Showing 75001 words to 78000 words out of 92582 words

Chapter 26 - MATAR MUKHTAR COMPLT

SAKINA   

16 Aug 2024

7159

ta fi gidanka fadi, ba zan taba iya sake aurenka ba Mukhtar. Allah ya tsari gatari da saran shuri!'

Ya bude baki zai katseta ta daga mishi hannu ta cigaba

'Kayi aurenka ma Alhamdulillah, don haka inaga baka ma bukata ta a rayuwarka tunda ma ka ga kai din ba ka cikin mazan da zasu iya hada mata biyu. Ba sai mun batawa junanmu lokaci ba Mukhtar, ba zan taba sake aurenka ba don haka mu bar wannan maganar. Dole yara sun hada mu ba zan yanke hulda da kai ba, amma don Allah mu cigaba da ganin mutuncin juna kawai ya isa.'

Tayi shiru yayinda shima yayi shiru yana binta da kallo. Ya sa hannu ya Shafa kansa, gaba daya ta goge masa haddar kalaman da ya shiryo don ya tsarata da su. Ya jijjiga kai yace

'Haba Safiyya! Baki ma saurareni kin ji da me na zo ba kika yanke wannan hukunci.'

Sai da tayi dariya sannan tace

'Uhm, duk wata kalma da kazo da ita na san ta na ji ta bazata yi tasiri a kaina ba. Kada mu batawa junanmu lokaci, mu bar wannan zancen kawai.'

Binta kawai yake da kallo ya rasa me zai ce mata.

Jimawa kadan tace

'Bari na koma gida yanzu zaka ji kiran magriba.'

'Hakane.'

Kafin ya mike ta mike, sannan ya tashi da kyar kamar wanda aka yiwa duka yana faman binta da kallo.

'Ka gaida yaran da su Hajiya.'

Ta fada tana shirin juyawa ta shige gida.

'Safiyya.'

Ya kirawo sunanta, ta juyo suka tsaya suna fuskantar juna sannan yace

'Kada ki zata wannan maganganun da kika gaya min zasu sa na rabu dake, in sha Allah baki da miji sai ni daga nan har Aljannah. Don haka zan dawo kuma zan yi duk abinda zan yi naga na mayar dake dakinki.'

Tayi murmushi kawai ta jijjiga kai

'Sai an jima.'

Kafin yace wani abu ta wuce cikin gida.

Ya bi bayanta da kallo yana mamaki, shi bai ma taba sanin Safiyya zata iya tsayawa ta karanta masa magana kamar haka ba. Lallai Safiyyan ta canza, canjin kuma ya burgeshi; dole ma ya san yanda zai yi ya tsaro Safiyya domin ita din tashi ce shi kadai.
........

Tana shiga gida ta sami Umma ita kadai a falo, bayan ta amsa sallamarta har zata wuce daki Umman tace

'Zo nan Safiyya.'

Ta dawo ta zauna a kasa gaban Umman. Sai da ta dan kare mata kallo sannan tace

'Neman me yake miki Abban Nurain din?'

Ta kau da kai sannan tace

'Uhm! Wai so yake ya sake aurena.'

'To kinga idan gidan nashi zaki koma sai ki gayawa yayanki ya nemi Baban Muhammad a dakatar dashi.'

A firgice ta kalli Umma kamar wadda aka tsikara da allura

'Umma ba zan sake aurensa ba, ko da Baban Muhammad ya fasa aurena ba zan sake auren Mukhtar ba. Allah ya kiyaye.'

Umma ta kama Haba tana mamaki

'Me yayi zafi haka, ko yaran ai kwa duba. Kina dai jin yadda matar tasa tayiwa Nana.'

'Hmm! Umma shima bai duba su ba lokacin da ya koro ni, in sha Allah babu abinda zai samesu.'

'Ai shikenan Allah ya zaba muku abinda yafi alkhairi gaba dayanaku.'

Ta amsa da Amin sannan ta mike ta shiga daki domin yin sallar Magriba wadda an riga an fara kira.

Bayan ta idar da sallar Magriba nan ta zauna a kan daddumar tana tunani kala-kala; ko babu maza a duniya ba zata sake auren Mukhtar ba, duka wani so da take masa ya kare ba zata sake iya zama da shi ba. Tabbas wani lokacin tana jin kamar ta koma don yaranta, tana shiga damuwa idan ta tuna dasu musamman bayan da taji labarin dalilin dawowarsu gidan Hajiya. Tana tunanin tarbiyyarsu, duk da tana yi musu addu'a amma wataran tana jin kamar ta koma don ta cigaba da kula da su.

Sai dai idan tayi tunanin akwai yiwuwar ta kare ragowar rayuwarta a cikin kunci kuma ga cututtuka da zai yi ta kwasowa yana saka mata, sannan kuma ga yanda abinda yakeyi da yaran mutane zai iya tasiri a kan nata yaran da yanda idan sun girma zasu shiga damuwa idan suka gane halin mahaifinsu sai taga gara ta hakura da shi. Su biyun kuma tana musu addu'a kuma duk lokacin da ta sami dama in sha Allah zata dawo dasu wajenta. Kai ba zata iya sake komawa gidan Mukhtar ba.

Ta daga hannunta sama ta yi addua a fili

'Ya Allah, Ya Hayyu Ya Kayyum kada ka jarrabeni da sake auren Mukhtar ko wani mazinacin Ya Allah.'

Ta tuno alwashin da yaci a kan dole ya san yanda zai yi ya mayar da ita dakinsa, ta san dai baya bin malamai amma mutumin da yake zina bata jin akwai abinda zai gagareshi aikatawa.

Akwai adduar da Malam ya basu a islamiyya ta kariya daga sihiri da kuma ta karya sihirin, duk da bata rubuta ba amma in sha Allah gobe idan taje islamiyya zata tambayo Malam don dolene ta dauki matakin kare kanta.
-------

Duk da ya shiga damuwa saboda yanda Safiyya taki amincewa da shi haka ya daure ya cigaba da shirinsa na zuwa conference dinsu na ICAN wanda wannan karon a Lagos za a yi shi. Kwana biyar ake gama conference din amma wannan karon kwana goma yake son yi don ya huta, saboda 'yan kwanakin nan damuwa tayi masa yawa kansa ya cushe.

Ya riga ya gama shiryawa da Felicia wdda dama ita a Lagos din take, ya hadu da ne a Abuja kuma tun daga lokacin ya zama in dai zata zo Kano shi zai sauketa tunda shima tana biya masa tasa bukatar.

Ya biya kudin registration dinsa dana hotel duk ya gama biya saboda saura kwana hudu taron.

Yana zaune a falonsa kan teburinsa na karatu yana aiki a computer, aiyuka ne da yake son ya gama ya bari a office saboda kar a nema baya nan.

Ta kofar da take shigowa daga dakinsa ta shigo falon, bayan ya amsa sallamarta ta wuceshi ta zauna. Ta dauki remote ta dan kara volume din TV sanna ta dubeshi tace

'Aiki ya ki ya kare to a barwa gobe mana.'

Yayi dariya yana kallon computer din yace

'Ba zaki gane ba, so nake na tattara aiyukan nan kada a nemeni. Au ashe fa ban gaya miki ba, ranar Lahadi mai zuwa zamu tafi conference Lagos.'

'Lallai, ka ma manta da ni, last year ai cewa kayi da ni zaka je wannan conference din kuma ni a shirye nake.'

Ya kyale computer ya taso ya dawo inda take ya zauna.

'To ke yanzu ina zaki je wani taro Lagos, ya zakiyi da Halimatu?'

'Wace Halimatu, yarinyar da ko yanzu na yaye ta bani da matsala. Duk wani abinci fa da naci tana ci kaga kuwa zan iya barinta wajen Inna ko Ummanmu, kwana dai biyar.'

'Ba zaki yaye ta ba yanzu, don mugunta? Ina ma laifi ki bari tayi shekara daya da rabi. Kawai ki bari next year in baki da ciki ko goyo sai muje.'

'To ai ni ba ce maka nayi zan yayeta ba, kwana biyar ne fa kawai ina dawowa zata cigaba da shan nononta ai ana haka, in ya so idan ta karasa shekara daya da rabin sai a yayeta.'

'Babu wannan zancen, bana son fitna. Kiyi zamanki kawai in Allah ya kaimu lokacin da baki da ciki ko goyo sai muje, kuma ma ni ba kwana biyar zan yi ba kwana goma zan yi don akwai abinda nake son yi a Lagos din idan an gama yaron.'

Nan da nan ta kara tsuke fuska , tabbas ta san akwai abinda ya shirya, babu mamaki ma da wata zai tafi, amma ko ma menene zata bincika don wannan tafiyar sai dai ya zabi daya ko ya tafi da ita ko ya fasa zuwa.

'Um!'

Ta bashi amsa ta koma tayi shiru ta cigaba da kallon TV, jimawa kadan kuma ta fice daga falon ta barshi a nan.

Ya bi bayanta da kallo yana jijjiga kai, bazai tafi da ita ba ko me zata yi duk da ma ya ga ta hakura ba tare da wata fitna ba.

Haka ta kwana a dakinsa kamar babu wani abu da ya faru, don haka ma ya kara sakankancewa ta hakura. Sai da suba bayan ya shiga wanka sannan ta sami dama ta lalube masa waya, bata sami komai ba a WhatsApp amma ta samu a telegram da email dinsa. Kuma da yake ita har password dinsa na banking app ta sani saida ta duba, taga ya turawa Felicia kudi naira dubu ashirin da biyar sannan kuma ya tura mata adress din hotel din da ya kama ta email. Sai da ta tura rasit din da email din wayarta sannan ta mayar masa da wayarsa ta ajiye ta fice daga dakin.

Haka tayi ta kaiwa da kawowa a dakin tana tunanin ta inda zata bullo masa; ya za ayi tana matarsa ba zai je da ita ba amma har yayi booking karuwar da zai kwana da ita; tabbas ba zata yarda da wannan wulakancin ba.

Har ya dawo daga masallaci bata fito daga daki ba don haka ya koma ya kwanta, sai wajen bakwai da rabi ya fito a shirye, har zuwa lokacin bata sauko ba. Da yake ya riga ya siyo burodi tun dare don haka sai kawai ya hada shayi ya karya. Bayan ya gama cin abincin sai ya wuce dakinta inda ya tura kofar a hankali ya leka, tana zaune a kan kujera tana bawa Halimatu nono.

Ya karasa ciki

'Ni zan fita, lafiya kalau Halimatun take ko?'

'Lafiyarta kalau, a dawo lafiya.'

Ya fice ya barta yana tunanin abinda ya bata mata rai tunda ya san kalau suka kwana.

Sai dab da la'asar ya dawo kuma har lokacin tana nan tana ta faman bata rai, don haka ma bai nemi abincin rana ba musamman da yake ya ci abinci a office.

Yana zaune a falon ta shigo ranta a bace, ko sallam bata yi masa ba ta nemi waje ta zauna kusa dashi. Bai kalleta ba saboda ya fuskanci da rigima ta shigo. Sai da ta dauki dan lokaci a zaune tana ta faman muzurai sannan tace

'Mukhtar.'

Ya daure fuska sannan ya amsa

'Na'am.'

'Don Allah sai yaushe ne kai a rayuwarka zaka daina neman matan banza ne?'

Tambayar ta shammaceshi kuma ta rikita shi, sai da ya dan yi kokawa da nutsuwarsa ya daure fuska sannan yace

'wannan wane irin cin fuska ne da rashin mutunci Jamila? Ni kike wa wannan tambayar?'

Tas take bin kwayar idonsa da kallo don haka sai shine ya gaji ya dauke idonsa daga cikin nata, ta dan kawar da kai

'Mtsewww! To ai dole na tambayeka. Kace bazaka je dani Lagos ba amma kayi appointment da Felicia, bayan ka tura mata adireshin hotel din da zaku hadu har dubu ashirin da biyar ka tura mata. To su kuma kudin dama haka kake biyanta ta bude maka tsakanin cinyoyinta ko kuma na gyara ne ka bata domin kafi jin dadinta?'

Da hanzari ya mike tsaye yana nuna ta da yatsa

'Na gaya miki bana son irin wannan ko Jamila, shikenan babu wata mace da zan yi appointment da ita sai idan nemanta nakeyi? Kwanan nan kika zagi matar mutane kika janyo min asarar miliyoyin kudi amma baki daddara ba ko?'

Itama ta mike tsaye tace

'Wallahi karya kakeyi Mukhtar, babu wata alaka tsakaninka da wannan Felicia din face alakar zina, kuma wallahi sai nayi maganinku da kai da ita.'

Ya daga hannu zai mareta yana fadin

'Nine nake miki karyar?'

Cikin zafin nama ta goce ya mari iska

'Ai na gaya maka ba zaka sake dukana ba, kuma idan har ka sake ka sake dukana sai na mayar da kai kalar tausayi a garin nan. Kai yanzu ko kunya baka ji matan banza kowacce kaje ka kwabe mata wando babu kunya babu tsoron Allah. Haka zan zauna ina kallonka kayi ta kwaso cuta kana shafa min, ga yara nan na fara da mace; wace irin tarbiyya kake son nuna musu da kake haka?'

'Ba zan tafi dake Lagos din ba kuma abinda nayi niyya bazan fasa ba, duk abinda kike jin zakiyi a kai kije kiyi.'

Ya sa hannu ya tureta gefe ya wuceta ya shige dakinsa ya mako kofar.

Ta zube a nan a kan gwiwoyinta tana faman kuka, zuciyarta sai tafasa take. Shikenan yanzu babu yanda zatayi da mutumin nan, tana kallo haka zai dinga bin matan banza ya dangwalawa wannan ya dangwalawa wannan kuma ya dawo ya juye a kanta sai kace wata masai.

Da kyar ta mike ta koma dakinta. Tana shiga ta turo kofar ta tsaya a bayan kofar tana faman fitar da hawaye. Ta dubi Halimatu wadda take bacci, tausayinta ya kara cika mata zuciya. Ta wuce cikin dakin ta sauke akwati daga wardrobe dinta ta hau diban kayansu ita da Halimatu tana zubawa a ciki.

Ba zata iya wannan zaman ba, kullum sai an yi rigima mutum yayi kamar ya daina sai ya koma ruwa; kuma idan tayi magana sai ya juya abun ya zama kamar itace mai laifi. Gaskiya bazata iya ba. Ta rufe akwatin ta goya Halimatu sannan ta janyo akwatin ta kulle dakin ta fice daga gidan.

KARSHE BABI NA TALATKN DA UKKU

MATAR MUKHTAR

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA TALATIN DA HUDU

34
Tun kafin a fara hidimar bikin Hamida Safiyya ta ware naira dubu hamsin a irin kudaden da take tarawa, ta bawa Umma tace ayiwa Hamidan wani abu. Tunda aka fara bikin ake ta shawara da ita, ita kanta abun har mamaki yake bata.

Lokacin da aka kawo kudin auren Hamidan babu wanda ya bi ta kanta, garama lokacin da aka kawo lefen saboda a lokacin ta fara kitso don ta bada dubu takwas a hada ayi snacks. Amma yanzu taga sai wani shawara Umma takeyi da ita, har Yaya Hajiyayyen ma duk sun canza. Yanzu sosai suke kulata.
Ta gode Allah ta fahimci ashe a duniya mutane suna daukanka yanda ka dauki kanka ne; domin lokacin da ta dorawa kanta damuwa ta banzatar da kanta suma hakan suka yi mata.

Haka aka gama biki aka kai Hamida gidanta da yake unguwar Janbulo.
-----

Kamar yanda Ahmad yayi mata alkawarin yana dawowa daga Dubai 'yan uwansa suka kawo kayan auren Fatima. A can gidan Baffansu a nan aka karbi kayan, wadanda mata ne suka kawo.

Yaya Ibrahim ne ya bayarda naira dubu dari tukuici sannan kuma ya bayarda naira dubu dari biyu aka shiryawa baki abinci da kayan snacks.

Cikin mutunci aka karbi kayan, suka dora naira dubu dari kudin dinki, aka rabu kowa na son barka. Aka saka ranar aure sati takwas.

Tun kafin a kawo wa Mommy kayan auren nan 'yan mata a 'yan uwan Fatima suka dinga turo mata da hotunan kayan auren nan. Akwati tara ne, daya me hudu a saiti daya kuma me biyar, ko wanne cike da kaya domin sutura sai da aka kirga kala dari cif ga tarin mayafai, abaya da sauransu.

Bayan an sallami baki kuma aka zuba akwatuna a mota aka taho gidan su Fatima. Tana daki ta jiyo shigowar mutane, take ta jiyo shewar su Badriyya, Zam-zam da Shukra sun nufo dakinta.

Suna shiga dakin sukayi kanta gaba daya, Zamzam tace

'Kai Fati, soyayya tayi. Kinga kayanki kuwa? Gaskiya kin more.'

Murmushi kawai take tana binsu da kallo, Badriyya wadda suke kira Badr; wadda kuma sa'anni suke da Fatima kuma kusan cikin damuwa daya suke ta rashin yin aure har kawo yanzu; ta karaso ta rike hannuwan Fatiman

'Sis Allah ya nufa jirginki zai tashi, saura nawa jirgin.'

Ta fada jikin Badr nan take su duka biyun suka rushe da kuka; ita Badr tana murna kuma tana tunanin yaushe nata auren zai zo itama ta huta da masu damunta wai taki aure, yayinda ita kuma Fatima take zullumin yanda ya ciko kayan nan idan ya gane bata kai masa budurcinta ba ya zatayi da shi? Sai da sukayi mai isarsu Zamzam da Shukra suna kansu suna ta faman iyayi sannan suka saki juna suka hau hira ana shirin biki.

Sai da kowa ya tafi sannan Fatima ta fito suka saka kayan a gaba ita da Mommy suna ta dubawa. Bayan sun gama Mommy ta kalli Fatima ta dafa kafadarta tana murmushi tace

'Ashe zan ga aurenki Fatima.'

Ta sunkuyar da kai cikin jin kunya.

'Allah ya ji kan Daddy, ina ma yana nan yaga Fatinsa ta zama matar aure. Wannan mutumin Allah ya sa ya rike min ke amana kema Allah ya baki ikon rike masa gidansa da amanar aurensa Fati.'

Kasa amsawa tayi sai hawaye, ta rungume Mommy sukayi ta yi.
........

Tunda aka kawo kayan auren nan Mommy ta shiga gyara Fatima, 'yayan wasu ma a dangi ita take gyarasu balle kuma tata.

Tunda aka fara maganar aure tsakanin Fatiman da Ahmad take ta wata rama don haka Mommy ta saka aka hada mata hadadden garin sabaya wanda zai sa ta murja ta cicciko ko ta ina. Kayan gyara kala-kala ta tanada sai dai tace da Fatiman ta shanye sabaya na sati biyu sai a fara sauran.

Ita kuma Fatima hankalinta a tsahe yake saboda abinda zai matseta take nema ba abinda zai kara mata ni'ima ba tukunna. Sunyi magana da Janan sai dai shawarar Janan batayi mata ba, domin cewa tayi ta turo kudi zata je mata wajen Malam ayi mata aiki babu yanda za ayi ya gane.

Bata son harkar Malam saboda wancan zuwan ma da tayi gani take kamar har yanzu Allah bai yafe mata ba duk da kullum ta tuno dai ta sake tuba ya za ayi kuma ace ta koma; ashe ba tayi hankali ba kenan. Don haka dole ta tsara Janan akan ta sami wani ma za ayi mata aikin don su rabu lafiya.

Maman Haidar ta nema amma ce mata tayi kayan gyara kawai take so, saboda na Mommy sun fara bata mata ciki don tana da ulcer. Nan take Maman Haidar

08, January 2025
Nafisa

I cant download the book

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login