Showing 90001 words to 92582 words out of 92582 words

Chapter 31 - MATAR MUKHTAR COMPLT

SAKINA   

16 Aug 2024

7157

sallama ya sa wasikar a aljihu ya wuce yana dariya.

KARSHEN BABI NA TALATIN DA TAKWAS

MATAR MUKHTAR

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA TALATIN DA TARA

39
Tun Safiyya tana sa rana Hamida zata dawo da su Nana har ta gaji ta hakura. Haka ake ta shirye-shiryen biki amma hankalinta baya wajen, tunda Umma ta gane matsalarta ta shareta suka cigaba da hidimarsu. Bata son ta cewa Hamida ta dawo dasu don kada Hamidan taga bata kyauta ba don haka ta daure aka cigaba da shiri.
......

Tun ranar da ya sa Aminu ya kaisu gidan su Safiyya yake jiran kiranta amma har yau Juma'a shiru, don ranar litinin din har wajen dayan dare idonsa biyu yana jira Safiyya ta kirawo shi amma shiru. Sai da kyar bacci barawo ya sace shi.

Gashi har kawo yau shiru, ko Hajiya ma tace basu kirawota ba don haka ya san suna can suna jin dadin hutunsu.

Jikinsa yayi sanyi, saura kwana bakwai yau a daura auren Safiyya da mutumin da ya tsana, shikenan yayi nasara ya rabashi da matarsa uwar yaransa. Zuciyarsa a jagule ya kirawo Aminu yace gobe da safe yaje ya dauko masa yaransa.

Washegari wajen karfe goma Aminu minu ya isa gidan Umma don ya dauko su, yana isa aka ce masa suna gidan Hamida ya bari za a dawo dasu. Yace gara dai ya daukesun kawai don haka aka yi masa kwatance ya wuce can ya daukesu.

Tunda Safiyya taji labari sun wuce daga gidan Hamida ta kasa tare hawayenta, don haka Umma ta saka ta a gaba ta ci mata mutunci sannan tace

'Idan mutuwa zakiyi to ki shirya ki mutu tun da wuri don ba zaki koma gidan wannan mutumin ba. Yara muma muna sonsu kuma muna tare da su in Sha Allahu amma tunda aka kawo yanzu to kowa tasa ta fissheshi, Allah ya raya mana su.'

Ta bar Safiyyan a nan tana kukan takaici; da sune suke so ta koma gidan Mukhtar amma yanzu sun tsangwameta saboda sunga tana tausayin yaranta. Ita a halin yanzu ma bata san me take so ba kuma bata san wa take so ba, so kawai takeyi a barta tare da yaranta.

Gashi AA yana maganar Abuja zai tafi da ita ko Lagos don haka ta san nisa zata yi musu sosai; idan ta tuna sai zuciyarta ta sake karyewa.

Sai da yamma Yaya Hajiyayye tazo ta sakata a gaba da fada da nasiha, ta kifa kai a kan cinyar Yaya Hajiyayye tayi kukanta ya isheta Hajiyayye tana lallashinta daga karshe tace mata

'Ki kwantar da hankali ki ke din matar AA ce ba matar Mukhtar ba da izinin Allah.'

Saida gari ya waye sannan ta dan fara samu nutsuwa saboda ta kwana tana sallah da addu'a. Aka cigaba da shirin biki domin a satin ne zata je gyaran gashi da gyaran jiki. Haka aka cigaba da shirin biki jikinta a sanyaye, ranar laraba tana kallo aka zabi mutum uku da Yaya hajiyayye suka tafi don gyara mata gidan. Bayan sun fice kuma mai kunshi ta zo ta zana mata mai dankaren kyau; dama gashi fatarta sai santsi da kamshi kawai takeyi. Kafin dare amarya ta fito fes da ita sai dai kawai kana kallonta zaka ga damuwa a fuskarta, domin har wani share kwalla takeyi.

Ranar Alhamis za ayi kamu a nan gidan Umman don haka tun safe su Inna Hajara suka zo da sauran yanuwan babansu Safiyya, nan da nan gida ya kacame da hayaniya.

Tunda amarya tazo gaida iyayen nata Inna Hajara ta san da matsala, ta san ba zai wuce a kan yaranta bane take bata rai don sunyi maganar da Umma a waya. Nan take Inna ta jata suka kule a dakin su Safiyyan da yake babu kowa a ciki. Bayan sun zauna a gefen gado Inna ta dubeta tace

'Ya akayi ne Safiyya?
Sai kace wadda za ayiwa auren dole? Kina ta wani zare ido.'

Kawai sai ta fada cinyar Innan ta fashe da kuka, sai da tayi mai isarta sannan ta dago ta dubi Innan tace

'Inna sai naga kamar ban kyauta ba idan na tafi na cigaba da haihuwa na bar yarana tunda ubansu yanzu yana so mu dawo.'

Inna tayi murmushi mai sautu, ta dago Safiyyan ta kalli fuskarta ta share mata hawaye sannan tace

'Ki bani hankalinki nan Safiyya. Uban yaranki baya son ku dawo, ya dai ga zaki auri wanda ya fi shi, shi yasa ya dawo ya mayar dake cikin wahalar da kika riga kika sani. Idan namiji yayi saki mace in dai da sauran kauna to kafin matar nan tayi wata uku a gida yake mayar da ita, idan aka wuce haka to babu so ko daya.

Shi dinma da ace ya ga wani kaskantacce zaki aura ba zai dawo ba dariya zai dinga yi miki kamar yanda ya dinga yi miki dariya yana tunanin kina cikin kunci zawarci. Yara kuma kowa da kaddararsa, baki da ikon tsarawa kowa rayuwa sai abinda Allah ya tsara don haka ki barwa Allah aikinsa kiyi naki; wato addu'a. Ke kika ce min kinyi istikhara a kan Allah ya zaba miki abinda yafi alkhairi gashi ya zaba miki amma kina so kiyi fatali da zabin Allah, idan kikayi haka kuwa anya bakiyiwa Allah butulci ba? Idan dai kin gode da abinda Allah yayi miki da ya rabaki da kuncin da kike ciki a baya to ki wanke fuskarki ki shirya ki fito yanzu naga kina ta walwala. Kin ji ko?'

Ta gyada kai alamar to, ta fada jikin Inna ta sake rungumeta tace

'Nagode Inna.'

Da dariya Inna tace

'Yauwa ta wajena, maza ki shirya ina falo ina jira naga kwalliyar amaryar Abdurrahman ba tsohuwar matar Mukhtar ba.'

Tayi dariya tana goge fuska, Inna ta fito ta rufo mata kofar dakin.

Ta sa hannu ta dafe kirjinta tana ajiyar zuciya, ko babu komai taji sanyi da tayi kukanta a jikin Inna ba tare da an hanata ba. Ta mike ta karasa gaba mudubi, ta kalli fuskarta wadda ta jike da nason hawaye tayiwa kanta murmushi; tabbas ta so ta yiwa Allah butulci duk da tarin ni'imomin da yayi mata domin ita ta nemi zabin sa kuma gashi yayi mata. Ta bude baki tace

'Alhamdulillah.'

Ta sake kallon kanta tayi murmushi, tabbas tana son mijin barrister sai dai soyayyar da takewa yaranta tana saka mata shakku a kan komai.

Wayarta ce da take ajiye a kan mudubin ta dau waka, ta kalli wayar hoton fuskar A A ya bayyana domin da kansa ya saka mata lokacin da ya siyo mata wayar. Ta bi hoton da kallo tana murmushi har wayar ta nemi tsinkewa sannan ta dauka. Bayan ta amsa sallamarsa tace

'Mijin Barrister.'

'Amaryar AA, ina kika shiga ne kike hora ni haka? Tun jiya nake waya bakya dauka. Kin san Allah kin ganni a mota da baki dauka ba yanzu gidan zan taho.'

Tayi da dariyar da ta kwana biyu batayi irinta ba

'Kaina bisa wuyana, a daki nake barin wayar saboda gidan da mutane.'

'Gobe ne fa, kin shirya ko na zo na shiryaki?'

Ta sake kyalkyalewa da dariya irin yanda take saka shi nishadi sannan tace

'Kaga bari naje na shirya kafin Inna ta biyoni don tun dazu tace na fita wajen mutane.'

Sukayi sallama ta fada bandaki, nan da nan ta gyara fuskar ta sako doguwar rigarta ta atamfa ta yafa mayafinta mai kyau ta fito ta shiga gaisawa da mutane kafin yamma tayi a zo kamu.
.....

Ana idar da sallar la'asar mai kwalliya ta zo, nan da nan tayi mata makeup dan daidai misali wanda ya kara mata kyau, ta saka leshinta kalar maroon. Ta riga ta ce ba zata saka goggoro ba don haka mai kwalliyar ta daura mata dankwalin leshinta irin yanda ake yiwa amare. Ta kawo mayafi irin na amare me ruwan gwal ta yafo tun daga kanta har kasa.

An riga an gyara dakin Umma don a nan za ayi kamu, an riga an gyara dakin an shimfida babban zanin gado ga fululluka an jera an baje carpets, ga turaren wuta mai sanyi kamshi na Xee Yaxeed da aka kunna a kowacce kwana don haka kamshi ne kawai yake fita daga dakin. Ta zauna a kan gadon kamar yanda saraki suke zama a kan karaga.

Saliha da Maimuna 'yar wajen Inna suka zauna a gefenta suna ta hirarrakinsu.

Basu dade da zama ba aka buga musu kofa aka ce ga 'yan kamu nan don haka suka gyara suka ja mata mayafi ta rufe fuskarta. Su Hamida da sauran cousins dinsu sukayi ta ciniki da iyayen ango hara aka tsaya a kan naira dubu dari. Suka zaro su sababbi dal 'yan naira dubu dubu suka mikawa Hamida. Nan da nan aka saka guda aka bude musu kofa suka shiga suka feshe amarya da turare.

Jimawa kadan aka fito farfajiyar gidan inda aka zuba kujeru duk da basu da yawa, nan malaman islamiyyar su Safiyya suka fara lakca aka baje ilimi ana ta tattaunawa ana raha. Ga abinci kala-kala hadadde da aka rarraba kowa yaci ya sha.

Sai gefin magriba aka fara raba souvenir wanda Xee yaxeed ce ta yi musu turare da kasko tare da gawayi aka bawa kowa, aka kwashi na dangin ango aka zuba musu a motar da suka zo da ita. Aka sallami malamai taro ya tashi.
......

Washegari ranar daurin aure tun karfe bakwai ta shirya suka wuce gidan Baban Hotoro, domin a can za a daura auren kuma haka sukeyi duk 'yar da zai aurar sai ta zo gidan. Sai bayan azahar sai yayi mata nasiha ta koma gida.

Sai karfe sha daya za a daura auren don haka saida suka gama hirarrakinsu da dangi suka ci abincin safe sannan amarya ta shirya.

Farar atamfa ta saka wadda aka dinka mata siket da riga sannan ta kawo farin laffaya lace wanda aka yiwa kwalliya da shudi da ruwan gwal ta nade jikinta da shi, nan da nan dakin ya dauki kamshi domin laffayar ta sha turaren wuta.

Karfe sha daya da rabi suka jiyo sanarwa a loudspeaker: "An daura auren Safiya da Audurrahman a kan sadaki naira dubu dari, waliyyan amarya sun karba kuma mun shaida Safiya ta zama matar Audurrahman."

Nan da nan kuma mata suka karade gidan da guda.

Bayan wajen awa daya suna zaune sun gama hotuna a cikin gida angonta ya kirawota, tana daga waya yace

'Mrs AA.'

Tayi murmushi kamar tana gabansa, yace

'Ina falon bakin Baban Hotoro ina jiranki minti biyu na ganki ko?'

'Ka ga mutane kuwa a cikin gidan, gaskiya ba zan iya fitowa ba fa.'

'Barin na turo a dauko min ke.'

Tana ta dariya ta ajiye wayar, ai kuwa ba jimawa Saliha ta shigo ta tasata a gaba har falon.

Shi kadai ne a falon yana waya suna shiga ya ajiye wayar ta karasa ta zauna a kusa da shi, Saliha tace

'Gata nan bari na hado kan dangi sai ku fito bakin gate muyi hotunan.'

Tana fita Sabir ya shigo, yana ganin zaman nasu ya daga waya ya danna video.

AA yace

'Kin wani sunkuyar da kai kamar mara gaskiya.'

Ta kara sunkuyar da kan kamar zata dungura, ya mika hannu ya kamo habarta ya dago fuskar. Ya bita da kallo yana murmushi, ta sake sunkuyar da kai, ya matso daf da kunnenta ya rada mata

'fine girl matar AA.'

Tayi dariya ta mike yayinda shima ya mike, ya tsaya a gabanta ya juyota yana fadin

'Sabir kayi mana hoto.'

Ya janyota jikinshi ta gefe suna murmushi sannan Sabir din ya kashe video din ya daukesu hotuna.

Suka fito cikin Jama'a mai hoto ya cigaba da dauka.
____

A zaune take a falo tana aikace aikacenta na gida. Tunda yaje gidan Baba ya ga Baban sun ci kwalliya shi da Nurain da Aminu wai zasu tafi auren Safiyya ransa ya baci, yayi magana kuma Baban yace wai ya zo suje. Don haka yana fitowa daga gidan ya dawo gida ya kwanta a falo Halimatu tana ta yi masa gwaranci.

Zuciyarsa babu dadi, bai san me zai yi ba shi yasa ya kwanta a nan ko motsinsu zai debe masa kewa. Ya daga waya ya gama zagayawa a Facebook, ya rufe ya dawo Whatsapp. Ya duba sakonnin sa kadan sannan ya fara kallon status, ya bude guda yana kallo yana gatsina baki wani yayi 'yar dariya.

Bai damu da sunan wanda ya dora ba don haka kallo kawai yake wannan yana wucewa wani ya fara.

Kamar da keta ya buda wani, tun kafin ta dago fuskarsa ya san Safiyya ce. Ji yayi kamar ya rusa ihu lokacin da AA ya mika hannu ya dago fuskar Safiyya. Haka sukayita soyayya yana kallo kuma yaki yan rufe status din zuciyarsa sai suya take yi.

Har hoton ya kusa karewa Jamila da take tsaye a kansa ta mika hannu ta dafe wayar tana fadin

'Wannan ai kamar Maman su Nurain ko?'

A fusace ya bata amsa tare da rufe wayar

'Eh itace.'

Har zuciyarta ta bashi amsa

'Allah sarki ta ji dadinta don da da gani suna son juna, inama ni ce ita.'

Ya juyo ya kalleta a fusace

'Ina ma ke ce kike auren ko me kike nufi?'

Tar ta kalleshi tace

'Eh, inama nice tunda kaga ko ba komai da matarsa zai raba mata kwana ba da karuwa ba.'

Ya mike a fusace yana nunata.

'Bafa na son irin wannan Jamila, wannan ai wulakancine. Ni kike gayawa wannan maganar banzar?'
'A'a fa! Ba ni na kar zomon ba ratayar ma ba a bani ba. Yauwa, kada ka daga min hankali daga fadin abinda ke raina.'

'Mtsewwww!'

Ya ja tsaki ya wuceta ya haye saman.

Haka suka koma tun bayan data dawo daga yajin data yi. Ta daina magana a kan neman matan da yakeyi amma fa duk lokacin data ga dama haka zatayi ta yaba masa maganganu marasa dadi, in ya biye mata kuma sai suyi tayi bata damuwa.

Idan abun ya ciyota kuma sai ta shige daki tayi kukanta ta koshi tunda ta daina gayawa kowa matsalarta. Ta riga ta yarda duk matan duniya munafukai ne tunda duka ce mata suke gaba daya maza haka suke da neman mata amma duk wadda ta tambaya

'Mijinki yana neman mata?'

Sai sauce mata a'a.

Saboda tsabar ta saba har ganewa takeyi idan yayi sabuwar budurwa. Saukinta daya tana zuwa aiki kuma tana karbar albashinta, sannan kuma hidimar gidansa ko ashana bata yarda ta siya sai ya biya don tace bazata yi asara ba, ta kaiwa 'yanmata nasa kudin ita kuma tayi hidimar gidansa da nata.

Yana shiga ya turo kofar dakin ya zauna a gefen gado, yanzu shikenan yayi asarar Safiyya? Anya kuwa zai iya karashe rayuwarsa da Jamila?
Shi mutum ne da baya son yawan fada da hayaniya, ita kuwa Jamila yanzu bata bari suyi sati suna zaman lafiya, haka kawai sai ta dinga gaya masa maganganun masu zafi har sai ya kulata sun yi fada. Idan sukayi fada kuma sai tayi kwana uku zuwa biyar bata shiga harkarsa.

Ita kuwa Jamila tambaya daya takeyiwa kanta kullum 'Anya kuwa ta yiwa 'yayanta adalci da ta zabar musu uba kamar Mukhtar? Me zata ce musu idan suka girma suka ga ubansu mazinaci ne? Wannan tambayoyi ba karamin razanata sukeyi ba suna kara mata damuwar da dama kullum a cikinta take.
Idan taga ance mijin wata ya mutu har ji take dama ace itace, Mukhtar ya mutu kawai ta huta.

KARSHEN BABI NA TALATIN DA TARA.


08, January 2025
Nafisa

I cant download the book

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login