Showing 153001 words to 156000 words out of 225093 words
ake ta faman yi,..
Game da hidiman bikin Wani boyayyen kuma zazzafan fito na fito ake shinfidawa tsakanin su hjy indirah da su Jahan khatun da sarauniya dilshada
Kowa yana so abikin nan ya kasance shine abun kallo,a ynzu haka da kyar aka raba musu wanda xai dauki nauyin hada kayan lefe na akwatin amarya da dama ba aayi shi ba..
Hjy indirah bata so ba da su jahan khatun suka fi karfin su a wannan fanniin da fannin tarbon baki da duk abunda zai shafe tsare tsare na hidimar
Da haushin haka hjy indirah ta hana bahi sakat,yi wannan ki bar wannan a yau ko lokacin kanta bata samu mai kyau ba..
Subaya ce mai designing weding dresss,itama bata samun lokaci most time in ta tafi aikin bata dawowa sai dare,..
Bangaren bahiyya,bata minti goma bata tuno da abunda ya faru tsakanin su da junnut ba amma da shike takan tuno cewa dazu da suke cin abinci kaaamil ya dada bata karfin gwiwa akan abubda ta gaya ma junnut sai ta ji hankalin ta yadan kwanta
Ayanzi jira take taga ko junnuut zata zo ta neme ta su warware magana,ga wani mummunan bugun zuciyat dake taso mata haka kawai batasaan dalilin sa ba
8.pm na dare tana site din ake mata gyaran,ita kadai ne a falon ta tana kwance dija ta kira ta suna Hirarkin su,..dija sam bata ji dadin marin da junnut tayi mata duk dama bahin ta nuna wannan bai dame ta ba,Tace ma bahi muddin ta dawo daga lagos insha Allah zata zo suyi maganan kayan da zata sa itama a hidimar bikin nata..dan tsokanan ta take yi suna dariya sai ga knock tayi saurin bada a ixini aka shigo, maid ne durkushe agaban ta tace mata, jahan Aarah na neman ta da gaggawa..
Ba bata lokaci ta katse wayar ta jawo mayafin ta ta nufi part din su,..
Tana shigowa falon tayo sallama da sanyin murya,jahan da hj indirah tagani sun zazzauna...tayi saurin isa gaban su a ladabce tace
Ina wuni mumy..
Suka amsa ba yabo ba fallasa,jahn tace noor, kinga shirye shirye sai tafiya yake,ayanzu baifi kwana biyar ya rage ayi hidimar nan ba,kinga mu tafiya xamuyi"are u sure u ok with it..wani bugu kirjin t yayi atake taji ta kasa amsawa "to jeki maza ki kiramin Saood din.. ..Dama yau ne karshen daman da na baku,hurry up sai asan nayi..ga hjy nan ita zata saurare ku yau
Wani fat fat kirjin ta yake bugawa,tsoron kar araba ta da mijin tan dagske shiya fara kokarin kama ranta yana neman saka ta nadaman fara wannan wasa.
Mikewa tayi kamar wata mara laka tace toh,Sai ta fice,tafiya take tana jan kafa kamar bazatayi ba
Tana bude kofar site din ta koma da baya adan razane
Cupcake ..taji sautin murya daga saman ta sai ta dago da sauri,nan ta hango kaamil na kokarin fitowa daga site dinsun,ta karr masa kallo amma bata ga alaman yadda ta saba gani a yanayin shi ba,.ina kika shiga tun dazu ne?..ya fada da sautin damuwa
Tace..waht?meyey ne kana nema ne?tun safe ina site din su mum ne yanzun ma ita tace ma zo na kirawo shi..nervouasly kaamil ya dan sauke ajiyan zuciya tana ta kallon shi yanayin sa na so ya bata mamaki..
" look bahi We need to talk..ya jawo hannun ta suka tsaya saga gefe
..meyafaru,naga kamar hanklin ka atashe..yace yes bahi,khaldun baiyi da lpya kinsan da haka?..wani kallon bazata tayi masa tayi rau da idanun ta tace,meya same shi...
"i dont know... Amma Nidai abar wannan game din haka..bro is worried..abun na affecting dinshi..
cupcake kinsan ba iya rabuwa da shi din zakiyi ba lets stop here kar wani abu yaje y same shi,..bahiyya da taji kamar zuciyan ta yake sosawa..cikin sanyi ta dago ido tace wai dagaske kakeyi ne?..to meya same shi?
Nifa tun safe rabo na da shi...kuma umma jira take muje taji shawarar da muka yanke ..
Kaaamil ya shafa kansa,yace just tell them,yes,dan Allah
Purnishment din ya isa cupcake..kije kiga yadda yake ..maybe u need to go and see him now..kije kawai..ya dan turata idanun sa duk sunyi wani iri alaman damuwa
Wani mumunan tashin hamkali ke neman kada ma ta hanji tana tsaye kamill"...ya juya da sauri ya barta durus tana binsa da ido..
site din jahan ya nufa a gaggauce
A hujajn ta juya Wani sauri take ta isa kofar dakinsan kamar zata fadi kasa,a hanzarce ta bude hannun ta tana rike da door knobs khaldun ne a tsakar dakin durkufe akan gwiwar sa..Da sauri Bahi ta koma kamar baya tana kallonsa kamar zata dauke numfashin ta har ya gama aman daya keyi sai taga ya rike kai, dawowa tayi gabansa ta dago kansa a hankli tana kallon fuskarsa, ya bude Idonsa da ya kada yayi jajir yana kallonta, samun kanta da yi masa sannu murya can ciki,bai amsa ba ya shiga kokarin mikewa tsaye sai yayi baya xai fadi ya rike kafadar ta da sauri, a hankli ya kuma durkushewa wajen,bahiyya da duk ta ma rasa abun yi ta matso kusa da shi ta shiga cire masa rigar jikinsa a hankli tana kallonsa har ya rage masa saura singlet
.."mikewa taga ya kuma yi ita ma ta mike tana kallonsa da kyar ta iya bude baki tace "ina xa ka" gefen bed dinshi ta ga ya koma..knck abakin door din ya dan fargan da ita,shiko bai ko dago ba tana budewa su jahan da hjya ne suka shigo
"Nan waje ya kacame da kalman meyasame ka?most time bahi takan sha mamakin yadda suke tarairayar su kamar kananan yara,..dama tun safe yau basu ganshi ba,dama an riga an sanar mata cewa yau yana da muhimimn meeting dan haka sunsan ba lallai sugan shi ba..hakan na daya daga cikin dalilin da yasa basu damu da zaman bahiyyar awajen su ba
Amma ayanzu dayace ai tun safen yana dakin baije ko ina ba,hjy indirah bata jira ba ta fara masife si,
Yanzu tun safe kake fama da jikin shine baza a samu wanda zai zo ya sanar mana ba?..ta yi ma bahi fada kadan,tace ke zaki xauna ki kula dashi zuwa gobe kafin aga likita..suna ta lailaiya shi batace uffan ba
hakan yasa ta shiga gyara gun da yayi aman agagauce, har ta gama sanan ta hada masa ruwan dumi dai dai wanda zai yi wanka,kafin ta fito su jahan sun masa sallama akan gobe zasu dawo su duba shi,..bahi ta dawo cikin dakin ta samesa zaune gefen gado ya dafe kai kamar mai jin zafi durkusa wa tayi kusa da shi tana kallonsa tace "na sa maka ruwan wanka" dago kansa yayi yana kallonta bai ce komai ba, can ya mike da taimakonta ya shiga bathroom don yin wanka,kasa fita tayi daga dakin ta gyara masa gadonsa, tana tsaye ya fito daure da white towel a kugun sa duk tsikar jikin shi ya tashi,wani dauke kai tayi da sauri, ya karaso bakin gadon ya zauna ya kuma rike kansa, juyawa tayi tana kallonsa ta rasa takamaiman abinda zata yi, a hankli ta nufi inda ya ke ta durkusa gabansa murya can kasa tace "baka da lfya ne"ciikin sanyin jiki ya gyada mata kai kawai yana kallon fuskarta tace "to in kira maka doctor yanzu" girgixa mata kai yayi, hakan yasa ta mike ta nufi wardrobe dinsa ta ciro masa gogaggiyar pyjams da ta gani, da taimakon ta ya saka, sanan yyi kwanciyarsa kan gado nan da nan bacci ya daukesa,
Bahi dai na xaune gefensa ta kafa masa ido tana kallonsa,bata taba ganin sa awannan mood din ba sai yau,"wani sabon salon tausayin sa ke nman shiga ranta,kanta shiga tunawa musamman lokacin da ya dauke ta daga london yaje yayi jinyar ta sosai agidan shi na US,
Ta dade cikin yanayin tunowa da sassanyar soyayyar su,juyawa tayi ta ga dare yayi nisa amma kuma sam bata jin baccin
,ayanzu ma ji take ta kago taga an ma kusa kiran sallhn farko, ta dan jigininar da kanta jikin gado nan da nan ita ma bacci ya dauketa nan a xaunen kusa da shi,
kiraye kirayen sallah ne ya farkar da ita ta bude idonta ta ganta rungume jikinsa ya wani kankameta ga jikinsa yy zafi,daga kai tayi tana kallon fuskarsa suka hada ido don idonsa biyu ne, tsaban taji tausayin sa sai ta boye fuskarta a kirjinsa da sauri
Sai taji ya dauro bakinsa a hankli kan gashin kanta ya nitsu,
har lokacin sallah ya shigo sosai idonsu biyu gaba dayan su, ita dai kin dago kanta tayi daga kirjinsa, a hankali taji ya kwantar da ita ya mike ya nufi bathroom ta bi sa da kallo, alwala yyi ya fito ya shimfida darduma nan cikin daki don yin sallhn sa, don bai jin zai iya zuwa masallaci
ita ma ta mike ta shiga bayin tayi alwala ta fito ta nufi dakinta don yin sallah, tana idar da sallah ta kasa xama dakinta hakan yasa ta fita ta kamo hanyar dawowa wajen san,
Abakin kofar taci karo da subaya da aut murja,cike da basu girma ta gaishe su..
Yawwa kije umma na kiranki..bari mu duba shi..tayi sauron gyada kai ta bar su anan ta nufi site din su jahan
Yau su biyu tagani da hjy indirah sun shirya tsaf cikin kaisautattun shiga basai an fada ba tasan ba zama zasuyi ba..bayan sun gaisa suka tambaye mai jiki..
Nan Jahan ta fito da wani maganin gargajiya tace ungo rike wannan maganin Aaban ne..ki tabbata kinsa mashi a abinci yaci
And dont let him see it herbs he can easily get irritated .
Tace ok maam..
Hjy indira ta dafa kafadun ta,cike da kulawa tace bayan kwana biyu zamu dawo ki kula dashi..
Dont leave his side kinji?bahi
Ta gyada kai..tana tsaye har suka kammala ta musu rakiya har bakin mota sannan ta dawo ciki,a kitchen din site din nasu ta aje maganin ta nufi dakin sa kai tsaye ta murda ta shigo babu kowa a bedroom din alaman su ant murja har sun tafi amma sai dai bata gansa ba yasa ta fara bin sauran hall din tana dubawa kirjin ta bai dena bugawa ba..
Tun jiya data gansa cikin wani hali sai gaba daya gabobin jikin ta suka sace bata jin karfin yin masa wani abu ko kadan Aranta ayanzu.
Bangaren su junnut kuwa tunda suka bar dakin bahiyya jiya cikin dare na abunda take yi sai kuka tana zage zage,hilda taga bazata iya ba da safiyyan Allah ta kai maganan gaban jahan khatun da sarauniya dilshad duk yadda akayi tsakanin bahi da junnut ta sanat musu
,sosai hankalin sarauniya dilshad ya tashi dataji hakan..
A dame tace bazai yuwa muzuba ido ana azabtar da yar mu ba,khatun U need ta calm her down ki gaya mata abunda yakamata tayi bata xauna tana musu kuka ba,jahan khatun tace toh angama ur majesty..
Ta juya ta kalle hilda,kije ki tabbata ta kintsa kanta ki bata abinci..bari na yi tunani yanzu xanzo komai zai wuce daga yau kunji?hilda ta gyada kai...go on..ta sallame ta ta koma site din nasu.
Anan jahan khatun ta zauna suna ta kule kulen me zasuce da kuma me zasuyi mai gaba daya akan al'amarin
Bahi ta mike da sauri ta nufi ta kasa ta dayan site dinsa shi da bai cika shigan ciki ba,nan ma falonsa ta shiga ta karasa wani fankacecen bedroom,
kwance ta samesa ya lullube da bargo har kansa, ta dade tsaye tana kallonsa daga bisanni ta karasa gadon a hankli ta durkusa gefensa tana kallonsa,bata san meke tunzura ta ba ,yaye bargon tayi a hankli suka yi ido hudu da shi ta mike da sauri xata bar wajen ya wani jawota ta fado jikinsa,sosai jikinsa yayi zafi yana fitar da turiri, tsam ya rungunmeta tare da lumshe ido tayi lamo jikinsa wani azaban tausayin sa na shigarta ta kowanni fanni,
ganin bai kyaleta ba yasa ta janye jikinta a hankli daga nasa ta mike zaune amma ta kasa kallon cikin idonsa, murya can kasa tace "ka sha magani" girgixa mata kai yayi ta mike da sauri ta nufi gaban madubinsa ta bude ta dauko ledan maganin da aka kawo dazun ta shiga ballesu kamar yanda doc din yace ayi, fridge ta koma ta bude ta dauko ruwa sann ta dauki cup din da ta gani kan fridge din ta bude ruwan hannunta ta dauraye cup din da shi ta xubar a bathroom sann ta kuma zubawa ta karaso kusa da shi ta durkusa tana mika masa, da kyar ya karba ya xuba maganin a baki sanann ya kora da ruwa,mikewa tayi ta dauki park din maganin ta nufi gaban madubin da shi zat ta ajiye,maganan jahan ne ya fado mata,ta dawo kusa dashi...
Did u need anything?Zaka ci abinci? Mezaka ci..
Yayi shiru kamar bazai amsa ba chan yace,"yambals"
Tace ok, shikenan?
Yace yeah.. babu bata lokaci ta fita ta nufi kitchen ta sarrafa abincin,cikin dabara tayi mixing maganin a balls din da driink din duk ta kimtsa ta hada atray xata taho masa da shi,tana bude door din kitchen taganshi tsaye,baice mata uffan ba ya shigo daga ciki ya zauna akan kitchen island
Tayi kamar xata basar sanda taji karamin gyaran muryan shi yana cewa,im eating here ta dawo ta aje tray din agabansa..
Dakan shi ya zuba drink dink da shike
Royal tortie fruity smothie ne sai taste din maganin bai fito bare ya nuna,yayi kitibir sai qamshin frozen raspberies,water melon almond milk da greek youghut yake da shike da suka kawai ta yi amfani..
Ya zuba a cup ya sha kusan rabi..tana kallon sa..fork ya mika hannu zai dauka tayi saurin kawo masa tana mai neman wajen zama,a hankli ya fara taba yamballs din but sabida taste din maganin sai bai iyacin ko gwara daya,tayi da shi amma yaki..kirar subaya yasa ta bar sa anan kitchen din ta nufi site din ta.
Da sallamar ta ta shiga,subaya yan ita kadaice a gaban mirror tana kwalliya mai jyau afuskan ta,tsayawa bahi tayi bayan ta yi sallama da mamaki tasake bakii tana kallon subaya
"..zauna ki jira ni baby..taceh to sai ta xauna a bakin gadon cikin ranta tana tuna cewa tun rabuwar big sis da sadat bar sake kwalliya akan fuskan ta ba sai yau..
Bayan ta gama ta taho kusa da ita ta zauna ta maida mata murmishi..
Big sis,U look beautiful
Subaya bata fasa muemushin ba bata riko hannun ta tace just for u my princess ya jikin khaldun,hope he is jmnot troublingbu tace yea jikin ma da sauki..subaya tace Allah ya kara sauki..kinsan Aaban bai cika ciwo ba..im sure he is going trouh alot har tausayi yake bani
bahi tayi shuru bata amsa ba..
" dauke ajiyan zuciya subayi tayi tace Bahiyya?..me kuke ciki ne da mum .?
I know ive not been paying too much attention to u,karkiyi fush dani kinji, im just tryna make ur weding dress impeccable, abubuwan ne sai a hankali..
Kince ma su umman baki son auren ko?bahi ta girgixa kai ta sauke kanta kasa..subaya tayi saurin dago fuskn ta suna fuskantar juna.tace pls Kiyi hakuri bahiyya..i know im the most selfish sister a duniyan but i want u to pls consider my brother kibar maganan baki son auren nan.. ki dauka laifi nane...wallhy nice nayi ta daga masa hankali duk abunda kikaga ya aikata miki ba yin kanshi bane.yana tsoron tashin hanklina ne sabida yasan idan baibani kulawa ba xan iya barin muku duniyar mai gaba days .im beggin u unbehalf of him kiyafe masa,
Kinga su mum?toj ba barin maganan zasuyi ba har sai Kince kin amince
...thy r jot jokin kuma kinga mijin ki baxai iya jure hakan ba,"in gaya maki wani sirrin sai ta dan dago suka kalle juna,khaldun is sick becos of that tension nacewa xaki bar shi..baki wajen ne amma doc ya mana bayanin cewa khal baya samun bacci,i know he is scared of loosing u.
Kiyo hakuri badon mu ba ki sassauta mashi.. pls my sis..
Purnish me instead ..ai nice mai laifin.
Bahi tayi saurin sauke kanta kasa tana tare hawayen ta da suka zubo cikin sanyin murya tace'big sis
Karkice hakan dan Allah nifa baki min komai ba..i dont want to purnish him anymore...ni bansan
Sabida ni yake ciwon ba..im sorrry..subaya tayi saurin jawota jikin ta,wani kuka ta fashe dashi tana lumewa jikin ta..nifa ba dagaske nake musu ba,kawai na fada ne..ai kaamil ma yace na dena fada musu hakan kuma bazan sake ba..
Cikin rarrshi subaya tce
"Shhhh its ok...im glad u wont..kisa aranki cewa qaddara ne ya sa zaki zauna da shi not becos of anyones mistakes.
Tashi kije ki duba shi,ni kukan nan bana son shi..
Ta shiga share mata hawaye ur fitting day is coming soon bana son inzo ina ganin ramar damuwa ko kashin wuya..
Get up..ni zan fita ne sai nadawo.m.bahi ta gyada mata kai sukayi sallama ta fito tana sauke ajiyan xuciya..
Duk abubuwn suna ta kashe mata jiki ayanzu bata jin wani zafi aranta face fargaban yadda zata gaya ma jahan tana son mijin ga in sun dawo..
Bangaren junnut kuwa,hilda ta samu ta taimaka mata yadda jahan khatun tayi mata oder,tasa wata figiyar rigar shan iska iya gwiwa .ta hade rai bata dariya abincin ma da kyar taci fuskan ta full of rage and war..
Sosai ta dau abun da zafi,musamman data kwana tana tunanin yau da safe bahiyya zata zo ta tsuguna gaban ta tana rokon ta,tana kuma mai sheda mata tabar mata khal..
Rashin zuwan bahin hakan ya sa taji wani mumumnan axaban haushi da ciwo aranta
Tana ta shan mamaki,yaushe bahiyya ta dawo hakan?tasan dai basu fada su kwana a waje daya batare da sun shirya ba
Wato akan namiji xata juya min baya ko?
Shigowar jahan khatun ya dawo da ita daga tunanin ta sai tayi sauri ta jawo ta jikin ta tana bubbuga bayan ya sigat lallashi..wani kukan shagwaba mai sarkafe da muhum kishin tsiya ta fashe da shi,kiyi hakuri junnut kar ma kice min komai duk nasan abunda ke faruwa..
Ta dada fashewa da kuka tace Mum ta aure min shi kuma taki ta bar min..
jahan khatun tace haka dan adam dama yake shiyasa tun da nake kinki dawannan yarinyar..
Shiyasa arayuwa kisa aranki cewa babu wani abun da Yayan talakawa da yayan matsiyata zasu ayyana maki Sai tsiya
Kece dama kika nace wai kawarki na yaranta,so what?wallhy baku ma dace ba..har yanzu bata ma lekoki ba ko?
Junnut ta dago tana goge hawayen nata
A xuciye Tace