Showing 6001 words to 9000 words out of 92582 words
za kiga wasu suna bin matan kwararo.'
Ta jijjiga kai cike da damuwa tace
'Wallahi Yaya ina iya kokarina, duk wani abu da kike tunani ina yi tsabar fitna ce kawai da wulakanci. Kuma ma yanzu mutum sai kace jahili idan matsala ce ba zai yi magana mu gyara ni da shi ba sai yaje ya fada sabon Allah. Kuma ace wai nayi hakuri!'
'To kinga dai ni yanzu ba hurumina bane nace zan yi masa magana, ki cigaba da hakuri ki dinga addu'a in sha Allahu zai daina. Kuma kin san tunda ya aureki ai yana sonki shi yasa ma bai auri su matan barikin ba, ki kwantar da hankalinki ki cigaba da addu'a ki rungume mijinki.'
Suka yi shiru na dan lokaci. Zuwanta wajen Yaya Hajiyayyaye Bai bata amsoshin tambayoyin da ke kanta ba sai ma kara mata wasu tambayoyin a kan nata. Allah ya sani tana iya kokarinta wajen duk abinda ya shafi aure, bata taba gazawa wajen biya masa bukata ba ko a wanne yanayi take ciki. Idan tana shayarwane kawai wani lokacin dole suke raba daki saboda bata son kwana da yaro da miji a gado daya saboda tarbiyya. Idan ta gama biyan bukatarsa sai ta barshi ta koma dakinta inda ta kwantar da yaran ta karasa kwanan. Kuma ta san yana samun gamsuwa da ita sosai tunda ita din gwanar gyara ce musamman yanzu da ta kara sanin dabarun gyaran. Ta yi ajiyar zuciya ta kawar da kai tana fadin
'Umm! Allah ya kyauta.'
'Amin Safiyya, Maza kam yanzu sai addu'a kowanne da irin ta sa matsalar sai dai kawai ka sami mai dan dama-dama. Ki cigaba da hakuri kina lallabawa in sha Allahu zai bari.'
Shigowar yara daga islamiyya ne ya katse musu hirar, da gudu Mujahid da Sulaiman suka fada jikinta da yake sune kanana suna kiran
'Anti Safiyya mun dawo baki tafi ba.'
Ta taresu da dariya tana fadin
'Dama jiranku na tsaya yi idan na gaisheku sai na tafi.'
Abdallah, Amina da Fariha da yake sune manya suka tsuguna suna gaisheta. Bayan ta amsa gaisuwarsu ta mike tana fadin
'Yaya bari na tafi yanzu za ki ji Magriba.'
Tayi sallama da yaran suka fito ita da Safiyyan , suka tsaya a bakin gate Yayan ta dubeta tace
'Kiyi hakuri Safiyya kin ji ko? Ki guji yin fito-na-fito da shi maza basa son haka sannan kuma basa so kina matarsu ki dinga gaya musu laifinsu. Idan abin ya ci tura dai kya iya neman mahaifiyarsa ki gaya mata cikin hikima idan ta fahimceki sai ki ga ta tsawatar. Amma kada ma ki bari wannan ya zamar miki wani abun damuwa.'
'To Yaya, nagode.'
Sukayi sallama, har ta kusa fita gate Yaya Hajiyayyaye ta kirawo sunanta. Ta waigo ta dawo tana sauraronta
'Kada fa ki je kina gayawa wani wannan zancen, don ba abin yadawa bane in ba haka ba sai ki sayowa kanki raini a dinga kallonki banza-banza.'
Tayi 'yar dariya
'Babu ma wanda zan gayawa Yaya ballema tunda ga yanda mukayi dake in sha Allahu babu wanda zai ji.'
'Yauwa akwai wasu kayan gyara da na saya daga Sokoto, gobe in sha Allah za a kawo su. Da na karba zan dibar miki ki kara ki kara dagewa sosai, zai bari in sha Allah.'
Sukayi sallama ta tafi gida zuciyarta a jagule.
--------
Tun da safe da ya sauka a Abuja Fatima ta kirawo shi ta sanar da shi cewa tana da test gobe da safe don haka zata canza ticket dinta sai ta biyo jirgin Talata da karfe sha biyun rana. Hotel din da ya sauka yana da nisa da wajen da ake Taron don dama haka yake yi, in dai zai taho da wata baya kama hotel kusa don yawancin bakin nan kusan suke sauka. Baya so ya sauka a kusa don kada a dinga ganinsa da mata daban-daban, duk da dai matan da yake mu'amala da su basu wuce uku ba ko ma biyu.
Ranar farko ba wasu abubuwa ake yi a conference din ba, sai dai ana bawa kowa dama su karasa registration su karbi kyautarsu wadda ake bawa duk wani wanda ya halarci taron don haka iya abunda yayi kenan ya koma masaukinsa. Sai da zai kwanta sannan ya kirawo Safiyya suka dan taba hira, bayan yayi mata sallama Kuma ya shiga hira ta Whatsapp da 'yan matansa.
---------
Kanta cike da tambayoyi ta dawo daga gidan Yaya Hajiyayyaye, tana shiga Nana ta makale mata saboda kusan ranar gaba daya basu hadu ba. Dole haka ta hakura ta zauna wajen yaran da Hamida, suna kallon TV suna hira har akayi Isha suka ci abinci ta kwantar da yaran. Sai da ta kulle gidan ta rufe ko ina sannan tayi sallama da Hamida wadda take falo tana kallo, ta shiga daki ta kintsa ta kwanta.
Maganganun da sukayi da Yaya Hajiyayyaye ne suka dinga yi mata yawo a kwakwalwa. Kenan ma laifinta ne da ta ga abinda yake yi, shikenan yanzu babu yanda za ayi da shi haka za ta zuba masa ido yana raba mata kwana da karuwai? Duk wani abu da miji yake bukata a wajen mace tana yi iya kokarinta, amma tayi alkawarin zata cigaba da addu'a da kuma sadaka kamar yanda Yaya Hajiyayyaye tace mata. Haka ta kwana da takaici saboda yanda zuciyarta take tuna mata yana can a rungume da wata 'yar iska. Ko da ya kirawo a waya da daddare sai da tayi kamar bazata dauka ba amman dai haka ta daure ta dauka tayi kamar babu wani abu suka taba hira.
...........
Haka ta hakurkurtar da zuciyarta ta cigaba da rayuwarta, musamman da taga damuwarta tana nema ta shafi mu'amalarta da yaranta. Tana addua sosai saboda tanaso ta dawo da nutsuwarta kafin ya dawo daga Abuja domin bata so ta rasa mijinta.
Shi kuwa Mukhtar tunda Fatima ta isa Abuja ya sake shiriricewa domin kullum idan ya gama hidimar conference din haka zai koma hotel din su kwana suna lalacewarsu.
......
Ranar alhamis da safe ya kirawo Safiyya a waya bayan sun dan taba hira ta kirawo Nurain da Nana suka karbi wayar suka gaisa da Abbansu sunata yi masa labari. Bayan ta karbi wayar ta sallami yaran ta kara a kunnenta tace
'Gobe za ka dawo ko?'
Yayi gyaran murya sannan ya bata amsa
'No, sai jibi. Akwai wani mutum da nake son gani to yace sai Saturday da safe in sha Allah by Azahar na gama sai na biyo jirgin karfe hudu.'
Ta danyi shiru sannan tace
'Um! Allah ya nuna mana.''
'Akwai matsala ne?'
'A'a babu komai muna nan muna jiranka.'
Yayi dariya, sukayi sallama suka ajiye waya.
Ya juya ya dubi Fatima wadda take kwance a bayansa tana murmushi yace
'Shikenan kin ji dadi ko? Za mu kara kwana dayan in ya so ranar Asabar sai mu tafi da yamma.'
Ta matso jikinsa tana dariya
'Ko kai fa Baby na, ai ma tafi a nutse.'
Suka yi shiru na dan lokaci.
'Um, komai dai sai an tambayi Madam nima dai na kusa na shigo daga ciki.'
Yayi dariya ya lakace mata hanci
'Kwarai kuwa ga dakinki ga nata.'
'Ka ga daga wannan session din saura semester daya na gama, itama don ina da spill over ne. Idan aka yi hutu na tafi Zariya sai ka turo a zo ayi gaisuwa ai ko?'
Ta bi fuskarsa da kallo kamar a nan zata karanto amsar
'Haka za ayi in sha Allah, ko babu komai mu huta da buya da satar hanya.'
Suka yi dariya gaba daya.
--------
Tunda suka gama waya da Abban Nurain damuwarta ta dawo sabuwa, wannan kara kwanan da yayi ya tabbatar mata ba shi kadai ya tafi Abujan ba. Ko da yake dama ai bai boye mata ba da ta tambaya. Ta kasa sukuni gaba daya, sai can wajen shabiyu na rana tayi masa waya ta sanar da shi tana son suje gidan Ummanta ita da yaran. Ba tare da wani musu ba da yake dama bai fiya hanata fita ba yace sai sun dawo. Don haka ko abinci bata iya tsayawa sun ci ba tace su tafi idan sun je gidan Umman sa ci.
Har sun fito Hamida ta tuna mata akwai jakar da ta cika da kwancen kayansu wanda za a kaiwa Umman ta bayar don haka ta koma ta dauko suka tafi da ita.
Suna shiga Umma ta hau hidima da jikokinta, suna ta zuba shagwaba irin yanda suke so. Tuwon shinkafa miyar taushe aka dafa don haka nan da nan aka zuba kowa ya sa hannu ana ci ana hira.
Ana gama cin abinci aka tashi don yin sallar azahar, Umma ta shiga dakinta don yin Sallah nan da nan Safiyya ta bawa Hamida umarnin ta jire mata yaran ta bi bayan Umman. Bayan sun idar da sallah Umma ta shafa addu'arta ta juyo ta dubi Saffiyan tace
'Tunda kuka zo bakinki yake motsi, Allah ya sa dai lafiya kuke.'
Ta Kalli Umman ta koma ta sunkuyar da kai
'Lafiya kalau Umma.'
Umman ta kalleta suka hada ido alamar tana dai sauraronta. Ta kau da kanta ta bude baki a hankali tace
'Abban Nurain ne Umma.'
Da mamaki tace
'Me ya sami Abban Nurain din?'
Kafin ta fara magana kwalla ta kwace mata, ta share kwallar sannan tace
'Umma mata yake nema harda wadda take turo masa hotunanta tsirara.'
Ta zaro ido tana tafa hannu
'Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun! Amma yaron nan ya bani mamaki kuwa, ya za ayi yayi haka gashi kamar mai ilimin addini. Kai jama'ah! Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun.'
Suka yi shiru na dan lokaci Safiyya tana cigaba da share hawaye, Umma ta katse shirun tace
'Anya kuwa Safiyya kin tabbatar, ke wa ya gaya miki? Kada fa ki sa zargin a cikin aurenki ga mijinki da kokari kuma yana nuna miki duk wata kauna da kulawa.'
Ta share kwalla tayi kwafa, kowa yana kyautata masa zato basu San shi babban mai ta'asa bane.
'Wallahi Umma da idona na gani a wayarsa, kuma da nayi masa magana cewa yayi duk abinda zan yi a kai naje nayi.'
Umma ta rike haba cikin matsananciyar damuwa
'Ikon Allah! Shi Mukhtar din dai? Kai maza basu da tabbas.'
Suka sake yin shiru na dan lokaci, Umma ta gyara zama tace
'To ke me ya kaiki ma kika bincika masa waya? Wannan shine dalilin da yasa ake hanaku binciken wayoyinsu tunda yanzu waya ta riga ta zama fitna ga ma'aurata. Shi bincike ma gaba daya a wajen musulmi bashi da alkhairi ka dinga bibiyar mutum har ka ganowa kanka tashin hankali.'
Wannan fadan binciken da ake yi mata shi yake kara bata mata rai, ta hadiye malolon da yake makogoronta da kyar sannan tace
'Umma ba fa bincike na yi masa ba.'
Ta bata labarin yanda akayi taga sakonnin sannan tace
'Kuma fa Umma da na gaya masa ce min yayi duk abinda zanyi naje nayi.'
'To me kike so yace Miki? su maza ai dama basa karbar laifinsu shi yasa da kin sani ma shiru kika yi masa kawai ki bishi da addu'a.'
Ta share hawaye
'To Umma ni yaya zanyi, haka zan cigaba da zama da shi yana yawon zina?'
'To ya za kiyi? Ina fatan dai kin san mutuwar aure ba zabi bane ko? Duk mace da kika gani a dakin miji hakuri takeyi da shi, mazan yanzu kuma in dai harkar matace sai dai kawai mu bisu da addu'a. Ke dai ki tabbatar duk wani hakki na aure kin sauke masa Kuma ke ma ki samo dabarun da zaki janye hankalinsa daga kan matan banza.'
Hawaye kawai take sharewa, wajen Umma ne karshen inda zata kawo maganar nan amma gashi ba wata mafita; nema kawai ake a dora mata laifi. Ta zata ma akwai wata dabara tasu ta manya ko kuma Umman zata sa Yaya Habibu yayi masa magana tunda yanzu shine waliyyinsu tunda ba ran Abbansu. Allah sarki Abba ta san da yana raye da tabbas sai ya samar mata mafita, ba zai barta ta cigaba da rayuwa cikin kunci ba.
Ummace ta katse mata tunanin tana fadin
................
Ku taho muje telegram mu karanta har karshe.
N800 kacal 😍
Send to
7037834664
Opay Digital Services
Sakina Muhammad Yazid
MATAR MUKHTAR
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
BABI NA HUDU
04
Magana da Ummanta bata kara mata komai ba sai tsananin damuwa, ranar haka ta kwana tana kuka gashi gobe zai dawo. Haka ta bawa kanta hakuri kuma tayi alkawarin zata bi shawarar Ummanta da Yaya Hajiyayyaye; zata kara dagewa da addu'a kuma duk wani abu na gyara da kulawa da miji zata sake mayar da hankali a kai.
Sai la'asar yace mata zai dawo don haka ta san abincin dare zai ci, tun sassafe suka fara aiki ita da Hamida. Suka yi cake mai dadin gaske don ta san yana son snacks irin haka wanda take ajiye masa a dakinsa ya kwana biyu yana ci; suka hada kunun aya sannan tayi tuwon semovita da miyar kubewa danya don shine abincin da yafi so musamman da daddare.
Kafin la'asar sun gyara gidan tsaf sai kamshin turaren wutarta ne yake tashi, ita da yara kowa fes. Sai wajen karfe biyar da rabi ya iso gidan, kaninsa Saifullahi ya kawo shi. Bayan sun gaisa ta kawowa Saifullahi cake da kunun aya sannan suka gaisa, ya dubi cake din yace
'Maman Nurain ai wannan kayan dadin juye min abuna zakiyi in tafi in dinga ci a hankali kada su kare da wuri.'
Ta yi dare tace
'Uhm, wato yau tun kafin a fara cin abincin ake santi Allah ya so dai akwai makari a bayan kujerar.'
Shima dariyar yake yi yana fadin
'To ai abincin naki ne matar Yaya kullum mai dadi kike girkawa babu kama hannun kishiya.'
Ta harareshi tana dariya, ya sa hannu ya toshe bakinsa yana fadin
'Au ashe an hana ni wannan maganar.'
Ta mike tana masa dariya saboda ta san in dai ta biye masa haka za ayi ta hira ana dariya, ta sami roba ta zuba masa kunun ayar da cake din a leda. Yana karba yayi mata sallama ya fice ita kuma ta wuce daki wajen Abban Nurain.
Yana zaune a gefen gadon ya tokare hannuwansa ta baya yana hutawa ta shiga da sallama tana dauke da cake da kunun aya a tray, ya riga ya bawa su Nurain chocolates din da ya siyo musu don haka sun fice wajen Hamida ta bude musu.
Da fara'a ya amsa sallamarta ta karasa ta ajiye kayan hannunta a kan durowar gefen gado tana dubansa tana murmushi. Haushinsa take ji saboda yanda ya tabbatar mata shi da wata suka tafi Abuja suka kwana biyar suna aikata sabon Allah Amma babu yadda zata yi, dole ta danne zuciyarta ta kara fada murmushinta.
Ta fara zuba masa kunun aya tana yi masa sannu da zuwa.
Da fara'arsa yake amsa mata saboda bai ma zata zai sameta haka da walwala ba saboda yanda suka rabu. Ya karbi kunan ayan daga hannunta ya kai bakinsa yayinda ita kuma ta zagayo ta zauna a gefensa. Saida ya shanye kunun ayan sannan ya dago ya dubeta yace
'Ya na sameku da yaran?'
'Lafiya Alhamdulillah, ya taro da gajiyar hanya?'
Nan suka dan taba hira jimawa kadan suka jiyo kiran sallar magriba don haka ya tashi ya yiwo alwala ya wuce masallaci.
.........
Haka Safiyya ta mayar da komai ba komai ta hakura, kuma a hankali sai taga kamar abun ya wuce. Komai na Abban Nurain ya koma kamar yanda ya saba, dama kuma bai taba fashin kwana a gida ba sai idan yayi tafiya kuma bai fiya yin dare sosai ba a waje.
Karkarin dadewarsa ya kai sha daya na dare, ya kan ce mata yana tare da abokansa su Shamsuddin; wannan bai fiya damunta ba saboda ta san shi da yawan abokai. Yanzu ne ma ya fara damunta tunda zuciyarta ta fara zargin ba wajen abokan yake ba wajen matan banza yake zuwa.
Duk wani abu da ta san zai kara musu kusanci yanzu shi take yi, lallaba shi kawai takeyi. Kuma kawo yanzu ta fara ganin kamar hakan ya sa ya daina kula matan banza.
Tunda ya dawo daga Abuja ta faki idonsa ta haddace pattern din da yake bude wayarsa da shi, don hak duk lokacin da ta faki idonsa ta kan samu dama ta bude wayar ta caje tas. Bata kara ganin messages din Sucre ba wanda da alama gogewa yayi, amma ko cikin contacts dinsa ma da ta duba babu sunan Sucre kuma babu wani sabon suna don haka ta dan sami nutsuwa kwana biyu. Duk lokacin da zata faki idonsa ta bude wayar tasa idan ta duba Whatsapp bata samun wasu hirarrakin na 'yan mata sai hirarrakinsa da suka shafe shi. Ta gode Allah da ta dauki shawarar Ummanta bata cigaba da fada da mijinta ba don yanzu haka ma ya rabu da yarinyar.
MATAR MUKHTAR
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
FIKRA WRITERS ASSOCIATION
BABI NA BIYAR
05
.....Suna fitan ta koma ta zauna, kafin ta gama gyara zamanta wayarta ta fara waka don haka ta mike ta dauko wayar.
Tana kallon screen din wayar ta fara murmushi, kawartace Karimatu Jibril Saminaka. Tare sukayi karatu a KADPOLY, bayan sun gama kuma aure ya dawo da su Kano gaba daya wanda ita Safiyya dama 'yar Kano ce karatun ne ya kaita Kaduna.
Tana murmushi ta kara wayar a kunnenta
'Kawata ta kaina.'
Kamar nai gaggawa ta bata amsa
'Um kawata ya weekend? Ki bude Whatsapp na turo miki message, ki duba yanzu don Allah.'
'Allah kawata, bari nayi sauri ma gaisa a can.'
'Yauwa.'
Ta ajiye wayar tana dariya ta san yanzu haka wata gulmar ce take son yi mata kuma maigidanta yana kusa, don sun saba haka. Ta dauko katin da aka siyo mata tun safe ta sa a wayar sannan ta sayi data din MTN ta naira dari biyu, nan da nan kuwa ta kunna ta hau Whatsapp.
Mintuna kadan sakonnin suka gama shigowa, a kan idonta sakon kariman ya shigo don haka nan da nan ta bude.
Video ne guda daya sai kuma rubutaccen sako a kasan video din
"Wannan ba Abban Nurain bane?"
Gabanta ya fadi, bugun zuciyarta ya kara sauri yayinda ta zaku sakon video din ya gama sauka. To shi kuwa Abban Nurain me ya faru da shi Karima take tambaya?
Kafin ta bawa kanta amsa videon ya gama sauka ba tare da bata lokaci ba ta bude, tana kalla bugun zuciyarta yana kara gudu hawaye yana bin fuskarta.
Tabbas Abban Nurain ne, yau ne ma wannan don kayan da ya fita dasu ne kuma bai taba saka su ba sai yau din.
A tsaye suke
08, January 2025
Nafisa
I cant download the book