Showing 3001 words to 6000 words out of 92582 words

Chapter 2 - MATAR MUKHTAR COMPLT

SAKINA   

16 Aug 2024

7135

na safe Aminu zai zo ya kaishi airport saboda jirgin karfe takwas da rabi zai bi.


Wajen karfe goma na dare suna kwance a daki, da yake bai gama abinda yake ba fitilar a kunne take. Hankalinsa yana kan wayarsa yanata 'yan karance-karancensa yayinda ita kuma take kwance ta rufe idonta amma ba bacci take ba, yanayi yana sosa mata tafin kafarta da yatsunsa na kafa.

Hankalinta baya wajen saboda yanda kwakwalwarta take caji; yanzu haka ma wannan tafiyar tare da Sucre din zasu je, ko kuma sai yaje can zai nemi wasu matan oho. Ta dai san masu neman mata sun saba yin tafiya su bar iyalansu a gida su tafi su kama hotel su kwana da matan banza, ta sani ma ko 'yan matan nasa suna da yawa.

Ta gyara kwanciyarta a karo na babu iyaka, ya rankwafo kadan ya hura mata iska a kunne, tayi firgigit


'Aaah!'


Yayi dariya


'Haka kawai zaki dinga yi min labe da sunan bacci.'


Ta sake gyara kwanciyar


'To kanata sosa min kafa ina zan iya bacci.'


Suka sake yin shiru ya mayar da hankalinsa kan waya.


Jimawa kadan ta mike zaune ta dubeshi, shima ya dubeta yana dariya yana fadin


'Kin fasa baccin kenan zaki taya ni hira ko kuma kewata kika fara tun yanzu kike kare min kallo?'


Ta sunkuyar da kai tace


'Hmm! Don Allah kai da wa zakuyi tafiyarnan?'


Ba tare da ya kalleta ba yace


'Ni da sauran ma'aikata mana.'


Suka sake yin shiru na dan lokaci.


'Mukhtar.'


Ta kira shi da sunansa wanda ba haka ta saba kiranshi ba. Ya sauke wayar da yake dubawa a kan cikinsa ya dubeta sannan ya amsa


'Yes.'


'Ita Sucre din sai kun je can zaku hadu kenan?'


Tambayartata ta shammaceshi don bai san ta san da Sucre ba balle har ya sa rai ta san tare da Sucre za su tafi, nan da nan fuskarshi ta canza. Ya tashi zaune da hanzari har wayar da ya ajiye a kan cikinsa ta fado kasa, ya dauke wayar ya ajiye a kan durowar gefen gado tare da tattaro nutsuwarsa sannan ya juyo ya kalleta. Yayi wani gyaran murya kamar na mara gaskiya tare da kara tsuke fuska


'Me ya hadaki da wayata har kika yi min bincike? Daman shi ya sa kwana biyu kika sa kanki cikin damuwa ko?'


Ya tsagaita yana saurarenta.


Ta tashi zaune sannan tabe baki da kyar cikin tsananin damuwa ta dubeshi tace


'Idan ka amsa min tawa tambayar in sha Allahu nima zan amsa maka taka.'


Ya kalleta a wulakance ya ja tsaki mai cike da takaici sannan ya bata amsa


'Tare da ita za mu sai me, me zaki iya yi a kai?'


Ranta ya kara baci, zuciyarta ta harzuka kwarai, take hawaye ya fara bin fuskarta ta fara hasbunallahu wa nimal wakeel a zuciyarta.


'Babu abinda zan iya yi a kai sai dai nace Allah ya kiyaye hanya kuma na tuna maka itama 'yar wanice ubanta yana sonta yana son ya kare mutuncinta kamar yanda kake son kare mutuncin Nana, sannan malamai sun tabbatar mana zina bashi ce idan ka shiga zuri'ar wani da ita sai an shiga taka.'


Ta kalleshi da idanunta da suka riga suka ciko da hawaye, suka hada ido, zai yi magana ta daga masa hannu sannan ta mayar da hannun ta dafe kirjinta da a yanzu yake mata zafi tace


'Allah ya yafe maka, kada Allah ya nuna min ranar da wani zai yiwa Nana abinda kakeyi da 'yar wasu.'


Ya harzuka sosai ya mike daga kan gadon ya tsaya a jikin wardrobe yana mata wani kallon wulakanci da takaici


'Kin yi min bincike a waya kuma kin sani a gaba kina gaya min maganganun banza kina nema ki aibata min 'ya saboda tsabar wulakanci ko Safiyya. Toh Allah ya baki sa'a ki cigaba da bincika min waya watarana za ki ga abinda zai sa zuciyarki ta buga.'


Ta bude baki zata yi magana ya nuna mata kofar yace


'Ki fice min daga daki tunda kin gama rashin kunyar kafin yanzu ki sa na buge miki baki.'


Itama da yake ta gaji da jan zancen kuma ba son ganinshi take yi a halin yanzu ba kawai sai ta sauko daga kan gadon ta dauki wayarta ta fice daga dakin tana share hawaye.

Dakinta ta wuce kai tsaye, tana shiga ta turo kofar ta sa mukulli ta rufe da yake yaran suna wajen Hamida suna baccinsu a dakin baki.

Ta zauna a gefen gado ta zuba fuskarta a tafukan hannunta tana kuka, hotunan da ta gani na tsiraicin Sucre ne a wayarsa suke dawo mata da kuma maganganun batsar da yake aika mata da su. Yanzu wannan mutumin da take kallonsa a matsayin mutumin kirki shine ya aikata wannan badalar kuma wai ita yake son ma ya dorawa laifi.


'Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun.'


Ta share hawaye ta cigaba da kuka, sai da ta gaji da kukan sannan ta mike ta yiwo alwala. A kan dadduma ta zauna ta dauki kur'ani ta bude don ta karanta domin bata jin kafafunta za su iya daukarta tayi tsaiwar Sallah.

Duk yanda take son tayi karatun kur'ani ta kasa saboda yanda bata gani sosai, gaba daya hawaye ya hanata gani sosai. Dole ta rufe kur'anin ta ajiye, ta cigaba da share hawaye. A hankali ta mike tsaye ta kabbara Sallah, tana yi tana kuka har ta samu nutsuwarta ta dawo. Nan a kan daddumar bacci ya dauketa bayan ta idar da sallar.


..........


Tana fita daga dakin ya ja tsaki ya koma ya zauna a kan gadon ya dafe kansa. To yaushe Safiyya ta duba masa waya har taga sakonnin Fatima wadda yayi saving sunanta da Sucre don ya badda kama, in dai yana cikin gidan baya kiranta itama bata kiransa don haka ya san tabbas sai dai idan ta Whatsapp Safiyya taga sakonnin su. To yaushe ta gani?

Maganar da suka yi jiya ma ya tura mata kudin jirgi don ta sameshi a Abujan suna gamawa ya goge, don haka yake mamakin yanda akayi Safiyyan ta san tare za su tafi.

Yayi tsaki ya dunkule hannunsa ya naushi daya hannun dashi.

Maganganunta sun so suyi tasiri a kansa musamman da ta sako batun Nanansa, amma shi wane irin sakaci ne zai sa ya bar Nana ta yi jami'a a wata jihar da ba a nan yake ba sannan ya barta ta zauna a hostel. Ya jijjiga kai, ba yadda za ayi ya bar Nana tayi nisa da gida kamar Fatima(Sucre).


Shekararsa daya da auren Safiyya ya hadu da Fatima. Yar Zariya ce karatu ya kawota jami'ar Bayero ta Kano, basu da dangi a Kano don haka dole ta kama hostel ta zauna duk da ba haka mahaifiyarta ta so ba amma da yake mahaifinta ya goya mata baya dole ta kyaleta. Tun bata saba da Kano ba suka hadu da Mukhtar don haka shi ya dinga daukarta yawo yana nuna mata gari har ta saba.

Soyayya mai karfi suka kulla har yayi mata alkawarin aure, don haka ta saki jiki da shi matuka.

Ita din ba lalatacciya bace don haka da fari soyayya suke mai tsafta, duk inda take so zai je da kanshi ya kaita kuma duk abinda take so zai saya mata. Har Zariya yake kaita gida idan aka yi hutu don haka ya gaisa da mamanta sun san juna.

Bai taba boye mata yana da mata ba itama kuma bata da matsala da auren mai mata musamman da yake tana tsananin son Mukhtar din.

A hankali ya saba da rike mata hannu daga nan ya saba da rungumarta yana tsostsar bakinta yadda yake so. Sai da ta saki jiki ta saba da wannan sosai sannan ya fara daukarta su fita da daddare, idan suka gama cin abincinsu sai ya kama daki a hotel ya lallatseta sannan ya mayar da ita hostel. A haka har ya kai ga biyan bukatarsa a kanta inda shi kansa ya san a budurwa ya sameta.

Ta so ta daga hankalinta amma da yake shi din mutum ne da ya iya tsara zance sai ya lallabata ya nuna mata ai shine zai aureta wanda jira kawai yake ta gama karatu kafin nan aurenshi da Safiyya ya kwana biyu don haka ba za a ce komai ba. A hankali ya mayar da ita kamar matarsa, sai dai kawai ya kama musu daki idan ya gama da ita ya mayar da ita hostel. Da yake yana amfani da condom sai ya zama a bata tsoron samun ciki.


Bai san tsawon lokacin da ya dauka yana zaune yana tufka da warwara ba har dai ya gaji ya tashi ya kwanta, ba zai canza tsarin da yayi ba don ya riga ya gama komai itama yayi mata booking jirgin, sai dai ita jirgin karfe goma ya kama mata don ko daya baya so a gansu tare. Haka ya kwana yana juyi yana tunani, bai so ba Safiyya ta gane alakarsa da Fatima sai dai babu yanda zai yi. Idan ya dawo ya san yadda yayi ya tsarata, amma dole sai ta daina yi masa bincike don ya san in dai bata daina ba to zasu cigaba da samun matsala.

.........



Duk da bata yi baccin kirki ba kuma ranta a bace yake amma haka ta tashi tun kafin karfe shida don ta hada masa abincin safe. Idan zai fita da sassafe baya iya cin abinci da yawa don haka ruwan shayi kawai ta dafa ta soya masa kwai ta hada da burodi wanda ya siyo tun dare ta ajiye masa a falo inda ya saba cin abinci.

Wajen shida da rabi ta ga kamar lokaci zai kure bai fito ba don haka ta wuce dakin don ta duba kada taje ko makara yayi. Da sallama ta shiga dakin, yana zaune a kan 'yar kujerar gaban mudubi ya gama shiryawa tsaf yana dube-dube a waya. Bayan ya amsa sallamarta ya dubeta sau daya ya dauke kansa ya cigaba da abinda yake yi a waya, ta karasa ta zauna a gefen gadon ta inda yake zaune. Ta kakalo murmushi tace


'Ina kwana Abban nurain.'


Ba tare da ya kalleta ba ya amsa a takaice


'Lafiya.'


Ta kula shi a dole fushi yake yi da ita, bata so yayi tafiya suna halin fushi da juna don haka ta sake kakalo murmushi tace


'Baka fito kayi breakfast ba, kada ka makara.'


Ya kalleta zai yi magana sai kuma ya fasa ya cigaba da abinda yake yi, jim kadan ya ajiye wayar a kan mudubin ya dubeta yace


'Kin dafa ne?'


Ta daga masa kai alamar eh. Ya mike ta bi bayansa suka fice daga dakin. Bayan ya zauna ta kunna socket din TV da yake akwai wuta, ta mika masa remote sannan ta zauna a gabansa tana hada masa shayi.

Yana cikin cin abincin ya ajiye kofin shayin ya dubeta yace


'Nurain da Nana basu tashi ba?'


'Eh.'


'Za su tashi kenan suga bana nan.'


Tayi murmushi tace


'Ma yi maka waya.'


Bayan ya gama cin abincin ya dubeta yace


'Akwai kudi a cikin durowa, idan kuna bukatar wani abu sai kiyi min waya ko ki kirawo Saifullahi ko Aminu.'


'To.'


Ta tashi ta fara kwashe kwanukan, kafin ta gama kwashe kwanukan wayarsa tayi kara bayan ya gama amsawa ya mike ya shige dakin.

Tana fitowa daga kicin shi kuma ya fito daga daki yana rataye da jakarsa ta matafiya da wayarsa a hannu.


'Aminu ne ya zo, za mu wuce.'


Ta karasa inda yake tana murmushi ta danyi dage da yake ya fito tsawo sosai; ta sumbaci lebansa tace


'Allah ya kiyaye hanya.'


'Amin.'


Ya fada yana yi mata murmushi a karo na farko tunda garin ya waye. Ya ja hannunta suka fito har kan baranda sannan ya dan tsaya ya dubeta yace


'Ki kula da gidan da yaran kuma ki daina sawa kanki damuwa, sai munyi waya.'


Tayi murmushi, suka yi sallama ya nufi waje ita kuma ta koma ciki.


..........


Gaba daya ranar haka ta wuni a kwance, zuciyarta babu dadi. Duk da ta san taro ya tafi amma zuciyarta tana gaya mata da wata zai kwana, ta kasa cire tunanin daga zuciyarta kuma ta kasa gamsar da kanta cewa shi kadai zai dinga kwana a hotel.

Sunan Sucre kawai zuciyarta take maimaita mata, ta kasa ganewa ma yarinyar musulmai ce ko kuwa? Tunda duk hotunan da ta gani nata tsirara take. Haka tayi ta gyara kwanciya tana share hawaye, zuciyarta sai tafasa takeyi ta rasa wanda zata gayawa taji sanyi. Har azahar bacci yaki ya dauketa duk da yanda take jinsa, kuma da yake ta gayawa Hamida bata jin dadi duk ta rike mata yaran babu wanda ya nemeta.


Sai wajen karfe biyu da ta tabbatar bacci ba zai iya saceta ba ta tashi ta zauna a kan gadon ta tankwashe kafafu ta zuba tagumi.

Gidansu take son zuwa ta gayawa Ummanta ko zata ji sanyi a ranta, sai dai kuma bata son ta dorawa Umman damuwa. Don haka ta fasa, gara ta je ta gayawa Yaya Hajiyayyaye tunda ta san duk wata shawara zata samu daga gareta.


Take ta sauko daga kan gadon ta shiga bandaki domin tayi sallah ta shirya ta tafi.
MATAR MUKHTAR

Written by:
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA UKU

03

Saida ta idar da sallah ta ci abinci sannan tayiwa Hamida sallama ta bar mata yaran ta wuce gidan Yaya Hajiyayyaye.

Da yake karfe uku ta wuce lokacin da ta isa tana shiga taci karo da yaran gidan suna tafiya islamiyya, sukayi mata sannu da zuwa suka wuce. A falo ta sami Yaya Hajiyayyayen tana jin rediyo. Bayan sun gaisa ta dubeta tace


'Ya na ganki ke kadai ina yaran nawa?'


Tayi murmushi


'Suna gida, da yake Hamida tana nan kuma ba dadewa zanyi ba.'


'To Allah ya sa dai lafiya, na ganki firgai-firgai.'


Tayi dariya ta kau da kai


'Lafiya kalau Yaya, zuwa dai nayi.''


'Cikine dake ko?'


Tayi dariya


'Wallahi ba wani ciki Yaya.'


Kiran sallar la'asar ne ya katse musu hirar, suka tashi gaba daya sukayi sallah.


Tana zaune a kan daddumar da ta idar da sallah a dakin Yaya Hajiyayyaye yayinda Yaya Hajiyayyayen take zaune a kan daya daddumar inda itama ta idar da tata sallar. Ta shafa addu'arta bayan ta idar da azkar ta dubi Yaya Hajiyayyayen tace


'Bari na tashi na koma.'


Ta kalleta tana murmushi


'Uhm, ai baki gaya min abinda ya kawo ki ba.'


Tayi yar dariya. Tana mamakin yanda Yaya Hajiyayyaye take karantarta sosai, ta san ko da tace mata babu komai bazata yarda ba duk da ita din ma bazata tafi ba tare da gaya mata ba. Sukayi shiru na dan lokaci, jimawa kadan ta dubi Yaya Hajiyayyaye tace


'Dama Abban Nurain ne?'


Ta mayar da hankalinta gaba daya kan Safiyyan sannan ta bata amsa


'Me ya faru da Abban Nurain din?'


Ta kau da kai ta share kwallar da ta taru a idonta, ta rasa dalilin da yasa in dai ta tuno wannan bakin cikin sai tayi hawaye.


'Yaya wai ashe Abban Nurain yana neman mata ban taba sanin ba sai kwanakin nan.'


Ta kama haba tana mamaki


'Ke Safiyya, kin san me kike fada kuwa? Kada fa kije ki bata aurenki a kan wani zargi na banza da wofi.'


Ta sake share kwalla sannan ta bata amsa


'Yaya wallahi ba zarginsa nake ba, da idona na gani a wayarsa kuma dai wadannan abubuwan da na gani basuyi kama da na mai neman aure ba wallahi sai dai mai aikata zina.'


'Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun.'


Ta taso daga tata daddumar ta dawo daddumar da Safiyyan take zaune ta zauna a gabanta tana kallon fuskarta


'To ai kinga abinda ake gudu ake hana mata duba wayar mazajensu, yanzu da can tunda kuka yi aure da baki duba ba kinga kuna zamanku lafiya. Haka kawai yanzu kinje kin bincikowa kanki abinda zai hanaki sukuni.'


'Ni fa ba bincike nayi masa ba Yaya, kuma ma da ban yi masa binciken ba ai tunda mukayi auren nake fama da ciwon sanyi. Ke kanki fa sau biyu kina karbo min magani, duk gidan da naje bana shiga bandaki saboda a zatona a nan nake samo ciwon. Sai faman kame-kame nake ashe shi yake kwasowa ya shafa min. Tsabar idona ya rufe kuma zuciyata babu zargi shi yasa ma ban kawo komai ba don wani lokacin ko gaya masa bana yi saboda kada ransa ya sosu.'


Nan dai ta bata labarin yanda akayi ta gane da kuma kadan daga cikin irin sakonnin da ta ji ta gani. Hajiyayyaye ta bude baki tana tafa hannu da mamaki domin gaba daya basu taba zaton Mukhtar zai aikata wani abu mai kama da wannan ba. Suka yi shiru na dan lokaci, jimawa kadan ta cigaba


'Kuma fa da nayi masa magana jiya da daddare cewa yayi duk abinda zanyi naje nayi.'


Ta kama haba tana mamaki


'Subhanallahi! Shi Mukhtar din ne ya fada miki haka?'


Ta jijjiga kai tana share kwalla.


'Kai jama'ah! To ai shi yasaka dai ake hanaku duba wayar miji domin ita wayar miji kamar albasa take, in dai za ki duba to zakiyi kuka. Kuma da yake baki da wayo sai kika yi masa maganar ai dama kin taro rigima.'


Ta kalleta ta kawar da kai don ta fuskanci Yaya Hajiyayyaye so take ma tace laifin nata ne, bata ma tunanin yanda za ayi ya daina so take kawai tayi mata fadan yi masa bincike.


'Kenan yanzu shi bashi da laifi, nice nayi laifi da naga abinda yakeyi kuma nayi masa magana?'


Ta kamo hannunta tana kallon fuskarta


'Ba haka bane tabbas yana da laifi to amma ya zakiyi da shi? Ko babu komai dai kin san shine yake da shugabanci a kanki don haka ma ba zai saurareki ba. Kuma ma idan banda abinki mazan yanzu ai duk haka suke, sai dai kawai kiyi ta hakuri.'


Ta zare hannuwanta duka biyun ta share hawayen da kawo yanzu ta bari yana zuba ba tare da wani shamaki ba


'Yanzu kenan haka zan zauna ina ji ina gani ya dinga raba mana kwana ni da matan bariki, kuma duk cutar da ya debo ya zo ya shafa min ba yanda na iya.'


'A'a ba haka bane, ai kema ba zama zakiyi ba. Dagewa za kiyi ki ta addu'a kina sadaka, sannan kuma duk inda kike da gazawa sai kiyi kokari ki gyara. Don wani mijin matar ce take sa ya fara yawo saboda halinta. Ki kara tsafta da kula da jikinki sosai, kuma ki dage da kwalliya. Wajen kwanciyar auren ma kuma ki kara dagewa, duk abinda kike jin yana bukata kiyi masa. Kin san wasu matan basa zagewa su sarrafa miji a wannan lokacin shi yasa

08, January 2025
Nafisa

I cant download the book

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login