Showing 66001 words to 69000 words out of 92582 words
Safiyya ta kirawo shi domin shi bai karbi lambarta ba. Sai dai kafin ya tafi Abuja ya saka ayi masa bincike a kanta don baya son ya zo yayi aure a sami matsala a rusa masa gida.
Kafin karshen satin an sanar da shi duka abinda yake son sani game da Safiyya. Sai dai har zuwa lokacin bata kirawo shi ba saboda kusan duk malaman makarantar suna da wani aikin ko yaran da sukewa lesson in an tashi. Don haka ta kyale kawai ta cigaba da iya kokarinta wajen ganin ta taimakawa Muhammad din.
Ranar Juma'a jirgin karfe bakwai na safe ya biyo sai Kano, daga airport da direba ya daukeshi kai tsaye suka wuce office din Yaya Habibu. Bayan ya gabatar da kansa a wajen Yaya Habibu wanda yake ta mamakin wannan ziyarar yayi gyaran murya yace
'Na san kana mamaki, wato akwai Safiyya kanwarka kamar yanda na sami bayani. Yarona dalibinta ne a makaranta don a nan ma na santa, to gaskiya ina son na shiga neman aurenta ne shi yasa naga ya kamata na nemi izininka domin ba wai zamu tsaya wasa bane. In dai har ta amince nan da wata shida ma ana iya daura auren.'
Nan da nan fara'ar Yaya Habibu ta karu yace
'Ah, ma sha Allah. Wannan ai ba zai zama matsala ba in dai ta amince.'
Suka dan taba hira, ya sanar da Yaya Habibu ranar Lahadi zai zo bayan la'asar. A nan yayi masa kwatancen gidan sannan sukayi sallama.
Yana tashi daga office ya wuce gidan Umma, sai da ya gama hirarsa zai tafi yaja Safiyya suka fice daga gidan. Suna zuwa bakin gate yace
'Akwai wani mutum Alhaji Abdurrahman Anas, yayi min magana a kan zai zo neman aurenki.'
Nan da nan idonta ya kawo kwalla ta sunkuyar da kai, ya cigaba
'Ba fa wani abu bane, ba dole za ayi miki ba shi yasa ma ban yi magana a gaban Umma ba. Idan ya zo ki dan bashi dama idan kun fahimci juna shikenan, idan kuma da matsala ki sanar dani sai a hakura. Amma dai so far na dan samu bayanai daga wadanda suka san shi sosai mutumin kirki ne, sai dai kawai wajen aikinsa da zan sa a bincika saboda kada a sake.'
Cikin rawar murya tace
'To Yaya.'
'Yauwa, ki natsu kiyi tunani a hankali kuma ki bashi dama. In sha Allahu zai zama alkhairi. Ranar Lahadi zai zo in sha Allah don haka sai ki zama cikin shiri.'
Sukayi sallama ta shiga gida tana tunani kala-kala domin ita har kawo yanzu tsoron maza takeyi, musamman 'yan kwana kin nan da har samari ma tare ta suke a hanya zasu tsarata; abinda take gani kamar rashin kunya.
-------
Yau ranar Lahadi ce don haka bai fita ba, a daki ya zauna yana ta aiki a computer. Yana dawowa daga sallar azahar ya zauna a falon don yaci abincin rana. Nan suka zauna suna ci tare, tana yi tana bawa Halimatu wadda ta kai wata shida yanzu.
Ko rabin abincin basu ci ba aka kirawo shi a waya, yana kallon screen din wayar ya saki murmushi. Ya dubeta yace
'Cigaba ina zuwa.'
Ya tsallake abincin ya wuce daki da wayar a hannunsa wadda har ya amsa ya fara magana cikin girmamawa.
Ta bi bayansa da harara tare da jan dogon tsaki. Tana da yakinin matar da ta saba kiransa ce kwannan nan, ba yarinya bace don ji tayi yana kiranta Hajiya kuma yana girmamata sosai. Tayi kwafa ta rike Halimatu wadda take kokarin rarrafawa ta bishi.
Yanzu dai ya tabbata Mukhtar sugar mommies ya fara bi. Sai jiya ta samu ta gane pattern din da yake bude wayarsa don haka duk yanda za ayi yau zuwa gobe zata sato lambar matar nan ta kora mata jawabi; an girma ana bin mijin yara.
Motsin fitowarshi ne ya karkato da hankalinta, ya fito dauke da mukullin mota da kuma computers guda biyu sababbi a kwali wadanda dama ya gaya mata ya sayar da su jira yake a zo a karba. Ya dubeta yace
'Bari na kai wadannan, idan na dawo na kara abincin.'
A ciki ta amsa
'A dawo lafiya.'
Ya sa kai ya fice.
Sai yanzu ta game ya Raina mata hankali don yanzu haka karuwa aka sayawa computer ita tana gida bata da ita. Tabbas za ayi balai kuma har shima zai ji daga gareta amma sai ta kirawo matar nan ta kora mata jawabi dole; don in ta kama zata iya zuwa duk inda matar nana take ta sameta tayi mata rashin mutunci.
KARSHEN BABI NA ASHIRIN DA TARA
MATAR MUKHTAR
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
FIKRA WRITERS ASSOCIATION
BABI NA TALATIN
30
Tana zaune a kan dadduma ta idar da sallar la'asar Yaya Habibu ya kirawota, bayan sun gaisa yace
'Bakonki ya zo, yana waje. Amma nace ya turo yaro ya kirawoki domin Umma ta sani.'
Tana ajiye wayar kuwa ta ji sallamar yaro, Umma tana kicin don haka ita ta amsa. Tana jin yaron ya gayawa Umma sakon, nan take kuwa tace
'Je kace tana zuwa.'
Domin ita Umma duk wanda yazo neman Safiyya in dai ta ji labari to dole Safiyyan ta fita, tunda ita so take kawai Safiyya tayi aure. Musamman a 'yan kwanakin nan da an riga an saka ranar auren Hamida; yanzu haka saura wata biyu.
Nan da nan ta leko daki ta daga labulen ta dubi Safiyyan
'Ana sallama dake, taso kije ki gani.'
'To Umma gani nan zuwa.'
Tana mikewa ta kalli kanta a mudubi; hijabinta babu abinda yayi kuma fuskarta ma kalau take don haka ta fito sanye da hijabinta ta wuce waje.
Tana fitowa ta dan karewa bakin gate din kallo, mota daya ta gani da alama mai motar shine a jingine a jikin motar. Daga shi bata ga alamar kowa ba sai masu wucewa, don haka ta karasa wajen da yake.
Tana kusantar wajen tayi sallama, ya juyo tare da amsa sallamarta fuskarsa da fara'a. Da mamaki ta bude baki
'Ah! Baban Muhammad.'
Tana fada tana waige waige ko zata ga ainahin wanda yake sallama da ita, sai kuma ta tuna ai Yaya Habibu Abdurrahman Anas yace mata; don haka a sanyaye ta dube shi. Ita yake kallo yana murmushi don haka tana dubansa suka hada ido, ta sunkuyar da kanta cikin sauri. Yayi 'yar dariya yace
'Nine nake nemanki Anti ba wani bane.'
Ta danyi yake tace
'Bismillah mu karasa daga ciki.'
Ya bi bayanta suka karasa farfajiyar gidan inda ta janyo kujerun roba guda biyu ta saka musu, ta nuna masa daya tace Bismillah. Bayan ya zauna itama ta zauna.
Suka sake gaisawa sannan kuma suka danyi shiru na dan lokaci, da ya ga dai ba zata ce komai ba shi sai ya fara magana inda ya gabatar mata da kansa a matsayin Assistant Commander General na Civil defence a headquarters dinsu dake Abuja, kuma yana da mata daya da yara hudu wadanda ta sansu don dalibanta ne. Har ya gama bata ce komai ba, sai da shima yayi shiru yana kallonta.
A hankali ta dago kai ta dubeshi, da yake ita yake kallo suka sake hada ido, nan da nan ta mayar da nata idon kasa ta sunkuyar da kai. Yayi murmushi; yana mamaki kunyarta kamar wata budurwa, shi ya zata mata sun daina kunya domin ya dade bai ga mace mai kunya kamar Safiyya ba.
Ta danyi gyaran murya cikin damuwa tace
'Don Allah kayi hakuri Baban Muhammad, ka ga makaranta bata yarda malama ta kulla Alaka irin wannan da mahaifin dalibinta ba; da na tura wasikar ma mahaifiyarsa nace ta zo shine kai kazo. Ai sai a zata dama don haka nace ka zo, kuma ka ga headmistress ba zata ji dadi ba don ko ita ma mahaifiyarsa tace na kirawo. Za ka sa mata su kwashe yaransu daga makarantar mu.'
Yayi murmushi
'To ai a lokacin mahaifiyarsa bata nan, shi yasa ni nazo; kuma ina zuwa kika sace zuciyata kin ga ai dole na biyo ki nima na sace taki zuciyar ko?'
Ta dago ta kalleshi ta sake sunkuyar da kai, shi da gaske yake wannan maganar kamar wani yaro; gashi a haka gani take kamar ma zai girmi Yaya Habibu.
'Uhm! Don Allah dai kayi hakuri.'
Yayi dariya yace
'Gaskiya ba zan hakura ba.'
Ta kalleshi ya daga mata kai, a ranta tace na shiga uku. Muryarshi ce ta katse mata tunani
'Kada ki damu, headmistress itace ta bani cikakken bayani a kanki kuma ta hada ni da Yayanki tace na je wajensa na nemi aurenki, kin ga da izininta kenan na zo ko? So ki kwantar da hankalinki.'
Ta yi matukar mamaki jin wannan zancen amma dai haka ta daure suka dan kara hira, wajen karfe biyar ya dubeta yace
'Bari na tafi na barki ki huta ko? Gobe karfe takwas na safe zan koma Abuja so may be zan biyo na ganki kafin ki tafi aiki.'
Ta kalleshi da mamaki
'Da sassafe ne fa.'
Dariya kawai yayi mata sukayi sallama ya wuce ya tafi bayan ya karbi lambar wayarta ya bata tashi.
Haka ta kwana tana tunanin mutumin nan, tana fatan Allah ya sa dai kada ya janyo mata matsala a wajen aiki. Bashi da wani laifi kuma tabbas ya kai a so shi, sai dai tana jin cewa a yanzu ta sami daidaito a rayuwarta bata so ya zo ya haifar mata da matsala. Tana jin tsoron zama da kishiya balle ace mara imani ce, ita auren ma gaba daya tsoronsa take; kaje ka zauna da mutum da zuciya daya kana masa biyayya kai ka hakura da abinda kake so amma shi yana maka wulakanci a karshe ka tashi babu wata riba. Amma dai zatayi istikhara ko don saboda bata so ta watsawa Yaya Habibu kasa a ido.
.......
Karfe bakwai da minti goma suka fito daga gate din gidansu ita da Sabir da Hamida zasu tafi makaranta. Yana tsaye a jikin mota ya rungume hannuwansa. Bude baki kawai tayi tana kallonsa shima ya bita da kallo yana murmushinsa wanda yake sata murmushi, ta sunkuyar da kai ta dubi Hamida tace ku dan jirani ina zuwa. Tana zuwa kusa dashi tace
'Sai da ka zo Baban Muhammad? Ina kwana.'
Taji shiru bai amsa ba, ta dago ta kalleshi ashe harararta yakeyi ta kyalkyale da dariya yace
'Idan kika kuma ce min Baban Muhammad sai na lakace wannan dogon hancin naki ya koma irin nawa, inama dai laifin saurayin Safiyya? Ai ban yi tsufa ba ko?'
Ta kyalkyale da dariya tace
'Babbar magana. Bari naje mu karasa makaranta kada mu makara.'
'Hakane kam, tunda na ganki nima yanzu sai na kama hanya.'
Sukayi sallama ya ja motarsa ya wuce, ya so ya karasa da ita makarantar amma ya san ba zata taba yarda ba don haka kawai ya hakura.
Tana dawowa Sabir ya fara
'Ya Safiyya senator ne bazawarin naki?'
Ta harareshi
'Kaine ai bazawarin.'
Yayi dariya
'To abinki da ba saurayi ba, don Allah idan senator ne ki hadani da shi a bani kwangila.'
Hamida tace
'Kai dai Allah ya shiryeka baki abun magana.'
Haka har suka karasa makarantar su Safiyya suna ta raha.
--------
Duk kokarin da Jamila tayi a kan ta samo lambar sugar Mommy din Mukhtar a wayarsa abun ya ci tura, sai da aka dauki wajen sati biyu. Ta samu ta kwafo lamabar amma dai bata kirawo ba saboda ta ga abun ya dan yi sauki, gaba daya harkar matan ma kwana biyu da sauki tunda yana yawan dawowa da la'asar kuma baya sake fita sai da safe. Don haka ta dan saurara tana fatan Allah ya sa sun rabu.
A shirye ya fito da Shirin office bayan ya gama cin abincin safe, ya zauna a falo yana wasa da Halimatu wadda take ta kokarin mikewa tsaye a jikin abun koyon tafiya tana ta gwaranci yana yi mata dariya. Ita kuma Jamila tana kicin tana ayyukanta.
Ba a jin ringing din wayarsa don haka bata jiyo lokacin da wayarsa tayi kara ba, sai dai tana jiyoshi ya amsa wayar. Ko bata sani ba ta san wannan sugar Mommy din ce saboda yanda yake magana, ta matso kusa da kofar kicin din don ta kara jiyo abinda yake fada duk da yanda yake magana kasa-kasa.
'Eh, ai na san wajen.'
'Ok. Yanzu zan iso nan da minti talatin.'
'Ok.'
Tayi sauri ta koma can cikin kichin din data ji ya mike tsaye, ya kwalo mata kira daga falon yace
'Zo ki dauki Halimatu, fita zanyi.'
Bai saurari amsar da ta bayar ba ya shige daki.
Jimawa kadan ya fito a shirye da jakarsa ta computer, ta riga ta dauke Halimatu ta koma kichin don haka yana daga falo yace mata
'Ni na fita.'
'A dawo lafiya.'
Ta bashi amsa daga kichin din, ya sa kai ya fice.
Har azahar tana ta faman share kwalla saboda takaicin Mukhtar, daurewa kawai takeyi saboda a tunaninta suna tare. Don haka ta bari sai wajen karfe uku zata kirawo matar tayi mata wulakancin da ba a taba yi mata ba a rayuwarta.
..........
Yana fitowa daga office dinsa zai karasa masallaci suyi sallar la'asar ya ci karo da Suraj a bakin kofa, sukayi musabiha suka gaisa. Mukhtar yace
'Kayi sallah ne mutumina.'
'A'a nima fitowa ta kenan ina hanya akayi kira muje in mun idar sai mu zauna.'
Suka rankaya suka tafi masallacin gaba daya. Bayan an idar da sallah suka dawo office din Mukhtar suka zauna suka hirarrakinsu.
Suraj yace
'Kawai sai naga alert mutumina.'
Mukhtar ya kau da kai
'Haba abokina 10k ce fa ba yawa, ai data kawai nace ka saka.'
'Ina godiya mutumina, ai ganina computer biyu ai ba yawa. Ni na ma zata fa da yawa zata siya shi yasa na hadaku wallahi.'
Yayai dariya yace
'Wa ya gaya maka? Ai kwannan nan ma alert din dubu dari zaka ji mutumina. Ka san bayan ta sayi computers din nan guda biyu yau da safe ta kirawo ni, tace na sameta a makarantarta. Ina zuwa ta nuna min sabon computer lab da suka gina tace na bata estimate na kudin da zasu hada computers guda arba'in kowacce da teburinta da kayan aikinta tsaf.'
Ya mika masa hannu suka tafa
'Kai amma na maka murna, dama ai na gaya maka bata wasa da kudi tunda senator yana turowa kuma kasan makarantar tata ta yaran masu kudi ce sosai.'
'Ai dagaske kuwa mutumina. Ka san ina zama a office nayi lissafi na tura mata, tana gani ta kirawo ni. Yanzu haka tace zuwa magriba zata sa a turo min 60% na kudin kayan idan aka kawo sai ta kara 20% sauran kuma idan aka hada computers din aka kunna sai tayi balancing. Ai ina tunanin da kaina zan je China na yo order kayan nan don akwai samuwa sosai Alhamdulillah.'
'To ma sha Allah abokina, ai ka riketa idan dai kayi mata aiki mai kyau zata hadaka da mutanen kirki sosai.'
Suna cikin hirarsu ya dauki wayarsa yana dan dubawa, ya budo Whatsapp yace
'Ka ganta ma voice message ta turo min yanzu haka ma an saka kudin'
'Ai Prof akwai harkar arziki.'
Take ya kunna voice note din wanda yana fara magana kuma ta rubuta masa lambar waya ta turo a kasa ta sa
"with this number."
Suna fara jin sakon Mukhtar ya saki wayar ya bude baki yayinda shi kuma Suraj ya zaro ido tare da dora hannu a ka suka cigaba da sauraro kamar haka ...
"Wai me kike fadane haka, kin san kuwa da wa kike magana?"
Muryar Professor Hajara Bala Gombe ce take wannan tambayar, kafin ta numfasa kuma wata muryar ta shigo wadda ba Mukhtar ba hatta Suraj ma ya gane muryar Jamila ce ta cigaba
"Na sani, da ke nake magana Babbar karuwa mai bin mazan yara. Ko bai gaya miki yana da mata bane Mukhtar din. Kullum cikin waya kike da mijina to wallahi duk karuwancinki na fi ki hauka, idan baki rabu da mijina ba sai na tona miki asiri kuma na nuna miki ke karamar 'yar iska ce wallahi. Matukar baki ji kunyar budewa mijina tsakanin cinyoyinki ba nima ba zan ji kunyar tona miki asiri ba. Ki rabu da mijina idan kina son zaman lafiya, ki rabu da mijina idan kina son zaman lafiya! Idan ba haka ba kuma zaki gane ni yarinya ce 'yar wannan zamani tsohuwar banza kawai! Mtsewwww."
A nan voice note din ya kare
.
A take kira ya shigo wayar wanda yana ganin lambar ya san ta prof ce duk da bai yi saving ba, ya kalli Suraj wanda shima yayi tsamo-tsami kamar shine yayi laifin , Suraj din yayi masa alamar ya dauka don haka hannunsa na rawa ya amsa wayar ya sa a loud speaker. Kafin yayi magana tace
'Mukhtar ka san ni ka san ina da aure kuma ka san waye mijina ko? Me ka gayawa matarka a kaina take kirana karuwa tana yi min cin mutuncin da kaf tsawon rayuwata ba a taba yi min irinsa ba?'
Bakinsa yana rawa yace
'Wallahi ban taba maganarki da ita ba Prof, wallahi babu abinda na gaya mata. Don Allah kiyi hakuri bari na zo yanzu, wallahi bani na...'
'Kada ka zo inda nake, bana son ganinka.'
Ta tsinke kiran ta barshi yana ta faman hada gumi duk da AC din da take kunne a dakin.
'Innaa lillahi wa inna ilaihi rajiun!'
Ya dubi Suraj wanda yake kallonsa kawai yace
'Suraj yarinyar nana zata kashe ni, zata sa a daureni a garin nan. Tunda na aureta ban huta ba, fitna daga ta gama wannan ana murna tayi hankali sai kuma ta sake wadda ta fi ta da. Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Yanzu ya zanyi da Prof, ni na yafe kwangilar ma amma don Allah tayi hakuri.'
Suraj ya jijjiga kai yace
'Allah ya sauwake, ina ga bari naje na sameta duk da ni din ma a kunyace zan je tunda ni na hadata da kai kuyi business.'
Ya mike ya kama hannun Suraj wanda
08, January 2025
Nafisa
I cant download the book