Showing 24001 words to 27000 words out of 92582 words

Chapter 9 - MATAR MUKHTAR COMPLT

SAKINA   

16 Aug 2024

7142

fara al'ada do ta san shima lissafinsa al'adarta bata dawo ba.

Haka ta dinga dunkulewa a kan gadon nan saboda yanda ciwon mara yake karuwa, jimawa kadan taji ta jike don haka ta shiga bandaki ta wanke jikinta ta sami audugar da Hamida ta rage saura daya ta sa a jikinta. Ta fito daga bandaki tana tunanin inda zata sami kudin sayen pad, domin da ta tambayi Umma kudi a sayo mata Panadol sai da ta gwammace bata tambaya ba saboda yanda Umman ta dinga yi mata gori da tuna mata yanda tana fama da marayun kannenta ta kaso aurenta zata kara mata nauyi madadin ta tambayi mijinta. Ta zauna a gefen gado ta dafe mararta, a hankali kuma ta dunkule ta kwanta tana fitar da hawayen da ta kasa tantance na menene; ciwon mara ko kuwa tunanin inda zata sami kudin pad ko kuma dai bakin cikin yanda Mukhtar yaki ya zo ya mayar da ita.

Karfe uku Sabir ya dawo daga makaranta, kana shigowa gate din gidan kafin ka shiga cikin gidan dakinsa yake. Sai da ya ajiye kayansa sannan ya shiga cikin gidan, ya sami Umma a falo. Bayan ta amsa sallamarsa yace

'Umma Yaya Safiyya tana daki.'

'Eh tana ciki'

Yana shiga dakin ya sa hannu a aljihu ya zaro gyadar da ya siyo mata; tunda ta dawo haka yakeyi in dai ya dawo daga makaranta sai ya kawo mata wani abu, gyada, kwakwa, cashew da sauransu.

Yanda ya hangota a tsakiyar gadon a dukule ya san ba lafiya ba. Da sauri ya karasa ya ajiye gyadar a gefen gadon

'Ya Safiyya baki da lafiya.'

Ta dago kanta ta dubeshi, goshinta ya jike da gumi ga hawaye a idanuwanta da sun riga sun yi jawur da kyar tace

'Cikina Sabir, ciwo.'

Ta koma ta dunkule tana numfashi da kyar. Cikin hanzari ya fito ya sami Umma a falo

'Umma Ya Safiyya bata fa da lafiya asibiti ya kamata a tafi.'

Harararsa Umma tayi tace

'To ubanta, ai ta sha magani kuma ba wani abu bane period pain ne.'
Ya jijjiga kai

'Ki zo dai ki gani Umma.'

Ta ja tsaki sannan ta mike ta bi bayansa, yanda taga Safiyyan itama ya dan razana ta. Ta karasa ta zauna ta dafa bayanta

'Safiyya wai dama haka al'adarki take miki ciwo da yawa.'

Tana cije baki tace

'Na manta Umma, ai tunda na haifi Nana banyi ba, wannan ne na farko.'

Da sauri Sabir ya fice daga dakin ya dawo falo ya dauki wayar Umma ya kirawo Yaya Habibu, ya dauka kafin su gaisa yace

'Sabir ne Yaya, gara kazo a kai Yaya Safiyya asibiti bata da lafiya sosai kada ta mutu.'

'Subhanallahi, ka ganni dama ina hanyar gidan yanzu zan karaso ka ce da Hajiyan su shirya.'

Kafin minti goma shabiyar Yaya Habibu ya karaso Umma ta kama Safiyya ta cewa Sabir ya zauna saboda Hamida zata dawo daga makaranta, suka wuce asibiti.

Asibitin Mallam Aminu Kano ya nufa wanda shine ya fi kusa da su, suna isa Yaya Habibu ya wuce da su emergency inda daga nan aka ce tunda matsalar mara ce su wuce bangaren mata.

Da kyar likitan ta samu ma'aikatan jinyar suka mikar masa da ita, ta daure ta amsa tambayoyinta bayan ya lallatse cikin. Take aka turasu scanning wanda a nan kusa dakin yake, suka gama Yaya Habibu ya biya suka karbo takardar suka kawowa likitan.

Likitan tana zaune a kujerarta yayinda Yaya Habibu yake zaune a gaban teburin inda Umma take tsaye a gefen Safiyya wadda take kwance a kan gadon tura mara lafiya da yake dakin likitan. Likitan ta dubi Yaya Habibu tace

'Yallabai dama an san tana da ciki ko?'

Ya juya ya kalli Umma, wadda tace

'Ban sani ba gaskiya.'

Ta mayar da dubanta kan Safiyyan ta dunkufa kusa da fuskarta tace

'Kin san kina da ciki ko Safiyya?'

Ta share gumin Dake fuskarta tace

'Ban sani ba wallahi, ai na gaya miki idan ina shayarwa bana al'ada kuma kin san idan na sami ciki bana laulayi sai dai kawai naga ciki yana girma. Gaskiya idan cikine sai dai ko kafin na yaye Nana na sameshi tunda kinga yanzu kusan wata uku ko biyu ne da yayeta ban yi al'ada ba don ko yanzun ma na zata al'adan zan yi.'

Wadannan bayanan duk a kunnen likitan don haka ta dubi Yaya Habibu tace

'To gaskiya ga scanning dinta ciki ne da ita sati goma sha hudu, ya riga ya lalace a ciki shine yasa marar take ciwo zubewa cikin zai yi. Don haka yanzu zamu yi mata allura sannan mu bata magungunan, amma in sha Allahu nan da awa daya idan ta dan huta abinda ke cikinta ya fado sai ku tafi da ita gida don ba wani abu ne da yake daukar lokaci ba.'

Tuni yawun bakin Safiyya ya kafe, ta kawar da kanta daga hararar da Umma take zabga mata wadda idon likita da Yaya Habibu ne suka hanata magana. Yaya Habibu yace

'To babu damuwa Doctor, a ina za a biya kudin?'

Ta miko masa takardu tana fadin

'Ka sa mana hannu a wannan sai ka fita nan waje ka kai takardun za su rubuta maka kudin idan ka biya sai ka dawo da takardu da rasit din sai a yi mata.'

Ya mike ya fice, likitan ta kirawo ma'aikatan jinya ta umarcesu da su tura Safiyya dakin wankin ciki, suka turata suka fice Umma na biye da su.

A bakin kofa Umma ta zauna ita da Yaya Habibu suna jira a gama da Safiyya, Yaya Habibu ya dubi Umma yace

'Kinga ikon Allah ko Umma, aure ya kare ita da Mukhtar sai dai idan ya sake shiga sawun manemanta.'

Umma ta jijjiga kai

'Babu yanda banyi da yarinyar nan ba ta kirawo shi ta bashi hakuri, da tuni ta koma dakinta amma tayi kunnen uwar shegu dani yanzu gashi ai ta zama bazawara ko?'

Da mamaki ya dubi Umma

'Umma ai sai hakuri, bata da laifi tunda kinga aure baya hannunta shi ya kamata ya mayar da ita kuma bai yi ba. Allah ya tabbatar musu da alkhairi kawai.'

Kafin tace wani abu ya zaro waya yana fadin

'Bari na gayawa Baban Hotoro don ya sanar da iyayen Mukhtar din, don ni ba zan sake yi masa waya ba tunda ranar da ya sako ta na kirawo shi bai daga ba buma bai biyo bayana ba.'

A take kuwa ya sanar da Baban Hotoro wanda yace yanzu zai kirawo iyayen Mukhtar din, in yaso da daddare zai zo ya samesu a gidan Umman.
Sai da likita tazo sallamarsu Safiyya ta dubeta tace

'Likita dama ana haka, ban fara al'ada ba fa tunda nayi yaye amma na sami ciki gashi har wata uku ban sani ba?'

Tayi dariya ta bar rubutun da takeyi ta fuskanci Safiyyan sannan tace

'Me zai hana? Abun ai ikon Allah ne, bakiga wasu idan suka haihu da zarar jinin haihuwa ya dauke suke samun wani cikin ba? Kuma ai kince wannan shine na uku, Kinga cikin fari shine yake motsi da wuri gashi kuma kince ba kya laulayi. Kuma da yake kin taba haihuwa marar ta bude ba lallai ya daga miki mara da wuri ba, watakila shi yasa baki san dashi ba tunda ma kin saita kwakwalwarki a kan kina jiran al'ada.'

Tayi dariya ta dafa kafadarta tana fadin

'Kada ki damu, yanda aka wanke miki cikin nan ba lallai ma kiyi al'ada ba zaki ga wani cikin ya shiga.'

Ta sunkuyar da kai, ita kuma likitan ta cigaba da rubutunta ta gama ta sallamesu.



KARSHEN BABI NA GOMA SHA BIYU
MATAR MUKHTAR

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA SHA UKU

13
Tunda ya shigo gidan ta fito daga falon Hajiya da gudu ta makale a jikinsa, ya sa hannu ya dauketa yana duba fusakarta, yace

'Nanata ya akayi ne? Ko Yaya ya tsokaneki ne in zane shi?'

Ta kara zumbura bakinta wanda dama a zumbure ta fito da shi, ya kalleta yana shafa bayanta yayi murmushi. Ya san yau muskilancin Khadija ya motsa. Ya karasa falon Hajiya dauke da ita, babu kowa a falon sai Bahijja wadda take zaune tana kallon tashar MBC 4, bayan Bahijjan ta gaisheshi yace

'Anti Ba yau me kika yiwa 'yar taki ne take fushi, ko magana ma taki yi.'

Ta harare ta tace

'Wallahi yau haka ta tashi Yaya, takiyiwa kowa magana wai dole sai an kaita wajen Mamanta abinci ma yau sai da na zare mata ido taci.'

Ya dubi Nanan yace

'Nanata wajen Mama za ki je?'

Ta kara zumbura baki ta jijjiga masa kai alamar eh.

'Gobe zan kai ki wajen Mama kin ji. Bahijja ina Hajiya ne?'

'Tana wajen Baba.'

Ya gyara zama don ya jira ta ta sauko kafin yaje wajen Baban, Bahijja ta mike tana fadin

'Bari na dubo abinci Yaya, ko akwai abinda za a kawo maka?'

'A'a babu komai.'

Ta wuce kicin ta barshi da Nana tana ta faman cika tana batsewa. Sati mai zuwa zai je ya dawo da Safiyya don ko shi ma ya gaji da kewarta, duk da ya sami damar yin abinda yake so da 'yan matansa amma baya jin dadin shiga gidansa ya tarar bata nan. Yana kallon sakonninta a WhatsApp jira yake har sai ta bashi hakuri in ya so sai ya kafa mata sharuddan dawo da ita, smma ya ga bazata fadi abinda yake ranta ba don sallamace kawai sakon da take tura masa. Ya yanke ko ta bashi hakuri ko bata bashi hakuri ba zai je da kanshi ya gayawa Umma bincike takeyi masa, idan Umma tayi musu shari'a sai ya mayar da ita su tafi gida. Ko don su Nana ma ai ya mayar da ita, duk abinda suke so ana musu a nan gidan amma ya san suna kewarta. Ga shi Nurain ya fara zuwa makaranta ya bar Aminu da aikin kaishi har unguwarsu, shi kuma kullum sai ya baro office da rana ya dauko shi ya dawo da shi gidan Hajiya.

Sallamar Hajiya ce ta katse masa tunanin, bayan ya amsa sallamarta ta shiga ta zauna ya gaisheta ta amsa. Ta mikawa Nana hannu tana fadin

'Taho Nana kawata kinji, zo in baki labari.'

Ya sauketa yana fadin

'Yau ai na ga kawar taki rigima take ji.'

'Hmm! Khadija dama ai gidan rigima ce. Kaje Baba yana sama yana kiranka.'

Ya tashi ya fice.

Yana shiga ya tarar da Baban a kan kujera ranshi a matukar bace, ya tsuguna a gabanshi yana mamakin abinda ya bata masa rai haka. Da kyar a ciki ya amsa gaisuwarsu, sukayi shiru na dan lokaci.

'Mukhtar.'

Baban ya kirawo shi, ya dago da kansa suna hada ido ya koma ya sunkuyar da kai. Baban ya cigaba

'Ka yi waya da Safiyya ne?'

'A'a Baba.'

'Ka mayar da aurenta ne?'

'A'a Baba amma in sha Allahu ranar Asabar zan je na mayar da ita.'

'To ka barshi ma don ko ka mayar ma ba zai yiwu ba.'

Zuciyarshi yaji tana neman ta daina harbawa don ya zata mutuwa Safiyya tayi. Take ya fara Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun a zuciyarsa. A firgice yake duban Baba da ayar tambaya a fuskarsa.

'Ka saketa da ciki kuma cikin ya zube dazu, wanda hakan yake nufi ta gama iddarka idan kana sonta sai dai ka shiga cikin zawarawa ko zata saurareka.'

Ya ji wani abu ya tokare masa zuciya, take yawun bakinsa ya kafe. Ya lashe lebe yace

'Baba bata da ciki fa.'

Ya harareshi sannan ya yi masa bayani kamar yanda Baban Hotoro yayi musu. Ya goge fuskarsa wadda ta jike da gumi, tabbas ya tuna tana ta ciwon kai a daidai lokacin da yayiwa Fatima birthday wani lokacin kuma tace cikinta ya kumbura. A lokacin yayi tunanin saboda ta dorawa kanta damuwa ne shi ya sa kanta yake yawan ciwo, ya san kuma itama abinda ya hana ta bawa ciwon mahimmanci kenan. Kuma ya san in ta samu ciki bata laulayi ko daya sai dai kawai yawan ciwon kai. Yana Allah-Allah ya tsokaneta yace mata cikine da ita; don ta gaya masa da tayi al'ada zata je tayi tsarin iyali sai Nana ta shiga makaranta zata sake haihuwa; sai ya manta kuma ya zo yayi wannan sakin.
Ya sunkuyar da kai yayi shiru kamar wanda ruwa ya cinye, Baba ne ya katse shirun yace

'Hakane ko ba haka bane?'

'Hakane Baba.'

'To sai ka koma cikin zaurawa Allah ya bawa mai rabo sa'a, idan kuma cikin 'yan kallo zaka koma sai muyi mata addua Allah ya bata mijin da yafi tsohon mijinta.'

Suka yi shiru kowa da abinda yake tunani. Wai shi Baba yake cewa tsohon mijinta, lallai da ba Baba bane sai ya zagi mutum.

'Tashi ka bani wuri.'

Ya tashi jikinsa babu kwari ya sauko ya nufi falon Hajiya. Tana zaune tana bawa Nana custard yayinda Bahijja take ta danne-danne a waya. Ko sallama bai iya yi ba ya zube a gaban Hajiya, ta harareshi tace

'Meye haka kake nema ka fado kan mu?'

Bahijja ta mike ta shige kichin. Ya dubi Hajiya ya goge fuska

'Wallahi Hajiya ban san tana da ciki ba, jibi Asabar nake cewa zan je da dawo da ita.'

'To ai yanzu ka sani ko?'

Ya sunkuyar da kai, suka yi shiru. Jimawa kadan Hajiya ta sauke Nana ta mika mata kwanon custard din data shanye tace

'Jeki ki kaiwa Anti Ba.'

Ta karba ta wuce kichin.

Ta mayar da hankalinta kan Mukhtar wanda yake zaune a gabanta ya sunkuyar da kai kamar mai daukar karatu

'Damuwar me zaka yi, ka huta da wadda take damunka? Ai sai kawai ka fara sabuwar rayuwa babu mai damuwa da abinda kayi, ka dai cutar 'yayanka tunda ka rabasu da uwar da ta haifesu bayan kai ba haka mahaifinka yayi maka ba. Allah ya sauwake.'

Kafin yace wani abu ta tashi ta shige daki ta barshi a falon, jimawa kadan shima ya tashi ya fice.
------

Tun da aka fito da Safiyya daga dakin wankin ciki Yaya Habibu yake faman tambayarta ko wani wajen yana mata ciwo tana cewa a'a, amma kuma yana kallonta ta kasa daina kuka. Kuma yana kallon yanda Hajiya take ta faman harararta tana kwafa, ya san dukansu su biyun mutuwar auren Safiyyan ne yake tada musu hankali musamman ita Safiyyan da yake matukar jin tausayinta. Bayan sun dawo gida ya dade a falon shi da Hajiya yana ta faman bata baki a kan tayi hakuri ta kyale Safiyya ta sami natsuwa. Yana nan a zaune a falon ya kwalawa Safiyyan kira, zuwa lokacin tayi wanka ta canza kaya tana shirin kwantawa don ta huta.

Ta lallabo ta fito ta zauna a kan kujerar da take kusa da kofar dakin, a nutse ya dubeta da kulawa

'Ki yi hakuri kin ji ko Safiyya, aure rai ne da shi kamar mutum idan kwanansa ya kare babu wanda ya isa ya rikeahi sai ya rabu. Kuma ko wanne bawa yana tare da kaddararsa wadda Allah ya gama rubutawa tun kafin a halicci mutum, don haka ki barwa Allah al'amarinki ki yawaita addu'a. Allah karimi ne kuma Yana sane dake kin ji.'

Kai kawai ta daga masa, ya cigaba

'Gobe in sha Allahu zan zo da mota sai na dauke ki muje mu debo kayanki, in ya so sai na wuce da su can gidana na rufe M
miki su a daya gareji na zuwa lokacin da za a bukata.'

Yayi musu sallama ita da Hajiya, har ya kama hanya ya dawo Safiyyan tana zaune inda ya barta ya zaro kudi a aljihunsa 'yan naira dari biyar-biyar guda hudu ya mika mata

'Ungo wannan ko zaki bukaci wani abu kafin na zo goben.'

Ta karba tayi godiya shi kuma ya kama hanya ya wuce. Sai can bayan magriba Sabir ya shigo da ledoji ya sami Umma da Hamida a falo, ya ajiye ledojin a gaban Umma yace

'Yaya ne da zai tafi ya bani ya ce na siyo kaji guda biyu a dafawa Yaya Safiyya da kuma wannan lemo da ayaban yace na kawo mata.'

'Ajiye a nan.'

Ya ajiye a gaban Umma ya juya.

Duk da tana jini haka ta tashi cikin dare tayi alwala ta zauna ta kalli gabas, da yake tana da hadda haka tayi tulawar wajen izu guda sannan ta dauki lokaci tana zikiri. Kafin ta tashi daga wannan zaman nauyin da take ji a zuciyarta ya ragu da kaso nai yawa, tayiwa kanta alkawarin daga wannan daren ba zata sake yin kuka a kan Mukhtar ba.
........

Washegari da wuri Safiyya ta tashi daga bacci kamar yanda ta saba sai dai bata fito ba, da yake ranar babu aiki Hamida sai juyi take a gado. Tana nan zaune a kan teburin gaban Mudubi tana duba wayarta Sabir ya shigo, ta bashi dari biyar kudin da Yaya Habibu ya bata ya siyo mata pad, ya karbo ya fito.

Yana fitowa tsakar gida ya nufi waje Umma da take aiki a kicin tace

'Ina zaka fita baka ci abinci ba Sabir?'

'Ya Safiyya zan siyowa pad.'

'Koma kace ta bayar da kudi ka siyo mana sabulun wanki da Omo, na ga jiya yayanku ya bata kudi.'

Tana jiyo duk abinda Umman take fada daga inda take zaune a dakin don haka kafin ma ya shigo ta dauko dari biyar, yana shiga ta mika masa ya tafi. Bata ji komai ba domin ta san watakila babu kudi ne a hannun Umman sai dai kuma jiya tana kallo Yaya Habibu ya bawa Umman kudin da yawansu zai iya kaiwa naira dubu goma, ta daga kafada ta bar wannan tunanin.

Yanda aka sanwa kowa kazar nan haka itama Safiyya aka saka mata yanka uku; hakarkari da cinyoyi biyu, ta cinye ta lashe romon shike nan tare da shayi da burodin safe kamar yanda kowa yayi.

Sai wajen karfe tara sannan Yaya Habibu ya zo, ba tare da bata lokaci ba ya dauki Safiyya da Sabir suka kama hanyar gidan Mukhtar me akorikura yana binsu a baya.

Basu sanar da shi zuwansu ba don haka babu

08, January 2025
Nafisa

I cant download the book

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login