Showing 84001 words to 87000 words out of 92582 words
da taketa rikewa suka kwace.
Tana son yaranta kuma zata so ace tana tare dasu, amma ya zata yi? Tana son A A so ba kadan ba sai dai kuma a halin yanzu duk duniya wanda take so bayan Nurain da Nana ne. Anya kuwa zata iya daurewa wannan damar ta wuceta? Anya kuwa ta yiwa Nana da Nurain adalci idan ta auri wani taje can ta haifi wasu yaran? Anya kuwa zata iya yafewa kanta idan tarbiyyar su Nana ta shiga wani hali saboda rashinta?
Cikin kuka ta bude baki tace
'Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun!'
Ta saka tafukan hannunta ta rufe fuskarta, ta dauki lokaci a haka tana zubar da hawaye. Ta cire hannuwanta ta daga su sama tana addu'a
'Allah kaine Allah, Allah ka zaba mana abinda ya fi alkhairi garemu dani da su baki daya.'
KARSHEN BABI NA TALATIN DA SHIDA
MATAR MUKHTAR
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
FIKRA WRITERS ASSOCIATION
BABI NA TALATIN DA BAKWAI
37
Tunda Mukhtar ya daukota daga gida suka dawo ta fara neman aiki, tunda an ce ta zauna tayi ta hakuri to ta yarda zata zauna amma dole ta nemi abun yi. Ta san Abbansu zai iya samo mata aiki amma a yanda yanzu aka kawo masa wadannan laifukan nata bata jin zai saurareta, don haka ta bi ta hannun kawarta wadda yayanrta commissioner ce.
Satinta uku da komawa gidan offer ta fito don haka ta tambayeshi zata je gidan kawartata.
Sai da daddare bayan ya gama cin abincin dare yana zaune a falo ta sameshi, bayan ta zauna ta mika masa takardar tana fadin
'Na sami aiki fa.'
Ya karba yana mamaki
'Aiki kuma, ai ban san kina neman aikin ba.'
'To gashi nan dai, kasan da yake minister for women affairs Yayar Nur ce ina kai mata takardu gashi har na samu.'
Da fara'arsa yace
'Ma sha Allah, Allah ya sa a fara a sa'a.'
Yaji dadi domin shi kansa yana ganin aikin zai sa ta rage saka masa ido, tunda dama shi bashi da ra'ayin hana matarsa aiki; su biyun duka su suka zabi kada suyi aiki.
Sati yana zagayowa ranar litinin ta fara zuwa aiki.
........
Duk wani shiri na bikin Fatima da Ahmad an gama. Ahmad da kansa ya dauki Ibrahim suka tafi Abuja don ya nuna masa gidan da za a kai Fatima. Gida ne mai daki uku, ya riga ya gyara master bedroom da kuma dakin Hafiz ya saka furniture da komai, saura dakin Fatiman kawai. Falo kuma ya gyara dining area ga kayan kallo sababbi duk a kwalinsu da za a saka ga carpets, a kichin kuma akwai sabbin cooker da fridge masu kyau. Ya gaya wa Ibrahim duk abinda ya siya ba sai an kuma saya ba domin wannan din ma ita ya siyowa.
Duk wani gyara da Fatima take bukata tayi shi, domin ita kanta ta ji sauyi a jikinta gaba daya. Bata da kawaye don haka ta yanke ba zatayi wani event ba bayan kamu wanda za ayi a gidansu da daurin aure. Janan ce kawai kawarta ta amana sai dai bazata sami zuwa bikin ba saboda ta kusa haihuwa, kuma so takeyi ta ja baya da Janan saboda yanda ita Janan duk wata matsala sai tace a tafi wajen malami.
Nan da nan aka shiga hidimar biki. Naira dubu dari Ahmad ya bayar a matsayin sadakin Fatima, bayan an gama daurin aure aka dauki amarya aka wuce auyo yayinda mutum uku suka wuce Abuja don su karasa kafi su gyara gidan amarya.
Can ma a Auyo biki aka yi sosai, saida suka kwana biyu sannan suka wuce Kano tare da 'yan rakiyar amarya suka hau jirgi sai Abuja. Kwana daya 'yan rakiyar amarya suka yi a gidan suka kama hanya. Mutanen Auyo sune na karshen tafiya sai kanwar mahaifin Fatima wadda itama a Kano take. Tare da Fatiman suka tafi ya kaisu airport don tafiya Kano, inda daga nan mutanen Auyo zasu hau mota su karasa Auyo.
Tun da sukayi sallama da kanwar mahaifinta a airport Fatima take matse kwalla, tun Ahmad yana mata dariya har ya fara lallashi saboda kukan ya fara yawa. Haka suka dawo gida daga shi sai ita, da zarar ta kalleshi sai ta kara fashewa da kuka. Abinda takewa kuka daban yayinda shi kuma yake tunanin irin kukan nan ne na amare; tana ta addu'a Allah ya sa kada ta kunyata Mommy.
Haka ya dinga lallabata yana lallashinta har dare yayi.
Saboda tsabar tsoro Fatima har rawa jikinta yakeyi kamar mai zazzabi, a hankali ya lallabata suka kwanta. Duk yanda ta kai ga so ta ki sallama masa kasawa tayi, haka ta hakura ta bada kai bori ya hau.
...
A hankali yake busa mata iska a kunnenta, ta bude idonta a hankali ta dan noke wuya. Yayi dariya sannan ya sumbaci gefen wuyanta, ya sa hannu ya juyo da ita ta kwanta a rigingine ta yanda fuskarsa take kallon tata fuskar ba tare da zuba mata nauyinsa ba.
Suna hada ido tayi kasa da idonta a kunyace, yayi dariya yace
'Sarkin tsoro tashi gari ya waye.'
Tayi murmushi ta rufe fuskar da tafukan hannunta, ya sa hannu ya dauke hannuwan nata yana fadin
'Cire hannun zakiyi naga idon matsoraciya.'
Ta zumburo baki tana kokarin hadiye dariyar da ta taso mata tare da rufe idonta.
Haka suka wuni ranar yana mata dariya, suka bude sabon babi na soyayya domin bata taba sanin Ahmad ya iya soyayya ba sai yanzu.
Kuma ko ba a gaya mata ba ta san Allah ya amsa rokonta, don haka ta godewa Allah da bata gayawa Ahmad rayuwarta ta baya ba.
____
Tun bayan da tayi blocking din Mukhtar a waya bata kara ji daga gareshi ba, sai dai kawai tana cikin damuwa. Ta kasa cire yaran daga zuciyarta, musamman Nana.
Yaya Hajiyayye ce ta kawo musu ziyara yau, ita kadai ce ta zo domin yara suna islamiyya. Suna zaune da ita Umma da Safiyyan a falo , lissafi sukeyi saboda Baban Hotoro ya ce suyi lissafin kudin kayan daki shi da 'yanuwansu zasu bayar don a sayawa Safiyyan. Bayan sun gama lissafi duka Yaya Hajiyayye ta rubuta ta ninke ta saka a jaka ta cewa Umma
'Ina fita daga nan zan je na kaiwa Baban Hotoro, idan na bawa Yaya Habibu ba zai kai ba cewa zai yi su barshi. Kuma haka sukeyi, shi yasa ma Baban yace a kawo tunda ma ko nawa suka bayar karba za ayi.'
Jimawa kadan ta dubi Safiyyan sannan ta dubi Umman tace
'Umma ita wannan menene yake damunta naga duk tayi zuru-zuru sai kace auren fari.'
Safiyyan tayi dariya, Umma tace
'To wallahi kin ganta dai, nayi tambayar duniya tace babu komai. Sai kace mai gudawa sai karewa takeyi kullum.'
Safiyyan tace
'Umma wallahi babu fa wata matsala, kawai dai yanayi ne.'
'Uhm, ma ji idan tayi wari.'
Umma ta fada tare da mikewa ta barsu a falon. Hajiyayye ta dawo kusa da Safiyyan tace
'Idan wani abun ne ai gara ki fada don Allah,ba sai an je an kuma auren da na sani ba.'
'Wallahi Ya Hajiyayye babu komai.'
'Ai shikenan.'
Sukayi shiru na dan lokaci, jim kadan Safiyyan tace
'Ya Hajiyayye yanzu kuma sai na je nayi aure na haifi wasu yaran na manta da su Nurain?'
Hajiyayye tayi murmushi tace
'Yauwa, ni dama na san da akwai abinda kika saka a ranki kike wannan ramar kamar kudin guziri.'
Ta sunkuyar da kanta ta fara nadamar gaya mata abinda yake damunta. Yaya Hajiyayyen ta cigaba
'Babu inda uwa ta taba mantawa da yaranta duk duniya, kuma ba za a fara a kanki ba; ke mace ko dan shege ta haifa yana ranta balle ke da kika haifi yaranki cikin amincin Allah. Amma ai ba ke kika zabi hakan ba, haka ubansu ya zaba tunda shi ke rike da aure. Kuma tsari ne na ubangiji. Za kiyi aure ki haihu amma su Nana suna nan tare dake , ko bai kawo miki su ba za a daukosu a kawo miki su kuma addu'arki tana tare da su. Bana son ki sawa kanki wannan damuwar don ba zaki koma gidan Mukhtar ba don naji Sabir yace ya fara zuwa nemanki. Kuma dai kin san me Baban Hotoro yace ko? Muddin yana numfashi A.A ne mijinki. Ki kwantar da hankalinki kamar yanda shi ma ya sakeki ya kwantar da hankali har ya sami natsuwar auren wata. Don Allah ki natsu kafin sati biyar din nan kin ji?'
Ta dago ta kalleta tace
'In Sha Allahu Yaya.'
'Yauwa. Ke ba matar Mukhtar bace kuma kin fi karfin zama matar Mukhtar in Sha Allahu.'
Haka Yaya Hajiyayye ta dauki lokaci tana nuna mata ta cire damuwa daga rantata dan mayar da jikinta kafin bikin ya karaso.
Daga baya tayi musu sallama ta tafi.
.......
Maganganun Yaya Hajiyayye sun samar mata da nutsuwa don haka gadan-gadan ta shiga gyaran jikinta. Maganin sanyi ta fara neman bayan ta gama kuma ta shiga aikin gyara. Cikin sati biyu ta kara kyau ta murje duk da har yanzu da 'yar ramar.
Saura sati uku biki A.A ya zo da kanshi ya dauki Yaya Habibu wanda sun riga sun zama kamar abokai ya kaishi don ya gano gidan da za a saka Safiyya. Flat ne guda biyu a cikin gidan sai dai flat din barrister ya fi girma, na Safiyya shine a karshen gidan kuma daki uku ne da falo. Kusan duka dakunan ya zuba furniture sababbi don wasu ma ba'a bude ba.
Yacewa Habibu ya duba abinda babu kawai shi za a kawo.
Bayan Yaya Habibu ya tafi Kuma da kansa ya dauki hotunan gidan da kayan ya turawa Safiyyan. Don haka kudin da su Baban Hotoro suka hada mata na kayan daki Yaya Habibu ya karbi account number dinta ya tura mata yace idan ta tare ta ja jari.
Zuwa yanzu abu daya ne yake bata tsoro, yanda zata zauna da barrister. A iya labaran da ta samu mace ce mai ilimi kuma ga gayu don wasu ma suna makin abinda AA zai yi da wata mace bayan Barrister. Don haka Safiyya ta zage ta gyara jikinta, ta yi order din hadaddun turarukan wuta da Humra special order a wajen Xee Yaxeed me turaren wuta (08123164559) sannan Kuma tayi order kayan kamshin girki na Jolly Flavors daga wajen Innar su Amal; domin kamar yanda ta fada ba za a fita ilimin boko ba kuma a fita kula da miji da kuma kamshi mai dadi ba.
Sunyi maganar aiki da shi yace ta cigaba da aikinta direba zai dinga kawota, amma idan an kwana biyu zai tafi da ita Abuja sai ya samo mata wani aikin a can ko kuma ta bude saloon tunda ya ga tana son harkar gyaran gashi.
.......
Yau saura sati uku a daura auren Safiyya da A A. Ko daya Barrister bata bashi matsala ba, ta dai gaya masa bata son ya dinga yi mata maganar matarsa kuma idan ta tare ita ba ruwanta da wata amarya. Ya yarda da hakan duk da bai ji dadi ba don shi zai so yaga iyalansa ko ba sa shiri to kada su zama ba ruwan kowa da kowa.
Haka ya hakura ya kyaleta tunda dai bata bashi wata babbar matsala ba.
Ita kuwa a nata bangaren gani takeyi Safiyyan ba 'yar kowa bace kuma ba wani ilimi ne da ita ba don haka ba zata bata lokaci ta a kanta ba, ta san dai bata isa ta kwace mata miji ba tunda yana sonta itama tana sonsa. A tunaninta Safiyya bata ma kai ayi kishi da ita ba, shi kanshi auren nasu ma gaba daya gani takeyi ba zai yi wani tasiri ba.
------
Ajjiye wayarta kenan ta gama booking din lalle wanda za ayi mata ranar kamu; domin A.A yace mata 'yan uwanshi suna yin kamu don haka za su suyi mata kamu kamar na budurwa. Kafin ta tashi daga wajen ta jiyo hayaniyar Nurain da Nana a tsakar gida, tana jinsu suka gaida Umma sannan suka kwaso da gudu. A tare suka fada jikinta har sai da suka kwantar da ita a kan gadon da take zaune.
Ta daga su ta tashi tana dariya, ta lakacewa Nurain hanci tana fadin
'Kai har yanzu baka girma ba ko? Kun hadu da kanwarka kuna nema ku kadani.'
Suka sa dariya.
Bayan sun gaisa Nana ta gaya mata sakon su Hajiya da suka ce a gaisheta Nurain yace
'Mama jibi Saturday za ayi speech and prize giving day a makarantarmu, don Allah Mama ki zo. Kin san me? An yi musabaka na zo na biyu, nazo 1st position a class kuma nine best student in Maths. Duk ranar za ayi ta kirana ana bani gift kawai, don Allah Mama ki zo har party zamuyi ni da friends dina in an gama kuma ma..'
Safiyya ta katseshi tana murmushi
'Ka dinga jan numfashi idan kana zance mana Nurain.'
Ya rufe ido ya ja numfashi sannan ya bude idon yace
'To Mama na ja numfashi. Zaki zo?'
'Zanzo Nurain, ai na ji dadi sosai ka burgeni. Zanzo na ga gift dinka kuma nayiwa Anti da Ustaz godiya da suka iya koya maka karatu.'
'Yauwa Mama, za muyi selfie ma da wayarki.'
Tayi dariya ta juya wajen Nana wadda ta sha kunu
'Nanata ke kuma me za a baki?'
Ta kara zumburo baki sannan ta bada amsa
'Mama 5th fa na zo amma Uncle bai ce za a bani komai ba kamar wata dakikiya, na iya karatu, na iya hadda kuma har handwriting ma na iya da drawing amma ni ba za a bani komai ba wai.'
Ta rungumota tana murmushi
'Kai-kai-kai! Gaskiya Uncle bai san kokarinki ba, amma zanzo in bashi labari. Kuma ni da kaina zanzo miki da gift wanda ya fi na kowa kyau.'
Nan da nan ta fara dariya, shi kuma Nurain ya sa rigima shima dole sai Mama ta bashi wani gift din. Sai da suka gama musu da rigimarsu sannan Nurain ya rufe baki yace.
'Au Mama Baba Saifu ne ya kawo mu kuma yace kada mu dade yana waje.'
Nan ta tashi ta saka su a gaba ta fito dasu, suka gaisa da Saifullahi sannan ta saka su a mota. Sai da suka rufe kofar motar Nurain ya leko yace
'Mama kada fa ki manta, jibi ne karfe goma na safe kuma ku taho da kowa Hajiya, Baba Sabir, Anti Hamee harda Anti Hajiyayye ma da kowa na gidanta.'
Tayi dariya tace
'Inaga ma dai Nurain duka mutan garin zan gayyato muzo.'
Sukayi mata sallama suka wuce suna dariya.
Gari na wayewa ta shirya ta tafi Sahad stores dake kan titin Zoo road domin ta cika alkawarin da ta yiwa Nana. Tana cikin zagayawa wajen kayan wasa A. A ya kirawota, bayan sun gaisa yace
'Kina ina ne naji hayaniya, na zata an yi sallama da islamiyya.'
Tayi dariya
'An yi sallama da islamiyya ranka ya dade , na dan zo shopping ne.'
Nan ta bashi labarin alkawarin da tayiwa yara, don haka sukayi sallama ya barta ta cigaba da sayayyarta.
.......
Karfe bakwai da rabi kira ya shigo wayarta lokacin tana kwance a gefen gado tana ta dube-dube a wayarta. Tana kalla taga Hajiya tayi murmushi don ta san Nurain ne tana dagawa kuwa taji muryarsa. Ko gaisheta bai yi ba yace
'Mama yau ne fa, ai baki manta ba ko?'
Tayi dariya
'Ban manta ba sarkin zumudi.'
'Mama menene zumudi?'
'Idan na zo zan gaya maka kaji, ka bani Hajiya na gaisheta.'
'Ta shiga wanka ai.'
Nan sukayi sallama tana yi masa dariya.
Karfe goma da rabi suka kama hanya ita da Sabir.
Inda yaran suka zauna da ban da inda iyayen yaran suke, don haka cikin yara ta hango Nurain din yana ta faman daga mata hannu yana dariya. Itama ta daga masa hannu.
Tun kafin ta karasa wajen zaman iyayen yara ya hangota, ta kara kyau sai wani sheki take tana walwala. Wajen zaman mata daban da na maza don haka ya taso daga inda yake zaune ya nufo su.
Tun daga nesa yake ta faman yi mata murmushi don haka itama ta mayar masa da murmushin, yayinda shi kuma Sabir ya kara tsuke fuska yace
'Don Allah Yaya Safiyya ki hada bakinki, sai ki dinga wani yagewa mutumin nan baki anyhow.'
Ta sa kafa ta taka masa yatsa, ya dan ja baya. Tayi masa dariya tace
'Uban 'yayanka ne dai ko kana so ko baka so.'
Ya karaso ya mikawa Sabir hannu suka gaisa, yayinda Sabir din yayi sauri ya bar wajen ya wuce wajen zaman maza ya zauna yana hangosu.
Suka jero suna karasowa wajen. Bayan sun gaisa tayi masa murnar samun nasarar Nurain, bayan ya amsa yace
'Sai a nan zan iya ganinki Safiyya, wato yanzu ni kike gudu ko?'
Da mamaki ta kalleshi tace
'Ka je gidan Umma bana nan ne?'
'Ni na isa nazo bayan kin ki ki bude layika in nemi izinin zuwan. Ina wayarki?'
'Tana wajen Sabir.'
Yayi yake kawai domin da so yayi ya karbi wayar ya cire lambarsa daga blocking din da ta yi masa.
Suka karaso wajen zaman iyayen, ta karasa wajen mata ta zauna yayinda ya koma inda ya taso ya zauna bayan da ya sanar da ita idan an tashi yana son ganinta.
Malamai daban daban suka gabatar da bayanai bayan nan kuma yara suka fara rawa abun sha'awa ana ta kallo ana tafi.
Kamar da gefen ido ta hango A A yana shigowa filin makarantar, ta juyo ta kalli wajen sosai tabbas AA ne da wasu ledoji guda biyu a hannunsa masu kyau. Yana ta dube-dube kamar yana neman wani, ta san babu yaransa a makarantar don haka ta sa rai ita yake nema. Ta mike tsaye domin taje taji me yazo yi domin a jiya da sukayi waya ce mata yayi yana Abuja.
Tana mikewa Mukhtar ya mike don ya zata wani abu take nema. Daga tsakiyar mata ta tashi ba tare da kalli
08, January 2025
Nafisa
I cant download the book