

'Ni kuwa wace 'ya ce aka ce kana zuwa zance wajenta?'

Da mamaki ya kalleta don tambayar tata ta shammace shi

'Hajiya zance kuma? Ni babu wajen wadda nake zuwa.'

'Ka tuna dai domin kuwa wanda ya gaya min baka isa yayi maka karya ba.'

Ya kalleta suka hada ido, yanda ta tsattsareshi da ido yasan dole ta kawar kai

'Hajiya nifa babu wata da nake zuwa zance wajenta.'

Tana so ta yarda da zancen bakinsa amma a sanin data yi masa yanayinsa in yana fadan karya daban be, ta jijjiga kai tace

'To idan ma dai zancen kake zuwa ai ba wani abu zance maka ba, a matsayinka na namiji ai ka kai ka auri mata har hudu don haka idan kaje zance a halin yanzu babu laifi.'

Ya kalleta alamar mamaki don ya zata fada zata yi, har ya fara murmushi tace

'Sai dai ka sani kasancewarka namiji Allah bai baka dama ka dinga kula 'yayan mutane kana bata musu lokaci ba, kuma Allah ya sani bamuyi maka wannan tarbiyyar ba. Don Allah duk yarinyar da ka san ba aurenta zakayi ba ka rabu da ita, ka rabu da ita! Idan kuma aure zaka yi to ga mahaifinku can ka sanar dashi sai a hada da na Saifullahi. Ka kare mutuncinta ka kare mana namu mutuncin. Kuma ka duba kannenka mata gasu nan, ka duba 'yarka Nana. Allah ya sauwake.'

Ta mayar da hankalinta ga kallon talabijin din dake kunne a falo. Yayi tsuru kamar wanda ruwa yaci, tabbas wani ya kawowa Hajiya gulmarsa kuma ya san ba kowa bane sai Safiyya. Ya mike tsaye

'Bari naje wajen Baba.'

Ba tare da ta kalleshi ba tace

'Sai ka dawo.'
...........

Suna zaune a falo ita da Nurain da Nana bayan sallar isha'i taji dawowarsa, tayi mamaki saboda bai fiya dawowa da wuri ba sai wajen karfe tara na dare. Nan da nan ta karasa saka musu kayan baccin da take saka musu suka ruga bakin kofa suna jiranshi, yana shigowa kuwa suka rungumeshi suna

'Oyoyo Abba.'

Ya dauki Nana wadda ta tare gabansa tana daga masa hannuwa Nurain ya bi shi suka karasa ciki.

Tana kallon fuskarsa ta san da matsala, tayi masa sannu da zuwa ya amsa a ciki ba tare da ya kalleta ba. Ta mike tsaye ta karbi Nana a hannunsa tana cewa

'Bacci zasuyi.'

Sai da ta goya Nana sannan ta dauki ruwa ta kai masa dakin, ta ajiye a kan durowar gado tace

'Ga ruwa Abban Nurain, na ajiye maka abincin a falo zan kwantar dasu yanzu zan fito nima.'

Bazata iya cewa ya amsa ko bai amsa ba, ta dai san ko kallonta bai yi ba. Ta ja hannun Nurain suka fice daga dakin tana mamakin abinda tayi masa don a iya saninta lafiya suka rabu da zai fita da safe. Saida ta kwantar da Nana sannan ta fito, kai tsaye ta wuce falo. Tun kafin ta karasa ta hango kayan abincinta a kan kafet yanda ta ajiye kuma baya falon ma, don haka ta koma ta wuce dakinsa.

Ta tura kofa ta shiga da sallamar da bata tabbatar ya amsa ko bai amsa ba, yana zaune a gefen gado yana ta faman shafa waya don haka itama ta karasa ta zauna a kusa dashi tana kallon fuskarsa

'Habibi baka ci abincinka ba, ko ni kake jira?'

Ya galla mata harara

'Na koshi.'

Mamakinta ya karu tana bin fuskarsa da kallo yayinda shi kuma yake kuma bata rai yana dauke kai.

'Um wai me yake faruwa ne Abban Nurain?'

Ya juyo ya sake yi mata wani kallon

'Me kika je kika gayawa Hajiya?'

Mamakinta ya kara yawa kanta ya shiga duhu

'Hajiyan Baba? Ai tun last week rabona da gidan hajiya fa, me zan gaya mata kuma?'

Ya fuskanceta sosai kamar mai shirin kure mai karya

'Wanne munafikin ne yacewa Hajiya ina neman wata yarinya?'

Sai a lokacin ta gane inda ya dosa, ta kawar da kanta tayi dan gajeran murmushi mai kama da yake
'Iya abinda ta gaya maka shi na gaya mata.'

Ya kalleta a raine yana nuna mata yatsa

'Ni kike gayawa wannan maganar banzar saboda baki da mutunci ko? Kin gama sa min ido da bibiyata kin ga abinda ya dameki kin koma kina so ki hadani da mahaifiyata ko? To wallahi baki isa ba, kin ji na gaya miki. Ki fita daga idona na rufe in ba haka ba wallahi zaki tafi gidanku ki je kiyi wa wani wannan munfurcin da kika tsira kinji na gaya miki.'

Ta dago idonta da ya riga ya cicciko da hawaye ta dubeshi tace

'Allah ya baka hakuri.'

Ya ja tsaki ya mike tsaye, tayi sauri itama ta mike ta fice daga dakin tana jiyo tsakinsa.

Tana shiga dakinta ta turo kofar, ta karasa ta zube a bakin gadon saboda tana tsoron fadawa kan gadon ta tashi Nana. Hawayen da take makalewa ya kwace gaba daya, haka ta dauki tsawon lokacin tana zubar da hawaye kirjinta yana zafi. Wannan wacce irin fitna ce? Kenan yanzu babu wanda zai gayawa Mukhtar gaskiya ya dauka? Kenan idan dai tana sonshi haka zata kare rayuwarta ya kulleta a gidansa yana bin matan kwararo shida yake da damar ya auri mata har hudu? Ta dafe kirjinta wanda yake kara yi mata nauyi ta kwantar da kanta a gefen gadon ta lumshe idonta tana fitar da hawaye tana ambaton Allah a zuciyarta a haka har bacci ya kwasheta.
...

Mikewar da Mukhtar yayi dama ficewa zai yi ya bar mata dakin, don haka da yaga ta rigashi fita sai kawai ya ja tsaki ya koma ya zauna a inda ya tashi. Tunda taga sakonnin su da Fatima take masa fitna kala-kala, shi bai ma san yanda akayi ya bar sakonnin fatiman har ta gansu ba. Duk 'yan matan da yake harka da su baya saving lambarsu a wayarsa, haddacewa kawai yakeyi ko ya rubuta a wani dan littafi da yake ajiyewa a mota. Haka ma sakonninsu, da sun masa message yana gama karantawa yake gogewa. Amma na Fatima da yake suna masa dadin sake karantawa da kuma kallon hotunan lokaci-zuwa lokaci sai ya barsu tunda yaga sun dauki shekaru da Safiyyan baya taba ganewa ba.

Ya ja tsaki a fili ya kwanta a kan gadon kafafunsa suna kasa.
Yanda Safiyya ta kwana cikin damuwa haka ya kwana yana hirarrakin banza tsakanin sabuwar budurwar da yayi wadda yanzu ita yake yayi wato Amra da kuma wata inyamura wato Lindsay; wadda suka hadu a Abuja lokacin da yake taro ta taya shi kwana kafin Fatima ta sameshi a Abujan.
-----

Saida Abban Nurain ya kwana biyar baya yiwa Safiyya magana, baya cin abincinta baya ma zama inda take balle suyi magana. Yayi matukar bata mamaki saboda idan ma hakuri yake so ta bashi to ai tun ranar da yake mata fadan ta bashi hakurin don haka ta yiwa kanta alkawarin bazata bashi hakuri ba; don bata ga laifin ma da ta yi ba. Duk abinda ta sabayi na kula da gida da shi kansa bata fasa ba, sai dai kawai babu kulawa. Abinci kuwa yanda ta dafa ta ajiye masa haka zata kwashe kayanta, bata dai fasa girkawa ba saboda shima bai fasa cefane ba.

Wajen karfe tara da rabi na dare ya shigo gidan, tana kwance a falo ita kadai domin yaran sun yi barci. Wayace a hannunta tana karatun labari a group saboda babu wuta kuma bata tayar da inji ba. Bayan tayi masa sannu da zuwa yace

'Ke dai kina son zama a duhu, akwai mai a inji bazaki tayar ba kiyi ta fama da sauro.'

Tayi murmushi tana mamakin yanda ta ji maganar tasa kamar ba shine ya fita da safe ba tare da ya kulata ba, tayi dariya tace

'Na kasa tashi ne wallahi, kwana biyu duk jina nake kamar me zazzabi jikin ba kwari.'

'To ai sai kije asibiti a dubaki don yanzu haka malaria ce.'

Kafin ta amsa ya koma waje ya tada injin sannan ya shigo gidan, bata falon don haka ya wuce daki. Ta fito daga kicin da ruwa ta kai masa daki tace

'Na ajiye maka abincin a falo.'

'Ina zuwa.'

Taji dadi amma tayi mamaki, a ranta tace Abban Nurain mai abin mamaki kenan kai kadai kayi fadanka kuma ka sauko. Ta dawo falon ta zauna tana jiransa.

Jimawa kadan ya fito daga dakin da takardu a hannu sa, ta sauka daga kan kujerar da take zaune ta zuba masa abincin. Bayan ta gama ya janyo kwanon ya mika mata takardun yana fadin
'Idan an koma hutu da Nurain za a koma gashi nan na siyo form, tunda nan kusa ne idan na kaishi da safe sai ki dauko shi da yamma.'

Ta karba tana ta fara'a

'Ma Sha Allah, yayi hakan. Allah ya kara rufin asiri bari ya tashi nayi masa albishir.'

Yayi dariya

'Allah ya sa dai kada ya bada ke yayi mana kukan makaranta.'

'In sha Allah ba zai yi ba.'

Suka dan taba hira sannan daga baya suka wuce suka kwanta.

.........

Tun wajen sati uku da suka wuce take son ta yi gyare-gyare amma ta gagara, gidan duk yayi yana da kura. Tana so ta goge fankoki, tagogi da irin su karkashin gado da kujera amma yara sun hanata. Ta so Hamida tazo mata kwana biyu amma makaranta kuma gashi BUK ta fi kusa daga gida don haka Umma tace sai dai ta bari Hamidan ta sami hutu tukunna.

Bayan ya fita aiki suna zaune ita da yara Bahijja da Habiba suka kawo musu ziyara, bayan sun gaggaisa ta dubesu tana dariya tace

'Yau an tuna da mu kenan 'yan matan kulle.'

Bahijja tayi dariya tace

'Baba baya gari shiyasa muka sami kafar yawon Juma'ah.'

Nan suka wuni sai bayan la'asar suka fara shirin tafiya, Nurain ne ya dubi Habiba yace

'Anti Biba gidan Hajiya za ku tafi.'

Ta shafa kansa tace

'Can zan tafi Nurain, za ka je ne?'

'Zan je, don Allah ki tafi dani.'

Ta Kalli Safiyya tace

'Anti gaskiya zan tafi da yarona.'

'Kinga kuwa da na samu na yi kiba kafin ku dawo, amma ki kira babansu ki gaya masa.'

Take ta dauki wayarta ta kirawo Mukhtar, kuma ya bata umarni ta tafi da su idan ya zo zai dawo dasu. Nana tana ji za a tafi da Nurain itama ta dauki takalminta da gudu ta mikawa Bahijja tan fadin

'Anti Nima zan je.'

Don

08, January 2025
Nafisa

I cant download the book

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login