Showing 87001 words to 90000 words out of 92582 words
inda yake ba ta bi ta daya gefen ta nufi hanyar gate. Don haka ya kai dubansa inda ta nufa, inda ya ci karo da fuskar AA yana ta murmushi a daidai lokacin da ya hango Safiyyan. Nan take ya tsuke fuska zuciyarsa ta fara kuna; sau daya ya taba ganin mutumin nan amma ya ganeshi, baya son ganinsa saboda shine wanda yake shirin shiga tsakaninsa da Safiyya. Tabbas da za a bashi dama ya kashe mutum daya a duniya ba tare da da wani sakamakon ba to zai kashe mutumin nan. Ya koma ya zauna yana huci saboda takaici, ya kasa daina kallonsu duk da yanda kallon nasu yake kara masa zafi a zuciyarsa. Ba zai taba bari wannan mutumin ya aure masa Safiyya ba sai inda karfi sa ya kare.
Suka tsaya suna fuskantar juna, kuma da yake filin makarantar duka bashi da girma sosai tas yake hangosu.
Ta dubi AA tana murmushi tace
'Mijin Barrister, sai gaka a Kano.'
Yayi dariya yace
'Kanwar Barrister. Na biyo dare na dawo don naji electrician yana so yayi min shiririta a dakin amaryata.'
Sukayi dariya gaba daya.
Suna nan tsaye suna ta yiwa juna murmushi wanda Mukhtar yake ganin kamar da gayya sukeyi Nurain ya sheka da gudu ya tafi wajensu. Ya rage tsawo ya gaida AA, kafin ya amsa dubeta yace
'Mama kada fa ki tafi an kusa fara kiranmu.'
Ta shafa kansa tace
'Ba tafiya zanyi ba Nurain, ina nan.'
AA ya mika masa hannu suka sake gaisawa yayinda Safiyya ta gabatar masa da A A din. Ya dan rage tsawo ya dawo dai-dai da Nurain ya mika masa babbar ledar da take hannunsa yace
'Wannan naka ne saboda Mama tace min kaci musabaka na siyo maka, wannan kuma na Nana Khadija ne.'
Ya leka ledar yana dariya ya dubeshi yace
'Nagode sosai, next term ma 1st position zan dauka a musabakar.'
'Da kayau mutumina, Allah ya kaimu.'
'Nagode. Mama ki rike min na koma kada a fara kira.'
Ya fada yana mika mata ledar, tana karba ya zura da gudu ya koma inda ya fito. Suka nufi gate ita da AA tayi masa rakiya, kafin su karasa gate din tayi masa sallama ta koma ciki. Tunda ta koma ya sunkuyar da kai yana kokarin hadiye malolon da ya tokare masa zuciya.
Bayan ta zauna ta duba ledodin; digital Qur'an ya kawo wa Nurain yayinda ya kawowa Nana chocolate, ta hada ta ajiye musu.
Aka cigaba da taro har azahar sannan aka gama. Suka gaggaisa da malamai da mutane. Duk yanda Sabir yake son ya raba Safiyya da Mukhtar shi Mukhtar din yaki ya bar kusa da ita, don haka a jere suka nufo gate yayinda Sabir yake binsu a baya. Gashi wayar Safiyyan tana hannunsa balle yayi mata waya.
Suna fitowa daga gate taga motar AA, hadaddiyar marsandi ce ta zamani baka kirin sai sheki takeyi. Ta kalli motar tana mamaki, direban da yake tsaye bayan motar ya karaso gabanta ya sara kamar wata soja, yace
'Ranki ya dade ke nake jira, yallabai yace a kaiki duk inda zaki je.'
Mamaki ya bayyana a fuskarta tace
'Shi kuma a me ya tafi?'
'Tito ne yazo ya daukeshi.'
Ya sake sarawa yace
'Idan kin gama ina nan ranki ya dade.'
Kafin ta amsa ya koma jikin motar ya tsaya.
Tana juyowa Mukhtar yace mata
'sai an jima.'
Kafin ta amsa ya bar wajen, don haka ta wuce wajen motar AA. direban ya bude mata kofar baya yayinda Sabir ya shiga gaba yaja mota suka wuce.
KARSHEN BABI NA TALATIN DA BAKWAI
MATAR MUKHTAR
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
BABI NA TALATIN DA TAKWAS
38
Allah ne ya kaishi gida lafiya ba don yana tuki a hankali ba, ji yake kamar zuciyarsa zata fito ta bakinsa saboda kunar da takeyi.
Ya za ayi yana ji yana ga wannan mutumin ya aure masa Safiyya? Ba zai yiwu ba.
Da kyar ya amsa sannu da zuwan da Jamila take masa ya wuce daki, ya rufo kofa. Ta ja tsaki ta ci gaba da abinda takeyi.
Sai da ya sakawa kofar mukulli sannan ya zauna akan gadon kamar wanda aka tura, ya sa tafukan hannunsa ya rufe fuskarsa yana jin hucin numfashinsa a hannunsa wanda yayi dai-dai da sarawar da kansa yake yi; idan dai bai bata a lissafin da Baban Hotoro ya gaya masa ba yau saura sati biyu kenan a daura auren Safiyya.
'Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun.'
Ya fada a fili tare da mikewa tsaye, ya fara kaiwa da kawowa a dakin; wai me ya farune ya bari har Safiyya ta subuce masa haka? Gashi kawo yanzu ya tatabbatar duk wani abu da ake samu na nutsuwa a aure zai samesu ne kadai idan Safiyya ce matarsa.
Ya koma ya zauna a gefen gadon a daidai lokacin da dabara ta fado masa; tabbas Safiyya tana kaunar yaranta, idan akwai abinda yake mata ciwo a rabuwarsu bai wuce yanda ya rabata da yaran ba. Don haka zai aika mata Nurain ne ya tsaro masa ita; musamman ma da yake Nurain din yana yawan maganarta, yana so su dawo gidansu kamar yanda yake da. Don haka wannan shine damarsa ta karshe a tsakanin sati biyun nan ya rikita musu ita, in ya so in an taru ranar daurin auren a daura da shi.
Nan da nan ya mike ya dauki mukullin motarsa ya fito, babu kowa a falon don haka ya fice kai tsaye. Saida ya tsaya a makarantar almajiran dake can cikin unguwarsu ya bawa malamin sadakar naira dubu goma yace a yi masa addu'a a kan bukata da ta taso masa sannan ya wuce gidan Hajiya.
----
Ranar litinin da safe Safiyya tana daki tana wankewa Umma bandaki ta jiyo Umman a tsakar gida ita da Nurain. Ta tsame hannunta daga ruwan ta fito don ta gani da idonta, tunda shekaranjiya suka rabu a wajen taro basuce mata za su zo ba.
Tana fitowa ta samesu Nurain yana yiwa Umma bayani
'Abba ne yace Baba Aminu ya kawo mu muyi huta, idan mun yi kwana biyar a zo a daukemu.'
Nan da nan aka shiga murna ana ta hidima. Umma tana kula da yanda jikin Safiyyan yayi sanyi take ta wani faman zare ido tunda su Nurain suka shigo, shi yasa ma tayi zargin akwai abinda ubansu ya shirya ya kawosu a dai-dai wannan lokacin; domin tunda ya saketa ba a taba kawosu su kwana ba sai yau.
Haka dai ta kyalesu aka cigaba da hidimar gidan.
Suna dakin Umma inda Nana take bacci kan gado yayin da Umma da Nurain suke sallar la'asar, suna sallame sallar ya fice da gudu kamar wanda damam a kan kaya yake sallar. Dakin Safiyya ya shige inda ya sameta tana azkar a kan dadduma, ya karasa ya zauna a gabanta yana kallonta. Bayan ta gama azkar din ta dubeshi tace
'Ya dai? Nana tayi bacci ta barka ko?'
Yayi dariya bai ce komai ba. Sukayi shiru na dan lokaci, jim kadan yace
'Mama.'
Ta kalleshi ba tare da ta amsa ba, ta dade rabon taga Nurain ya shiga damuwa kamar yanda fuskarshi ta nuna yanzu. Cikin yanayi na kulawa tace
'Na'am Yaya Nurain.'
Yayi murmushin yake
'Mama don Allah kada ki auri mutumin nan da ya bani qur'an, ki dawo gidanmu kinga abbanma sabon gida zai siya mana.'
Ta kasa bashi amsa saboda yanda jikinta yayi sanyi, ta faki idonsa ta goge kwallar da ta taru a gefen idonta. Ya cigaba
'Kinga shi da yaransa a gidansa kuma su mamansu tana nan, Kinga Halimatu ma Mommynta tana nan amma ni da Nana bamu da Mommy. Zamu fi jin dadi idan kika zo muka koma sabon gidan da Abba zai siya mana.'
Da kyar ta hadiye hawayen da ya taso mata ta lalubi muryarta tace
'To ai kuna gidan Hajiya kuma na san Hajiya tana kula daku sosai ga baba, Anti ga su Baba Aminu ma duk suna kula daku.'
Ya sake langabe kai kamar zai yi kuka
'Mama ai kowa ya fi son Mamansa, kema kinga ai kin fi son ummanki. Muma muna so muyi bacci tare dake, kiyi mana abinci idan bamu da lafiya ki bamu magani. Yanzu kinga idan kika tafi gidan mutumin nan su yaran gidan suna da Mama guda biyu kenan mu kuma bamu da kowa sai Hajiya, ko Mama?'
'Ba haka bane Nurain, ni mamanku ce har abada, kuma duk inda naje za a kawo ku kuma nima zan dinga zuwa ina dubaku.'
'Dan Allah dai ki dawo gidanmu Mama, muma mu zama muna da Mamanmu.'
Tayi shiru yayinda shima yayi shiru yana tunani; duk abubuwan da suke faruwa bai fahimcesu sosai ba saboda karanci shekaru, amma dai ya san babu abinda yake so a halin yanzu fiye da gidansu ya koma kamar da; da Abbansu da Mama. Ya kalleta tayi shiru kawai tana kallon bango yace
'Mama zaki dawo muje mu fara gyara gidan?'
Tayi murmushin yake tace
'Sai nayi tunani Nurain.'
Suka sake yin shiru na tsawon lokaci, jimawa kadan yace
'Mama kinyi tunanin?'
Tayi dariya tace
'Ak ba yanzu ba sai an kwana biyu.'
Sallamar Umma ce ta katsesu, ta daga labulen tacewa Safiyya
'Kin san Hajiya Suwaiba tana jiranki kije ki karbo dinkunanki tunda yau kika ce mata.'
'Uhm, Umma inaga idan Sabir ya dawo ya karbo min kawai.'
'Ai kuwa tashi zakiyi ki tafi tunda tace kije da kanki don ki gwada a tabbatar sunyi kafin ki taho da su, kuma kin san Inna Hajara tana nemanki baki je ba tunda hanyar ne idan kika karbo kayan sai ki tsaya a gidanta in ya so shi Sabir din sai ya zo ya daukeki tunda na san idan Inna ta sa ki a gaba sai ku kai isha bata sallameki ba.'
Inna Hajara kanwar mahaifinsu Safiyya ce wadda itace auta a gidan, macece mai ilimin addini da dattako don haka duk yarinyar da za a aurar a dangi sai taje and mata lecture ta musamman. Shi yasa da aka kai goron biki tace a turo mata Safiyyan ma.
'Umma ai ko daga baya ma n...'
Umma ta katseta kafin ta karasa
'Safiyya tashi zakiyi ki tafi, in dai yara ne da aka kawo ai tare zaku kwana ko? Kije ki dawo suna nan.'
Yanda Umma take magana ta san bata da wata mafita don haka ta mike ta fara shiryawa yayinda Umma tasa Nurain a gaba suka fice daga dakin.
Bayan ta yiwa Umma sallama ta fice Umman tabi bayanta da kallo tana mamaki; lallai shi yasa hausawa suka ce mai 'da wawa. Saura kwana goma sha daya a daura auren amma an turo yaro zai jagula mata lissafi to ba zai yiwu ba.
Zuwa yanzu itama Umman haushin Mukhtar din take ji; shekara uku yarinyar tana jiransa Bai dawo da ita ba sai yanzu da ta sami miji mai kaunarta sannan zai dinga kawo mata fitna. Babu yanda za ayi a yanzu ta bari Safiyya ta sake auren Mukhtar sai dai duk abinda za ayi ayi, yaran ma zata san yanda zatayi da su bazasu daga mata hankali ba.
........
Safiyyan bata dade da fita ba Yaya Hajiyayye da Hamida suka shigo, kasuwa sukaje suka karaso sayayyar bikin daga can suka wuto nan don su kawo wa Umma kayan. Bayan sun gaisa Hamida take tambayarta yaushe aka kawo su Nurain; nan Hajiyan ta basu labarin abinda yake faruwa. Yaya Hajiyayye ta fara fada tana cewa
'Umma in ba ayi da gaske ba a kan yarinyar nan fa so take ta dawwama a matar Mukhtar, ni kuma wallahi ya fice min a rai mara kunya. Kai da aka bata lokaci ana jira sai yanzu zaka dawo.'
Hamida tace
'Ba dai yara bane, yanzu zan yi maganinsu. Ba zasu sake ganinta ba sai ta zama matar AA.'
Ta kwalawa Nurain kira wanda suke tsakar gida suna wasa tare da Sajida 'yar autar Yaya Hajiyayye wadda sa'ar Nurain din ce. Gaba daya suka shigo dakin da gudu suka fada kan Hamida suna dariya. Yaya Hajiyayye tace
'Kai kuyi a hankali kada ku lotse mana hancin jariri.'
Suka kyalkyale da dariya, Hamida ta dubi yaran tace
'Duk ku shirya gidana zamu tafi, gobe muje park na shop rite, jibi kuma na kaiku gidan zoo sai mu dawo daku ko?'
Nan da nan suka sa ihu, Sajida ta dubi Mamanta tace
'Mommy nima fa binsu zan yi.'
'To ki tafi na aiko muku da kayanki.'
A take Hamida ta yiwa maigidanta waya wanda ba tare da bata lokaci ba ya zo ya kwashesu ita da yaran suka tafi gidan bayan ta gayawa Umma ba zasu dawo ba idan Aminun yazo yaje gidanta ya daukesu.
Sai bayan magriba sannan Safiyya ta shigo gidan dauke da kayan dinkinta niki-niki. Can gidan Inna Hajara ta dade tunda sakata tayi a daki tana ta nasiha har sai da aka kira magriba.
Kafin ta ajiye kayan ta fara tambayar Umma ina yaran, tace
'Sun bi Hamida gidanta inaga sai gobe za ta dawo da su.'
Bata so hakan ba domin tana so su gama maganarsu da Nurain, amma ta san idan tayi magana Umma ba zata saurara mata ba. Don haka ta ajjiye kayan a dakin Umma ta koma nata dakin.
Tana shiga dakin ta kirawo Hamida, ita kuwa tana dauka ta saka a hands free ta bawa yaran. Gaba daya suke magana duk sun cika mata kunne
'Uncle ya siyo mana burger da ice cream da chocolate, gobe zai kai mu fun park muyi wasa.'
Haka sukayi tayi mata hayaniya daga baya Hamidan ta karba tace mata sai jibi zasu dawo.
Haka ta hakura ta kwanta tana ta wasi-wasi; ta daina son Mukhtar amma tana son yaranta kuma itama tayi kewarsu. Ta san Mukhtar ne ya aiko Nurain amma wannan ya nuna yana so ta dawo kenan. To ko dai hakura zatayi ta koma ta zauna ko don yaranta?
Haka tayi ta tufka da warwara ita kadai. Ko da AA ya kirawota ma haka tace masa kanta yana ciwo don haka babu wata hira sukayi sallama ya barta don ta kwanta.
Washegari haka kowa ya cigaba da harkarsa yayi banza da ita. Har Sabir ma kin kulata yayi domin ta fara bashi haushi, yana ji a ransa kamar sai ya je ya korawa Mukhtar jawabi sannan zai kyaleta.
Haka tayi ta hidimarta cikin damuwa suna kallonta suna ta shirin biki yayinda ita kuma take musu kallon basa tausayin yaranta.
......
Washegari da yamma Hamida ta hada kayanta da na yaran ta kirawo almajirinta ta bashi ya wanke mata. Bai jima da fita ba ya dawo ya mika mata takardar yana fadin
'Wannan a aljihun yaronki na sameta inaga ko aikensa akayi.'
Ta karba shi kuma ya koma ya cigaba da wankinsa.
Suna can suna kallon cartoon a falo don haka ta wuce da takardar dakinta ta zauna a gefen gado sannan ta fara dubawa; wasikace a cikin envelope wadda har likewa akayi da gam.
Tana ta mamakin inda Nurain ya sami wasika a envelope haka ta bude ta zaro takardar dake ciki, tana bude takardar mamakinta ya karu musamman da taga an rubuta sunan Safiyya daga sama:
"Safee"
Ta wuce kasan takardar ba tare da ta karanta takardar ba don taga waye zai rubutowa Safiyya wasika.
"Mukhtar"
Shine sunan da aka rubuta a kasan takardar, ta tuntsure da dariya sannan ta mike ta tura kofar dakin ta saka mukulli don kada yaran su shigo su ga takardar, ta koma ta zauna ta karanta kamar haka
"Kafin nace komai ina mai sake baki hakuri, in Sha Allahu duk abinda ya faru ba zai sake faruwaba, nayi miki alkawari.
Ni da yara muna kewarki. Bamu makara ba Safiyya ki yi hakuri mu mayar da aurenmu ko don yaranmu. Na tabbatar ko yanzu kika ce zaki aureni babu wanda zai hana sai dai ke din.
Ina sonki Safiyya kuma ke kin san ina sonki, abinda ya faru jarrabawace daga Allah. Na dan bazaki so ki rushe gidanki kuma kije kina gina gidan wani ba, kiyi hakuri mu maida aurenmu; mu hadu mu kula da tarbiyyar yaranmu kamar yanda iyayenmu suka yi mana.
Don Allah ki kirani a waya yanzu ko kuma ki cire layina daga blocking din da kikayi ni sai na kirawoki, please.
Your's
Mukhtar."
Hamida ta kyalkyale da dariya tana juya takardar a hannunta, tace a fili
'Mugu, Allah ya kama ka.'
Ta janyo wayarta ta dannawa Sabir kira, yana dagawa tace
'Wallahi akwai wata jarida kazo yanzu na siyar maka da ita.'
Tana magana tana dariya, Sabir yace
'Wa kika cuta ne haka zaki tsaga min kunne.'
'Don Allah kazo yanzu.'
'Allah ya soki da motar Yaya a hannuna gani nan zuwa amma wallahi da bazan zo ba.'
Sukayi sallama suka ajiye wayar.
Kafin wani lokaci ya isa gidan Hamidan. Tana jin tsayuwar mota ta san shine don haka kafin ya kwankwasa ta zo ta bude masa gate din. Yana shigowa ta mika masa takardar tana fadin
'Mutuminka ne yayiwowa Yaya Safiyya aike a aljihun Nurain.'
Ya karba yana mamaki, nan a farfajiyar gidan suka tsaya ya fara karantawa. Yana yi suna dariya. Bayan ya gama ga dubeta suka kece da dariya yace
'Mugun kaya, ya ji wuta yana rubuta kalaman soyayya. Kin san ranar da mukaje makarantar su Nurain A.A ya kunnashi da yawa.'
Nan ya bata labarin abinda ya faru a wajen speech and prize giving day din su Nurain.
'Ai dole ya rubutawa budurwa wasika ya ga za a ci shi yaki har gida.'
Suka kyalkyale da dariya Sabir yace
'Don Allah kada ki dawo da yaran nan daga nan ki mayar dasu gidansu idan an gama bikin sa dawo, tunda daman ba don Allah ya sa aka kawo su ba.'
'Ai in Sha Allah bazasu sake gamin Yaya Safiyya ba sai ta zama matar AA. Sun bani tausayi amma haka ubansu ya zabar musu, idan ta koma wahala kawai zata cigaba da sha har bakin cikinsa ya kasheta su zama marayu.'
Ko gidan bai shiga ba daga nan sukayi
08, January 2025
Nafisa
I cant download the book