Showing 78001 words to 81000 words out of 92582 words
ta bata lambar Maman Ilham (08034375920) tace mata
'A Kano take, ki nemeta zata baki masu inganci don ko kaza ta dafa miki ta amare lafiya lau zaki ci babu wani tashin hankali kuma kayanta akwai aiki.'
Don haka ba tare da bata lokaci ba ta nemi Maman Ilham inda tace mata kayan matsi tafi damuwa da su saboda ta taba amfani da wani magani na infection wanda kwaya ce ake tusawa, kuma ita bata san 'yan mata basa cusawa ba sai da ta cushe shi gaba daya. Nan da nan maman Ilham ta hada mata su kowanne da bayaninsa aka aika mata. Gidan Maman Haidar nan ta ajiye, sai an tashi daga makaranta sai su wuce taje taci.
Wanda ake sakawa kuma su a dakinta ta boye.
Haka suka cigaba da shiri, duk abinda Mommy ta bata sai ta wuce da shi dakinta ta zuba a toilet tayi flushing, ta kawo kofi tace ta shanye.
------
Mukhtar bai san Jamila bata gidan ba sai bayan magriba, bayan ya gama caje gidan ya tambayi maigadi ko ya ga fitarta inda ya tabbatar masa ta fita da akwati da goyon Halimatu.
Da ba don Hajiya da Baba ba da tabbas zai barta ta dana zaman gidan, amma ya san Baba ba zai masa a hankali ba idan ya sami labari. Sannan kuma ga yanda sukayi da Safiyya, daga ya barta ta dana zaman gida abubuwa suka dinga faruwa har auren ya kare ba tare da ya shirya ba, gashi nan yanzu ta ki sauraronsa.
Don haka ya dauki waya ya kirawo Yayanta Abdallah; wanda shine Babba a duk gidan kuma ba uwarsu daya da Jamila ba tunda shi uwarsa itace uwargida tafi kowa yara a gidan ita kuma uwar Jamila itace ta uku kuma su Jamila su hudu kawai ta haifa.
Bayan sun gaisa yake sanar dashi Jamila ta tafi gida, Abdallah yace
'Eh na ganta ai yanzu na fito daga gidan na zata ma ganin gida taje.'
Yayi gyaran murya
'Mun dai dan sami matsalane shine ta fice ban ma sani ba sai yanzu da na dawo.'
'Ikon Allah, to me yake faruwa ne?'
'Wallahi fitna ce kawai. Bani da ikon nayi waya ko message da wata mace kawai sai tace wai neman mata nakeyi, kuma ta san bayan aikin office ina sayar da computers.'
Nan ya bashi labarin abinda ya faru da Professor, sannan ya cigaba
'Yanzu ma kuma Lagos zan je conference wai sai na je da ita. Na gaya mata tana shayarwa ba zani da ita ba shine take tayi min bincike. To akwai wata mata marketing manager ce ta wani shagon computer da suke Lagos din wanda nake son idan zan sai computers dai-dai kawai na dinga siya a can don ya dan fi riba, to sai taga nayi appointment da matar nan cewa idan na zo Lagos zamu hadu shikenan fa take ta fada. Shine ina fita ta taho gida.'
Abdallah yace
'Ikon Allah, to so take ka daina business din kenan ka zauna a gidan kayi mata raino? Mtseww! Rabu da shirmensu na mata, zamuyi magana da Abba in sha Allahu da kaina zan dawo maka da ita ai ta sam Abba ba zai dau wannan shirmen ba. Goben nan zan dawo maka da ita.'
'A'a zan zo ma da kaina, na dai kirawo ka ne don ka san me yake faruwa. Inaga a barta a gidan in sha Allahu idan na dawo daga Lagos din sai na zo na daukesu.'
'To shikenan babu damuwa, zan yi mata fada in sha Allah, kuma na san Ummanta ma ba zata barta haka ba. Allah ya bada sa'a sai ka dawo din.'
Sukayi sallama.
Jimawa kadan ya sake daukan wayar ya kirawo Safiyya, har ta gama ringing ba a dauka ba. Tun ranar da yaje gidansu bata sake daukan wayarsa, kuma dama daya layin nasa bata budeshi ba balle yayi mata sako ta Whatsapp. Itama Hamida da yake tun tuni yana da lambarta Sau uku yana kira bata dauka.
Ya ajiye wayar cikin damuwa, babu yanda za ayi ya tafi Lagos bai yi magana da Safiyya ba kuma baya son yaje gidansu idan bata bashi izini ba don baya son ya sake ganinta da mutumin nan idan ba hawan jini yake nemarwa kansa ba.
Duk wata dabar da zai yi ta kare don haka yaga gara yaje ya sami Yaya Habibu a office, watakila idan suka fahimci juna komai ya zo da sauki.
Haka ya rufe gidan ya kwana shi kadai, gari na wayewa Juma'ah, ya shirya ya nufi office. Sai wajen goma sannan ya bar abinda yakeyi ya kama hanyar office din Yaya Habibu.
Duk da yayi mamakin ganinsa amma cikin sakin fuska ya karbeshi suka gaisa, bayan ya gama kame-kamensa yace
'Dama naje wajen Safiyya ne mun yi magana ina son dawo da aurenmu, duk da dai bamu wani fahimci juna ba amma dai naga ya kamata na sanar da kai don in dai ta amince ba wani lokaci za a dauka ba. Kuma kaima ina baka hakuri a kan abubuwan da suka faru, in sha Allahu wata matsala irin wannan ba zata sake dawowa ba.'
Habibu ya kalleshi ya dan tabe baki
'Allah sarki, to babu laifi idan dai ita Safiyyan ta amince na san zata yi min maganar ai, in ya so daga nan sai a san abun yi.'
Haka ya hakura yayi sallama da Yaya Habibu ya tafi ba don ya so ba, ya ga kamar Habibun bai gamsu da zantukansa ba amma dai ko babu komai ya sanar da su don in sha Allahu Safiyya tasa ce.
Idan ya dawo daga Lagos ma gidan Baban Hotoro zai je don shima ya san ya dawo sannan ya gayawa Baba, watakila idan ya shiga maganar sa fi sauraronsa.
-----
A zaune take a daki ta idar da sallar la'asar wayarta tayi kara, ta mika hannu ta dauka tayi murmushi bayan taga Yaya Habibu ne yake kiran. Bayan sun gaisa yace
'Wai meye kuma yanzu tsakaninki da Mukhtar?'
Tayi mamaki saboda bata gaya masa ya zo ba duk da dai ta san zai iya yiwuwa sunyi maganar da Umma.
'Yaya ba komai fa, ya dai zo nan yace yana son ya maida aurena kuma na gaya masa bazan taba sake aurensa ba yayi hakuri.'
'Kin tabbatar kin gaya masa haka?'
'Wallahi Yaya na gaya masa kuma tun daga lokacin ma ban sake daga wayarsa ba. Ba zan aureshi ba Yaya kada ma ka saurareshi.'
'Yauwa, abinda nake son ji kenan. Shi kuma A A (Abdurrahman Anas) fa? Za ki aureshi don in yazo na san da wacce zan tarbeshi.'
Ta dan yi jim sannan tace
'Zan aureshi Yaya.'
Sukayi sallama suka ajiye wayar.
.........
Ranar Alhamis ya diro birnin Kano yana sauka daga airport ya karbi mukullin motarsa a hannun direbansa ya sallameshi. Ya shiga mota ya kama hanyar office din Yaya Habibu. Bayan sun gaisa ya sanar da shi gobe Juma'a yake so a kawo kayan auren Safiyya. Yana so zasu hada kudin aure, kayan lefe da kayan sa rana a kai gaba daya kuma a sa wata uku.
Sosai Yaya Habibu ya ji dadi kuma ya gaya masa hakan yayi, sai dai akwai gidan Baban hotoro da yake son yaje ya gaisheshi. Yace
'Kwarai kuwa kayi min maganar. To ai in babu abinda kakeyi ko yanzu sai muje.'
Don haka tare suka fice suka hau motar AA suka nufi gidan Baban hotoro.
Sosai Baban hotoro yayi murna kuma ya ji dadi, duk da tun tuni Habibu ya kai masa labarin AA din har shima yayi nasa binciken. Sukayi masa sallama suka kama hanya.
Sai da suka rabu da Habibu sannan ya dauki waya ya kirawota, bayan sun gaisa yace
'Kin kusan zama matar A A fa, nan da sati goma sha biyu.'
Ta kyalkyale da dariya tace
'Shike nan ma an hutar da mutane ka riga ka saka mana rana.'
'Zaki sha mamaki. Yanzun nan muka fito daga gidan Baban hotoro kuma ya riga ya bani aurenki gobe za a kawo kayan aurenki.'
Tayi shiru na dan lokaci, sannan tace murya a sanyaye
'Allah da gaske?'
'Ina miki wasa ne? Ko kin fasa auren ne?'
Tayi murmushin da har saida ya jiyo sautinsa ta wayar
'Ni na isa? Babu fashi sai dai in kai ka fasa.'
'Yauwa matar AA kanwar barrister.'
Haka suka gama wayar yana ta tsokanarta.
Sai da daddare Yaya Habibu ya shigo yake gaya musu zancen kai kayan don har ya bawa Baban hotorom dubu dari tukuicin masu kawo kaya kuma ya aika an kai lemo da ruwa wanda za a basu.
Bayan ya gama zancen ne Umma tace
'Shikenan dai ba zaka barta ta koma wajen 'yayanta ba ko?'
Yace
'Haba Umma, shekarun Safiyya nawa? Da kuruciyarta fa balle ace taje tayi zaman 'yayanta. Kina kallon mutumin nan yayi aurensa ma sai da ya gama more amaryar sannan zai dawo yace ta koma. Haba Umma, yaje can ya karanta.'
'Ai shike nan, Allah ya sa haka ne yafi alkhairi.'
Tana jiyosu daga daki ta amsa a zuciyarta
'Amin.'
.......
Yanda ya alkawarta haka akayi, iyayensa maza sune suka kawo kayan auren Safiyya. Yaya Habibu yana zaune aka karba a falon Baban Hotoro.
Kudin aure naira dubu dari, akwati daya na sa rana sannan akwati shida na lefe, ga kuma buhunan abinci, kayan lalle da su tabarma da ake hadawa duka kamar na budurwa. Sannan suka bayar da dubu dari kudin dinki.
Bakin suna fita mata suka shigo aka hau bubbudawa, Sabir yana tsakiyar kayan yana yiwa Safiyya video don ya san sai a kai sati ba a kai kayan gidansu ba. Haka sukeyi duk kayan wanda aka karba sai dangin ubansu sun gama gani a gidan Baban hotoro sannan sai a kai gidansu amarya.
Tsakanin atamfa, leshi, material da shadda sai da aka kirga kala sittin da biyar kuma duka manya ne. Ga kuma akwatin abaya itama kala goma sha biyu masu kyau dinkin Dubai tare da kayan bacci. Takalma da jaka komai ya ji ga kayan sarkoki, mata sai guda sukeyi ana ta son barka domin kaya sun yi kamar na budurwa.
Nan aka ture kayan gefe a falon Baban Hotoro aka rufe su da Leda, idan aka gama gani sai a kaiwa Umma gida.
Baban hotoro da kansa ya kirawo Umma ya sanar da ita an saka ranar auren Safiyya sati goma sha biyu, maganar kayan daki da hidimar biki kuma zai tattauna da iyayenta maza abinda suka yanke zata ji.
KARSHEN BABI NA TALATIN DA HUDU
MATAR MUKHTAR
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
BABI NA TALATIN DA BIYAR
35
Lokacin da Jamila ta isa gidansu Ummanta bata nan, babu kowa a dakin Umman sai Tani me yiwa Umman nata aiki tare da Sultan dan waje yayarta wanda aka kawoshi yaye wajen Umman. Bayan ta ajiye jakarta ta dauki Halimatu suka shiga cikin gidan inda ta gaggaisa da sauran matan gidan, ta wuce wajen Abbansu da yake shima yana nan ta gaisheshi.
Duk wanda ya gansu ita da Halimatu ya zata ganin gida kawai tazo, bayan ta gaisa da mutanen gidan ta mikawa Tani Halimatu ta shiga dakin Umman ta kwanta.
Sai can kusan magriba Umman ta dawo, tunda taga Jamilan ta san da akwai matsala ta dai ji ta ne lokacin da ta ce zuwa kawai tayi ta kwana biyu saboda yayi tafiya.
Sai da dare yayi suka zo kwanciya Umman ta gama shafa'i da witri tana kan daddumar yayin da Jamilan take zaune a gafen gadon inda Sultan da Halimatu suke bacci, ta dubi Umman tace
'Umma.'
'Na'am.'
'Umma ni dai don Allah ki gayawa Abba ya yiwa Mukhtar magana, ya daina neman mata idan kuma ba zai daina ba gaskiya ni dai na gaji da zama da shi.'
Umma ta dan yi shiru tana duban fuskar Jamilan kamar mai karanta wani abu, tace
'Baki daina yi masa binciken ba kenan?'
Nan da nan ta fara hawaye, ta dubi Umman tace
'Umma nifa ba haka kawai na fara yi masa bincike ba saida ya sa min zargi a zuciyarta. Kuma wallahi Umma neman mata yake, har Zariya ya dinga zuwa wajen wata karuwa da kyar na samu Allah ya rabasu. Harda kuma kafirai fa yake nema Umma.'
'To yanzu ya kike so nayi miki? Ba a taba yin matar da ta binciki wayar miji ta zauna lafiya ba, an gaya muku ku bari kun ki. Yanzu ya kike so nayi miki kin je kin ganowa kanki abinda zai hanaki zaman lafiya.'
Ta share hawaye ta kawar da kai, ta rasa me yasa duk lokacin da ta yi maganar Mukhtar yana zina sai a kauda kai daga laifin zinar a dinga yi mata fadan bincike, ta hadiye malolon da ya tokare mata makogoro tace
'Umma ashe yanzu idan wani bangare na jikinka yana ciwo sai ace ka kau da kanka kada ka kalli ciwon. To ai ko ka kawar da kanka ciwon yana nan kuma zai cigaba da cin jikinka ko ka nemi magani ko ya kasheka idan kuma kana da nisan kwana ka sha wahala. Umma tunda fa na auri mutumin nan nake fama da ciwon sanyi, da ya warke sai ya dawo. Yanzu idan kanjamau ya dauko ya saka min wa zaiyi jinyata?'
Suka yi shiru na dan lokaci, ba a jin komai sai shesshekar Jamila. Umman tace
'Na fahimce ki, amma dai hakurin zakiyi tunda haka zamani ya zo da shi. Ni dai ba huruminane na yiwa Mukhtar din fada ba amma in sha Allah zan yiwa Abban naki magana yanzu idan na shiga wajen nasa.'
Ta tashi ta baro Jamila a daki ta dawo falonta, ta zauna a kan kujera ta kunna TV kamar me yin kallo. Wannan lamari na mijin Jamila yana damunta, ta fahimci abinda Jamila take fada sai dai ta san Abbansu ba zai saurareta ba, tunda ita kanta Jamilan ta yarda tana yi masa bincike. Sai da ta Jira wajen karfe tara da rabi sannan ta nufi wajen Abban, domin a lokacin ne yake zama afalonsa kuma ko ba kece da girki ba kina da damar ya saurareki.
Tun kafin ta yi masa zancen Jamilan yace
'Me ya hada Jamila da mijinta ta taho gida?'
Ta kalleshi da mamaki
'Au ashe ta gaya maka.'
'A'a shi mijin nata ya kirawo yayansu yayi masa bayanin ai. Ban dawo da wuri ba shi yasa na kyaleta sai da safe.'
Don haka itama Umma tayi masa sallama ta dawo dakinta tunda ba itace da kwana ba.
Ko da gari ya waye ma kafin Jamila ta tashi Abban ya fice ya tafi gona. Can wajen azahar kuma Inna ta shigo gidan; domin dama ta saba zuwa gidan tayi weekend tunda 'yayanta duka sunyi aure kuma mijinta ya dade da rasuwa. Ita din ma da ta ga Jamilan bata kawo wani abun ba don ta zata ganin gida suka zo.
Sai la'asar Abba ya dawo, karfe biyar na yamma Yaya Abdallah ya shigo gidan. A falo ya sami Abba suna hira da Inna, bayan ya gaidasu ya zauna ya mayarwa Abban yadda sukayi da Mukhtar din. Duk abun nan a gaban Inna akayi domin ita din Yayar Abban ce kuma yawancin abubuwa ko ba ayi a gabanta sun san Abban sai ya gaya mata.
Bayan sun gama sauraron Yaya Abdallah Inna ta dubi Abban tace
'Au dama Jamilan yaji kenan tayo? Kai wannan yarinya bata kyautawa, ta samu wannan yaron yana ta dawainiya da ita amma tayi ta tijara salo-salo. Da naje mata wanka ma fa haka ta dinga fitna irin wadda ma ni ban taba gani ba, don sai da ta sa ya kwashe yaransa na tsohuwar matarsa ya mayar gun mahaifiyarsa; wanda in da wani mijin nema sai ya korota a lokacin amma shine wai yanzu tana da kafar yaji?'
Abba ya tashi zaune daga kashingidar da yayi
'To ai Yaya baki gaya min duk wannan abubuwan ba kuma shima Mukhtar din bai fada ba.'
'Ai kafin na baro gidan sun shirya kuma na sakasu a gaba dukansu nayi musu nasiha, sai naga kamar ta ji fadan da nayi mata shi ya sa ko uwarta ban gayawa ba tunda abun ya wuce. To ashe bata ji maganata ba.'
A nan Abban ya dauki waya ya kirawo Umman Jamila, yace yana falonsa su zo ita da Jamila.
Tunda Jamila ta shiga falon ta ga Inna kuma taga irin kallon da Innan take mata jikinta yayi sanyi, don haka da Ummanta ta zauna a kan kujera sai ta zauna ta takure a kusa da kafar Ummanta.
Tun bayan sunan Halimatun take sa ran taji kira daga wajen Abba amma taji shiru, tana ta murna Inna ta rufa mata asiri. Domin ko dauke su Nana ma da yayi bata gayawa Ummanta dalili ba don ita kanta tana jin kunyar abinda tayi. Ta dai bawa Umman labarin yanda yaki ya kama mata event center ya kwashe kudin ya sayawa budurwa waya.
Sai da suka zauna suka nutsu Abban ya dubi Umman Jamila yace yana nuna Jamilan
'Me tace miki ya hadata da mijinta ta taho min gida?'
Zuciyar Umma a jagule saboda ganin wannan taron dangin da aka shiryawa Jamilan. Cikin sanyin murya tace
'To ita dai tace yana neman mata don ko nima nayi mata fadan zargi babu kyau yana lalata aure amma tace ba zargi take ba ta tabbatar.'
Abba ya kalli Abdallah wanda nan take ya mayarwa da Umman abinda Mukhtar din ya gaya masa, Abban ya dubi Jamilan yace
'Ko karya yayi mikine? Ita matar sanatan da kika kira karuwa itama nemanta yakeyi?'
Cikin rawar murya tace
'Abba ai wannan ban sani ba amma...'
Ya katseta yace
'Ohhh!.....kin jita ko?'
Yana duban Ummanta, ya dubi Jamilan ya cigaba
'Ke kin san girma kazafin zina a shari'a kuwa? Kin san duk wannan maganar da kike idan aka kai kotun a karshe ke za ayiwa bulala ko? Kuma ma a ina kika taba kamashi yana zina?'
Inna tace
'Wayace dai fitnarta, tunda da kanshi ya gaya min bai isa ya ajiye wayarsa ba sai ta bincike tas. Duk inda taga sako daga mace ko wata lamba da bata
08, January 2025
Nafisa
I cant download the book