Showing 27001 words to 30000 words out of 92582 words

Chapter 10 - MATAR MUKHTAR COMPLT

SAKINA   

16 Aug 2024

7141

tsammani ya gansu, yana ta wani faman sunkuyar da kai suka gaisa da Yaya Habibu. Yayi musu iso suka shigo falo, bayan sun zauna Yaya Habibu ya dubeshi yace

'Kaya muka zo diba na Safiyya.'

Ya gyara zama yace

'Yaya don Allah kuyi hakuri, wallahi ni kaina ban san yanda akayi ba.'

Ya kalleshi yana jin kamar ya buge shi saboda takaici

'Babu komai ai ya wuce, na san an sanar da kai cewa cikin da ya bare a jikinta ya kai sati Sha uku don haka kaga daga jiyan ta gama iddarka.'

Ya share gumi ya hadiye malolon da ya tokare masa makogoro. Yana daga zaune ya mike ya nunawa Yaya Habibu hanyar cikin gidan yace

'Bismillah.'

Ita da Sabir suka mike suka kama hanyar dakin, Yaya Habibu yana daga zaune yace

'Ki hada kayan sawar sai mu shigo mu balle gadon.'

Suka wuce suka barsu a zaune shi da Mukhtar, wanda so yake yayi magana da Safiyyan amma Yaya Habibu yayi masa kwarjin da yawa ba zai iya ba musamman da yake ya san bai kyauta ba. Basu dade da shiga ba aka bugowa Yaya Habibu waya ya tsahi ya fice yana fadin

'Ina zuwa.'

Yana fita yayi sauri ya shige dakin. Ta dora akwatinta a kan gado tana ta faman watsa kayan sawarta a ciki, ya karasa ya sha gabanta. Nan Sabir ya fice ya dawo falo ya zauna ya basu waje.

Ta dago ta dubeshi idonta cike da kwallar da take ta kokarin rikewa

'Safiyya baki gaya min kina da ciki ba, me yasa?'

Tana bude baki zata yi magana kwallar ta kwace ta gangaro kan fuskarta, ta sa bayan hannunta ta share ta dubeshi tace

'Ni ma ban san ina da ciki ba, ka san bana laulayi kuma bana al'ada idan ina shayarwa. Lokacin da na fara ciwon kai idan nayi magana sai kace na dorawa kaina damuwa, da yake a lokacin bana sa rai da daukar ciki sai na zata damuwar ce tunda ai akwai damuwar ko? Daga baya ma kuma zan iya cewa na manta da kaina kwata-kwata kokari kawai nakeyi na janye hankalinka daga kan matan da ba naka ba, shi yasa ban ma san da cikin ba. Sai dai kai din dama ai haka ka tsara, in ba haka ba me ya kawo saki. Sati na biyu a gida baka mayar da ni ba, ina kallo zan maka magana ta wahtsapp ka bude ka ki kulani ka ga kenan kai ka tsara haka. Allah ya sa haka ne ya fiye mana alkhairi.'

Ya sunkuyar da kai don shima nema yake ya zubar da kwalla, yana son Safiyya; wannan wacce irin jarrabawa ce? Ya bude baki a hankali yace

'Zan dawo mu mayar da auren mu in sha Allah.'

Duk da kwallar da take fuskarta sai da tayi murmushi irin mai dauke da takaici din nan ta raba ta gefensa ta wuce wardrobe din da yake bayansa don ta debi wasu kayan tana fadin

'Hmmmmn!'

Har ta kai gaban wardrobe din yana nan tsaye bai juyo ba, ta juyo a kaikaice tace

'Yaran fa?'

'Suna wajen Hajiya, za ki iya zuwa ki gansu duk lokacin da kike so ko kuma kiyi min waya sai na kawo miki su.'

'Toh.'

Ya fice daga dakin saboda yanda hawayenta yake neman saka shi hawaye, ya shige dakinsa ya turo kofar.

Jimawa kadan Sabir ya koma dakin bayan ya ji shigewar Mukhtar, ya tayata suka kwashe kananan kayan tsaf Yaya Habibu kuma ya shigo da mai mota suka balle gadon suka hada da kujerun da kayan kitchen dinta duk suka kwashe. Har suka isa gida tana bayan motar Yaya Habibu tana share hawaye, yana kallonta amma ya rasa kalaman da zai bata hakuri da su don ya san da ciwo. A gida ya ajiyesu ita da Sabir yayi wa Umma bayani sannan ya wuce da kayan.

KARSHEN BABI NA GOMA SHA UKU.

MATAR MUKHTAR

Written by:
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

BABI NA GOMA SHA HUDU

14
Sati guda kenan da yin hutun makaranta don haka daga Fatima har Mommy suna gida kullum. A hankali Fatima ta fara samun nutsuwa tana bawa kanta hakuri a kan Mukhtar, domin har tayi blocking din status dinsa saboda kullum ta ganshi a WhatsApp sai hankalinta ya tashi. Satin da ya wuce aka yi birthday dinta, wanda shine na shekaru ashirin da shida. Ji take kamar tafi kowa tsufa gashi ba aure ba dalilinsa, babu ma wanda ya tayata balle ta sa rai. Duk kawayenta sun yi aure Kuma da yawansu sun daina kulata ma saboda ita bata da aure, wadanda basu daina kulata ba ma ita ta janye jikinta saboda gudun fitna. Janan ce kawai suke tare wadda sati biyu da suka wuce akayi bikinta, a Kano akayi don haka Mommy ta hanata zuwa wanda ta ji dadin hakan don bata son duk wani abu da zai tuna mata da Mukhtar. Kullum sai Janan ta kirawota a waya sun sha hira, don haka take jin kawancensu mai dorewa ne.

So take idan Jami'ar Ahmadu Bello za su koma sabon zango ta koma tayi digiri na biyu (masters) amma bata san yanda Mommy zata dauki abun ba don duk abinda ta nuna tana son yi Mommy sai tace ta bari sai tayi aure. Saboda yanda Mommy take yawan yi mata zancen aure har bata son hira da Mommy yanzu, don in dai sun fara kafin su gama sai Mommy tayi maganar aure.

A falo ta sami Mommy tana zaune da remote din TV a hannunta tana kokarin kunna TV din, ta wuce ta zauna a kusa da Mommy a kan kujerar zaman mutum uku. Ta dubi Mommy tace

'Sannu da hutawa Mommy.'

Ta ajiye remote din a kusa da ita bayan ta kai tashar Arewa 24 ta amsa da fara'arta

'Yauwa Fatima.'

Sukayi shiru dukansu suka mayar da hankalinsu ga kallon TV din inda ake nuna wani fim na hausa. Gaba daya hankalin Mommy yana kan TV din yayinda Fatima ta mayar da hankalinta ga wayarta, jimawa kadan ta ajiye wayar ta dan yi gyaran murya tace

'Mommy.'

Ta juyo ta dubeta, don haka ta cigaba

'Mommy ina son komawa ABU na fara masters dina shi yasa ma bana kashe alawee don na dan tara sai Yaya ya cika mini.'

Ta sunkuyar da kanta saboda ta kasa gane ma'anar kallon da Mommy takeyi mata mai kama da harara. Mommy tace

'Kina da hankali kuwa Fatima? Anya kuwa kin san me kikeyi? Wane masters kuma zakiyi babu miji a hannu? Ai yanzu mayar da hankali zakiyi ki fito da miji idan kikayi aure sai ki cigaba da karatun a gidan mijinki idan ya amince.'

Ta karkata kai ta kwantar da murya

'Mommy wai gani nayi tunda mijin bai zo ba ai sai na fara karatun, watakila ma mijin yana makarantar. Duk lokacin da Allah ya kawoshi sai ayi auren.'

Sai da ta zabga mata harara sannan ta bata amsa

'Babu wani masters da zaki fara yanzu, ki ma bar wannan zancen sai kin yi aure. Idan kika fara masters maza kara gudunki zasuyi, ko yanzun ma wani wannan degree da kikayi ne zai hanashi kulaki. Kiyi kokari ki fito da miji in ya so daga baya a yi maganar karatun.'

'To Mommy.'

'Yauwa.'

Suka yi shiru na dan lokaci, jimawa kadan Fatima ta mike zata koma daki Mommy ta dakatar da ita

'Fatima.'

Ta dawo ta zauna tana sauraron Mommy.

'Dubu talatin ne alawee din naki ko?'

'Eh, ashirin da tara ne Mommy.'

'To kinga ba kya bukatar kudi da yawa, duk wata ki dinga turo dubu ashirin account dina. Kayan kichin kusan duka na gama saya miki su sai mu fara sayen na daki da falo, kema ki sayawa kanki wani abu.'

Ta kalli Mommy ta sunkuyar da kai

'To Mommy, daga next month zan fara turowa.'

'Yauwa. Kuma ki mayar da hankali ki saurari mutane ki samu ki fitar da miji, duk wata dama da kike da ita ta yin ruwan ido yanzu ta kare dole ki hakura ki karbi wanda ya samu.'

'To Mommy.'

Da taga alamar zancen ya kare ta tashi ta koma daki, tana shiga ta turo kofar ta kwanta a kan gadonta sai hawaye.

Tana son ta koma karatu saboda ta sami cigaba, bata son wannan zaman na jiran mijin da ba'a san ranar zuwansa ba. Kullum sai mommy ta dinga cewa ta fito da miji kamar wadda ta boye shi a jakarta, itama tana son auren kuma tana takaicin kuskuren da ta aikata a baya.
Amma haka zata zauna idan miji bai zo ba ba zata yi komai ba kenan? Sai da ta gama addu'a da shawarar me zatayi da kudin alawee din da take tarawa business ko karatu? Da kanta ta yanke ta fara karatun sannan ta jewa mommy da maganar amma gashi mommy tace kayan aure za a siya da kudin, ko a ina ake aure babu miji oho? Ta so tace ba haka za ayi da kudin ba amma ta kula kadan Mommy take jira tace bata son aure don haka ta hakura ta amsa kuma ta san dole ta yi yanda Mommyn tace.

Ta juya ta gyara kwanciyarta, ta share hawayenta da zanin gadon; babu wanda ya janyo mata wannan takaicin sai Mukhtar da kuma wautarta, Allah take roka ya kawo mata mafita. In dai masters ne ta hakura, Allah ya sa zuwa karshen shekara ta sami miji don ta kula zamansu da Mommy ya kusa ya fara tsami.
_

Tunda Umma taga Safiyya ta koma Sallah ta saka ta a gaba sai da ta fito aka raba aikin gida da ita, itama Safiyyan hakan yayi mata daidai tunda ta san yanzu kam babu wanda ya san iyakacin zaman. Abu daya ne yake bata haushi yanda duk wani aiki itace zata yi ko da Hamida tana nan, idan ta saka ta aiki sai Umma tace ta kyaleta ita karatu takeyi.

Idan dai kaji Safiyya tana hira a gidan nan to ita da Sabir ne, duk kusancin da suke da shi da Hamida basa doguwar hira domin ita Hamida miskila ce sosai kuma bata fiya hira ba sai ta wuni ba tare da ta cewa kowa komai ba.

Damuwarta ta karu musamman da yake duk abinda take bukata sai ta tambayi Umma, Yaya Habibu yana bata kudi amma a gaban Umma take bata. Yana tafiya Umma zata fara neman dalilin rabata da kudin; kawo a siyo maggi, kawo a siyo sabulu, saka min katin waya ko kuma kawo kudi a siyo mana salad; a haka tsaf sai Umma ta ga babu ko sisi a hannunta. Don haka wani lokacin ma in dai Yaya Habibu ya bata kudi yana fita zata mikawa Umman tace ta ajiye mata, bata sake bi ta kai.

Idan ta tuna yaranta kuma sai tayi kuka; ta san za a rikesu cikin kulawa a inda suke amma itama tana son yaranta, tana kewarsu tana son kasancewa da su. Haka zata yi kukanta ta bawa kanta hakuri. Wani lokacin sai ta yi kamar taje gidan Yaya Hajiyayyaye ta kwana biyu sai kuma ta fasa saboda bata ga fuska ba daga wajen Yayan, gani take kamar ba zata barta ta sake ba. Ko babu komai idan aikatau zata yi gara tayi a nan gidan Umman kawai.

A kwance take a daki bayan sallar la'asar ta jiyo muryar Nurain yana yiwa Umma magana a tsakar gida, da hanzari ta tashi ta matsa bakin tagar dakin ta daga labule ta hango su. Aminu ne ya kawo su bayan ya gaida Umma ya sanar da ita sai da daddare zai zo ya daukesu, yayi mata sallama ya fice.

Ta juyawa tagar baya ta runtse ido tana fuskantar sama tana murmushi tare da yiwa Allah godiya. Yau sati hudu kenan da kwaso kayanta, duk da yace idan tana son ganinsu ta gaya masa zai sa a kawo mata su amma ta kasa kiransa. Duk da tana gayawa kanta zata basu lokaci sosai su saba kafin ta nemesu, ta dafa kirjinta tare da bude idonta a dai-dai lokacin da suka shigo dakin da gudu. Nana ce a gaba tana kiran

'Mama Mama.'

Da karfi suka fada jikinta suna dariya, saura kadan su kada ita. Ta ja su ta zauna a gefen gado ta dorasu a kan cinyarta tana duban fuskokinsu. Nana ta kalleta ta rungume hannuwanta tana zumbura baki tace

'Mama kika gudu inata nemanki ashe kina gidan Umma.'

Kafin ta bata amsa Nurain ya cigaba

'Eh Mama, kinga har Abba ya sani a makaranta Baba Aminu ne yake kaini bakiga jaka ta ba.'

Ta hadasu ta rungume tana kokarin tokare kwallarta

'Iyye! Sabon dan makaranta.'

Nana ta juyo da fuskarta wajenta tace

'Mama muma a nan zamu zauna ko?'

Tayi murmushi tace

'Baba Aminu zai zo ya daukeku in an jima, amma gobe ma zai dawo daku.'

Nurain yace

'Haka ma Hajiya tace mana. To Mama yaushe zamu koma gidanmu da mu dake?'

Ta kallesu tayi shiru, tamabayoyin nasu suna neman sakata kuka, ta rasa wanda zata amsa. Kallonsu kawai takeyi tana murmushi.

Ummace ta shigo ta samesu tana fadin
'To Nurain ga karas an siyo maka, ga yalo harda goruba yanzu na sa aka siyo a makota.'

Da gudu suka sauka suka nufi Umma da take tsaye a bakin kofa saboda suna son irin wannan kwadayin kuma sai a nan gidan Umma suke ganinshi.

Haka suka karasa wunin, da daddare Umma tayi tuwon shinkafa da miyar kuka, tare su Nurain suka zauna da mamansu a daki suna ci suna hira. Sai can wajen karfe tara sannan Aminu ya zo daukarsu, Safiyya ta gode Allah saboda lokacin Nana ta yi bacci don haka a hankali ta dauketa ta saka masa ita a mota tana godewa Allah idan ta tashi tayi musu rigimar a can.

Bayan sun tafi Safiyya da Hamida suka dawo suka zauna a falo wajen Umma. Ta dubi Safiyya tace

'Me yasa Baban nasu bai kawo su ba?'

'Ban sani ba Umma, nima kawai haka na gansu.'

Sukayi shiru suka mayar da hankalinsu kan TV dake kunne a dakin.

Umma tace

'Kinga saki daya ne aurenki akwai damar a sake daurawa ku koma, ki bishi a hankali ki samu ki koma wajen 'yayanki. Duk matar da kika gani a gidan aure hakuri takeyi da miji, ki lallabashi ki koma wajen 'yayanki ya fi rufin asiri kada ki tsaya wannan miskilancin naki na banza.'

Ta gyada kai tace

'To Umma.'

Jimawa kadan ta tashi ta shige daki, wucewa tayi ta tsaya a bakin taga ba tare da tana kallon wani abu ba; wato ko a wane hali Umma so kawai takeyi ta mayar da ita gidan Mukhtar. Ita Umma sam har ya zu bata ga laifi sa ba, ina ma laifi ace tunda auren ya mutu Allah ya fito mata da miji na gari. Tabbas ta ji dadin ganin yaranta bazata bari wani tunani ya kwashe mata 'yar walwalar da ta samu ba don haka ta juya ta koma ta zauna a gefen gado. Ta dauko wayarta da take gefen gadon ta fara duba Whatsapp, tana cikin kallon status ta zo kan status din kawarta Karimatu wadda ta sa hoton Jawad yaronta. Har zata yi mata sako a kai sai kuma ta canza shawara, sun kwana biyu basuyi waya da Karima ba don haka kiranta zata yi su gaisa ta san bata kwanta ba tunda ta ganta online.

Tana kirawa kuwa aka dauka, da hayaniya da murnarsu suka gaisa suka fara hirarsu, Karima tace

'Kin san tun last week nake son kiranki ban samu time ba nayi miki albishir.'

'Allah kawata, na me?'

'Mun dawo Kano, nan kKarkasara. Idan ba na manta ba kusa da unguwarkune ko?'

A sanyaye ta amsa don Karima bata san aurenta ya mutu ba tace

'Eh kusane amm..'

Kafin ta rufe baki Karima tace

'Ai kuwa gobe da yamma za ki ganni.'

'Karima ai ina gidan Umma fa, aurena da Abban Nurain ya mutu.'

'Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun! Ke kawata? Garin yaya? Kar dai a kan maganar nan?'

Ta amsa cikin firgici.
Tayi murmushi tace

'Uhm, kusan hakan kenan.'

Ta dan bata labarin yanda abun ya faru yayinda ita kuma ta jajanta mata sosai. Tace

'Shiyasa nace ki shigo da manya ciki kawata kada kuyi abu daga ke sai shi.'

Ta jijjiga kai

'ba zaki gane ba kawata.'

'Allah ya kyauta, Allah ya sa ku daidaita ku koma kawata ko don yara ma.'

'Uhm, ta wajen ina kuke a Karkasaran zan fito ranar Asabar in sha Allahu sai na biyo mu gaisa mu sha hira.'

'Um, muna nan dai ta bayan Aminu Kano dai-dai farkon katangar idan kika tsallaka titi. Idan zaki taho kiyi min waya dai sai na karasa miki kwatancen.'

'To kawata in sha Allahu za ki ji ni.'

Suka yi sallama suka ajiye wayar.

Hirar da sukayi da Karima ta kara debe mata kewa don haka da farin ciki ta kwana.

Tunda aurenta ya mutu bata fita ba amma yanzu tana jin ranar Asabar din in dai ba ummace ta hanata ba zata fita idan taje gidan Baban Hotoro in tana dawowa sai ta tsaya su gaisa da Kariman. Gidan Yaya Habibu ma ta so zuwa amma shi Yaya Habibu matarsa bata son mutane, ko daya bata son taga wani a cikinsu ya rabe shi, don haka ma suke baya-baya. Duk kokarinsa na ganin ta canza ya ci tura don haka Umma tace ya rabu da ita tunda itace uwar yaransa kuma bashi da matsala da ita sai wannan kin mutanen kawai.


KARSHEN BABI NA GOMA SHA HUDU.
MATAR MUKHTAR

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

BABI NA SHA BIYAR

15
Tun ranar Juma'ah da daddare ta gayawa Umma tana son zuwa ta gaida Baban Hotoro sannan ta biya ta gidan Karima, ta ji dadi sosai da taga Umma batayi wani musu ba kuma da yake jiya da yamma da Yaya Habibu ya zo ya bata dubu biyu, Umma ta karbi dubu daya tana da sauran daya don haka bata bukatar ta tambayi kudin mota.

Ita ta dafa musu abincin safe don haka tana saukewa ta yi maza ta gyara gidan ta wankewa

08, January 2025
Nafisa

I cant download the book

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login