Showing 33001 words to 36000 words out of 92582 words
nace zan je na gayawa Baffa Kabiru in ya so sayi maganar da Baba.'
Ta dago ta dubeshi da damuwa a fuskarta tace
'Aure kuma Mukhtar, ina Safiyya? Yanzu ashe bazaka mayarwa da yaran nan mahaifiyarsu ba in ya so daga baya sai ka kara auren?'
Ya sunkuyar da kai yana shafa keya
'Hajiya ita din ma wannan mun yi magana da ita zata kula da su sosai in sha Allahu.'
Ta zuba masa ido na dan lokaci yayinda shi kuma ya kasa hada ido da ita, jim kadan tace
'Hmn! Mukhtar dan wani da uwar wani sai a hankali fa, zaman bai fiya dadi ba duk kokarin mutum amma Allah ya tabbatar da alkhairi. 'Yar gidan waye ita yarinyar?'
Ya fadada murmushi yana wani juyo da shafar kai
''Yar gidan Professor A. K. Tanko ce.'
'A. K. Tanko mai sharia'a?'
'Eh, shi Hajiya.'
Ta kada kai
'To Allah ya tabbatar da alkhairi, ka sami Baffan naka kuyi maganar.'
Yayi mata sallama ya tashi ya fita, tunda Baba baya nana gara yaje yau din nan ya sami Baffa Kabiru don aje ayi magana.
Ba tare da wata matsala ba Baffa Kabiru ya fahimceshi, duk da shi din ma ya tuna masa dawo da Safiyya amma sai ya nuna ba zai yiwu ba. Don haka Juma'ah tana zagayowa aka je akayi tambaya inda ba a taso ba saida aka bayar da kudin aure aka saka ranar biki wata hudu.
Nan da nan ya cigaba da gininsa wanda yakeyi a unguwar zoo road; gida ne matsaikaici me ban sha'awa. Lokacin da ya sayi filin sai da ya kai Safiyya ya nuna mata sannan sukayi shawara a gina gida mai bene don tana sha'awar gidan sama. Daki uku ne a sama da falo da kuma dining area, kasa kuma daki biyu da falo da kichin sai wani karamin daki da yace yara ya yiwa wajen karatu.
........
Yau Juma'ah don haka ana saukowa daga masallaci ya wuce gidan Suraj don sun yi zai rakashi sabon gidan don ya dubo ma'aikatan. Bayan matar Suraj tayi masa iso ta kawo ruwa sannan ta zauna suka gaisa yayinda Suraj din ya fito daga daki ya dubeshi yace
'To abokina muje ko?'
Ya mike ya dubi Maman Anwar yana fadin
'To Madam mu mun tafi zamuje mu duba ma'aikata ne a sabon gidana, kada ki damu har nana zan dawo miki da shi ba zan barshi ya je ko ina ba.'
Tayi dariya tace
'Da kuwa ka kyauta.'
Ta dubi Suraj tace
'A dawo lafiya.'
Suka wuce suka kama hanya a motar Mukhtar din.
A hankali suka dinga zaga gidan da yake an gama kusan duka ginin, masu aikin wutar lantarki ne suke saka wayoyi a cikin bango. Suna dubawa suna hirarsu yana kara yiwa Suraj bayanin dakunan, suka zo wajen karamin dakin da yake kasa wanda yayi don karatun yara. Suraj yace
'Amma dai wannan bai kai daki ba ko? Sai dai ko masu aiki?'
'A'a, su Nurain na yiwa shi don su samu wajen karatu da wasa.'
'Yayi kyau, ka yi dabara kuma suma za su ji dadin hakan.'
Suka dan yi shiru suka karasa suka shige kichin yana leka inda suka sako wayoyin, Suraj da yake kusa dashi yana taya shi dubawa yace
'Wai ya labarin Safiyya kuwa? Ko shikenan Jamila tayi fatali da ragowar son da ake mata?'
'Ba zaka gane ba mutumi na, ai Safiyya tuni na barwa mai rabo. Da dai ace zan iya hada mata biyu to da na dawo da ita ko da bayan Jamilan ta tare ne amma gaskiya bana sha'awar zama da mace sama da daya.'
'Allah sarki su Nurain, mutumina kai ko lissafinsu ma baka yi!'
'Kai! Ai dole nayi lissafinsu. Ai ko itama Jamilan sai da muka yi da ita zata rike min su amana sannan aka fara maganar auren, ai duk matar da ba zata rike min yaran nan ba to ba mata ta bace.'
'Ba zaka gane ba mutumina, ka ganni ko indai da rai da lafiya duk matar da ta haifarmin yaro ko daya ne ba zan iya rabuwa da ita ba sai dai idan yaron nan ya rasu.'
Ya kyalkyale da dariya ya dafa kafadarsa yace
'Matsoraci, Hajara dai ta saka ka a kwalba sai yanda tayi.'
Shima dariyar yayi yace
'Duk abinda zaka fada ka fada, ka gode Allah iyayenka suna tare har ka girma. Ni na zauna da matar uba kuma na san ciwon rashin uwa, makiyina ma bana masa fatan Allah ya jarrabeshi da irin wannan zaman. Kai ka san irin wahalar da muka sha ni da kannenna a hannun Anti. Idan dai ka bata yaran nan to ka sa ido sosai idan ba haka ba a gabanka zata kashesu ta ce maka mutuwa sukayi.'
Maganganun Suraj sun ratsa shi amma basu kai su sa ya duba yiwuwar dawo da Safiyya ba, shi zai so ma yaga idonta idan ta ga zai auri kyakkyawar yarinya kamar Jamila. Haka suka karasa zaga gidan zuwa magriba ya sallami sauran ma'aikatan suka kama hanyar gida.
Sai da Mukhtar ya ajiye Suraj a gida sannan ya kama hanyar gidan Hajiya.
Babu wadda yake gani a halin yanzu sai Jamila, idan ba ganinta yayi a cikin gidansaba ba zai sami natsuwa ba. Ya aminta da tarbiyyarta gata kuma wayayyiya, don haka yana ganin da shi da yaransa za su sami duk wata kulawa daga gareta.
--------
Safiyya ce a zaune a daki a kan dadduma bayan da ta idar da sallar la'asar, daga inda take tana jiyo hirar Umma da Hamida a falo wadda da ace zata zo ta saka baki a hirar da sai Umma ta san abinda zata yi mata fada a kai. Sai yanzu take gane abinda ya sa mata ke hakuri su zauna da miji komai wulakancinsa, bata san ko zuwa tsawon wane lokaci wannan zaman zai zo karshe ba. Kamata yayi ace ta je ta dora abincin dare, amma gajiya tayi mata yawa. Matar da take yiwa Umma wanki bata da lafiya kwana biyu bata zo ba don haka yau dolenta ta wanke kayan Umma ta hada da nata.
Tana nan zaune ta jiyo Umma na cewa Hamida taje ta dora abincin dare; ta tabe baki don ta kwana biyu rabon da ta ga Hamida tana girki kusan tunda ta dawo gidan. Ta dauki wayarta ta duba lokaci, karfe biyar saura minti goma, ta mayar da wayar ta ajiye.
Tana nan tana lissafin tashi ta jiyo sallamar Saliha da Rukayya; yaran Baban Hotoro. Suka zauna a falo suka gaisa da Umma da Hamida, Umma ta tashi ta shige daki ta basu wajen.
Saliha ta dafa cinyar Hamida tace
'Hmm, ga ankon ku ke da Yaya Safiyya, jiya na kama Yaya Habibu yaje gaida Baba na lika masa na ce yanzu ake biya, kin san kafin ya bar gidan sai da naji alert ya biya muku ke da Ya Safiyya har dubu goma ya bamu ni da Rukayya wai mu sai janbaki. Kin san Ya Habibu ba dai kyauta ba.'
Ta karbi ledar da murmushinta tana fadin
'Kai amma wallahi kin min dai-dai ta wajena, yanzu sai dinki kawai.'
Ta ta shi ta dauki ledar ta bi Umma daki ta nuna mata sannan ta dawo ta kawo musu ruwa suka cigaba da hira. Jimawa kadan Rukayya tace
'Wai ina Yaya Safiyya ne?'
'Tana daki.'
Hamida ta fada tana nuna kofar dakinsu, nan take ta mike ta fada dakin tare da sallama.
Ta karasa kan dadduma suka gaisa da Safiyya tana ce mata ya hidimar bikin, nan ta gaya mata labarin ankon da suka zo musu da shi. Suka yi shiru na dan lokaci Rukayyan ta dubi Safiyya tace
'Ya Safiyya wai baki da lafiya ne? Wallahi naga duk kin rame.'
Tayi dariya tace
'Lafiya ta kalau, bari ma ki ga yau nice zan dafa mana abincin dare amarya.'
Ta mike suka fito tare da Rukayyan, ta tsaya a falon suka gaisa da Saliha sannan ta wuce kicin kafin ta karasa Hamida tace
'Ya Safiyya na dora a abincin ai.'
Jimawa kadan suka tashi sukayi sallama da Umma da Safiyya suka wuce tare da Hamida wadda zata raka su. Suna Safiyya ta koma daki, gaban mudubi ta wuce ta tsaya ta zubawa fuskarta ido a mudubin; tabbas ta rame. Ta kai hannu ta shafa kasusuwan wuyanta tana kallonsu yanda suka fito wuyan nata ya kara sirancewa, tayi murmushi wanda yayi dai-dai da kwacewar kwalla a idonta. Ta goge kwallar ta juyawa mudubin baya ta dan zauna gefen mudubin. Ta sake shafa kasusuwan wuyan nata; ba dole ta rame ba, shekara hudu kacal da aure amma ace har auren ya mutu. Tana son mijinta tana son yaranta amma ace yanzu tsakaninta da su sai dai daga nesa, ga shi Umma duka ta tsangwameta kamar ita ta saki kanta. Gaba daya ma rayuwar ta fice mata daga rai, babu abinda yafi kona mata rai irin yanda Umma ta hada kai da Yaya Hajiyayyaye suka juya mata baya. Sune matan da suke cikin rayuwarta wadanda ya kamata ace sune za su bata baki a yanayin da take ciki amma sune suka juya mata baya, lallai dan Adam bashi da tabbas.
Ta yunkura da kyar ta hadiye malolon da ya tokare mata makogoro, hawaye ya gangaro kan fuskarta. Nan da nan ta saka hannu ta goge hawayen tare da mikewa ta fada bandaki don bata son Hamida ta shigo ta ganta tana kuka; duk ranar da Hamidan ta ganta tana kuka to idan ta gama lallashinta tana bata hakuri sai kuma ta gayawa Umma; ita Hamida tana gayawa Umma ne don Umman ta rage damun Safiyya amma ita Umman nan zata saka Safiyyan a gaba da fada da bakaken maganganu tana fadin
'To wa ya janyo miki, da zaki saka mutane a gaba da kuka? Ko ba Mukhtar din yana nan yana yawo a gari ba? Ki lallabo shi mana ku koma kina abu kamar ba mace ba.'
Ta tsani wadannan kalaman na Umma don haka ma tayi wa kanta alkawarin tunda ta kasa daina kuka to bazata sake yarda a ganta tana yi ba.
........
Washegari da safe suna zaune a falo gaba dayansu har Umman da yake wasu lokutan Safiyyan tana zama a cikinsu in Allah ya taimaka sai Umma ta barta su taba hirar ba tare da ta gwaleta ba, Hamida ta shiga dakin Umma ta dauko ankon da aka kawo musu jiya. Sai a lokacin Safiyya ta ganshi, leshi ne mai kyau shudi da kwalliyar ruwan kwai, sosai ya burgeta har taji tana sha'awar zuwa bikin. Hamida ta zauna kusa da Umma tace
'Umma ki kawo deposit na kaiwa Babangida ya dinka min.'
Kafin Umman ta amsa ta dubi Safiyya tace
'Ya Safiyya kema na hada har da naki a dinki mana.'
Tayi Dan murmushi tace
'Da kin kyauta kuwa.'
Umma ta dubi Hamidan tace
'Ina naga kudin biya muku ku biyu? Kin san wajen su Babangida yanzu za kiji sun kirawo dubu goma. Ita dai Safiyyan ta ajiye nata har na sami kudi ke da yake kina cikin 'yan matan amarya sai na biya miki.'
Hamida tace
'To shike nan Umma, bari na fito daga wanka yanzu zan je na kai. Allah ya sa ki sami kudi kafin bikin a dinka na Yaya Safiyyan.'
Ba a jima ba suka jiyo sallama Yaya Hajiyayyaye ta zo tare da yaranta, wuni suka zo yi.
Nan aka gaggaisa aka cigaba da hira. Zuwa bayan azahar Hamida ta fito daga wanka ta shirya tana dauke da leshin zata kai dinki, ta dubi Ya Hajiyayyaye tace
'Dinki zan kai Yaya Hajiyayyaye na ankon bikin su Saliha, da ma kina da kudi ki biyawa Ya Safiyya tunda ni Umma zata biya min.'
Nan take ta bata rai ta kawar da kai
'Bani da kudi, ita Safiyyan bata da shi ne.'
Hamida ta langabe kai tace
'Wallahi bata da kudi Yaya Hajiyayyaye, kema kin sani.'
'To ai kuwa dai nima bani da shi sai dai ko daga baya.'
Ta yi musu sallama ta wuce ta tafi kai dinkin ta.
Haka akayi ta wasa da hankalin Safiyya a kan dinkin, tana son ta tambayi Yaya Habibu amma tana jin kunyarsa saboda shi ya sayi ankon kuma leshin ance dubu goma sha biyu ne. Don haka ta tattara ta hakura, zuwa bikin ma gaba daya ya fice mata daga rai. Sai da ya zama saura kwana biyu a fara bikin sannan Sabir ya gayawa Yaya Habibu bata da kudin dinki, don haka Yaya Habibu da kanshi ya zo gidan ya bata dubu biyar yace ta tafi yanzu ta kai dinkin kafin magriba don lokacin la'asar ta wuce.
Ta saka hijabi ta dauki kayan, akwai wani gida da suke kai dinki tun kafin tayi aure gidan Umman Zee can ta nufa don nan ne kawai take jin zata samu dinkin a kwana biyu.
A tsakar gida ta samesu don haka itama nan ta zauna, suka gaisa da Umman Zee cikin fara'a. Ta bata dinkin tayi mata bayani sannan ta bata kayanta wadanda zata dauki awonta a ciki, ta duba ta gaya mata ta kawo naira dubu uku da dari biyar, sukayi alkawari a kan idan zata zo karba zata zo da kudin. Sukayi sallama ta mike, Umman Zee ta biyota don tayi mata rakiya. Sai da suka zo soro har Safiyyan zata fita sannan cikin murya kasa-kasa Umman Zee tace
'Umm Safiyya ni kuwa in tambayeki? Wai da gaskene aurenki ya mutu?'
Ta hadiye dan mamakin da yake fuskarta ta ta dubi Umman Zee suka hada ido, ta kara kakkafeta da ido kamar wadda aka kai kotu. Tayi murmushi ta sunkuyar da kai
'Eh, aurena ya mutu harma na gama idda akwai wani abu ne?'
Ta fada itama tana tsattsare Umman Zee din da ido tana jiran taji mai zata ce. Ta sunkuyar da kai tana sosa keya
'Uhm, a'a, babu wani abu. Hmm, dama kawai dai tambaya ce da yake kana ta ji a unguwa. Allah ya sa haka ne ya fi alkhairi, Allah ya daidaita tsakaninku.'
'Amin na gode.'
Ta amsa cikin halin ko in kula, ta juya ta nufi kofa tana fadin
'Sai na zo din.'
'To Allah ya mai mu.'
Ta kamo hanya tana tunani kala-kala; yanzu labarin mutuwar aurenta har ya karade unguwar kenan, lallai zancen duniya baya buya. Ta riga ta san Umman Zee da gulma don haka abinda tayi bai dameta ba
Ta kama hanyar komawa gida, tafiya take tana ta sauri saboda magriba ta kusa; saura kadan ta Fadi da tazo gaban wasu maza da suke zama a bakin hanya kafin a karasa gidansu. Da ba dan kada ace ta sa musu ido ba da sai tace gulmarta sukeyi, domin yawancinsu ta san su a nan unguwar.
........
Sai da aka idar da sallar isha'i sannan ta zubo tuwo, har zata wuce daki taga Hamida da Sabir a falo suna kallon wani fim din Hausa don haka ta nemi waje ta zauna a kan kujera don itama tayi kallon.
Ta cika bakinta da lomar tuwo suka jiyo sallama daga tsakar gida, da yake Umma tana kicin ita ta amsa sallamar. Yaron ya karaso tsakar gidan cikin daga murya yace
'Wai ana sallama da Safiyya.'
Ta saka lomar da take hannunta a baki don ta zata Hamida ake kira sai kuma ta tuna itace Safiyya, lomar tuwon ta kwace ta wuce ba tare da ta tauna ba. Kafin ta gama gyara zama ta jiyo Umma tana bawa yaron amsa
'Kace tana zuwa ka ji.'
Ta zaro ido suka hada ido da Sabir ya bushe da dariya yayinda ita kuma ta galla masa harara, Hamida ta kalleshi tayi gyaran murya. Ya mike yana fadin
'Ya Safiyya bari in je screening kafin ki fito.'
Kafin ta amsa Umma ta shigo falon ta dubi Safiyya tace
'Shine baki gaya min za kiyi baki ba?'
Ta kalli Umma ta sunkuyar da kai saboda yanda Umman ta tsattsareta da ido
'Wallahi Umma nima ban san waye ba, ban san da zuwan kowa ba.'
'To sai ki tashi kije ki gani, bamu sani ba ko za a dace.'
Ta so tace bazata je ba saboda bata san waye ba kuma bata jin ta shirya fadawa soyayyar wani namiji a halin yanzu, amma yanda Umma ta tsattsareta da ido ta san idan tace bazata je ba ta janyowa kanta fada. Don haka jiki a sanyaye ba tare da ta koshi da tuwon ba ta tashi ta kai kwanon kicin ta dawo ta wuce daki. Hijabi kawai ta ziro ta fice don ganin wanda yake nemanta.
Tana fitowa daga gate ta cinkaro da motarsu daf da bakin gate din, tana tsayawa suka fito daga cikin motar. Suka karaso inda ta ja ta tsaya tana kallonsu; bata gane fuskokinsu ba don bata jin ta taba ganinsu, amma tabbas motar itace wadda ta wuce dazu a daf da majalisar nan da take kusa da gidansu.
Bayan ta amsa sallamarsu tayi musu iso cikin farfajiyar gidan, da yake kawai irin kujerun robar nan a wajen sai kawai ta gyara kujerun ta ajiye su daf da kofar shiga tsakar gidan suka zauna gaba dayansu. Bayan sun gaisa suka yi shiru na dan lokaci, daya daga cikinsu wanda ta kula kamar shine dan rakiyar yace
'Malama Safiyya na san baki san mu ba, ni sunan Bashir wannan kuma abokina ne Sulaiman. Muna zaune dazu muka ga wucewarki shine abokina ya nuna bukatar ya zo ko zai dace shine na rakoshi.'
Tayi murmushi kawai ta sunkuyar da kai; har yanzu jin kanta take kamar matar aure ce ita, ji take kamar wannan hirar da takeyi da su bai dace ba. Sulaiman ya yi gyaran murya yace
'Baki ce komai ba malama Safiyya.'
Murmushin kawai ta sakeyi don bata san me zata ce masa ba. A haka dai suka dan taba hira wadda yawanci sune suke mata tambayoyi tana basu amsa. Jimawa kadan Sulaiman din yace
'Bari mu tafi haka kada mu cika ki da suruta, kin barni sai faman zuba nake.'
Bashir din ya mike yayi mata sallama ya dubi Sulaiman din yace
'Abokina ina jiranka
08, January 2025
Nafisa
I cant download the book