Showing 60001 words to 63000 words out of 92582 words
HND bai kai ya samar mata aiki ba tunda tana kallon yanda masu degree ma aikin yake musu wahala. Amma kuma yanzu tabbas ta san za ta iya samun aiki a private school don haka da Yaya ya zo zata yi masa magana.
Washe garin ranar kuwa Yaya Habibu ya zo gidan da safe kafin ya tafi office, bayan ya gaisa da Umma shi da kanshi ya fara maganar aikin. Sai da ya gama Umma ta dubeshi rai a bace tace
'Habibu wai me yasa kai baka son yarinyar nan tayi aure ne? Duk abinda zai sa ba za a kulata ba shi kake nuna mata. Kai da kanka ka san idan mace ta tara kudi mazan ma tsoronta sukeyi haka zata zauna ba zata yi auren ba?'
Yayi murmushi
'Umma ba haka bane, kin ga zaman haka shima babu dadi sai ki ganta kullum cikin damuwa. Amma yanzu kinga tanata walwalarta, kuma auren ma in sha Allah yana nan tafe Umma.'
Ya kwalawa Safiyyan kira, kafin ta fito Umma ta tashi ta shige dakin. Sai da ya karbi takardun Safiyyan sannan ya gaya mata lallai ta dinga lallaba Umma sannan ya tafi.
Sati biyu da karbar takardun ya samo mata aikin kuwa, makarantar ma a kasa take zuwa daga gida. Nan da nan suka bata koyar da yara 'yan primary 1 zuwa 3 computer science Kuma aka saka ta class teacher din primary 2.
Albashin dai ba wani mai yawa bane, dubu goma sha bakwai ne amma duk da haka ba karamin dadi ta ji ba. Ko babu komai ita kanta ta san tana cikin walwala gashi kasusuwan nan na wuyanta da ido zuru-zuru duk sun koma sannan kuma duk abinda take so yanzu tana iya siya; don ma tana yi a hankali don kada Umma ta zata wasu kudi take samu da yawa. Saboda ita Umma har yanzu ta dai rage tsangwamar tane saboda ko babu komai duk abinda ta nema zata saya mata, gashi duk Juma'a sai ta siyowa Umman kaza ko tsire duk su ci tare da su Sabir.
Amma wani lokacin har tausayi Umman take bata yanda taga tana so tayi aure. Gashi wani lokacin sai taga kamar Yaya hajiyayye tana kara zugata, don tana yawan cewa
'Shi wannan yawon na kitso ai gara kiyi aure ki huta da shi.'
Haka dai Safiyya ta cigaba da gudanar da rayuwarta.
-----
Tunda Mukhtar ya kwashe yaransa daga wajen Jamila sai kuma ya daina shiga harkarta, suka zama kowa rayuwarsa yake yi. Ita kuma Jamilan tana so ta kulashi amma tana tsoro saboda ta san itace mai laifi, kuma gashi sai wasu muzurai kawai yake mata da sun hadu, don haka itama sai ta ja jikinta.
Ranar da ta cika sati uku da haihuwa Inna ta hada kayanta, ta yiwa Jamila sallama Mukhtar ya dauketa domin ya kaita gida. Tana kallonsu ta san halin da suke ciki don haka har ya isa kofar gidanta babu abinda take masa sai bashi hakuri da kuma nasiha. Ya sauketa yayi mata goma ta arziki suka rabu kowa yana godiya.
Kwana biyu da tafiyar Inna Jamila duk ta shiga damuwa, daga ita sai Baby domin shi ko bi ta kansu baya yi.
Tana jinsa zai shigo haka kuma tana jinsa zai fita, yanda ta ajiye masa abincin a falonsa haka take gajiya ta dauke. Don haka yau ta yi niyyar dole ya saurareta, ta yarda tayi babban laifi amma ai ya kamata ayi mata afuwa ba don halinta ba.
Kamar yanda ya saba sai wajen goma na dare ya dawo, tana jin motsinsa har ya gama abinda yakeyi ya fito falon sama ya zauna ya kunna TV.
Sai da ta tattaro duk wata nutsuwa da take da ita, kayan bacci ne a jikinta amma sai ta dauki hijabi ta saka domin ta kula ko tsirara zata je ba zai saurareta ba gashi kuma bata yi arba'in ba.
Tun ranar da sukayi fada ya riga ya sakawa kofar dakinta wadda take shiga nashi dakin mukulli don haka sai da ta fito daga dakinta ta shiga ta falo.
Ko kallonta bai yi ba balle ya amsa sallamarta. Haka dai ta karasa ta zube a gabansa ta mika masa takarda da biro wanda ta shigo da shi, a fusace ya dubeta yace
'Meye haka kuma? Ko Sabon hauka kika fara ko kuma kema shaye-shayen kika fara?'
Nan take hawaye ya fara bin idanuwanta, ta zube hannuwanta wanda suke rike da takardar a kan cinyarta ta bude baki cikin shessheka tace
'Saki zaka rubuta min na tafi gidanmu.'
'Mtsewwww!'
Yaja dogom tsaki sannan ya cigaba
'An ki a sake ki din kin ji, ba zan sake ki ba sai ki je ki sake wani sabon hauka ko zaki dace.'
Cikin shassheka ta bashi amsa
'Don Allah Mukhtar ka sake ni in tafi. Ya zanyi? Na san nayi laifi kuma nayi kuskure amma ko sauraro na ma baka yi balle na samu damar baka hakuri, wajen sati uku ana abu daya. Ya kake so nayi don Allah?'
A fusace yake kallonta
'Oh, ashe ma kin san kin yi ba dai-dai ba kuma har kina da bakin bada hakuri? Ai na zata bakiyiwa kowa laifi ba.'
Ta dan matsa kusa dashi ta dafa cinyarsa da hannunta tana fitar da hawaye
'Don Allah kayi hakuri, don Allah! Wallahi ba zan sake ba , kayi hakuri.'
Tsaki kawai yayi ya kawar da kai, da ta fuskanci kamar ba zai ce komai ba ta cigaba cikin sanyin murya
'Don Allah kayi hakuri, ai Allah nace wanda shima muna masa laifi Kuma muna fatan ya yafe.'
Ta fuskanci ya fara saukowa don haka ta kara matsawa ta dan kwanta a kafadarsa, jimawa kadan tace
'In sha Allah ba zan sake ba, duk wani abu ma da zai saka ka damuwa nayi maka alkawarin ba zan sake ba.'
Tabe baki yayi kawai ya kawar da kai, ta mayar da kanta ta kwantar a kafadarsa. Jimawa kadan yace
'Ni in tambayeki ma.'
Ta dago ta dubi fuskarsa sannan ya cigaba
'Nana kawai kike bawa benilyn din ko tare kuke sha ?'
Mamaki ya cikata, sai yanzu ta gane kallon da yake mata tunda abun ya faru . Ta dafe kirji cikin rawar murya tace
'Haba Mukhtar! Ina shaye-shaye amma baka tana sani ba? Wallahi babu abinda nake sha, itama Nanan matsala aka samu kuma likita ne ya rubuta mata wannan maganin da farko katin ma yana wajenka zaka iya dubawa. In sha Allah kuma ba zan sake irin haka ba.'
Ta karasa tana sunkuyar da kai. Jijjiga kai kawai yayi yace
'Hmnn?'
Jinta kawai yayi amma shi ya san sai ya sake saka mata ido sosai, domin daga baya ya fara tunanin ko ita ma tana shan benilyn din musamman saboda yanda ta zo tayi masa wannan haukan har ta fasa masa waya. Kuma ya san dole ya saka mata ido kada taje ta bawa Halima wani abun da zai mayar da ita 'yar kwaya.
Haka a hankali har ya hakura suka sake, sai dai tana kula da yanda yake wani kaffa-kaffa da ita ya ki sakewa.
Babu yanda bata yi da shi ya dawo da su Nana ba amma ya ki. Daga karshe ma ce mata yayi ba zai kuma bata rikon dan da bata haifa ba, ko wanda ta haifa din ma kuma idan yaga babu hali zai kwashe yaransa don haka ta zama cikin shiri. Don haka ta hakura ta daina maganar su Nanan.
Tana son taje gidan ta bawa su Hajiya hakuri amma ta kasa, ga bukuwa a gidan an saka rana ta kasa zuwa murna. An kawo kayan auren Habiba Yar kishiyar Hajiya sannan kuma itama Bahijja Aminu ne zai aureta don haka aka hada aka sa rana daya. Kaf dangi kowa ya je ganin lefe ita kuwa ta kasa zuwa saboda kunya.
.......
Yau Juma'ah ce don haka tunda taga yana shirin tafiya office ta fara shiga damuwa, tana so ta tambayeshi Zariya zai je amma tana tsoron abinda zai ce mata don har yanzu lallabawa take yi. Bayan ya gama cin abincinsa yayi mata sallama ya fice.
Yana fita ta kirawo kaninta tace
'Don Allah ka bi min Mukhtar ko ka sa a bi min shi kawai ku gani hanyar Zariya yayi ko wani wajen ya nufa?'
Ta ajiye wayar ta zauna tana ta faman kumbura saboda takaici. Domin tun tuni kanin nata ya gaya mata abinda yake zuwa yi a Zariya da ta saka shi ya bincike shi, hatta adireshin gidan su Fatiman sai da ya gaya mata da inda Fatiman take aiki. Lokaci kawai take jira amma tabbas ba zata dauki wannan wulakancin ba.
Sai can an jima tana ta hidimarta ya kirawo ta, tana dagawa yace
'Gaskiya Maman Baby mutumin nan Zariya ya tafi, don ya tsaya a office bai fi minti goma ba ya fito ya kama hanya don wanda na sa ya bishi sai da ya raka shi har suka wuce Naibawa sannan nace ya dawo.'
'To shike nan na gode, za ka ji alert in sha Allah.'
'Yauwa Hajiyata, ni da abokai na muna godiya.'
Sukayi sallama ta jefa wayar kan kujera ta ja tsaki. Ta cije lebe saboda takaici a yayinda hawaye da take kokarin ta danne suka kwace; yanzu haka zata zauna yana raba musu kwana da wata karuwa a Zariya, tana da yakinin kuma wannan yarinyar ya bawa kudin da zai kama mata event center taje ta sayi waya. Tabbas dole ta dauki mataki, yanzu dai tana lallabawa abubuwa su dawo dai-dai don ta kula yana mata kallon mahaukaciya.
Tana nan da lambobin wayar 'yan matan nasa da ta dauka a tsohuwar wayarsa tun kafin ta fasa kuma yanzu ma da ta sami dama zata duba sabuwar wayar ta sake hado wasu don ta san da saura. Tana jira ne shi ya gama nasa haukan tunda shi bai yadda ma yana yi ba, a lokacin ne zata bi 'yan matan nasa daya bayan daya ta kora musu jawabin; domin a yanzu tana jin tabbas zata iya bin yarinya har dakin uwarta ta kora mata jawabi idan bata daina bi mata miji ba.
Ta share hawaye ta cigaba da hidimarta, tana yi tana kwafa saboda takaici.
KARSHEN BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI.
MATAR MUKHTAR
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
FIKRA WRITERS ASSOCIATION
BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS
28
A zaune take ta fito daga wanka a gaban mudubi tana shiryawa. Zuwan Mukhtar take jira don shi ya saka ma take shiryawa da wuri. Kwana biyu takurawa kanta kawai takeyi tana sauraronsa, gaba daya ya gama fice mata daga rai.
Ta bar shafa man da takeyi ta kalli zoben da yake hannunta, ta juya zoben a yatsanta. Kwana biyu ji take kamar zoben yayi mata nauyi a hannunta.
Tabbas a da tana son Mukhtar, amma yanzu kam ya fice mata daga rai. Ta kasa tuna irin rayuwar da zata yi idan ta zama matar Mukhtar.
Bata son gori ko daya, kuma tabbas ta san idan ta auri Mukhtar wata rana zai goranta mata, ko kuma ma yayi mata wulakanci.
Ta sake kallon zoben; to yanzu kenan ko bayan ta zama matarsa idan ta cire zoben nan komai zai iya faruwa kenan. Ta jijjiga kai tana so ta daina wannan tunanin.
Ta mike ta karasa gaban wardrobe ta zaro kayan da zata saka.
Mommy bata nan ta tafi Umra tare da Yaya Ibrahim don haka daga ita sai Baba Habi a gidan. Sai jibi zasu dawo, don haka ne ma ta sanar da Mukhtar ya zo ya kaita Abuja gidan Mami inda daga can idan aka dauko Mommy daga airport sai su dawo tare.
Tana son Mommy ta dawo domin tayi kewarta, amma tana fargabar dawowarnan saboda Mommy ta gaya mata da sun dawo zata sa Yaya Ibrahim ya nemi Mukhtar a fara maganar aurensu; domin ita Mommy so take kafin karshen shekara ayi bikin Fatima.
Kafin ta gama shiryawa har Mukhtar ya karaso, haka ta karasa ta fito suka kama hanya. Shi kanshi Mukhtar din sai da ya fahimci wani abu yana damunta saboda yanda bata da walwala sosai, amma haka ya kyaleta saboda shi kanshi yana zaton kewar Mommy take yi.
Kullum lallabata yake yi a kan ta bari ya fito ayi aurensu amma ta ki, yanzu ma da tace ya bari ita da kanta zata yi masa maganar sai ya zama tsoron ma tada zancen yake yi. Gaba daya ya kare a hanyar Zariya, ga kudin mai ga wahala gashi kullum sai ta gaya masa abinda take so ya taho mata da shi daga Kano wanda wata ran sai ta bukaci abun sama da dubu goma; kuma dole ya kawo.
Haka har suka isa Abuja suna yi suna hira wadda yawanci shine yake hirar. Yana sauketa ya kamo hanyar Kano.
...........
Ta kasa gane murna zata yi ko fargaba, a haka dai ta tashi ta shirya suka tafi airport don su dauko su Mommy.
Inda ake tarbar passenger nan suka zauna ita da Faisal dan wajen Mami, wanda shi ya kaisu airport din. Suna kallo jirgin ya sauka, aka gama abinda za ayi fasinjoji suka fara fitowa. Tana hango su Mommy ta mike ta karasa bakin kofar da zasu shigo tana ta faman murmushi.
Suna shigowa ta rungume Mommy, bayan ta saki Mommy ta dan rage tsawo tace
'Ya Ibrahim sannu da zuwa.'
Da fara'a ya amsa sannan suka gaisa.
Mutumin da yake binsu a baya wanda yake tafe tare da wani yaro mai kimanin shekaru tara ya danyi gyran murya sakamakon tare masa hanya da Ibrahim yayi. Don haka suka matsa daga hanya.
Ta ja Mommy suka zauna a wajen da ake jira yayinda shi kuma Ibrahim ya ja Faisal suka tafi don su dauko musu kayansu. Bayan sun dauko kayan suka nufi su Fatiman, har sun kusa isa wajensu wannan mutumin da yayi masa gyaran murya don ya matsa masa ya dan sha gabansa tare da yi masa sallama yana mika masa hannu. Suka tsaya shi da Faisal din duka suka gaisa da mutumin da alamar mamaki a fuskar Ibrahim.
Mutumin wanda yake ta fara'a yace
'Sunana Ahmad Muhammad Auyo, Ina aiki a Federal Inland Revenue Services dake nan Abuja.'
Ya juya ya nuna masa yaron da da ya gansu tare yana fadin
'Wancan yaronane Hafiz.'
Mamakin Ibrahim ya karu don Bai fahimci dalilin wannan bayanin ba, kafin ya gama tunanin Ahmad ya cigaba
'Amm, dama ina so ne idan ba kayiwa kanwarka miji ba ka dan bani dama ko Allah zai sa nine mijin nata don ina sonta.'
Ibrahim yayi 'yar dariya yace
'Wai Fatima?'
'Ma sha Allah, sunanta Fatima ko? Waccan mai abayar wadda take zaune kusa da Mommynta don naji tace Mommy.'
'Hakane, to babu damuwa. Mu karasa sai ku gaisa.'
'No, ka kyale Fatima amma muje na gaida Mommy. In ya so sai ka bani lambarka kayi min kwatancen inda kuke gobe sai na zo na kawo kaina.'
Ya danyi murmushi
'To babu laifi.'
Nan sukayi musayar lambar waya kuma yayi masa kwatancen gidansu a Zariya. Suka karasa ya tsuguna har kasa ya gaida Mommy yayinda ita kuma Fatima ta dan rusuna ta gaisheshi domin ta zata abokin Ibrahim ne.
Sukayi sallama suka kama hanya.
Sosai Ibrahim ya ji dadin haduwar da sukayi da Ahmad. Shi dama tuntuni yake fama da Mommy a kan a sallami Mukhtar amma Mommy taki yarda saboda tana ganin kamar idan aka bari Mukhtar ya subuce ba lallai Fatima ta sami wani mijin ba, don haka tace masa tunda dai Fatiman ce ta kawoshi kada ma ya tada wata magana kawai ya bari ayi auren.
Don haka kafin su koma Zariya ya sa an yi masa bincike a kan Ahmad din kuma an tabbatar masa da cewa Ahamad mutumin Auyo ne kuma matarsa uwar wannan yaron nasa Hafiz ta rasu tun Hafiz din yana shekaru hudu da haihuwa.
Ta zo haihuwar kanin Hafiz Allah ya karbi rayuwarsu ita da abinda yake cikinta, kuma tun wannan lokacin Ahmad din bai sake aure ba. Kuma ba'a sameshi da wani mugun hali ba, don haka Ibrahim ya sake jin dadi don duk yanda za ayi sai ya raba Fatima da Mukhtar ya aura mata Ahmad.
Shatar mota suka dauka daga Abuja har Zariya, aka sauke su a gidan Mommy. Suna sauka Ibrahim ya dauko mukullin motarsa wadda ya bari a nan, Fatima tayi masa rakiya wajen mota. Kafin ya shiga motar ya juyo ya dubi Fatiman yace
'Gobe za kiyi bako sai ki shirya.'
Ta dan zare ido
'Eye, bako kuma?'
Ya bata rai yana hararta
'Eh, bako. Saura in ji wani labari.'
Ta sunkuyar da kai, ya ja motarshi ya barta a nan.
Ta shiga gida tana zumbura baki tana addu'a Allah ya sa ba tallanta Yaya Ibrahim yaje yayi wa wani ba don ita bata so mutum ya zo ya raina ta.
.........
Mutuwar mahaifiyar Hafiz ta gigita Ahmad sosai; suna ta shirin tarbar baby din da zata haifa wanda an riga an yi scanning an sanar da su namiji ne. Katsam ciki yana wata takwas ta kama nakuda, suna zuwa asibiti aka ce aiki za ayi a cire yaron saboda akwai matsala. Ya saka hannu a duk wasu takardu ya tafi siyo allurai da magungunan da aka bukata yana dawowa aka sanar da shi ta rasu ita da abinda yake cikinta.
Haka suka koma gida akayi mata sutura. Tun wannan lokacin har kawo yanzu shekaru biyar kenan bai sake aure ba kuma bai sake marmarin soyayya da wata mace ba. Mahaifiyarsa da danginsa duk sunyi fada sun gaji, an yi masa tayin 'yan mata sau ba iyaka amma duk ya ki kulasu.
Don haka kawo yanzu addua kawai ake masa, shima kuma da kansa addua yake wa kansa. Wannan tafiyar ma da suka je Umra sai da yayi dawafi ya roki Allah ya bashi mace ta gari wadda zata zauna da shi da Hafiz cikin amana. Ya gaji da zaman Hafiz din a Auyo wajen babarsa, so yake ya dawo da shi Abuja amma ya san hakan ba zai samu ba dole sai yayi aure.
Tun suna saukowa daga jirgi ya hango Fatima tana tsaye a inda take jiran mommy; da yake glass ne ya
08, January 2025
Nafisa
I cant download the book