Showing 9001 words to 12000 words out of 92582 words

Chapter 4 - MATAR MUKHTAR COMPLT

SAKINA   

16 Aug 2024

7144

sun kallon juna rike da hannun juna sun ta hira cike da matukar nishadi, ba a dai jin me suke fada saboda da alama daga nesa kadan aka dauki video din kuma a karkace ma wayar take. Ya kamo hannunta ya sumbata yayinda suka cigaba da magana, jimawa kadan kuma ya janyo kwankwasonta ya mannata a jikinsa suka yi murmushi sai kuma ya saketa suka kama hannun juna suka bar wajen.


Ta share hawaye ta sa hannunta na hagu ta dafe kirjinta


'Innalillahi wa inna ilaihi rajiun.'


Ta fada a fili. Wato Mukhtar gaba abun nashi yake yi tunda yanzu ta kai a kwararo ma yake rungumar 'yan mata. Ta sake kunna video din ta kara masa girma ta karewa fuskar yarinyar kallo; tabbas wannan itace Sucre. Ashe basu rabu ba goge lamabarta yayi kawai don yaudara?

Shigowar wani sakon na Karima ne ya katse mata tunani, ta dago wayar ta kalla. Hotone guda daya don haka nan da nan ta saukeshi. Suna zaune a kan kafet tare da wasu 'yan matan gaba daya sun sha kananan kaya, ga cake nan an yanka har ya dauka zai sa mata a baki. Da alama birthday ake yiwa ita Sucre din.

Wani rubutaccen sakon ya shigo


"Safiyya ko ba Mukhtar bane wannan?"


Ta share hawaye, sai yanzu ta tuna ya kamata ta tura amsar sakon don haka ta rubuta ta tura


"Shine Karima, haka ya mayar da kansa."


Kafin minti biyu wayar Karima ta shigo, kamar ba zata daga ba sai kuma ta canza ra'ayi. Me zata boye mata bayan ta riga ta ga komai, don haka ta amsa wayar ta kara a kunnenta. Kafin tayi magana Karima tace


'Safiyya wanna karuwar yarinyar da take tare da Mukhtar fa? Na dai san ba kara aure yayi ba don babu mutumin da zai fito da matarsa a haka.'


Ta share hawaye


'Um Karima ba wani aure wallahi tsabar wulakanci ne da rashin tsoron Allah. Kin san ban taba sanin mutumin nan yana neman mata ba Karima sai kwanaki lokacin da nace miki yayi hatsari a mota; wallahi sai a lokacin na sani kuma wannan yarinyar ce dai.'


Da mamaki ta bata amsa


'Ikon Allah! Kin ganmu birthday din Jawad muka zo yi a Minjibir park kawai sai ganinsu nayi, Ina jin birthday yake mata. Yanzu haka ma gasu can sai wani iyayi suke babu ko kunya, ko da yake bamu taba haduwa ba nima a hotuna na sanshi.'


A halin yanzu bata cikin yanayin da zata iya wani bayani saboda yanda zuciyarta ta cunkushe, don haka tace


'Uhm! Ki bari kawai Karima, za muyi waya zuwa gobe in sha Allah za ki ji bayani.'............

Domin jin yanda take kasancewa, ki turo kudin karatu

N800

7037834664
Opay Digital Services
Sakina Muhammad Yazid

Sai ki turo receipt ta wannan lambar
07037834664

BABI NA BIYAR ya sauka da zafinsa a telegram, BABI NA SHIDA yana tafe in an jima da yamma in Sha Allah.
MATAR MUKHTAR

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA SHIDA

06

Ta sake kunna video din tana kallo kamar wadda take neman wani abun a ciki. Wato dama inda za shi kenan ya ce mata daurin aure zai tafi? Wato birthday ma yakewa budurwa? Tun kafin aurensu tana yi masa happy birthday wataran harda 'yar kyauta amma shi kullum nuna mata yakeyi birthday babu kyau a addini don haka ita in nata yazo sai dai kawai yace mata happy birthday. Tunda sukayi aure ma baya ko tuna ranar haihuwar tata har abun ya daina damunta, amma shine ya kwashi budurwa bayan gari yana mata birthday.

Ta jefer da wayar a kan kujerar ta mike tsaye tare da dora hannunta a ka, ihu take so ta kurma ko zata ji sanyi a ranta amma bata so ta tarawa kanta mutane. Ta koma ta durkusa a gaban kujerar tana share hawaye. Wai dama haka ake auren? Shikenan yanzu ya daina sonta sai matan banza? Shikenan yanzu haka zata kare sauran rayuwarta?

'Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun.'

Ta fada a fili tana ajiyar zuciya, ta kwantar da kanta a jikin kujerar tare da runtse idanunta, ta cigaba da ambaton Allah don taga alama idan ta cigaba da tunanin nan zuciyarta zata buga gaba daya. Tana nan a haka dabara ta fado mata, ta tashi ta koma kan kujerar ta dauko wayar ta fara laluben Abban Nurain din a WhatsApp.

My love shine sunan da tayi saving lambarsa da shi, ta kalli sunan ta ja tsaki. Ta fara rubuta masa sako

'My love.'

Sai da aka dauki mintuna kamar uku sannan ya bude sakon, ba wai don yana so ya bude sakonta ba sai don ya san idan bai bude ba yanzu zata kirawo shi. Yana karantawa ya turo mata da amsa

'Yes matar Mukhtar.'

Ta ja tsaki a fili. Ta budo videon da Karima ta tura mata ta tura masa, minti biyu taga alama ya bude videon. Tayi murmushin takaici ta rufe Whatsapp din, dama so take ta tabbatar ya gani in ya so idan ya dawo ya ji bayanin ta.

Tana shirin mikewa daga wajen ta jiyo shigowar su Rukayya ta dawo da su Nana, tayi sauri ta goge fuskarta ta amsa sallamarsu.

Suna shiga falon nana ta fizge daga hannun Rukayya ta fada jikinta da gudu tana kuka tana fadin

'Mama kitso ne!'

Ta dauketa ta rungume tana bata hakuri. Jamila ta dubeta tace

'Anti kema fuskarki kamar kinyi kukan kitson.'

Tayi yake tace

'Kawata ce mijinta ya rasu yanzu muka gama waya shi yasa kika ganni a birkice.'

Cikin tausayawa tace

'Allah sarki, Allah ya ji kanshi Anti. Bari na tafi maggi zan siyowa Ummanmu.'

Ta fice ta barta a nan da yaran.
.............

Tunda ya bude videon nan da Safiyya ta turo masa ya shiga rudani, ya kalli samarin nan da suke zaune nesa kadan yaga harkarsu sukeyi kawai. Saurayi da budurwar nan ma suna nan makale da juna, ga masu yiwa yaro birthday yanzu ma su rawa sukeyi. Samarin nan da suke zaune kasa kan ciyawa kuma sun tafi daga inda suke lokacin suna tsaye shi da Fatima.

To waye ya dauki wannan video din ya turawa Safiyya? Duka mutanen dake wajen ma babu wanda yayi kama da wanda Safiyya ta sani, to ya akayi ta sami wannan video din? To ko sakawa tayi a dinga binsa?

Ya gaza amsa tambayoyin don haka ya dubi Fatima yace

'Ya kamata mu tafi ko? Kada magriba tayi mana a hanya.'

Ta kara kwantowa a jikinsa yayinda ya fara wasu waige-waige yana gyara zama

'Gaskiya ne Baby, ka ga zamu je shopping.'

Nan da nan suka fara hada kayansu suna zubawa a mota, ba tare da bata lokaci ba suka bar wajen suka kamo hanyar Kano.

Motar Mukhtar na tashi Karima ta ja tsaki ta dubi Suwaiba wadda suke tare tace

'Aikin banza mugu kawai, ya cuci kawata.'

Suwaiba tace

'Ai kam, da kin sani dai baki gaya mata ba.'

'Ba wannan tsakaninan da Safiyya dole na gaya mata ko don ta san irin zaman da zata yi da shi. Kana yawo a gari wai kai me miji ashe miji duk ya gama yin tsirara a wajen marasa mutunci. Mtsewww!'

'Ki bari kawai Ya Karima, Allah ya sauwake.'
Received at 10:43 AMReactions: 👍 3, 👏 1

Viewed 103 times

Suka cigaba da hidimarsu.

-------

Sai wajen karfe tara na dare sannan Mukhtar ya mayar da Fatima hostel ya kamo hanyar gida, hakan ma don ya kasa natsuwa sosai ne tunda Safiyya ta tura masa video din nan. Ji yake kamar ana binsa ana daukar mata hotunan abinda yakeyi.

Fatima ta so ya mayar da ita Zariya da kansa amma haka ya tsarata ya bata kudin mota a kan sai ya zo Zariyan. Yana tuki yana ta tunani kala-kala; tabbas idan Safiyya ta nemi fitnarshi yau din nan sai ta gane kurenta. Kuma sai ya ji dalilin da yasa ta sa ake binsa, dole sai ya koyawa yarinyar nan hankali don fitnarta ta fara isarsa. Ta sa masa ido daga tayi masa bincike sai kuma ta sa a fara binsa, ai dole ma ta canza hali in ba haka ba wallahi zai ci mutuncinta. Ya gama tanadin duk wani wulakanci da zai yi mata idan ya koma gidan.

A falo ya sameta tana zaune tana kallon tashar Zee World. Da kyar ya kakalo sallama sai wani muzurai yake yana shakar numfashi da kyar, tana kallonsa ya bata dariya. Ta danne ta fadada fara'arta ta amsa sallamarsa tare da yi masa sannu da zuwa. Ya amsa yana ta wasu muzurai, ya wuce dakinsa. Ta tashi tana 'yar dariya ta wuce kichin ta dauko ruwa kamar yanda ta saba idan ya dawo ta bi shi dakin. Ya riga ya shiga bandaki don haka ta ajiye ruwan a kan durowar gefen gado ta zauna tana jiransa, jimawa kadan ya fito daga bandakin ya wuce ya fara kokarin canza kaya ba tare da ya kalleta ba.

Sai da ta bari ya gama saka kayan sannan ta zuba ruwa a kofi ta tsaya a gabansa ta mika masa tana fadin

'Sannu da zuwa, ya gajiyar biki?'

Fuskarsa take kallo shi kuma yana ta kokarin kauce hada ido da ita, ya karbi ruwan yana fadin

'Alhamdulillah.'

Ya wuce ya zauna a gefen gadon ya kurbi ruwan ya ajiye a kan farantin, ta karaso ta zauna a kusa dashi tace

'Na sa maka abincin dare?'

Ya fara wani waige-waige kamar mara gaskiya, kafin yayi magana tace

'In kuma kaci kayan dadi a wajen dinner na bar tuwona mayi dumame.'

Yayi sauri yace

'Eh, ma ci dumamen.'

Gaba daya ma shi ya manta ashe ma ce mata yayi za suje dinner din auren da suka daura da safen. Ta mike tsaye tana fadin

'Bari naje na shirya na zo na kwanta.'

Kafin ya bata amsa ta fice daga dakin, ya bi kofar da kallo yana mayar da numfashi.

Gaba daya tayi masa kwarjin ya kasa yin fadan da ya shiryo zai yi, ya yi zaton zata fara tsiwa amma sai ya ga tayi kamar bata ga video din ba. To me yake faruwa ne? Ya fi so tayi rigima yanda zai yi mata kaca-kaca ya juya laifin kanta amma gashi ta basar.

Yana nan zaune ta dawo sanye da rigar baccinta tana rike da wayarta. Yana nan zaune a inda ta barshi, bayan ya amsa sallamarta ta karasa ta zauna a kusa da shi tace

'Ba yanzu za ka kwanta bane Abban Nurain.'

'Eh, sai an jima kadan.'

'Kafin nan nayi nisa a bacci.'

Ta zagaya ta kwanta a daya barin gadon daga bayansa, ta warware abun rufa ta rufe kafafunta. Ta gyara kwanciya ta juya masa baya, kwallar da take rikewa ta gangaro, ta ja abun rufar ta faki idonsa ta goge.

Ta riga ta gane duk ranar da yayi irin wannan fitar ba zai kulata ba saboda an riga an biya masa bukatar a waje, a da kafin ta gane abinda yake yi ta zata gajiya ce ta sa idan dai yayi dare bai dawo ba to baya bi ta kanta amma yanzu ta gane.

Yanda taga ya shigo gidan yana muzurai ya sa ta canza shawara, gara tayi kamar bata san an yi ba ta zuba masa ido taga iya gudun ruwansa. Ta riga dai ta gane muzuran da yakeyi duk don kada tayi wani wargi ne, to ta kyaleshi itama ta yarda yau kwanan Sucre ne ba nata ba. Kwalla ta sake gangarowa ta kara gogewa.

Ta jiyo kukan nana ta farka daga bacci tana yi tana kwala kira

'Mama.'

Kafin ta karasa mikewa Abban Nurain ya juya ya dubeta yace

'Ga Nana can tana kiranki.'

'Hmm! Na ji ta, yau rigima take ji Allah ya sa ta barmu muyi bacci.'

Ta sauka daga kan gadon ta dauki zaninta wanda yake ajiye a cikin wardrobe din dakin ta daura a kan rigar bacci ta fice.
Received at 10:43 AMReactions: 👍 1, ❤ 1

Viewed 101 times

MATAR MUKHTAR

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA BAKWAI

07

Ta so kwarai da gaske ace Mukhtar ne zai mayar da ita gida don tana so ya kara gaida Mommy taji daga bakinsa cewa nan da karshen wata zai turo maganar aurensu, amma babu yanda zata yi don ya nuna mata aiki ba zai barshi ba. Tun dare ta hada kayanta, kafin karfe takwas na safe ta bar hostel ta nufi tasha domin hawa motar Zariya. Karfe goma da 'yan mintuna motarsu ta kama hanyar Zariya, da yake a jikin kofar motar ta zauna hanya kawai take bi da kallo tana murmushi; ta san bazata sake zuwa Kano ba sai a matsayin amaryar Mukhtar.

Duk da ta san da farko Mommy bata so alakarta da Mukhtar ba saboda yana da mata, takan ce ina jiye miki zaman kishi Fatima gara ki auri saurayi kya fi samun natsuwa. Amma da ta dage kuma shima Mukhtar din ya je suka gaisa da Mommyn sai ta yaba da hankalinsa.

Su biyu ne a wajen iyayensu daga wanta Ibrahim sai ita, wanda shekaru takwas ne a tsakaninta da shi. Shekarar da ta wuce akayi auren Yaya Ibrahim don haka Mommy ta sake kwallafa rai a kan lallai tana son Fatiman ma ta fitar da miji.

'Ku biyu mahaifinku ya mutu ya bar min, yanda muka rabu da shi lafiya haka nake so kema na kaiki dakinki lafiya Fatima. Aurenki shine abu na karshe da zai faranta min rai.'

Haka Mommy take cewa duk lokacin da take maganar auren Fatima.

Ta kauda kanta daga kallon hanya lokacin da ta ji kwalla tana neman fitowa daga idonta sakamakon tunowa da Abbanta da ta yi. Abba yana sonta, yana matukar sonsu gaba dayansu ita da Yaya Ibrahim da Mommy. Ta sa hannu ta dafe kirjinta tana kokarin boye hawayenta saboda kada wadanda suke kusa da ita a motar su gane kuka takeyi. Mutuwa tayi musu yankan kauna, bata fi awa daya da gama waya da Abban ba ya gama yi mata fadan karatu yana cewa

'Ki mayar da hankali ki gama karatunki kin kinji Fati, Allah yayi miki albarka.'

'Amin Abba.'

'To maza ki je kiyi karatunki nima yanzu Kaduna za mu tafi daurin aure, Allah ya bada sa'ar jarrabawa.'

Sukayi sallama ta cigaba da karatunta tunda dama jarrabawa za suyi da karfe uku na yamma. Tana fitowa daga jarrabawa taga labarin rasuwar Abbanta a status din wani Jamil dan wajen amininsa, take ta sumewa su Janan. Da kayar suka riketa ta kwana saboda yamma tayi kuma Mommy tace ta zauna sai gobe za a turo a dauketa.

Ana sallame sallar asuba ta kasa jira don haka ta kirawo Mukhatar ya kaita Zariyan; haka ta rasa jarrabawa biyu wadanda sune na karshe kuma sune suka janyo mata spill over don a lokacin tana ajin karshe ne.

Wannan shine karo na farko da ya gaisa da Yayanta da Kuma Mommy.

Allah dai yasa kada su Mukhtar su ja bikin da nisa don a yanzu kam ta fi Mommy matsuwa da ta zama matar Mukhtar.

Kafin azahar ta isa gida, babu kowa a gidan sai mai aikin Mommy Baba Habi don haka da suka gaisa sai kawai ta shige dakinta. Da yake ta sanar da Mommy dawowarta Baba Habi ta riga ta gyara mata dakin, sai ta haye kan gadonta sannan ta kirawo Mukhatar ta sanar da shi ta isa gida lafiya. Ta kwaso hira yace

'Zan shiga meeting ne yanzun, idan na fito sai muyi waya.'

Da haka suka yi sallama suka ajiye wayar.

Sai bayan azahar Mommy ta dawo da yake malamace a makarantar 'yan mata. Fatima ce tayi mata oyoyo ta karbar mata kayan hannunta ta raka ta har dakinta.

Suna shiga Mommy ta cire mayafinta ta ajiye a kan kujera sannan ta wuce ta zauna a gefen gado, ta dubi Fatima da take zaune a kusa da ita tana murmushi tace

'Fatin Abba, an gama karatun ko?'

'Na gama Mommy in sha Allah duk da dai spill over din nan sai ta rage min points amma ina sa rai da 2-2 ko mai sanyi ce.'

Tana murmushi ta dafa kafadarta tace

'Babu komai Allah ya sa albarka, Allah ya nuna mana aurenki kuma.'

Tayi murmushi ta sunkuyar da kai, Mommy tace

'Ina Mukhtar din?'
Received at 11:16 AMReactions: 👍 3, 😁 1

Viewed 93 times

Koda suka gama hirar ma tana ajiye wayar ya ja tsaki ya mayar da wayar mazauninta ya ajiye.

Ta so ta bashi tausayi amma gaskiya ba zai iya aurenta ba, shi ba ya ma sha'awar zama da mace sama da daya. Kuma ko ta kama zai kara auren ma ba zai iya auren Fatima ba. Ya san shine ya bude mata ido don a budurwa ya santa, amma a yanzu ba zai taba amincewa shi kadai take bawa kanta ba duk da bai taba kamata da wani ba. Ba zai iya aurenta ba amma dai yana yi mata addua Allah ya bata miji na gari, don shi yanzu a rayuwarsa ma baya jin zai kara zuwa Zariya.

Ya karya mota ya shigar da ita farfajiyar gidansu bayan da Abbati dan autan gidan ya bude masa gate.

KARSHEN BABI NA BAKWAI
Received at 11:16 AM
4 people reacted with 👍
Viewed 90 times

MATAR MUKHTAR

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA TAKWAS

08
Tunda suka yi waya da Karima take so ta sameshi ta bashi shawara ya kara aure amma bata sami dama ba, ta fi so sai tana cikin walwala shima yana cikin walwalar sannan tazo da maganar domin bata san irin amsar da zai bata ba. Tana so duk amsar da ya bata ta kwantar da kanta ta lallabashi wanda haka ba zai samu ba idan ita da shi basa cikin yanayi na walwala.

Sama da sati daya kenan da tura masa video din shi data yi, tun yana muzurai yana daure mata fuska har ya saki ya dawo yanda ya saba.

Ita kuma ba wai ta hakura bane tana nan tana tara shi ta fatan azo wata gaba da ta dace da zancen.

Tana shirin dora abincin dare wayarta tayi waka, tana dubawa taga Hamida ce. Da murmushinta ta amsa wayar

'Yaya Safiyya ina wuni.'

Kafin ta bata amsa ta cigaba

'Yaya na sami admission an

08, January 2025
Nafisa

I cant download the book

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login