Showing 18001 words to 21000 words out of 92582 words

Chapter 7 - MATAR MUKHTAR COMPLT

SAKINA   

16 Aug 2024

7140

haka da suka gama shirinsu suka tafi da yaran gidan Hajiya.

Sai da ya tashi daga aiki sannan ya biya gidan, bayan sun gaisa da hajiya yace mata a shirya su Nurain zai tafi dasu. Ta dubeshi tace

'Baza su bika ba, na riga na cewa Aminu ya biya ta gidan ya karbo kayansu sai sun kwana biyu za su koma. Haba yara suna son shiga mutane amma kana faman hanasu, itama Safiyyan ta huta da hidimarsu su shiga dangi suga gari.'

'To Hajiya.'

Haka ya taho ya barsu ba tare da yana so ba. Baya son yaran nan suna yin nisa , duk inda za su in dai ba tare da uwarsu bane to baya farinciki. Tun Safiyyan tana damuwa tana ganin gidansu yake hanata kai yaran har ta gane ba haka bane don ko wajen Hajiyan tace a kaisu sai yace a'a.

Ba karamar murna Safiyya tayi ba da taga ya dawo babu yaran, ko babu komai zata samu ta gama gyare-gyarenta kafin a dawo dasu don tana sane ta sami akwati ta cika musu da kaya da Aminu ya zo karba.
........

Da yake ranar asabarce ta san yakan kai goma ko sha daya bai fita ba, wataran ma sai yaci abincin rana sannan ya fita. Tun wajen shida na safe ta sulale ta tashi zata fita daga dakin ya riketa yana dariya

'Ina jinki, ina zaki bayan yaran basa nan bazaki huta ba sai sun dawo kice bacci baya isarki.'

Tayi yar dariya don da ta zata bacci yake

'Hm! Kwalema zanyi gaba daya gidan zan gyara yau kafin su dawo idan na gama sai na zauna na maida kibata kafin su dawo.'

'Sarkin aiki.'

'Um kai da kanka fa kace karkashin gadonka kamar bola ai gara na share na goge ko? Sai a tara wani dattin.'

Ya saketa ta fito tunda ya san tagama hidimarsa.

Tana fitowa ta fara hada abincin safe ta rufe sannan ta fara gyaran gidan. Zuwa karfe tara ta gama gyara falo, tagogin ne kawai bata goge saboda su gaba daya na gidan zata goge a lokaci guda. Ta nufi dakinsa tana sanye da t-shirt da gajeran wando rike da tsintsiya, tana so ta duba idan ya tashi sai ta gaya masa ta sa abincin safe idan ya fito sai ta fara gyara dakin nasa tunda bata sani ba ko zai fita ko ba zai fita ba. Tana shiga corridor din ta jiyoshi a bandaki yana wanka, da alama shower a kunne take. Ta so taji kamar yana waya a bandakin amma zubar ruwa bai bari ta tantance ba , kuma da yake tunda ta karanta sakonnin Sucre ya tsiri shiga bandaki da wayarsa abun bai dameta ba. Ta dawo kicin ta dauki tsintsiyoyinta ta koma dakin.
Sai da ta debi kayan da zai saka da duk abinda yake bukata na shiryawa ta kai dakinta, tana nufin idan ya fito sai yaje can ya shirya saboda kura. Da yake zanin gadon ya riga yayi datti sai bata cireba, ta dai rufe wardrobes. Da yake karkashin gadon ne a ranta ta nan ta fara.

Katifarsa tana da nauyin sanna kuma katakon gadon ma bashi da dadin sha'ani don haka sai dai ta kwanta ta sharo sannan ta zura mopper ta goge duka ta karkashi.

Ta zagaya can ciki ta kwanta tana leka karkashin gadon, ta zura tsintsiyar kwakwa ta fara kokarin sharo kasan gadon. A dai-dai nan ya fito daga wanka yana daure da tawul da waya a kunnensa, hira yakeyi cikin nishadi bai ma kula da tsintsiyarta a gaban mudubi ba balle ya san tana cikin dakin. Ya nufi gaban wardrobe ya tsaya ya bawa gadon baya yana cigaba da wayarsa cikin nishadi

'Ke matsoraciya ce ai, babu abinda zata yi miki.'

'Me kike so kiji ne, ai na gaya miki a kanki na fara soyayya kuma tunda kika ga na nace kinsan ta gidan bata kaiki komai ba.'

'Ai babu yanda zata yi dake, ba naje dake na nuna miki gidan da nake ginawa ba. Ke kika dace da wannan gidan don haka ko zata shiga ma sai bayan kin tare ki daina damuwa da ita. Jiyan ma na gaya miki ba ita ta hanani zuwa ba don bata isa ba, kawai dai ina wajen Baba ne.'

'Yauwa, ki shirya gani nan zuwa yanzu kuma yau sai lokacin da kika ga dama kika sallameni sannan zan barki.'

'Minti talatin.'

'Yauwa Baby sai na zo.'

Tayi gyaran murya daga inda take tsaye rike da tsintsiyar kwakwa bayan da ta mike daga karkashin gadon, firgigit ya juyo yana kallonta don bai yi zaton tana dakin ba. Yanayin fuskarta da kallon da take masa ya tabbatar masa taji abinda ya fada a wayar.
Har ya juya kamar me shirin dauko kaya sai kuma ya juyo a fusace yana mata wani kallo.

'Me kike yi a nan?'

Da kyar ta hadiye malolon da ya tokare mata makogoro tace

'Shara.'

Ya watsa mata harara

'Da kuma labe ko? To ai gashi nan kin ji abinda kike son ji.'

Ya juya ya cigaba da kokarin zaro kaya daga wardrobe din. Ta share kwalla daga idonta ta bude baki da kyar tace

'Mukhtar yanzu karuwar kake gayawa ni matarka ban kaita komai ba? Ashe ma soyayyar da ka nuna min lokacin kana neman aurena duk karyace tunda yanzu ne ka fara soyayya? Ashe ginin da kake yi nake faman raba dare ina addu'a ka gama mu rabu da gidan haya ashe ba don ni ake yi ba, har an kai karuwa ta gani ni ina nan zaune? Yanzu Mu...'

Ya daga hannunsa yana dakatar da ita

'Kada ki gaya min maganar banza, sau nawa na gaya miki ki daina bibiyata ki daina yi min labe yanzu ai kin ji abinda kike son ji ko?'

Ta bude baki tana nuna kanta da yatsa

'Yanzu nice karuwarka ta fi ni komai Mukhtar?'

Ya bita da kallo daga sama zuwa kasa

'Shi kike son ji ai kuma kin ji ko?'

Tsintsiyar da take hannunta ta subuce ta fara busar da iska mai zafi

'Allah ya isa Mukhtar, Allah ya saka min....'

Ya daga hannu ya dakatar da ita yana matsowa yana kokarin zagayawa inda take, don haka itama ta fara tahowa suka hadu a gaban mudubi

'Wallahi idan kika sake kika zageni sai na kwakkwada miki mari juma na daki banza wallahi. Sai dai ki tafi gidanku kije kiyi a can.'

Idonta gaba daya ya rufe saboda hawayen da kuma kunan rai, ta bashi amsa

''Kai ai sai ka zageni ko ba komai haka maza na gari sukeyi, shima zagin yana cikin sunnar aure da kuma bin karuwai.'

Ya dunkule hannunsa kamar zai kai naushi sai kuma ya dago daya hannun ya nausa a ciki.Ya ware yatsa ya nuna mata kofa

'Zo ki fice min daga gida Safiyya, nace zo ki fice min daga gida ba zan dau raini ba.'

Duk maganar da zata fada ba mai dadi bace kuma bata so takai ga zagin nasa don haka ta ja kafa ta fice, dakinta ta shiga ta mako kofar iya karfinta. Ta zauna a kan gadon jagwaf, gaba daya kanta ya kulle zuciyarta tafasa kawai takeyi.

Yanzu ashe duk soyayyar da Mukhtar ya gwada mata a baya karyace? Tana gida tana jin kanta a matar aure ashe duk ya gayawa 'yan matansa ita din banzace? Wannan wane irin cin fuska da wulakanci ne Mukhatr yake mata? Haka ta zauna hawaye yana zuba a fuskarta ba tare da ta goge ba saboda babu yanda zata yi, babu wanda
zata gayawa taji sanyi a ranta.

Tana fitowa daga dakin shi kuma ya cigaba da shirinsa, tabbas sai ya koyawa Safiyya hankali. Shi bazai kai kararta wajen iyayenta ba amma tabbas zai korata gida taje da kanta ta kai karar kanta, idan sun mata fada tayi hankali ta dawo.

A shirye tsaf ya fito ya turo kofar dakin nata a fusace, ta daga kai ta kalleshi da idonta cike da hawaye. Baya son kukanta amma baya son sa idon da take masa don haka dole ya koya mata hankali.

'Me kike min a gida? Baki ji nace ki tafi gidanku bane? Ki tashi ki fice min daga gida.'

Take hawayenta ya bushe malolon da ya tokare mata makogoro ya fara neman hanata numfashi, ta kalleshi tsaf suka hada ido sannan tace

'Idan naje me zan ce musu?'

Ya kalleta a banzace

'Kice na sakeki saki daya.'

A razane ta dago kai ta dubeshi, abinda ta so fada ba shi ta fada ba saboda yanda ta gani a fuskarsa yana jin dadin yadda sakin ya razan ta, ta bude baki da kyar tace

'Ka rubuta saboda na basu hujja.'

Yaja tsaki ya juya ya koma dakinsa, jimawa kadan ya dawo ya sameta a zaune a inda ya barta ya mika mata takardar da ke hannunsa

'Gashi nan, kizo ki fice min daga gida saboda zan rufe gidan na fita.'

Ya juya ya koma falo ya zauna yana jiranta.
Duk wani takaici da take ji ya juye ya koma mamaki, yanzu ashe Mukhtar zai iya sakinta? Shike nan so ya kare? Yanzu me zata je ta cewa Umma? Gashi yace dole sai ta fita balle tace zata zauna tayi idda a gidan. Ta daga hannunta sama tana addu'a

'Allah Kaine Allah, ka kawo min mafita.'

Ta mike a hankali saboda yanda jiri yake kwasanta, ta karasa kan dadduma ta dauki hijabinta ta saka ta dauko jakarta ta ciro wayarta da take chaji ta hada da chajar ta jefa a jakar. Ta fito falon tana zaune kawai, har ta nufi hanyar fita ta juyo ta dubeshi tace

'Yaran fa?'

A cikin halin ko in kula ya dubeta yace

'Ai ba da su kika zo ba ko?'

Ta sunkuyar da kai murya a sanyaye tace

'Hakane.'

Bata jira me zai ce ba ta juya ta fice daga gidan.


KARSHN BABI NA GOMA
MATAR MUKHTAR

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

FIKRA WRITERS ASSOCIATION


BABI NA GOMA SHA DAYA

11
Da kyar ta samu ta share hawayenta ta saita fuskarta saboda bata so ta hadu da wanda ta sani a tambayeta dalilin kukanta, saida ta tsaya a bakin titi sannan ta tuna bata ma da kudin mota don kudin da suke cikin jakartata bazasu kaita gidan Umma ba. Dole haka ta dauki shatar dan sahu a kan sai ya kaita zata shiga ta karbo masa kudin motarsa a gidan.

Tana shiga Umma ta fara tambayarta

'Lafiya na ganki haka.'

Ta ajiye jakar hannunta tace

'Kudin mota zaki bani na sallami mai adaidaita-sahu yanzu zan shigo.'

Ta shiga daki ta dauko naira dari biyu ta mika mata, ta juya ta fice, Sabir da yake zaune yana game a waya ya bi bayanta. Jimawa kadan ta dawo Sabir din yana biye da ita. A nan falon inda suka bar Umma nan suka sameta, Safiyyan ta zauna kusa da Umma ta kalleta, itama nata idon yana kanta don haka suka hada ido. Nan take ta saki kuka tare da rufe fuskarta da tafukan hannunta.

A razane Umma take dubanta

'Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun, Ke Safiyya wai me ya faru ne za ki sani a gaba kina kuka? Ina yaran da babansu?'

Ta share hawayenta tana ajiyar zuciya, ta janyo jakarta ta zaro takarda ta mikawa Umma tare da fadin

'Ya sakeni.'

Sabir da ke zaune yana saurarensu ya bude baki cikin mamaki tare da rufe bakin da tafin hannunsa yayinda Umman tace

'Subhanallahi, kin san me kike fada kuwa Safiyya, shi Mukhtar din ne ya sake ki?'

Kafin tabata amsa ta gama bude takardar, nan da nan ta karanta harda tsallaken kalmomi. Ta saki hannunta me rike da takardar a kan cinyarta tana fadin

'Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, ke kuwa me kika yi masa?'

'Wallahi Umma babu abinda nayi masa.'

Nan ta mayar mata da abinda ya faru. Cikin takaici tace

'Amma kuwa yaron man bai kyauta ba wallahi, wannan ai wulakanci ne.'

Sukayi shiru, Safiyya na ta faman share hawaye. Umman ta dubeta da takaici tace

'Kema ke ce da shegen taurin kan tsiya, na ce ki fita harkarsa ki rabu da 'yan matansa. Daga ganin yanda ya aureki ya ajiye ki a gidan ai kin san kin fi duk wata mace da yake tare da ita, yanzu ga abinda kika janyowa kanki. Ko da ya zo ya mayar da ke dai ai kin ragewa igiyar auren kima.'

Ta ja tsaki tare da kauda kai. Suka dauki lokaci shiru kowa da abinda yake tunani, Sabir ya mike yana fadin

'Umma bari naje na dawo.'

Bata cikin yanayin da zata amsa masa don haka kallonshi kawai tayi ya fice ya barsu. Jimawa kadan shirun ya gundiri Safiyya ta tashi ta nufi dakin Umman, har ta kusan shiga ta tuna indai a dakin Umma zata sauka to akwai alamun zasu kwana Umma tana yi mata fada don haka ta juya ta wuce dakin Hamida wanda shima yana nan cikin falon.

Tana jiyo Umman daga falo ta kirawo Kanin Abbansu wato Alhaji Safiyanu wanda suke kira Baban Hotoro, ta sanar da shi halin da ake ciki sannan ta sanar da Yaya Habibu ma.

Sai bayan sallar la'asar sannan Baban Hotoro ya iso gidan; tun bayan rasuwar mahaifinsu shine wanda yake kula da lamuransu duk da ba wani kudine da shi ba ammma dai shine ubansu. Bayan sun gaisa da Umma ya jajanta mata yasa aka kirawo Safiyya, ta bashi labarin duk yanda abun ya faru. Ranshi yayai matukar baci duk da shima din yayi mata fadan binciken

'Tunda ba shi ya aike ki kika yi masa bincike ba ai da abinda kika gani sai ki hadiye a cikinki ke kadai tunda ciki ba don tuwo kawai aka yi shi ba.'

Ta sunkuyar da kai tana share kwalla. Suna nan zaune ya dauko wayarsa ya kirawo Alhaji Kabiru Balarabe wanda wa ne a wajen mahaifin Mukhtar kuma shine madaurin auren Mukhtar din. Bayan sun gaisa ya sanar dashi abinda ya faru, suka jajantawa juna sannan ya gaya masa su basu ma san an yi hakan ba amma in sha Allahu zai yi magana da Mukhtar din.

Sai da ya gama wayar ya dubi Umma wadda take ta faman cika tana battsewa kamar zata doke Safiyyan yace
'Hajiya Umma hakuri za kiyi tukunna muji daga wajensu, in sha Allahu komai zai daidaita.'

Ya dubi Safiyyan yace

'Kiyi hakuri Safiyya, shi bawa baya wuce kaddararsa kuma rayuwa gaba dayanta jarrabawa ce. Idan da sauran zama zai zo ku daidaita idan kuma akasin hakan ne to sai mu nemi mafita daga Allah, Allah shine ya san yanda zai yi da bawa kuma in sha Allahu baza ki tozarta ba.'

Har cikin ranta taji dadin wannan maganganu na Baban Hotoro, tun bayan sakin da Mukhtar yayi mata babu wanda ya gaya mata wata kalma mai dadi kamar wannan. Haka Baban Hotoro yake, duk girman rigima a dangi haka zai kwantarwa da kowa hankali kuma cikin hukuncin Allah ba a tozarta. Yayi musu sallama ya tafi bayan ya sanar da Umma idan yaji daga wajen iyayen Mukhtar din zai sanar da ita sannan kuma ya gaya mata ya kirawo Yaya Habibu yace ya sameshi a gida da daddare don su kara tattauna maganar.
Kafin ya tashi sai da ya kirawo Baba shehu; wato kaninsu da ke zama a Kaduna ya sanar da shi suka jajanta. Ya bashi Safiyyan a waya shima ya kara yi mata nasiha ya bata hakuri kuma yace ta cigaba da addu'a.

-------

Tunda yaje office yake tunani kala-kala, yana son Safiyya baya son rabuwa da ita, sai dai baya nadamar sakin nan da yayi mata don yana so taje ta dana zaman gidan da zawarci taji idan da dadi. Yana da tabbacin cewa idan ta dan taba zaman gida in ta dawo zata shiga hankalinta, kuma ya san za a nemeshi a gidansu zai sami damar da zai gayawa Baban Hotoro irin yanda take bibiyarsa kuma tana kokarin yi masa rashin kunya.

Yana zaune a office bayan sallar azahar wayarsa tayi kara, yana dubawa yaga Baba ne. Cikin girmamawa ya daga bayan ya amsa sallamar Baban ya gaisheshi. Baban yace

'Kazo gida yanzu ina son ganinka.'

Kafin yace wani abu Baban ya ajiye wayar, ya cire wayar daga kunnensa ya dubeta cikin faduwar gaba. Yace

'Allah yasa dai lafiya.'

Take ya mike ya hada tarkacensa ya fito daga office din, ya sallami masinjansa ya kama hanyar gida yana ta mamakin neman da Baba yake masa yanzu-yanzun nan.

Yana tsayawa a bakin gate din ya danna honk yaji babu wanda ya bude gate din don haka ya gyara parking a waje ya kulle motar ya shiga ciki.

Bai kula da motar Baffa Kabiru a farfajiyar gidan ba saboda tsabar sauri, babu kowa a wajen don haka kai tsaye ya haye saman wajen Baban. Yana shiga falon ya tarar dasu a zaune shi da Baffa Kabiru, nan take gabansa ya fadi, ya tsuguna har kasa ya gaida Baffan sanna ya matsa kusa da kafar Baban yace

'Baba ga ni.'

Ya dubeshi suka hada ido sannan yace

'Sai yaushe zaka gaya mana ka saki matarka har ka koreta daga gidanka? Maigida.'

Take gumi ya karyo masa duk da AC din falon a kunne take, bai taba tunanin labarin sakin zai riga shi zuwa gidan ba don shi bari yayi sai ya tashi daga office sai ya sami Hajiya yayi mata bayani gashi har su Baba sun yi masa taron dangi. Shirun ya tsawaita baba yace

'Kai muke saurare.'

Ya shafo kansa idonsa yana kasa yace

'Ayi hakuri Abba, daman ina nufin idan na taso daga aiki nazo sai na fada.'

Ya kwalawa Bahijja kira wadda nan da nan ta shigo falon da sallama, ta riga ta gaisheda Baffa Kabiru tun zuwansa don haka ta tsuguna daga nesa kadan tace

'Ga ni Baba.'

'Ki kirawo min Hajiya.'

'To Baba.'

Nan da nan ta fice ta barsu zaune sun yi shiru, jimawa kadan Hajiya ta shigo da sallama ta nemi kujera me zaman mutum daya ta zauna tace

'Ga ni Baba.'

'Daman Mukhtar ya gaya miki zai saki matarsa

08, January 2025
Nafisa

I cant download the book

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login