Showing 21001 words to 24000 words out of 92582 words

Chapter 8 - MATAR MUKHTAR COMPLT

SAKINA   

16 Aug 2024

7139

shi yasa ya kawo miki yaransa?'

Ta zare ido tare da dafe kirji tace

'Subhanallahi! Saki kuma? Ni bai gaya min ba yara su Habiba ne suka je gidan suka taho da su, ya ma zo daukansu nace bazasu tafi ba sai an kwana biyu.'

Baba yace

'To ya saketa yau kuma saboda tsabar rashin hankali bai yi shawara da mai zuwa masa neman auren ba yayi sakin.'

Baffa Kabiru ya dubeshi yace

'Wai me tayi maka ka sake ta?'

Da kyar ya hada yawun bakinsa ya nemo muryarsa ya sake shafo kansa sannan yace

'E dama Baffa bincike take min a waya kuma tana min rashin kunya don yau din nema tayi ta zageni.'

'Shine kai kuma kayi mata saki nawa?'

'Daya ne Baffa.'

Hajiya tace

'Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun, yanzu ka kasa shawara da ni idan da wata matsala Mukhtar? Ai shikenan daga ni har iyayen naka bamu da wani amfani kenan.'

Ya bude baki zaiyi magana Baffa ya dakatar dashi

'Kayi kuskure Mukhtar, mace idan ka aureta ka sameta tana maka biyayya to rike ta kake yi, idan ka sake ta fita taje ta ga abubuwan dake faruwa a duniyar waje to za ayi dayan biyu; ko taki dawowa gidanka ko kuma idan ta dawo ta canza hali ka kasa gane kanta.'

Baba ya dubeshi yace

'Ai shikenan, Allah ya sauwake. Tashi ka bani waje.'

Da sauri ya tsahi ya fice yana neman yin tuntube saboda dama kamar a kan kaya yake jinsa. Hajiya ta dubi Baba tace

'Alhaji ai ce masa zakayi yaje ya dawo da ita yanzun nan ka barshi ya fita, in ba ayi wasa ba yanzu zai gudu tunda bashi da gaskiya.'

Ya jijjiga kai yace

'Duk lokacin da ya shirya ya dawo da ita idan ya gane mahimmancinta a rayuwarsa, idan aka saka shi ya dawo da ita ba da son ransa ba haka zai saka ta a gaba yayi ta muzguna mata abun ya kara lalacewa. Kina nan zaune zai zo da zancen aje a dawo masa da ita, za ki ga yanda zamuyi dashi.'

Baffa Kabiru yace

'Gaskiya ne, duk da ban yarda da zancen bakinsa ba amma dai wani abun sirrine na aure idan tayi wari ma ji.'

Suna nan zaune Baffa Kabiru ya kirawo Baban Hotoro ya sanar dashi abinda sukayi ita da Mukhtar din yarinta ne amma yana ga idan an basu lokaci komai zai yi dai-dai, ya sake basu hakuri sukayi sallama.
........

Sai da daddare sannan Yaya Habibu yazo gidan, ya sa Safiyya a gaba da nasiha daga karshe yace

'Ki daina damuwa kinji, ki mayar da hankali kiyi ta ibada komai zai wuce in sha Allah.'

Umma da take zaune bata saka musu baki ba tace

'Kada ma ta daina damuwar, wa ya janyo mata? In banda shegiyar fitnar tsiya tunda ya zabi ya bi matan banza ki kyaleshi mana ki rungumi yaranki amma s..'

Yaya Habibu ya katseta da murya mai cike da girmamawa

'Umma, in dai abinda ta fada gaskiya ne bata fa da laifi, mutumin da yake da damar auren mace hudu amma ba zai yi auren ba ya dinga bin yaran mutane yana lalatawa. Ga ya mace nan ta haifa masa idan hakki ya fado a kanta kuma sai muce ita ta barta ta lalace bayan haka ubanta yayiwa yaran wasu. Kumafa Umma Allah cewa yayi 'ku amfusakum wa ahlikum naara..' kin ga itama hakki ne a kanta tayi iya kokarinta taga ta tseratar dashi fushin ubangiji, ba zai yiwu ta zuba masa ido ba. Kuma idan ya dawo din ma za a zauna ayi magana ai mu ba arna bane musulmai ne.'

Harararsa kawai Umma tayi ta kawar da kai, dama ta san za ayi haka.

Jimawa kadan yayi musu sallama ya tafi.

Haka suka kwana a dakinsu na da wanda yanzu ya zama dakin Hamida, suka kwanta kai da kafa a kan gadon dakin tunda dama Babba ne. Haka Safiyya ta kwana tana kuka sai wajen karfe uku na dare ta tashi tayi sallah tayi ta addu'a da karatun kur'ani, kafin asuba zuciyarta ta sami natsuwa hawaye ya daina bin idanunta.

Tun karfe bakwai suka tashi, nan da nan Hamida ta hada musu abinci da yake tuwo ne na daren jiya zasu dumama sai shayi, gaba daya suka zauna a falo suna karyawa harda Sabir da yake sanye da uniform dinshi don shi yana SS3 ne a halin yanzu. Safiyya ta dubi Umma tace

'Umma ban taho da kayana ba don Allah idan sun dawo daga makaranta Sabir da Hamida suje su debo min kayan sawa.'

Nan da nan Umma ta hade rai

'Ba za su je ba, ke da kike neman shiri. Idan ma za a debo kayan to ke da kanki za ki datsi lokacin da yake gidan kije in ya so idan kin sameshi kika bashi hakuri ba sai kiyi zamanki ba.'

Ta sunkuyar da kai ba tare da ta ce komai ba; itama tana so ta koma amma a halin yanzu bazata iya zuwa inda yake ba balle har ta bashi hakuri
To me tayi masa ma da zata bashi hakuri? Saboda dai ita bata da gata? Indai sai taje debo kayanta gara tayi ta zama da zani daya idan an gaji da ganinta a bata ko na aro ne.

Sabir ya Kai kwanukansa kicin ya dawo ya goya jakarsa bayan ya karbi kudin makarantarsa yayi musu sallama ya fice makaranta. Yana fita suma duk suka tashi, Hamida ta shiga wanka yayinda Safiyya ta koma daki ta zauna ta kafa tagumi; tana son Mukhtar kuma tana son komawa gidansa amma a halin yanzu zata hakura ta zauna har sai lokacin da ya bukace ta ya zo ya mayar da ita.

Bata dade da zama ba Sabir ya dawo da gudu, Umma na falo tace

'Ya haka? So kake ka makara ko?''

'Calculator dina na manta a wajen Hamida.'

Kafin ta bashi amsa ya fada dakin da gudu ya nufi Safiyya wadda take zaune a gefen gado ya zauna kusa da ita ya kai bakinsa kunnenta yace

'Zan debo miki kayan Yaya Safiyya, yanzu zan je don na sameshi a gidan.'

Kafin ta bashi amsa ya sake tashi ya fito da gudu ya kama hanya. A gurguje ya tsaya a gidan Mukhtar, ya bude masa dakinta ya shiga ya debo mata kaya kala shida, ya ga underwears dinta a kan gado wadanda ta wanke ya debo su ya hada da kayan ya kalli kan mudubin ya dauko mata turarukanta da Mai, har ya juyo ya koma ya dauko takalmi guda daya wanda ya gani a tsakar dakin. Ya fito ya karbi leda awajen Mukhtar ya zuba kayan a ciki a yayi tafiyarsa. Yana zuwa makaranta ya bawa malamar ajinsu ajiyar kayan sannan ya shige aji.

KARSHEN BABI NA GOMA SHA DAYA.
May 9
MATAR MUKHTAR

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

FIKRA WRITERS ASSOCIATION


BABI NA SHA BIYU

12
Sai bayan suna sannan Fatima ta koma gida. Tana komawa gidan damuwarta ta dawo; tana son Mukhtar sosai kuma bata taba tsammanin zai yi mata haka ba amma babbar damuwarta itace hotunanta da ta tura masa. Bata sani ba ko yana nan da su kada ya zo yayi amfani da su ya cutar da ita nan gaba. Idan kuma ta tuna ya rabata da budurcinta sai taji kamar ta bar duniya ta huta, yanzu kenan idan tana da rabon aure haka zata jewa mijinta ita ba budurwa ba kuma ba bazawara ba? Ta kasa yafewa kanta yanda ta banzatar da kanta ta wulakanta kanta a wajen Mukhtar, gashi ya kasa yi mata halacci yana wajen matarsa wadda ya aura a cikakkiyar budurwa.

Haka a daddafe har aka kafe musu posting na bautar kasa, da taimakon Yaya Ibrahim ya sa aka mayar da ita nan Zariya. Kwanakin da sukayi a camp suka dan kara debe mata kewa sannan ta hadu da mutane daban daban. Suna fitowa daga camp aka turata koyarwa a makarantar 'yan mata wadda take nan kusa da gida don haka kullum daga gida take zuwa.

Yaran da take koyarwa su suka zama masu debe mata kewa daga tunane tunane barkatai, suna sakata nishadi watarn kuma su bata tausayi.

Haka ta cigaba da rayuwarta tana kokarin cire Mukhtar daga zuciyarta kuma tana fatan Allah ya fito mata da miji tayi aure kafin ta gama bautar kasa.
_

Kwanci tashi yau satin Safiyya biyu a gida, kullum da daddare sai ta tashi tayi ibada ta roki Allah mafita mafi alkhairi kuma tana addu'a Allah ya bata hakurin zama da Umma zuwa lokacin da mijinta zai mayar da ita.
Iya takurawa Umma tana takura mata. Yanzu kullum itace take dafa abincin safe sabanin da da kullum Hamida kafin ta tafi makaranta sai tayi, amma yanzu ko asabar ce Hamida sai ta kai goma na safe tana bacci amma da sassafe Umma zata tashi Safiyya tayi musu abinci. Ga aikin gida, komai sai ace ita. Duk lokacin da Umma ta sami dama tana gaya mata ta san yanda zatayi ta hilato mijinta ya zo ya mayar da ita dakinta. Babu wanda take jin dadinsa a gidan sai Sabir, Yaya Habibu ba zuwa yake sosai ba kuma ko ma ya zo ba wani zama suke ba kullum yana gaban Umma, Yaya Hajiyayyaye kuwa ra'ayinsu daya da Umma; ta san yanda zata yi kawai ta koma dakinta, ita kuwa Hamida miskila ce ta gaske sai a wuni da ita ba ayi hira ba.

Yau asabarce don haka Yaya Hajiyayyaye tazo gidan ita da yaranta gaba daya za su wuni, tunda suka zo Safiyya take tsaye tana hidima da su, da an bukaci wani abu Umma zata kwala mata kira duk da kasancewar Hamida tana gidan. Ita tayi abinci ta raba aka gama ci aka tara wanke-wanken da ta san ita zata yi shi don Hamida tana zuwa islamiyya, ta rasa da da bata zo ba ya sukeyi da wanke-wanken.

Sallar la'asar ta idar a daki ta mike a kan dadduma ta lumshe idanu, bacci ne yake kokarin dibanta saboda yanda ta gaji. Tana jiyo hayaniyar yaran Yaya Hajiyayyaye daga falo, kamar a mafarki taji Umma tana kiranta. Cikin hanzari ta mike ta fito ta nufi dakin Umma. A zaune Umman take a kan dadduma da alamar itama sallar ta idar yayinda Yaya Hajiyayyaye take zaune a gefen gado, ta shiga da sallama ta zauna a gaban Umma. Kafin ta karasa zama Umma ta dubi Hajiyayyaye tana nuna Safiyyan tace

'Kin ganta nan babu yanda banyi da ita ba a kan ta kirawo shi a waya ta bashi hakuri yazo ya mayar da ita amma ta ki, ta zabi zawarci a kan ta koma dakinta. So take sai an fara nuna ni a dangi, ta mayar da kanta karamar bazawara.'

Ta sunkuyar da kanta tana fatan kada Allah ya bari idonta ya zubar da hawaye. Ya Hajiyayyaye ta dubeta tace

'Dole fa ki nemo shi Safiyya, ya zo ya mayar dake dakinki. Ko ni ai na gaya miki mazan yanzu duk haka suke idan dai a kan mata ne sai dai kiyi hakuri da su, kuma tunda shine shugaba ai kinga dole ke zaki bashi hakuri.'

Sukayi shiru suna jira tace wani abu amma itama tayi shiru kanta a kasa, Yaya Hajiyayyaye tace

'Me yasa bazaki kirawo Mukhtar din ba Safiyya?'

Ta rasa yanda zata yi da su don haka ta yanko karya

'Baya dauka Yaya Hajiyayyaye, kusan kullum sai na kirawo shi amma baya dauka. Wallahi nima inaso ma koma.'

'To gaskiya dai ki kara dagewa, ko ta Whatsapp ne kiyi masa magana ku daidaita ko kuma ma in ta kama kije ki sameshi.'

Ta kalleta da mamaki suka hada ido, ta jijjiga kai ta cigaba

'I mana, mijinki ne fa kuma yana kusantarki aure ya koma don haka in kinje ba laifi kika yi ba. Ko a 'yan uwansa idan da wanda kike ganin zai muku sulhu ko mahaifiyarsa. Tunda Umma ta ce da kanta ta kirawota tana bata hakuri kuma ta tabbatar mata zai zo ya mayar dake. Kina kallo Umma tana fama da marayun kannenmu duk nauyin gidan yana kan Yaya Habibu sai abinda Umman ta samu ke kuma ki zo ki kara mata nauyi ai da kunya ma ko?'

Ta hadiye malolon da ya tokare mata makogoro ta share kwalla, wadannan maganganun na Yaya Hajiyayyaye sunyi kama da cin fuska amma dole ta saurarensu tunda bata da yanda zata yi da su. In sha Allahu in dai Mukhtar ya mayar da ita ko barikin karuwai zai mayar da gidan bazata ce masa komai ba, hakuri za tayi ta zauna don gara nashi wulakanci da na mutanen da take gani bata da na biyun su. Cikin takaici Umma take dubanta tana fadin

'Kin gani ko Hajiyayye, da ka yi magana sai ta sa kuka sai kace wadda aka daka.'

'Ai ba kuka zakiyi ba, ki lallabo mijinki ki koma gida. Ai ko don yaranki ma kya hakura ki zauna da shi komai mugun halinsu tunda dai yana kula da duk wani hakki naki.'

Ta sake share kwalla tace

'Zan sake kiransa in sha Allahu.'

'Gara dai ki dage gaskiya.'

Sai bayan magriba sannan mijin Yaya Hajiyayyaye ya zo ya kwashe su ita da yaran suka tafi.

Sati biyun da Safiyya tayi a gidansu jinta take kamar a kurkuku, gaba daya tayi baki ta rame bata ko son kallon kanta a mudubi. Ga wani ciwon kai da bazata iya tuna tun lokacin da ta fara shi ba. Bata taba zaton saboda tana auren Mukhtar bane Umma take sonta, gaba daya yanzu gani take kamar an canza mata Umma da 'yanuwanta. Ga shi tana kewar Mukhtar da yaranta, ba za su iya gane yanda take tsananin son Mukhtar ba ji take kamar ta mayar masa da kanta. Tun da ta kwana daya a gidan take masa magana ta Whatsapp amma zuwa jiya bai kulata ba, tana gani zai bude sakon ya mayar ya rufe ba tare da ya bata amsa ba. Ta dai yiwa kanta fada a kan ta hakura da yi masa maganar haka, amma har yanzu kokawa take da zuciyarta. Da kyar ta danne zuciyarta ta kwanta baccin dare ba tare da tura masa sako ba, amma tayiwa kanta alkawarin gobe da safe zata shirya taje gidan ta sameshi idan ba zai mayar da ita ba sai dai ya kasheta ya kawo musu gawarta, a haka bacci ya kwasheta.

Haka kawai ta farka tana tsakiyar baccinta, ta tashi zaune ta lalubi wayarta taga karfe biyun dare da minti uku. Sai karfe uku alarm dinta yake kararrawa ta tashi sallar dare don haka ba shi ya tada ita ba, ta sa hannu ta shafa mararta saboda yanda marar take mata ciwo, take ta gane ciwon marar ne ya farkar da ita. Sai da tayi dogon tunani sannan ta gane yanzu haka al'ada zata yi shine dalilin ciwon. Idan tana shayarwa bata al'ada don haka rabonta da jini tun na haihuwar Nana, Kuma da yake bata dade da yaye Nanan ba wannan shine karo na farko da zatayi al'ada.

A lissafinta ma ya kamata ace tayi al'adar tun tuni amma saboda tsabar damuwa da bacin ran da Mukhtar yake dora mata gaba daya ma ta manta da lissafinta, yanzu ma da take jin zai zo tana tunanin wannan ciwon marar yana da alaka da damuwar da take ciki don ciwon da yake mata bai kai haka ba.

Babu wuta don haka ta haska da fitilar wayarta ta sauko daga gadon ta shiga bandaki don ta duba. Jini Bai zo ba sai ciwon kawai don haka ta dauro alwala, tana fitowa ta dauki Panadol a kan mudubin ta Sha sannan ta zauna a kan dadduma ta fara karatun kur'ani don bazata iya tsaiwar Sallah ba.
Nan a kan daddumar ta karasa baccinta har asuba. Hamida da Sabir suka shirya suka fice makaranta yayinda Umma ta koma bacci don bata ma san Safiyyan bata da lafiya ba. Haka ta lallaba ta gyara gidan tsaf ta dora abincin rana. Sai wajen Sha biyu da rabi Umma ta fito ta zauna a falo, daga kicin Safiyyan ta fito ta shigo falon da sallama saboda ta jiyo motsin Umman

'Sannu da fitowa Umma.'

Ba tare da ta kalleta ba ta amsa

'yauwa.'

Jimawa kadan ta sake wucewa ta dubo abinci, bayan ta dawo ne Umma tace

'Me yake damunki ne kike ta wani yatsuna fuska.'

Ta dan tsaya ta juyo

'marata ce take ciwo Umma, amma na Sha Panadol.'

Ta tsareta da ido na dan lokaci, ta yafito ta tana fadin

'Zo nan ki zauna.'

Ta karaso ta zauna kusa da Umman a kan kujerar zaman mutum uku. Umma ta dubeta da kyau sannan tace

'Al'ada zakiyi?'

Ta sunkuyar da kai

'Eh.'

'To ina fatan kin san idan kika gama wannan al'adar saura al'ada biyu aurenki ya mutu gaba daya, kin zama bazawara kenan.'

Sai yanzune Safiyya ta tuna da wannan lissafin, take gabanta ya fadi yayinda mararta ta kara kartawa da ciwo. Ta sunkuyar da kai ba tare da ta ce komai ba, Allah ya tsareta da zama bazawara ko jin kalmar bata son yi balle ace ta tabbata a kanta. Umma tace tana nunata

'Kinga ki mayar da hankali ki nemo mijinki, ki san yanda za kiyi ki sanar dashi kinga al'adarki don yanzu haka shima baya lissafi gara ku san me kuke ciki. Kuma fa ni yanda nake ganinku ma kallon mai ciki nake miki wallahi.'

'Bani da ciki fa Umma, tunda na yaye Nana ban ma yi al'ada ba. Dama kuma idan ina shayarwa bana al'ada.'

'Hmmm! To Nana ai ta kusa wata uku da yaye, don haka idan ance ciki ne da ke ai babu mamaki. Amma dai bari mu gani zuwa kwana biyu. Sai ki sanar da Mukhtar din don ku san lissafin da kike ciki.'

Haka ta tashi ta bar Umma a nan ta koma daki.Tana shiga daki ta fada kan gado ta sa kuka; yanzu nan gaba idan ta kara al'ada biyu ta zama bazawara? Tana hango wayarta a chaji, da zarar ta gama kafin nan mararta tayi sauki zata tura masa sako ta

08, January 2025
Nafisa

I cant download the book

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login