Showing 45001 words to 48000 words out of 92582 words

Chapter 16 - MATAR MUKHTAR COMPLT

SAKINA   

16 Aug 2024

7147

unguwace kamar kowacce, ga mutane nan da kwalliyar sallarsu ana ta harka. Sai da suka shige soro daya sannan suka isa tsakar gidan, wasu mata su biyu wadanda da alama sune matan gidan suka yi musu iso. Daga gani ma sun san Janan; daya cikin matan ta shigar dasu wani daki wanda kofarsa take daf da bakin kofar shiga tsakar gidan. Kana shiga zaka ga kamar falon ba a cikin wannan gidan yake ba saboda yanda aka kawata shi da kujerun masu kyau ga carpet, ga tv plasma fankokin guda biyu dake saman falon sunata gudu suna karawa kamshin freshener din da yake tashi a falon sanyi.

Kan kafet suka zauna Janan ta janyo filo daga cikin filallukan dake watse a tsakar falon ta tokare hannunta, matar da ta shigo da su ta karasa ta bude firjin dake falon ta dauko ruwan roba kanan guda biyu ta dora a kan farantin da yake kan firjin sannan ta dauki lemon five alive da kuma kofunan tangaran guda biyu duka daga cikin firjin ta hada ta kawo musu. Bayan ta ajiye a gaban su ta zauna suka gaisa cikin girmamawa sannan tace

'Bari a turo muku Mallam din.'

Ta fice ta kofar da suka shigo. Fatima ta dubi Janan tace

'Allah dai yasa ya fito da wuri.'

'Kada ki damu bashi da wasa, yanzu zaki ganshi kuma kin san tun jiya na sanar da shi zuwanmu.'

Sukayi shiru Fatima tana ta karewa falon kallo, ta dubi Janan tace

'Kalli falon kamar ba a gidan ba, tsakar gidan kaca-kaca amma falon fes kanshinsa ma da ban.'

'Kin san Malam dai ba boka bane, ilimi ne kawai Allah ya bashi yake bada taimako.'

Ta jijjiga kai kafin tace wani abu ya turo wata kofa da take cikin falon ya shigo da sallama. Bayan sun amsa sallamarsa ya karasa ya zauna a kan kujera mai zaman mutum uku sannan ya fara gaisawa da su. Suna gaisawa Fatima tana kare masa kallo tana mamaki; dan tsurut da shi kuma ba wani babba ba, sai wani cika yake yana faman kawar da kai tare da zare ido. Ta dubi Janan wadda gaba daya ta nutsu kamar tana gaban sarki. Yayi gyaran murya yana duban Janan yace

'Itace kika yi min bayaninta?'

Cikin girmamawa Janan tace

'Eh itace Mallam.'

Ya mayar da dubansa zuwa kan Fatima yana fadin

'To babu laifi, yanzu za a gama aikinki babu bata lokaci. Za a saka miki ruhinsa a kwalba ko kuma a zobe; idan aka saka miki a kwalba zaki sami waje mai duhu inda ba fuskar gabas ba ki boye kwalbar, matukar baki budeta ba to duk abinda kika fada sai ya aikata; amma fa da kwalba ta fashe aiki ya baci. Idan kuma a zobe aka saka miki to zaki saka zoben a hannunki na hagu ba zaki cire shi ba sai idan da lalura kuma idan kin cire to akwai jaka da zamu baki sai ki mayar ciki amma kada ki bari ya dade ba a hannunki ba. Idan kika rabu da zoben aiki ya baci. Wanne za ayi miki?'

Ta kalli Janan suka hada ido, kafin Janan din tace wani abu Fatima ta dubi Malam tace

'Zoben dai Malam.'

Yayai gyaran murya yace

'An gama, tun jiya da ita Janan ta yi min waya aka fara aikinki don haka nan da minti talatin za a gama sai bayani kuma.'

Ya zaro wata takarda da biro a aljihun gaban rigarsa ya mika mata yace

'Rubuta min sunanshi a nan da sunan mahaifiyarsa da na mahaifinsa.'

Ta karbi takardar ta rubuta sunansa da na mahaifinsa sai kuma ta kasa tuno sunan mahaifiyarsa, sai a hankali kuma sai ta tuna ai yace Nana sunan Hajiya ne da ita kuma sunan Nana Khadija; nan da nan ta rubuta ta mika masa. Ya karba ya tashi ya koma ta kofar da ya shigo. Yana shiga Fatima ta dubi Jana tace

'Kawata anya kuwa?'

Ta dafa ta tana murmushi

'Kada fa ki damu wallahi aikin sa kamar yankan wuka, don ma ana bikin sallah ne da wallahi wataran da kyar ake ganinsa bakiga yanda matan manya ke masa zarya ba. Ko nima idan na kasa gane kan Adnan nan nake kawoshi nan da nan zakiga mutum yayi biyayya; zaki sha mamakin aikin Malam.'

Sai da yayi kusan minti talatin sannan ya fito daga dakin dauke da wani bakin faranti da zobe a ai. Yana zama ya mikawa Fatima farantin yace

'Dauki ki saka a yatsan tsakiyar dake hannun hagunki.'

Ta dauki zoben ta saka kamar yanda yace, tabi yatsan da kallo. Zobe ne kamar na azurfa da wani jan dutse mai kyalli a tsakiyarsa, yayi matukar kama da normal zobe, sai dai kawai yafi zoben azurfa girma. Gyaran muryan Malam yasa ta dago daga duban zoben, yace

'Matukar kina tare da wannan zoben sai yadda kikayi da rayuwar Mukhtar dan Abdullahi da Hadiza, ko ita Hadizan ba zata iya sakashi ya saba umarninki ba.'

Ta jijjiga kai tana mamakin aikin na Malam, cikin murya kasa-kasa tace

'To yanzu idan na je gida sai na kirawo shi kenan Malam?'

Ya kyalkyale da dariya har ya so ya bata tsoro saboda sai ta ji dariyar kamar ta fi Malam girma, kamar ba shi yayi dariyar ba. Ta zare ido tana kallonsa, yace

'Wane Mutum! Babu ruwanki da shi, ki bashi awa ashirin da hudu da kansa zai kawo miki kansa, daga nan kuma sai yanda kika yi da shi. Kada ki kuskura ki neme shi zai zo har inda kike.'

Jijjiga kai kawai takeyi.
Janan tayi gyaran murya tace

'Mungode Malam, mungode. Allah ya kara daukaka. Yanzu nawa ne kudin aikin?'

'Naira dubu dari biyu.'

Ya fada tare da tura mata farantin da ta dauki zoben a kai don ta dora kudin.

Fatima da Janan suka kalli juna domin tun suna gidan Janan Fatima ta gaya mata dubu dari ne da ita; shima saida ta hada da kudin da Yaya Ibrahim ya bata don ta sayi kayan sallah dubu talatin da kuma tarin alawee dinta da takeyi. Janan tayi mata alama don haka ta zaro dubu darin dake jakarta ta dora masa a kan farantin, Janan ta tura masa farantin tace

'Malam ayi mana afuwa da wannan muka zo amma zuwa karshen satin nan zan turo sauran ta account din da ka bani.'

Yayi murmushinsa mai kama da yake

'Babu laifi Hajiya Janan kina cika alkawari don haka kuje sai na ji ku.'

Sukayi sallama suka fito suka bar Malam a falon, suna fitowa tsakar gidan Janan ta zaro bandir din naira hamsin ta mikawa yaran dake wasa a tsakar gidan wadanda ga dukkan alamun 'yayan malamin ne

'Ga barka da sallah ko, a siya alawa.'

Suka karba suna ta murna, suka yiwa iyayensu sallama suka wuce.

Suna zama a mota Fatima ta dubi Janan tace

'Haba kawata, madadin kice yayi ragi. Yanzu ina zan ga naira dubu dari na biya shi, kin san fa aikin da nakeyi voluntary ne babu abinda suke biya kuma wallahi bani da me bani dubu dari a halin yanzu.'

Ta dafa cinyarta tana murmushi

'Haba mana Fati, ai shi zaizo ya baki dan rainin hankali.'

Ta zaro ido tana dubanta

'idan fa bai zo ba.'

Tayi dariya ta tada mota tana fadin

'Shi din banza, ni na baki garanti yanda Malam ya fada in the next 24hours ko wacece ta haifi Mukhtar sai ya kawo miki kansa. Amma kada ki damu idan bai zo ba ni zan biya Malam.'

Ta ja mota yayinda Fatima ta mayar da idonta gaba tana duban hanya tana tunani kala kala, a yanzu dai tafi so suyi sauri su koma kafin su Faisal su dawo.

Ai kuwa basu dade da shiga gidan Janan ba su Faisal din suka dawo, ba tare da bata lokaci ba suka kama hanyar Abuja. Har suka iso Abuja Fatima tana faman kallon zoben nan tana mamakin yanda za ayi yayi aiki; amma dai zata jira zuwa gobe taga ta yanda Mukhtar din zai nemeta.

KARSHEN BABI NA ASHIRIN
MATAR MUKHTAR

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA ASHIRIN DA DAYA

21
Tunda aka kawo su Nurain bata zauna a gida ba saboda yawon sallah, sai yau. Ta gaji sosai don haka ta kwanta bacci suma su Nana da Nurain ta zare musu ido suka kwanta suna baccin dole. Don haka ko da ya shigo gidan ya leka dakin ya gansu sai kawai ya dawo falon kasa ya zauna a doguwar kujera. Bai jima da kwanciya ba wayarsa ta dauki waka, ya riga ya saita wayarsa bata kara sosai don haka in tana ringing shi kadai yake ji. Ya kalli wayar yayi murmushi saboda jin dadi

'M. H.'

Shine sunan da ya fito a kan wayar, wato Meena Habu. Haka ta gaya masa sunanta lokacin da suka hadu washegarin sallah don haka yasa M. H. saboda ya badda kama. Yanayinta ya tabbatar masa da cewa ita din a barikinta take amma dai basu taba mu'amala ba, yaune tace masa zasu fita don haka dama kiranta yake jira.

Ta riga ta sanar da shi ba sai ya je daukanta ba ya bata adress zata sameshi, ya san kuma abinda ta kirawo taji kenan. Ya kara wayar a kunnensa yana fadin

'Hello, 'yan mata.'

Da murmushi ta amsa har sai da ya jiyo sautin murmushin

'Uhm, to a ina za mu hadu.'

'Bristol hotel, ai kin san wajen ko?'

'Eh.'

'Room No. 36, sai mun hadu.'

'Kada fa ka barni in jira please.'

'Kada ki damu, sai na rigaki zuwa ma don yanzu zan fito kin s......'

Ya karasa a sanyaye sakamakon ji da yayi a jikinsa kamar mutum yana kallonsa.

'Babu damuwa, thank you.'

Ya fada tare da ajiye wayar ba don ya gama maganar ba. A hankali ya juya ya dubi kofar da ta fito daga corridor; wanda ta nan ake saukowa daga dakin da ya barsu suna bacci; wadda ya bawa baya, tana tsaye a jingine tana kallonsa da alamar tambaya. Yayi sauri ya yake baki

'Ah kun tashi ne?'

Ta karaso tana goge fuska, ta zauna a kusa da shi

'Sannu da zuwa.'

'Yauwa, ke da 'yayan naki sai bacci kuke ba kwa jin motsi.'

Da kyar ta bude bakinta wanda ya cika da yawu; tara yawun da ya zamar mata jiki tunda ta sami ciki. Wata biyu da cikin amma bata da aiki sai bacci da tofar da yawu, ga baccin nauyi yake shi yasa ma bata jin motsi idan tana yi. Tayi yake tare da mikewa tsaye don taje ta zubar da yawun dake bakinta, tana shigewa bandaki shi kuma ya mike ya shige daki. Ta kuskuro bakinta ta fito daga bandakin ta tarar babu kowa, ta harari wajen da ya zauna sannan ta karasa ta zauna a inda ta tashi.

Tun bata fi sati daya a gidan ba take zarginsa da neman mata, tayi shiru ne saboda bata da hujja; amma sosai take zarginsa. Bata fahimci wani abu ba daga maganar da ta ji yana yi amma dai ta fahimci appointment ya hada kuma da mace, kawai dai zata yi shiru ne don bata da hujja amma dole ta bincika. Ta saka masa ido sosai tana so ta gane pattern din bude wayarsa. Tabbas idan ta kamashi da neman mata za ayi rigima don bazata dau wulakanci ba.

Motsin fitowarsa ne ya katse mata tunani don haka ta dago ta dubeshi, a shirye yake tsaf ya canza kaya kamar mai shirin zuwa zance. Ta tashi ta wuceshi ta zubar da yawun bakinta a bandaki tana fitowa tace

'Fita kuma zakayi?'

Ya washe baki kamar wani mara gaskiya yana shafa gemu ya bata amsa

'Eh zamu wajen wani Alhaji ne da Suraj wanda muke so ya bamu wani aiki, dama shi nake jira ya kirani shi yasa na kwanta a nan.'

Da dabara ta bude bakinta da ya riga ya fara cika da yawu tace

'Uhm, a dawo lafiya.'

'Allah ya sa.'

Har ya kusa fita ya juya ya dubeta tana zaune a kan kujera yace

'Kada kiyi abincin dare da ni don zamu zauna gidan Suraj din mu duba wasu takardu idan mun dawo, na san cewa zai yi sai mun ci abinci.'

'Ok, sai kun dawo.'

Ya fice ya turo mata kofar. Ta yi 'kwafa tana harara kofar da ya fice saboda takaici. Bai jima da fita ba yara suka tashi daga bacci don haka ta cigaba da hidimarta da su tana tunanin hanyar da zata bullowa Mukhtar.
Sai bayan sallar Magriba sannan dabar ta fado mata, don haka ta dauki wayarta ta shiga daki ta turo kofa. Hajara ta kirawo; matar Suraj. Duk da ba wani shiri sukeyi sosai ba amma dai suna gaisawa, ita Jamilan ce ta kasa sakin jiki da matan abokansa saboda a tunaninta duk kawayen Safiyya ne don haka ma bata shiga cikinsu. Cikin mutunci suka gaisa sannan Jamilan tace

'Uhm, don Allah maman Anwar Baban Anwar yana kusa.'

'A'a wallahi, bai dawo ba tunda ya fita wajen karfe biyu na rana. Ina jin dai yana gidan yayansa.'

'Allah sarki. Don Allah kiyi min wata alfarma mana.'

Da mamaki tace

'Allah ya bani iko.'

'Mukhtar ne dama yace min tare zasu fita da Baban Anwar shine nake so na san ko haka ne, ya ma ce min a nan zasuyi dinner . Don Allah idan sun shigo ki sanar da ni ko ta Whatsapp ne.'

Ta riga ta san halin Mukhtar don shi yasa itama take kokarin ta raba shi da Suraj din, don haka tayi murmushi tace

'Kai gaskiya dai ba a nan zai yi dinner ba don idan zai kawo wani su ci abinci yana sanar dani, amma in sha Allah da sun shigo tare zan gaya miki.'

Sukayi sallama suka ajiye waya.

Ta jefa wayarta kan gado ta ja tsaki, dama ta san karya Mukhtar ya shirya mata amma bari ta Jira kiran Maman Anwar.

Basu fi minti talatin da ajiye waya ba Maman Anwar ta kirawota, bayan ta dauka tace

'Jamila Baban Anwar din ya dawo yanzu, sai dai bana jin ma sun fita da Mukhtar din don daga gidansu yake.'

'Ok, babu damuwa nagode sosai Maman Anwar, don Allah kada ki bari su san munyi wannan wayar.'

'Kada ki damu, in sha Allah babu wanda zai ji.'

Sukayi sallama suka ajiye waya.

Jamila ta jefa tata wayar a kan gado ta ja tsaki

'Wallahi zaka dawo ka sameni, dan rainin hankali kawai!'

Ta karasa ta zauna jabar a gefen gadon ta zuba fuskarta a tafukan hannunta kawai sai jin danshi tayi. Ta daga ta dubi hawaye da yake kan hannunta tayi kwafa, ta bude bakinta wanda yake cike da yawu tace

'Ko shekara ba'ayi da auren ba amma zan fara karbar takaicin ka Mukhtar, duk wannan kyan nawa da kake gani har ya zama muni ka koma bariki. Lallai za ayi rigima don wa.....'

'Mommy na gama.'

Muryar Nana ta katse mata tunanin, kashi ta gama take kira azo ayi mata tsarki. Ta ja tsaki sannan ta mike ta nufi bandakin da yake a falon da ta barsu.

Yanzu haka ma wannan yawon da yake shi ya fitar da uwarasu, ya zo ya hada mata yara ga wani a cikinta shi kuma ya tafi yawo. Kenan yanzu ita ta zama Nanny, aikinta raino kawai, shi kima yayi ta yawo yana fafe matan mutane. Ta sake yin kwafa dai-dai lokacin da ta karasa bandakin.

Sai wajen sha daya da rabi na dare sannan ya dawo gidan, a hankali ya shiga da sanda saboda yana tunanin sunyi bacci ita da yaran, ga mamakinsa tana zaune a falon a kan kujera da take kallon kofar. Da murmushi ya karasa ciki yana sallama, ta riga ta shirya don haka bakinta babu yawo saboda ta saka cingam a bakinta wanda take taunawa.

Bayan ta amsa sallamarsa ya karasa ya zauna a kusa da ita yana kokarin duban fuskarta yana fadin

'Ah, bakiyi bacci ba har yanzu?'

Murmushin yake tayi ta ce

'Baka son ganina ido biyu kenan, shi yasa ka jira sai nayi bacci zaka dawo ko?'

'A'ah, kin ma fi kyan gani idan kina ido biyun ai.'

Ta kawar da kai ba tare da ta ce komai ba, suka yi shiru na dan lokaci. Ya mike ya kulle gidan ya kama hannunta ta tashi tsaye suka shige daki yana fadin

'Na gaji sosai, bacci nake ji mu je mu kwanta.'

Sai da ya gama shirinsa tsaf zai kwanta yana zaune a gefen gadon tayi gyaran murya tace

'Wai don Allah yau ina kaje ne?'

Da mamaki ya kalleta

'Ah, ce miki fa nayi fita zamuyi tare da Suraj kuma gidansa za mu ci abinci.'

Ta tsattsareshi da ido sannan tace

'To ai ba kwa tare don maman Anwar ta ce min shi kadai ya koma gida tun magriba kuma bai sake fita ba.'

Maganar tata tayi masa ba-zata don bai yi zaton zata bibiye shi ba, da sauri ya kau da fuskarsa tare da shan kunu
'Oh, ai da yake mun gama da wuri sai na ajiye shi a gida na tsaya majalisa wajen su shamsu, nan muka ci abincin dare ma.'

Ko wanda bai san Mukhtar ba yaji wannan maganar ya san mai fadarta karya yakeyi, ta kawar da kanta sukayi shiru na dan lokaci. Jim kadan ta dubeshi a tsiwace tace

'Mukhtar.'

Ya juyo suka hada ido tanayi masa wani kallon raini tana tauna cingam din da yake bakinta tace

'Na san da mace kuka fita, Kai kadai ba tare da Suraj ba. Idan aure kake nema ka sanar dani tun wuri kafin nazo nayi abinda ni da kai za muyi nadama, kuma kayi shi cikin mutunci. Wallahi ba zan yarda da cin amanar aure ba, ina zaune a gidanka na tsare mutuncinka kai kuma kana yawon barbadar da nawa mutuncin. Wallahi sai na tayar muku da hankali da kai da duk yarinyar da kake nema na gaya maka.'

Kafin yace wani abu ta mike ta fice daga dakin ta mako masa kofa.
Nan ta barshi zaune yana mamaki; bai taba tunanin Jamila ta iya tsiwa haka ba ko

08, January 2025
Nafisa

I cant download the book

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login