Showing 36001 words to 39000 words out of 92582 words
a waje.'
Ya mike shima ya mika mata waya yace
'Ki sa min lambarki ma gaisa kafin na dawo gobe.'
Ta karba ta saka masa lambar tana fadin
'Ba gobe za ka dawo ba sai wani satin, rana i ta yau kenan.'
Ya kalleta yana jijjiga kai
'Haba dai, kullum fa sai na zo unguwar nan hira kinga kuwa ai ya kamata in na zo ko gaisawa ne muyi.'
'Ka bari dai wani satin.'
Yayi murmushi yace
'To ai shike nan, yanda kika ce haka za ayi.'
Sukayi sallama ta shige gida shi kuma ya tafi.
Tana shiga gida ta tarar da Umma tana jiranta a falo
'Umma na dawo.'
Fara'ar da Umman takeyi ne ta bawa Safiyya mamaki domin ta dade bata ga Umma nayi mata murmushi ba, kafin ta gama mamakin Umma tace
'Yauwa, wane yazo?'
Ta sunkuyar da kai
'Ban san shi ba Umma, ya ce sunanshi Sulaiman.'
'To don Allah ki mai da hankali tunda dai shi Abban Nurain din ya ki dawowa, Allah ya tabbatar da alkhairi. A hankali za ki fahimci manufarsa sai ku daidaita.'
Ta yiwa Umma sai da safe ta wuce daki don ta kwanta. A halin yanzu bata shirya wata soyayya ba don bata ma san me take so ba, amma ko don saboda ta rabu da tsangwamar Umma duk wanda ya fito hakura zatayi ta aureshi kawai.
KARSHEN BABI NA GOMA SHA SHIDA.
MATAR MUKHTAR
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
FIKRA WRITERS ASSOCIATION
BABI NA SHA BAKWAI
17
Tun bikin yana saura kusan wata daya Mukhtar da Jamila suka fara daukan hotuna don shagalin bikinsu, ya riga ya kammala gininsa don haka shirye-shiryen biki kawai ake yi.
____
Kamar yanda ya zamar mata jiki tana zaune a daki ita kadai domin Hamida bata dawo daga makaranta ba kuma lokacin abincin dare bai yi ba balle ta shiga kicin. Wayarta ce a hannunta ta bude Whatsapp tana karatun littafin hausa; ta samu jiya Sabir ya siya mata kati ta sayi datar naira dari. Kiran Maman Ashraf ne ya katse mata karatun; sun kwana biyu basuyi waya ba, ita kadai ce suke magana a cikin makotanta na da tun bayan rabuwarta da Mukhtar, kuma sai ya kasance Ashraf da Nurain tare aka saka su a makaranta kuma ajinsu daya.
Bayan sun gama gaisawa Maman Ashraf tace
'Ya jikin Nurain kuma?'
Cikin mamaki tace
'Nurain kuma? Bashi da lafiya? Ai ban san ma bashi da lafiya ba.'
Murya a sanyaye Maman Ashraf din ta amsa
'Aah baki sani ba? Ai wancan satin ma gaba daya Ashraf yace bai je makaranta ba, gashi wannan satin ma yau Juma'ah har yau bai jeba. Kuma yace Abbanshine ya je ya cewa Anti bashi da lafiya.'
Mamakinta ya karu da taji har an kai sati guda yana kwance amma ba'a gaya mata ba, murya a sanyaye tace
'Ikon Allah, kuma kinga babu wanda ya gaya min duk da dai suna wajen Hajiya kin san.'
'Eh mana na zata kin sani shi yasa nake miki jaje.'
'Yanzu dai da na sani zan je na gani.'
Suka cigaba da hirarsu, a nan ne Maman Ashraf take sanar da ita Mukhtar tashi zai yi saboda mutum daya ne suke hayar gidajen wajensa shi ya gaya musu nan da wata biyu za a saka sabon dan haya.
Suka gama waya suka yi sallama suka ajiye.
Tunda taji Nurain bashi da lafiya ta kasa samun nutsuwa, so take kawai taje ta ganshi. Sama da sati guda ko makaranta baya zuwa amma ko su gaya mata, ciwo idan na ajaline kenan sai dai ta tarar da gawa? Lallai mutan gidansu Mukhtar basu kyauta mata ba. Ta dauki wayarta da take kan cinyarta, ta shiga lalubo lambar Aminu ko Saifullahi domin ta kirawo taji jikin nasa. Har ta samo lambar Saifullahi sai kuma ta sake shawara; gara kawai ta bari zuwa gobe ta je ta duboshi. Sai dai kuma bata da kudin mota kuma ta san in dai tace Umma ta bata sai ta sha gori da mita, bata son ta tambayi Yaya Habibu saboda yana iya bakin kokarinsa sai dai ko nawa ya bata Umma sai ta karbe. Wasu zafafan kwalla suka zubo daga idanunta; Allah ya kawo mata mafita, miji ya saketa ya rabata da yaranta, kullum ta tuno yaran nan sai zuciyarta tayi ciwo amma bata da zabi. Wani lokacin ma ta kan gode Allah da bai korota da yaran ba su zo suga yanda aka mayar da ita mai aiki, gara suyi zamansu a can watakila sa fi walwala.
Sai da daddare sannan take sanar da Umma Nurain bashi da lafiya, suka zauna suna ta jaje itama Umma ta nuna bacin ranta a kan rashin gaya musu. Sai dai Safiyyan ta kasa gayawa Umman cewa tana son zuwa ta duboshi saboda yanda take tsoron bakaken maganganun da Umman take yawan gaya mata. Haka ta tafi ta kwanta cikin matsananciyar damuwa tana neman mafita a wajen Allah.
Washegari ya kama ranar Asabar, suna zaune wajen karfe sha daya na safe sai ga Yaya Habibu. Bayan an gaggaisa ya cewa Umma daurin aure yazo nan kusa shine ya karaso, suka zauna suka cigaba da hira a falon Umman. Jimawa kadan ya dubi Safiyya sannan ya dubi Umma yace
'Umma wannan yarinyar sai ramewa take kamar ana tsomen shayi da ita, ko Mukhtar din ta sa a ranta haka?'
Umma ta tabe baki tace
'Wane Mukhtar da ta daina zancensa, damuwa dai tata wadda ita kadai ta sani. Ko kuma don an ce mata Nurain bashi da lafiya ne ban sani ba?'
Ya dubi Umman da mamaki
'Ah, Nurain bashi da lafiya? Tun yaushe kenan?'
'Ina jin zai kai sati kusan biyu don an ce mata wancan satin gaba daya bai je makaranta ba ga wannan satin ma haka.'
Ya dubi Safiyyan yace
'Subhallahi, shine baki gaya min ba? To an je an dubo shi?'
Umma tace
'Wace dubiya, ai babu wanda ya gaya mana rashin lafiyar ma itama a gari ta tsinta.'
Ya sake duban Safiyyan
'Ikon Allah, ai sai ku tashi muje yanzu na kaiku a dubo shi. Ai muma danmu ne ko sun kirawo mu ko basu kirawomu ba dole ne muje, je ki shiryo muje.'
Ya dubi Hamida da Sabir da suke zaune yace
'Kuma ku shirya muje gaba daya ai ba dadewa zamuyi ba.'
Ya sake duban Umma yace
'Yanzu zamu dawo Umma.'
'To, kwa gaishe min da shi. Ka saya mishi gugguru a hanya kace masa in jini.'
'To Umma.'
Suka yiwa Umma sallama suka kama hanya a motar Yaya Habibu.
Saida suka tsaya a hanya Yaya Habibu ya cika musu leda da ayaba da apple, kuma ya sayi gugguru na Naira dari biyar sannan suka wuce.
A bakin gate ya tsayar da motar ya dubi Safiyya yace
'Ku shiga, minti goma sha biyar na baku ku fito mu tafi. Ku gaishe min da Nurain din da Nana.'
Suka amsa suka shige gidan.
Sosai aka karbesu a wajen Hajiya kamar wasu manyan baki, bayan sun gaisa Hajiya tace
'Sai da suka gaya miki ko? Cewa nayi su kyaleki idan ya sami lafiya a kawo miki shi kada su daga miki hankali. Yana sama wajen Baba yana ta surutu shi da 'yaruwar.'
Kafin ta bata amsa kuwa sun shigo da gudu shi da nana kowa da alawa a hannunsa wadda Baba ya basu, nan take suka fada jikinta suna ta murna. Ta dubi Nurain tace
'Ya jikinka Nuraini?'
'Na warke harma Baba yace Monday zan je makaranta.'
Nana tayi caraf tace
'Kuma yayi kukan allura.'
Ya harareta yace
'Mama ai kin san allura da zafi ko? To ma na daina kula Baba Aliyu shi yake kaini ana yi min me zafi, don haka nayi fushi dashi.'
Tayi dariya tace
'Hakuri zakayi ai tunda ka warke, za ka ga shima Baba Aliyun ba zai sake kai ka allura ba.'
Ya jijjiga kai yace
'Hmm, baki san shi bane Mama.'
'To ku tashi Baba Sabir ya kaiku waje ku gaisa da Daddy din su Sayyid sai mu tafi.'
Nan da nan kuwa suka mike suka nufi wajen Sabir wanda ya kama hannun su suka fice. Ta tura ledar da suka je da ita gaban Hajiya tace
'Gashi Umma tace a kawo.'
'To an gode, Allah ya bar zumunci. Don Allah ki gaishe min da Umman sosai.'
'In sha Allah.'
Jimawa kadan suka mike ita da Hamida suka yiwa Hajiyan sallama, ta dubi Bahijja wadda itama take zaune a wajen tace
'Anti Bahijjan taso muje ki dauko 'yarki don na san yanzu haka tace sai ta bimu.'
Ta mike tana dariya ta bisu suka wuce, suna gaba ita da Hamida yayin da Safiyyan ke biye da su a baya. Sun kusa isa gate din Mukhtar ya turo kofa ya shigo gidan, a takaice Hamida ta gaisheshi suka fice ita da Bahijja.
Yana kai idonsa suka hada ido da Safiyya, suka kasa kawar da ido na dan lokaci. Tayi dan gajeran murmushi ta sunkuyar da kai tace
'Ina wuni.'
'Uhm, lafiya kalau ya mutanen gidan?'
'Lafiya kalau. Ya jikin Nurain? Shi muka zo dubawa daman.'
'Eh haka Yaya Habibu ya ce min, ya sami lafiya ai.'
'Allah ya kara lafiya, bari na je suna jirana.'
Ta wuce shima ya wuce ciki, sai da ya waiwayo ya kara kallonta kafin ta fice daga gate din. Duk da hijabin da yake jikinta ya hango yanda ta rame sosai domin idanuwanta ma duk sun nuna. Gashi tayi wani baki da kuraje a fuskarta, ya jijjiga kai kawai. Shi dama ya san zawarci wahalace kawai, haka kawai ta saka masa ido sai da ta sa ya sake ta ai gashi nan ta janyowa kanta. Wa ma zai hadata da Jamila, lallai ya sake tabbatarwa a halin yanzu Jamilan ce ta dace dashi. Gashi bashi da ra'ayin zama da mace sama da daya da sai ya dawo da Safiyyan, yanda yake son Jamila ma baya jin zai iya yi mata kishiya don haka itama Allah ya bata wani mijin ta aura.
..........
Tunda suka zauna a mota Safiyya ta kasa cewa komai, ganin da ta yiwa Mukhtar ya taso mata da kewarsa da take ciki. Kafin su kai gida suka ga Yaya Habibu ya tsaya a Sahad store, gaba daya suka shiga yace Hamida da Sabir kowa ya dauki abu daya ita kuma Safiyya yace ta dauki abubuwan da take bukata.
Tabbas da ace kafin su hadu da Mukhtar ya kawota da sai ta fi jin dadi, amma duk da haka ta samu ta dauki pad guda uku, turare, man shafawa da ribbon da kanshi ya debar mata chocolates guda Huda da yoghurt, ya biya kudin sannan suka wuce gida.
Suna shiga gidan Hamida ta yi sauri ta dora abincin rana don ta san in ta bari Umma cewa zata yi Safiyya ta dora kuma ta kula da yanda Safiyyan ta shiga damuwa.
Ita kuwa Safiyya suna shiga ta wuce daki ki mayafi bata ajiye ba ta fada kan gado. Allah ya sa Mukhtar yana jin yanda take ji. Tayi sauri ta kawar da tunanin don bata son abinda zai saka ta cikin damuwa. Haka ta wuni babu sukuni, ita Umma tana tunanin ko don ta gano yaran ne take kewarsu don haka tayi banza da ita.
Tana idar da sallar isha'i ta kwanta don ko abincin dare bata iya ci ba. Bata fi minti goma da kwanciya ba wayarta ta fara kara, ta sakankance Mukhtar ne don haka da hanzari ta dauka. Tana dubawa taga Sulaiman ne; tayi tsaki ta mayar da wayar ta ajiye a gefen filonta. Ta mayar da idonta ta rufe ta cigaba da tunanin Mukhtar tana fatan bacci ya dauketa. Sai da Sulaiman ya kirawota wajen sau goma bata daga ba don daga karshe ma a silence ta saka wayar ta koma ta rufe idonta. Tana ji Sabir ya shigo dakin ya zo har daf da gadon yana kiranta a hankali amma tayi shiru kamar nai bacci don haka ya fita.
Gaba daya ta manta ta cewa Sulaiman ya zo yau, don haka kiran da yake mata yana tsaye ne a kofar gidansu. Da ya gaji da kira ya turo Sabir kuma haka ya koma yace masa tayi bacci, ya wuce ya barshi a nan. Ranshi yayi matukar baci saboda da safe suka yi waya tace yazo yau shine zata yi masa wulakanci; yana da matarsa don haka ba zai dau wulakanci daga wajen wata bazawara ba musamman da yake jin rufa mata asiri zai yi ya aureta. Ya tuka motarsa yayi gaba da niyyar ba zai sake zuwa wajen Safiyya ba don shi baya juran wulakanci.
Har wajen goman dare da Hamida tayi bacci ita tana kwance tana juyi. A karo na babu adadi ta gyara filonta ta gyara kwanciyarta, ta ji danshi a fuskarta sai da ta kai hannu ta shafi idonta sannan ta tabbatar kuka takeyi. Tun safe take rike hawayen don ta riga tayi alkawarin ta daina kuka a kan Mukhtar amma ta kasa jurewa don haka ta saki hawayen gaba daya. Tana kewar mijinta, da yanzu tana jikinsa tana bacci. Tabbas da ta san yi masa magana zai janyo mata wannan damuwar da bata yi ba, da ta barshi ya cigaba da yawonsa tunda dai duk tsiya da ita zai kwana.
Ta Kai hannu ta dafe zuciyarta wadda take ta bugawa da sauri, Allah ya sa dai Mukhtar ya zo su mayar da aurensu, ko babu komai ta zauna itama da nata 'yayan kuma Umma ta daina jin haushinta. Ta lalubo wayarta ta kunna data dinta wadda ta riga ta kasheta kafin ta kwanta, so take ta duba ko zata ga hoton Mukhtar da yake kan dp dinshi na Whatsapp don tun bayan da tayi barin nan ta goge duka hotunansa daga wayarta. Sai kuma ta tuna ashe tayi blocking dinsa a WhatsApp don haka ta lalubo lambar ta bude blocking din da ta yi masa. Ta gyara kwanciyarta ta mayar da idonta ta rufe.
KARSHEN BABI NA GOMA SHA BAKWAI.
MATAR MUKHTAR
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
FIKRA WRITERS ASSOCIATION
18
Zuwa yanzu su Fatima saura 'yan watanni su gama bautar kasarsu, don haka ta sanar da shugaban makarantar da take aiki a kan zata cigaba da koyarwa kyauta zuwa lokacin da zata sami aiki ko kuma lokacin da Umma zata barta ta fara masters.
Dawowarta kenan daga aiki ta ajiye jakarta a kan mudubin dake dakin, har ta juya ta nufi bandaki ta jiyo karar wayarta daga cikin jakar don haka ta dawo ta dauka. Tana dubawa taga Janan ce don haka da murmushinta ta dauka, tana kara wayar a kunnenta tace
'Kawata mutanen Minna.'
Itama tayi dariya daga daya bangaren tace
'Aminiyata kenan, ya Zazzau? Ya Mama?'
'Lafiya kalau, ya angonki? Ya bakunta kuma? Ko da yake yanzu ai kin saba kin zama Uwargida ko?'
Sukayi dariya gaba daya
'Ke kika sani tunda dai kin kasa ziyarata.'
'Kin san dai Mommy bata barina fita wallah, amma zan zo in sha Allah.'
'Yanzu dai ba wannan ba, ranar Asabar din nan zanzo gida. Adnan yana da daurin aure a KD don haka zai kawo ni idan ya gama sai ya dauko ni mu koma kinji ko.'
Sai da tayi ihu da tsalle sannan tace
'Allah kawata, kai gaskiya na ji dadi wallahi.'
'Kamar gaske, ki dai ajiye min abun dadi kuma da sassafe zaki ganni sai na zo nan zan yi breakfast don na tara zafafan labarai duk da ma ina jin haushin ki shegiya.'
'Allah sarki kawata to ni din kuma me nayi?'
'Idan na zo kya ji.'
Suka karasa hirarrakinsu suka yi sallama suka ajiye waya.
Ta ji dadi da Janan tace mata zata zo, ita kadai ce kawar da ta rage suke zumunci duk da tayi aure. Ragowar kawayen nasu da sun yi aure suke daina kulata da yake ita kadai ce tayi saura a kawayen nasu batayi aure ba.
A falo ta sami Mommy bayan sallar isha'i tana zaune ta kunna TV tana kallon tashar Aljazeera kuma tana rike da waya, ta nemi guri a kan kujerar zaman mutum uku kusa da Mommy din ta zauna. Bayan sun dan taba hira tace
'Mommy jibi Janan zata zo?'
'To Allah ya kaimu, daga Minna din zata zo ina maigidan nata?'
'Shine ma zai kawota ai, idan ya gama abinda zai yi a Kaduna sai ya dawo ya dauketa su tafi.'
'Allah sarki, Allah ya nuna mana. Ai gara ta zo tayi miki fada kema ki dage ki fito da miji kina nan zaune muna hada kafada ga kawayenki nan duk suna gidan mazajensu.'
Tayi murmushi ta sunkuyar da kai ba tare da tace komai ba yayinda mommy ta mayar da hankalinta ga kallon TV.
Ta riga ta saba kawo yanzu duk wata dama da Mommy ta samu sai ta yi mata gorin aure, ta gode Allah Mommy tana da seminar ranar Asabar din don haka ta san ba za su hadu da Janan din ba. Domin yanzu duk wata kawa ko 'yaruwa da take shiri da ita idan Mommy ta ganta sai tace 'ki yiwa kanwarki fada itama ta fitar da miji' don haka yanzu bata ma so Mommy ta hadu da kawayenta ko cousins dinta masu aure. Hirarsu ta daina tsawo da Mommy saboda bata son gorin da Mommy take yi mata, itama tana son auren, zaman hakan ya dameta. Gashi ta saba Mukhtar ya mayar da ita kamar matarsa don haka lokaci zuwa lokacin tana jin bukatar kasancewa da namiji; dagewa kawai takeyi tana bawa kanta hakuri saboda bata so ta sake maimaita kuskuren da tayi a baya.
Ta dago ta dubi Mommy tace
'Bari naje nayi sallar isha'i Mommy.'
Ta wuce ta barta a nan.
Tana shiga dakin ta fada kan gadonta a rub da ciki, hawayen da ta kasa denawa ya kwace mata. A haka bacci ya kwasheta da yake dama ta riga tayi sallar isha'i dinta tun kafin taje wajen Mommy.
Can wajen goma na dare Mommy ta taso daga falo, zata wuce dakinta ta hango fitilar Fatima a kunne don haka ta tura kofa ta shiga dakin. Ta
08, January 2025
Nafisa
I cant download the book