Showing 63001 words to 66000 words out of 92582 words

Chapter 22 - MATAR MUKHTAR COMPLT

SAKINA   

16 Aug 2024

7162

rabasu da inda jirgin ya sauka. Haka kawai ya ji ta burgeshi sai dai bai kawo komai ba. Yana shigowa ciki kuma ya ganta da su Mommy ya ji ta kara burgeshi, take ya ji in dai zata aureshi to zai iya aure yanzu. Har zai fito daga wajen sai kuma ya ga gara dai ya koma ya karbi lambar ta, don haka ya sami waje yace da Hafiz ya zauna zai je ya dawo. Shine ya dawo ya tare Ibrahim suka yi magana.

Tun safe suka kamo hanyar Zariya domin daga nan Auyo zasu wuce ya kai Hafiz gida. Ya tsaya a gidan abokinsa nan Zariya ya ajiye Hafiz sannan ya karasa gidan su Fatiman shi kadai.

Ibrahim ya kirawo don haka shine ya kirawota ya sanar da ita zuwan bakonta, ya riga ya gama yiwa Mommy bayani don haka ba tare da bata lokaci ba Fatiman ta fito wajen Ahmad.

Tunda ya hango fitowarta daga gidan ya fito daga motarsa ya mayar ya rufe ya jingina da motar, ya kafa mata ido yana ta wani murmushi. Ya saka ta jin kunya sosai don haka da kyar ta daure ta karasa. Bayan sun gaisa tayi masa iso cikin gida, suka zauna a falo. Da kanta ta tashi ta kawo masa ruwa da lemon; domin da ko ruwan bata yi niyyar bashi ba. Amma yanda ta ganshi ya zarta tunaninta, ba wai kyau yayi da yawa ba amma yayi kwarjini kuma ga kamala duk ya cika mata ido.

Ta ajiye masa ruwa da lemon ta zauna suka dan taba hira, kafin wani lokaci an kulla soyayya mai karfi.
..........

Tuni abubuwa suka dawo dai-dai tsakanin Jamila da Mukhtar, duk da har yanzu tana sane da yanda ya sa mata ido. Ita din ma nata idon yana kansa, domin tana sane da yanda har yanzu duk Juma'a sai ya je Zariya sannan kuma tana zargin 'yan matan nasa sun kara yawa domin yanzu harda wata wadda take tunanin sunanta Felicia duk da yayi saving sunan da Felix ne. Ga kuma wata wadda take tunanin kamar irin sugar mommies din nan ce, domin ita idan suna waya har wani rusunawa yakeyi kamar wata uwarsa.

Duk wannan abun in yana falo aka kirawoshi daki yake komawa amma haka take bin bayansa ta labe a kofa shi yasa ta san halin da yake ciki. Duk ta kwafe lambobinsu, lambar sugar Mommy din ne kawai bata samu ta kwafa ba saboda ya canza pattern din bude wayarsa wanda har yanzu take kokarin ta gane.

A halin yanzu wadda take Zariya itace ta tsaya mata a rai domin ta gaji da wannan abun, ko me zata ce masa sai ya je Zariya ranar Juma'a. Har karyar rashin lafiya tayi masa ranar wata Juma'a amma haka ya yi mata wayo ya wuce ya tafi Zariya.

Yau Alhamis don haka ta san gobe zai ce zai je Zariya, ta gaji da wannan abun hakurinta ya kare musamman a kan wannan yarinyar don haka dole yau ta dauki matakin da ya dace.

Tun safe da ya tafi office take bitar abubuwan da zata fada, bata sami dama ba har sai bayan la'asar. Ta kwantar da Halimatu wadda ta riga tayi bacci sannan ta sallami mai aikinta wadda dama zuwa da dawowa takeyi; ta rufe gidan ta dawo falo ta zauna. Ta dauko takardar da ta kwafi lambobin ta kwafe lamabar da take tunanin itace ta Fatiman. Bata jima tana ringing ba aka dauka, ta danyi jinkiri magana don haka daga daya bangaren aka ce

'Hello, Salam alaikum.'

Duk da natsuwar da ta ji a muryar ta rage mata karsashin yin masifa amma cike da isa ta amsa

'Wa alaikumussalam.'

Ta numfasa sannan tace

'Fatima nake nema.'

'Nice Fatima, sai dai ban ganeki ba saboda bani da wannan lambar.'

So take ta fara ruwan asharan da bakaken maganganun amma bakinta yaki bawa zuciyarta hadin kai, gashi kuma natsuwar da take muryar Fatiman tana nema ta sa mata natsuwa itama. Ta bada amsa cikin isa tana batsewa

'Ba zaki gane ni ba domin dama baki sanni ba, Sunana Jamila, kuma nice matar Mukhtar. Na san yanzu kin gane ni.'

Fatima taji wani banbarakwai, ta tashi daga kashingidar da tayi ta zauna ta zuba kafafunta gefen gadon da take, ta danyi gyaran murya cikin karfin hali tace

'Allah sarki, kwarai na ganeki. Ya gida? Ya Halimatu da su Nurain?'

Cikin isa ta amsa tana ta wani gatsine fuka kamar wadda take a gaban Fatiman

'Ba shi na kirawo ki muyi ba. Kiranki nayi na baki shawara kuma na gargadeki, Ina so ki rabu da mijina. Duk wani iskanci da kike yi ina sane dashi, ki rabu da mijina ki nemi naki tun kafin dare yayi miki don bana son nayi abinda ke da shi za kuyi nadama. Na gaji da raini da wulakanci.'

Sai da ta numfasa sannan Fatima tace

'Allah sarki, ai mun bar iskancin ma tun tuni. Sai dai shi mijin naki bani na kirawoshi ba shi yake kawo min kansa don haka ya rage naki ki hanashi zuwa inda nake....'

'Au h...'

Jamilan ta fara magana zata katseta don haka itama Fatima ta dan daga murya ta katseta ta cigaba

'Yanda na saurareki kema hakuri zakiyi ki saurare ni. Ni dinma zan baki shawara, mijinki serial mazinaci kuma bana jin zai iya dainawa sai dai ko in ya kasa don ko ke bana jin zaki iya hanashi. Ni din kuma ba zan auri mijinki ba, kema da Allah ya jarrabeki da zama dashi ina fatan Allah ya kawo miki mafita.

Nayi miki alkawari daga yau ba zaki kara ji mijinki ya zo Zariya wajen na ba; sai dai da yake ni kaina na jima ina zargin in yazo wajena akwai wadda yake zuwa wajenta nan cikin Zariya ko Kaduna to watakila ki ji ya cigaba da zuwa, amma ni nayi miki alkawarin daga yau ba zaki kara jin mijinki yana zancena ba.'

Ta dan tsagaita ko Jamilan zata ce wani abu, taji shiru sai numfashi kawai take ji don haka ta cigaba

'Na barki lafiya. Ki Shafa min kan Halimatu; Allah ya rayata yayi mata albarka.'

Ta katse wayar ta ajiye.

Ta jefa wayar kan gadon ta mike ta nufi tagar dakin, ta daga labulen tana hango waje sai dai ba ganin abinda yake wajen takeyi ba tunani kala-kala a ranta. Dama ta gaji da dakon soyayyar Mukhtar kuma ta gaji da dakon zoben da yake hannunta, tunda suka daidaita da Ahmad take son rabuwa da Mukhtar din sai dai da tayi niyyar ta wanke shi a karo na karshe.

Jamila ta bata tausayi sosai, tabbas ta san ba zata iya zama matar Mukhtar ba. Ahmad zata aura, sai dai abu daya take tsoro yanda zatayi idan ya gane ita din ba ta kai budurcinta ba tunda ya san bata taba aure ba.
Amma tana nan tana addu'a kuma tana da yakinin Allah zai amsa mata rokonta, domin zaman aure take so tayi mai tsabta da aminci.

Ta dago hannunta ta kalli zoben da Mallam ya bata, ta gaji da zoben sosai. Kuma dama Mallam ya gaya mata duk lokacin da ta cire wannan zoben soyayya ta kare. A hankali ta zare zoben daga yatsanta, ta zubawa zoben ido tana kallonsa. To yanzu ya zatayi ma da zoben?

Tana nan a tsaye da zoben a hannunta dabara ta fado mata, don haka ta saka hijabinta ta fice daga dakin. Ta lallaba ta leka dakin Mommy ta hangota tana kwance a kan gado don haka cikin sanda ta fice ta nufi boys quarters inda dakin Baba Habi yake. Tana shiga taga dakin a rufe don haka ta san Baba Habi bata nana, nan da nan ta shiga bandakin wajen wanda yake da masai irin na kasa din nan. Ta jefa zoben a ciki ta tari ruwa cikin bokiti a famfon bandakin ta kora. Tayi sauri ta fito ta kamo hanyar cikin gidan.

Haka kawai taji zuciyarta ta washe, ta manta rabon da ta jita a cikin irin wannan walwalar domin har ji take kamar ta rage nauyi. Tana shiga daki ta ta turo kofa ta jingina da bayan kofar, ta daga kanta ta dafe kirjinta ta bude baki a hankali tace

'Alhamdulillah.'

Haka kawai kuma sai taji hawaye yana bin fuskarta, ta saka hannu ta goge tana murmushi. Ta karasa gefen gadon ta zauna; tuba ma ya kamata tayi domin ta san wannan abun da tayi sabon Allah ne, don haka dole ta tuba kuma tayi addua Allah ya tabbatar da aurensu da Ahmad kuma ya sa musu albarka a ciki.

Ta kwanta rigingine a kan gadon zuciyarta cike da farin ciki.

KARSHEN BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS.

MATAR MUKHTAR

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

BABI NA ASHIRIN DA TARA

29
Fatima tana tsinke kiran Jamila ta saki tata wayar wadda ta fada kan cinyarta, ta hada tafukan hannunta ta rufe fuskarta. Tana cire hannun sai hawaye, ta maida hannun ta dafe kirjinta wanda yake mata suya a halin yanzu. Ta kasa daina jin muryar Fatima tana maimaita mata abinda ta gaya mata

'Mijinki serial mazinaci ne, ba zai daina ba...'

Ba wai maganar ce ta bata mata rai ba, amma ashe yanzu abinda Mukhtar yake yi ta kai har 'yan matan nasa sun sani?

To kenan shi yanzu a duniya babu wanda zai gaya masa gaskiya?

Ta gayawa yayarta yana neman mata, ta gayawa kanwar babarsu har dama maman nasu ta gayawa amma kowa cewa yake tayi hakuri. Yanzu kenan haka zata nade hannu ta cigaba da kallonsa yana yanda yake so? Ya kwana da karuwai ya kwana da ita gata nan kullum cikin shan magani take saboda bata rabuwa da ciwon sanyi.

Gaba daya tunaninta ya kare, ta ma rasa me zata yi. Duk da haka dai ta ji dadi da Fatima tace ta yi alkawarin ta rabu dashi, kuma tana ji a jikinta kamar ba karya Fatiman tayi mata ba don haka sai ta danji sanyi a ranta.

A wannan zaman da tayi niyya tayi bayan ta kirawo Fatima ta kirawo Felicia, amma Fatima ta kwance mata lissafi don ta zata za ta sami dama tayi rashin mutunci. Don haka ta bari sai wani lokacin sai ta kirawo Felicia. Yanzu dai zata zuba ido taga ko za a cigaba da zuwa Zariya, kuma zata saka a bibiyeshi aga inda yake zuwa.
.....

Har gari ya waye ranar Juma'a zuciyarta babu dadi, shi kansa Mukhtar din ya kula da haka. Yana sane ya share ta domin baya so ko daya ya nuna ya san tana da damuwa, domin yana tunani ko taga wani abune a wayarsa. Tun dare da ya kula da damuwarta yake faman duba wayar ko ya bar wani abu amma bai ga komai ba, don haka ya kyaleta.

A cikin walwala da nishadi yake, shima bai san dalili ba haka kawai yake jin ranshi fes don haka baya son ta gusar masa da farin cikinsa.
Nan da nan ya shirya yaci abincinsa na safe sannan ya yi mata sallama zai fita. Har ya kai bakin kofa sai kuma ya dan dawo ya dubeta tana tsaye a kusa da dining table da goyon halimatu

'Ki ajiye min abincin rana, zan dawo da azahar.'

Ta kalleshi da mamaki

'Ah yau ba zaka Zariya ba?'

'Eh, office kawai zan je.'

'Uhm! An gama kwangilar Zariyan kenan?'

Ya dan tsuke fuska ya kama hanyar fita yana bata amsa

'Eh, tun last week.'

Ya fice kafin ya amsa a dawo lafiyarta.

Ta ja tsaki ta murguda baki kamar yana kallonta tace

'An dai fadi ba nauyi, ba a jin tsoron Allah sai tsoron karuwa.'
.........

Tare suka gama cin abincin safe a falon Umma da yake Sabir da Hamida ma suna da lecture din safe. Safiyya ta dauki kofin shayin ta ta kurbe, ta daga kai ta kalli agogon bango wanda ya nuna karfe bakwai da minti goma. Ta mike tana fadin

'Bari nayi sauri na karasa shiryawa don na shiga kafin a fara tarar makara.'

Hamida ta mike da nata kwanukan a hannu tace

'Kawo na wuce da kwanukan kichin.'

Sabir ma ya mike da hanzari ya dora nashi kwanukan kan wanda suke hannunta yana fadin

'Yauwa yarinyar kirki, hada da wannan ma.'

Ta watasa mishi harara ta take masa yatsun kafa tana fadin

'Dan rainin hankali, waye sa'anka a nan me bakin baya.'

Ya wuce da gudu ya bar musu falon Safiyya tana bata hakuri.

Doguwar riga ta saka ta atamfa mai dogon hannu don haka ta dauki mayafinta matsakaici ta nade kanta da shi sannan ta tsaya a gaban mudubi tana kara goge fuska. Sabir ne ya shigo dakin da sallama

'Ya Safiyya kin shirya na baki lift a legedisbenz dita?'

Ta kyalkyale da dariya ta fara shafa lip gloss tana fadin

'A silifas dinka dai.'

Ya dan bata rai

'Haba Ya Safiyya, idan kika fada a gaban 'yan mata ai sai su raina ni.'

Ta kyalkyale da dariya ta dauko Jakarta ta wuceshi tana fadin

'To muje.'

Ya biyo bayanta suka fito yana fadin

'Kin ganki kuwa Ya Safiyya, koyarwarnan ta karbeki fa. Wallahi kin yi fes dake kamar Ya Safiyya, sai yanzu kika rabu da matar Mukhtar kika dawo 'yar gayunki kamar da.'

Suka yiwa Umma sallama Hamida ma ta fito suka kama hanya tare, idan suka je makarantar da take koyarwa sai ta shige ciki sunkuma su hau mota a nan.

Ko Sabir bai fada ba ta san ta koma Safiyyan da ta sani da. Ta yi fes da ita gashi wannan aikin ya sa ta kara sakewa kuma ga sutura yanzu duk gayunta ya dawo, duk wata ga albashinta ga kudin kitso wanda Sabir yake tattala mata. Ita kadai ta yiwa kanta murmushi a dai dai lokacin da take sa hannu a littafin signing na malamai.

Bata da aji da safe don haka bayan tayi kiran suna a ajinta sai ta koma ofishin malamai mata ta zauna ta fara sa hannu a litattafan 'yan aji daya da suka yi homework.

Ta zo kan littafin Muhammad Abdurrahman Anas, yaro ne dan shekara shida. Kullum in ta basu aikin aji tsaf yake aikinsa, amma idan aikin gidane to bazai yi ba. Kuma duk sauran malamai haka suke fama da shi domin su sun riga sun ce dakiki ne shi tunda su ko aikin ajin suka bayar baya yi, har malamar ajinsu ta shaida.

Bayan ta gama saka hannun ta dauki littafin Muhammad ta wuce wajen shugabar makarantar ta sake yi mata bayanin ya kamata a kirawo mahaifiyar yaron nan don shi ba dakiki bane, tana ganin dai akwai wata matsala ne ko daga gidan.

Shugabar makarantar ta dubeta tace

'Safiyya nifa ba zan kuma kiran matar nana ba, sai an aika mata sako sau biyar kafin tazo sau daya. Ta shigo tana wani yauki tana neman ta zagi mutane ita a dole ga mai ilimi. Shi kuma uban kullum aka kira shi yana Abuja, basu fa da lokacin yaran nan. Amma ki rubuta wasika ki basu su kaiwa iyayen, in ya so idan ta zo ke sai ki ganta don ni kam kar ta zo min nan.'

Tayi murmushi

'Hakan ma yayi Hajiya, in sha Allah yanda muka yi zaki ji.'

Ta fito ta koma office.
Sai da aka tashi sannan ta saka masa wasikar a jaka, tace masa idan ya je gida ya bawa mommy ko Daddy.
.....

Washegari da wuri ta shiga makaranta domin bata san lokacin da uwar Muhammad zata zo ba, amma ga mamakinta sai wajen takwas saura Muhammad din ya shigo. Yayansa wanda yake primary 5 shine ya rakoshi ajin, bayan sun gaisheta yayan Muhammad yace

'Anty Mommy tana Abuja amma daddynmu yace na gaya miki zai zo in an tashi.'

Duk da bata son abinda zai tsayar da ita idan an tashi haka ta hakura ta dan yi jinkiri, tana da masu yin kitso da yake yau Alhamis. Tana zaune tana nadamar aika wannan sakon mutumin ya shigo ajin inda suke zaune ita da Muhammad da wasu yaran, Yayan Muhammad yana biye dashi tare da Yayarsu wadda ita a secondary take JSS 1.

Cikin girmamawa suka gaisa, ya zauna akujerar da take gaban teburin da take kai. Cikin nutsuwa ta koro bayani bayan ta gama nuna masa duka litattafan Muhammad din, ta rufe da

'Muhammad yana da kokari fa, kawai dai baya yin aiki ne. Kuma ina ga yana bukatar kulawa ne kawai, shi yasa na so ace mahaifiyarsa ce ta zo domin itace yafi dacewa tayi wannan aiki.'

Yayi shiru na dan lokaci, jim kadan yace

'To Anti ki taimaka min mana ki dinga yi masa lesson after school, in ya so ko nawa kikace ni sai na biya.'

'Gaskiya ba ni da lokaci, sai dai a malamai zan duba maka zuwa gobe. In an samu zan rubuta maka note na bawa Muhammad din.'

Nan ya bata lambar waya yace ta kirawo shi idan an samu. Sukayi sallama kowa ya kama hanya.
........

Duk yanda Alhaji Abdurrahman Anas ya so ya cire Safiyya daga ransa abun yaci tura, da farko yana tunani bai kamata ya yi soyayya da malamar yaronsa amma daga baya dole ya hakura tunda shi aurenta yake son yi. Sai dai bai sani ba ko tana da aure ko bata da aure.

Yana da matarsa daya Barrister Amina Bala Rogo wadda take aiki da ma'aikata shari'a ta tarayya inda take aiki a kotun su dake Kano. Wannan aikin nata bata hada shi da komai ba, domin shi mijin nata ma yana tunanin idan aka ce ta zaba tsakanin aikinta da aure to tabbas zata zabi aikin nan. Yaransu hudu, biyu maza biyu mata. Kuma gaba dayansu bata da lokacinsu, masu aikinta guda biyu sune komai nasu.

Mafi yawancin lokuta idan ta fita sai karfe biyar take dawowa, wani lokacin kuma idan suna da case sai ta kai dare.

Shi kuwa Abdurrahman tun kafin ya aureta yake aikin civil defense kuma ba'a taba kai shi Kano ba, domin a halin yanzu ma Abuja yake aiki sai dai idan ya zo hutu.

Da kyar ya kyar ya daure ya koma Abuja, yana fatan

08, January 2025
Nafisa

I cant download the book

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login