Showing 48001 words to 51000 words out of 92582 words
ta iya ma bai taba tunanin zata iya yi masa ba. Lallai idan bai yi da gaske ba komai ma zata iya aikatawa don yaga tana nema ma ta zageshi. To wa ya gaya mata da mace ya fita? Ko matar Suraj ce ta gaya mata yana da 'yan mata don ya san bata son ganinsu tare da Suraj?
Haka ya kwanta yayi ta juyi a gado ya kasa bacci saboda tunanin yanda zai bullowa Jamila, sai gefin asuba sannan bacci ya kwasheshi.
Ita kuwa Jamila tana fita ta wuce dakinta ta rufo kofa, ta jingina a bayan kofar da ta rufe tayi kwafa ta share hawaye da ya fara bin fuskarta. Duk da bata tabbatar da abinda take zargi ba amma wannan kame-kamen da yake ya tabbatar mata da zarginta, amma wannan abu ne da bazata dauka ba don tana jin zata iya zuwa gidansu yarinyar ta kora mata warning idan ta dawo shi kuma ta sauke masa rashin mutunci a ka. Ta jijjiga kai ta fada a fili
'Ba zai yiwu ba wallahi, ba zan dauka ba.'
Ta wuce ta kwanta a kan gadon bayan da ta gyarawa Nana kwanciyarta a kan katifarsu da take tsakar dakin.
Yanda ya kasa bacci haka itama ta kasa baccin tana tunanin mafita,ba zata juri zama da mazinaci ba domin ita ko aure zai kara to tana so ya kai matar wani gidan ba inda take ba saboda gaskiya tana da kishi; balle ace tana nan gidansa yana bin matan banza.
Bata son yanda kullum Nana take tashinsu daga bacci tun shida na safe amma yau taji dadin hakan duk da batayi wani isasshen bacci ba. Nan da nan ta fito da yaran ta shirya musu breakfast; indomie ta dafa sannan ta soya kwai. Suka zauna ita da yaran gaba daya a dining table suka ci suka koshi. Nan ta bar kwanukan a kan table din ta zaunar da su a gaban TV ta kunna musu sannan ta wuce dakinta ta koma bacci.
Kamar yanda ya saba sai wajen takwas da rabi sannan ya fito da shirinsa tsaf na tafiya aiki, abinci kawai zai ci ya wuce. Bayan su Nurain sun gaishe shi ya wuce dining table don yaga alamar abinci kuma Nurain yace masa sun ci abinci su da Mommy. Ya karewa table din kallo bai ga alamar an ajiye masa abinci ba don haka ya wuce kicin inda har tukunya ya buda babu wani abu, ya tabbatar dai bata ajiye masa komai ba.
Ya fito daga kicin din ya wuce dakinta, ya tura kofa a hankali ya shiga da sallama. Tana kwance a kan gado ta bawa kofa baya, bata motsa ba don haka yayi gyaran murya ya kira sunanta. Ta juyo tare da gyara kwanciya ta dubeshi ba tare da tace komai ba, yace
'Ina abincin nawa zan fita ne fa?'
'Mtsewww!'
Ta ja tsaki sannan ta cigaba
'Inda kake zuwa can ai naga suna baka abinci don naga sun baka na dare shi yasa ban girka ba.'
Mamakinsa ya karu, cikin bacin raia yace
'To yanzu ya kike so ayi, haka zan tafi office banyi breakfast ba kenan?'
Cikin halin ko-in-kula tace
'Zabi ya rage naka, ni kam ai nayi breakfast yanzu kuma bacci zan yi.'
Cikin bacin rai yace
'Jamila ba fa na son raini da wulakanci, ni kike gayawa wannan maganar banzan?'
Ta kalleshi a raine tace
'Uhmmm! Kan ka ake ji.'
Ta juya ta gyara kwanciyarta ta rufe idonta ta barshi nan tsaye.
Ransa yayi matukar baci, wato ma ta mayar da shi mahaukaci. Ya rasa mai zai ce mata don haka yayi kwafa ya fice daga dakin tare da maka mata kofa. Ta gayar kwanciya tayi tsaki tace
'Ka balla kofar gidan naka sai kaji dadin gyarawa dan rainin hankali.'
Ta juya ta yi kwanciyarta.
Yana fitowa falon ya dauki jakarsa ya fice ya kama hanya, ranshi a bace sosai. Ba wai abincin ne bazai siya yaci ba, wannan ba wani abu bane a wajensa amma wannan wulakanci da tayi masa ya tsaya masa a rai. 'kanka ake ji' shine abinda ya fi tsaya masa a rai. Wato ma shi ta mayar mahaukaci kenan? Lallai za ayi rigima don sai ya saita ta. Ba zai dauki raini ba don ba haka ya saba, ko me yayiwa Safiyya sai ta yi masa abinci bata taba fasawa ba.
Cikin hanzari ya kawar da tunanin Safiyya don baya son ya dinga tunata da yawa, amma tabbas sai ya koyawa Jamila hankali.
KARSHEN BABI NA ASHIRIN DA DAYA
MATAR MUKHTAR
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
FIKRA WRITERS ASSOCIATION
BABI NA ASHIRIN DA BIYU
22
Saboda tsabar bacin rai mantawa yayi bai sayi abinci ba sai bayan ya shiga office, don haka sai da ya zauna sannan ya aika masinjansa ya siyo masa dankali da kwai. Bayan ya kawo ya hada shayi ya zauna a kujerar zaman baki ya fara karyawa, yana cin abinci yana tunani kala-kala.
Haka kawai yaji yana kewar Fatima, yana tuna lokuta da dama da yake tare da ita. Aiki yake amma har azahar ya kasa cire Fatima daga lissafinsa, don haka bayan azahar da ya dawo office din daga masallaci sai ya zauna a kan kujerar zaman mutum biyu da take gefe daya a office din ya zaro wayarsa yana lalubar lambar Fatima domin ya kirawota.
Babu suna ya adana lambar domin tun bayan da Safiyya ta gane lambar ya cire sunan don haka sai da ya dauki lokaci yana tunani sannan ya gano lambar wadda kusan sama da shekara guda kenan rabon da ya kirawota. Har wata 'yar karamar murna yayi da ya gano lambar, wanda shima da kansa ya rasa gane me yasa yake murna don zai yi magana da Fatima.
Sai da ya kirawo layinta kusan sau goma amma wayar bata shiga, duka layikansa biyu yake kiranta da su amma duk ko ringing bata yi take katsewa. Sai da ya nutsu sannan ya gane blocking din layikansa Fatiman tayi; bai taba zaton zata iya blocking dinsa ba, amma sai ya tuna shi ya fara blocking dinta. Har ya hakura da neman nata ya cigaba da aiki sai kuma zuciyarsa ta cigaba da azalzalarsa a kan son jin muryar Fatiman, don haka sai ya mike ya fice daga office din.
Da yake akwai mai sayar da layin MTN a nan bakin gate din office din nasu nan ya tsaya ya sayi sabon layi wanda ya saka a karamar wayarsa wadda dama layi biyu take ci amma shi daya ya sa mata; aka yi masa rajista ya sa kati ya koma office.
Tun kafin ya karasa zama ya danna mata kira yana ta addu'a Allah ya sa ta shiga domin ya fara tunanin ko aure aka yiwa Fatiman.
Bata dade tana ringing ba aka dauki wayar, ta amsa da zazzakar muryarta wadda ta sa ya saki wani murmushi
'Hello, salam alaikum.'
Sai da ta jiyo sautin murmushinsa a daidai lokacin da ya amsa sallamarta. Tsaf ta gane shi; musamman da yake tun safe take jiran wayarsa tunda Malam ya gaya mata kafin awa ashirin da hudu zai nemeta; amma sai tayi kamar bata san me maganar ba. Bayan sun gaisa yace
'Fatima.'
Cikin halin ko in kula tace
'Na'am da wa nake magana?'
Yayi murmushin da har sai da ta jiyo sautinsa sannan yace
'Fatima baki gane muryata ba? Mukhtar ne fa.'
'Uhm! Allah sarki. Da yake mun jima bamuyi magana ba kuma bani ma da lambar taka yanzu.'
'Hakane, to ai kin yi blocking dina a lambobin da kike da su ko da yake ban san ma ko kin yi deleting ba bayan blocking din.'
'Uhm.'
Suka dan yi shiru, ta fuskanci dai ba zata yi magana ba don haka yace
'To yanzu ya za ayi Fati? Duk da na san ni mai laifi ne amma ina son ganinki. Kina gidan Mommy ko? In ya so ko gobe ma sai na shigo Zariyan.'
Ta gatsine fuska kamar yana gabanta tace
'A'a bana nan, ina Abuja gidan Anti.'
'Ah to ai ta kwana gidan sauki ai ko Abujan sai na shigo, in dai zan ganki ai duk inda kike zuwa zan yi.'
'Ba ma sai ka zo nan din ba, ka dai jira idan na koma Zariyan na kirawo ka sai ka zo.'
Ya marairaice
'Haba Fati, kiyi hakuri mana na zo Abujan. Ko da wuri zaki koma gidan?'
'A'a nima ban sani ba, may be next week may be upper week. Zamu dai yi magana kawai.'
Ta bashi amsa cikin kosawa.
Ya fahimci kosawarta kuma baya son ya gajiyar da ita tunda lallabata yake yi don haka yace
'To shikenan babu damuwa.'
Sukayi shiru na dan lokaci, jimawa kadan yace
'Fati.'
Ta amsa a gajarce
'Um.'
'Kiyi hakuri ki bude lambobi na da kikayi blocking kinji, kin ga ko ta whatsapp ma dinga hira.'
Ta danyi jinkiri sannan tace
'To.'
'Yauwa. Kiyi hakuri kinji, na san ni mai laifi ne shi yasa ma nake so nazo da kaina na bada hakuri.'
Sukayi shiru kamar masu sauraron numfashin juna, jimawa kadan tace
'Bari na je zan dan taya Anti aiki ne, mayi magana daga baya.'
'Ok. Please ki bude ni fa, zan miki magana a WhatsApp din yanzu.'
Ta amsa da kyar sannan suka yi sallama suka ajiye wayar.
Yana murmushi ya tashi ya koma kan kujerar jikin tebur din ya zauna domin cigaba da aiki. Shi kansa bai gane dalilin da yasa yake jin dadi ba kawai saboda ya ji muryar Fatima, amma a halin yanzu yana jin zai iya auren Fatima saboda yanda yake so ta kasance a tare da shi kullum; musamman da ya tuno yadda suka rabu da Jamilan yau da safe.
Ita kuwa Fatima suna ajiye waya ta jefa tata wayar kan gadon da take zaune, ta dunkule hannu ta naushi iska sannan ta kyalkyale da dariya sannan ta fada a fili da yake ita kadai ce a dakin
'Alhamdulillah, ka zo hannu dan rainin hankali za ka gane baka da wayo.'
Tana gama murnar ta dauko wayar ta dannawa Janan kira, nan ta bata labarin abinda ya faru sukayi ta dariya. Ta tsara mata yanda zasuyi Fatiman ta karbi kudi a wajen Mukhtar din idan ya zo Zariyan domin ta cikawa Malam kudin aikinsa. Suka ajiye wayar kowaccensu tana dariya.
.........
Duk yanda yake tunanin idan ya share Jamila zata nemi shiri ba haka ce ta kasance ba, domin ita din ma fushi take da shi sosai. Hatta dakinsa na kwana daina shiga tayi balle ta gyara, abu daya dai da zai sa ya raga mata da yaga fushin da take da shi bai sa ta daina kula su Nurain ba duk kuwa da yanda laulayin ciki yake damunta. Don haka gaba daya sai ya mayar da hankalinsa wajen lallashin Fatima saboda yanda zuciyarsa take azal-zalarsa da son ganinta.
Ya samu dai ta bude blocking din da tayi masa don haka suna magana ta Whatsapp, duk da idan yayi mata sako da safe sai ta kai dare bata bude ba; wataran har sai ya kirawota yace ta duba.
A haka har aka kwana shida, ya ma daina shiga gidan sai ya ci ya koshi don ya san ko da abinci Jamila ba zata bashi ba.
Sai ranar kwana na bakwai da ya kira Fatima ta sanar da shi jibi zata koma Zariya don haka suka alkawarin a kan washegarin ranar da ta koma zai je Zariyan.
Baya son Jamila ta zargi wani abu idan ya fara zaryar zuwa Zariya don yana jin akalla duk sati zai dinga zuwa, don haka da kanshi ya hakura ya nemi shiri da ita.
Sosai ya tsarata a kan matar da taji suna waya Director ce a office dinsu kuma shi babu yarinyar da yake nema. Ta ji shi dai amma bata hakura ba don ta yiwa kanta alkawarin sai ta bincike shi sosai domin ko babu komai ta sami natsuwa. Haka suka warware suka koma harkokinsu kamar da.
Saida ya dauki wajen sati biyu yana lallaba Fatima sannan ta ce masa ta dawo kuma zai iya zuwa. Ji yayi kamar ya tafi a ranar da ba don yamma tayi ba, a haka dai ya daure sai washegari da zai kama Juma'ah sai kawai ya hakura da zuwa office ya wuce Zariya.
Tun dare ya sanar da Jamila zai je Zariyan, ya gaya mata akwai wani abokinsu da babansa ya rasu don haka can zai je masa gaisuwa. Bata zargi komai ba ta yi masa ta'aziyya ta sanar da shi ya siyo burodi don ba zata iya tashi ta girka abincin safe ba tunda Nurain yana hutun makaranta.
..........
Sai ranar Juma'ah sannan Fatima ta samu ta tsara Mommy, ta tuna mata dama mahaifiyar Mukhtar ce ta hanashi kara aure saboda Safiyya 'yar kanwarta ce kuma bata so ayi mata kishiya; kamar yanda ya gaya mata; amma yanzu ta yarda saboda Babanshi yayi magana.
A daki ta sami Mommy din tana shirin tafiya aiki da yake daman ita Fatiman bata zuwa aiki ranar Juma'ah tunda voluntary takeyi ba biyanta ake ba. Bayan ta gama sauraronta ta bata rai tana harararta tace
'Mai zai dawo yayi? Nifa bana son yaudara. Dama shi kike jira kika ki kula mutane ko?'
Ta sunkuyar da kai
'Mommy wallah ba haka bane, kuma yanzu ai da gaske yake.'
Suka yi shiru na dan lokaci yayinda Mommy ta zuba mata ido ita kuma ta sunkuyar da kai. Jim kadan Mommy din tace
'Shike nan, amma idan ya zo ki bashi lambar wayar yayanki ya nemeshi suyi magana ni kuma zan yi magana da Yayan naki kafin nan.'
Sukayi sallama Mommy ta wuce wajen aiki tana ta juya maganar dawowar Mukhtar a ranta. Bata ji dadin dawowar tasa ba don da ace akwai wani mai neman Fatiman ba zata bar Mukhtar ya dawo ba, to amma har yanzu babu wani manemi da yake neman Fatiman ga shi ta kusa shekaru talatin da haihuwa; domin har an fara yarwa Mommy magana a dangi. Don haka tana ganin tunda dai ita Fatiman ta amince gara a bawa Mukhtar din dama ya fito ayi auren.
Sai wajen sha daya saura sannan ya isa Zariya, tun kafin ya tsaya a bakin gate din gidan su Fatima yayi mata waya don ta fito. Sai da ta dauki sama da minti ashirin tana bata masa lokaci sannan ta fito. Tun kafin ta karaso inda yake a cikin motarsa yake ta kallonta yana murmushi; ya ji dadin ganinta kuma tayi matukar yi masa kyau da kwarjini; nan da nan aka tayar da tsohuwar soyayya.
Kafin ta karaso ya mika hannu ya bude mata kofar gaban motar yana ta faman murmushi, ta karaso ta tsaya a daidai inda yake tace
'Ka fito mu shiga ciki sai mu zauna a falo.'
Bai ga fuskar yin korafi ba don haka ya rufe motar ya fito ya bita a baya, suka shiga har falon baki. Ta nuna masa kan kujerar zaman mutum uku ya zauna ita kuma ta zauna a kujerar zaman mutum daya. Basu dade da zama ba Baba Habi ta shigo ta kawo masa ruwan roba wanda ta dora a faranti tare da kofi guda daya.
Suka dan taba hira ya sake bata hakuri tare da yi mata alkawarin duk lokacin da ta shirya zai turo maganar aure. Suna nan zaune wayarta tayi kara, tana dagawa kafin ta fara magana ta dube shi tace
'Janan ce.'
Yana murmushi ya amsa
'Allah sarki, kice ina gaisheta.'
Ta cigaba da magana da Janan din a waya
'Kai Janan bani fa da kudi, nifa in ban samu ba ma sai na fasa zuwa bikin.'
Ta dan yi shiru tana sauraron abinda Janan din take fada sannan ta cigaba
'Allah kawata, to ai na gaya miki bani da kudi.'
'To shikenan ki bari dai mayi maganar daga baya. Mukhtar yana gaisheki.'
Sukayi sallama ta ajiye wayar fuskarta babu walwala. Ya dubeta yace
'Wani abun zaki saya ne kike ta faman babu kudi?'
Ta kawar da kai cikin damuwa sannan ta bashi amsa
'Hmm! Wallah bikin wata kawarmu za ayi an kawo anko kuma gaskiya mai tsada ne don a Abuja ma za ayi biki, to ita Janan mijinta ya saya mata ni kuwa ka ga babu wanda na ajiye ai sai dai na hakura.'
Yayi murmushi
'Haba dai, nawane kudin ankon naki sai na tura miki, tunda kema kin ajiye ni ko?'
Tayi dariya tace
'Haba dai, 120k ne kawai komai da komai.'
Bai zata kudin zai kai haka ba shi yasa yayi saurin cewa zai yi, to amma tunda ya ce zai yi yana ganin dole yayin musamman da yake tunda ya zo bai ga walwalarta yanda yake so ba.
Ya zaro wayarsa ya fara lalubawa
'Account dinki na UBA zan tura miki ko?'
Ta fadada murmushinta harda dariya
'Eh, ai kuwa na gode.'
Ya cigaba da kokarin tura kudin wadanda kudi ne da ya ware saboda haihuwar da Jamila zata yi nan da wata shida, duk da baya son taba kudin amma ya kasa hana kansa haka ya tura mata.
Nan take taji alert, ta dubeshi tana dariya tace
'Gaskiya na gode sosai, ba zaka gane yanda naji dadi ba.'
Cikin walwala suka karasa hirarsu sai wajen sha biyu da rabi lokacin an fara kiran azhar tace masa
'Bari naje gida kai kuma ka kama hanya don Mommy tace kada na dade, kuma wallahi idan na dade da yawa Baba Habi gaya mata zata yi.'
Yayi 'yar dariya
'To ai babu laifi, gara Mommy ta kular min dake.'
Ya mike ta raka shi bakin mota suka yi sallama ya kama hanya yana ta wasiwasi.
Sosai yake son Fatima yanzu kuma aure yake so suyi, amma ya ga kamar ita din bata saki jiki da shi sosai ba. Saboda yana kula da ita, duk yanda ya so ya rike koda hannunta ne bata bashi dama ba domin shi a motar ma yaso suyi zancensu amma taki. Ya so ma yace mata su dan je cikin gari yawo amma bai ga fuskar ba, dole haka ya hakura suka rabu.
Har yazo gida yana tunanin ta
08, January 2025
Nafisa
I cant download the book