Showing 42001 words to 45000 words out of 225093 words
ka fada min yanzu kafin na shiga dakin nan na duba da kaina..khal what happen to bahi
...her voice was seriuosly cracking kamar zata Yi masa kuka..
Sadat kuwa har wuya yake sai tsaki yake yi shikadai yana jinjina kai
Wani Miskilin kallo ya mata na 2secnd Sai da ma ya gyara tsayuwan shi yana mai sakaya hannun shin a cikin aljihun sa kafin yaji aransa zai iya responding.
"Aranshi Yana matukar kaunar subaya Amma ya kasa sanin dalilin daya sa bazai taba samun jituwa da halayen mijin ta ba
Kuma Yasani sarai sadat yana pumpa ta da maganganu akansa and now she want to react sabida ta nuna tafi kowa sanin yadda yake treating din bahiyya...
Wani Karamin boyayyen ajiyan zuciya ya sauke baice uffan ba sai ya dawo ya bude musu kofar dakin da bahiyyar take dukan su suka hango ta a lullube
Peacefully tana baccin ta,bai kalle su ba amma tasan da ita kawai yake maganan sa
Yace See?she is sleeping kuma ni bansan me kike cewa ba mmm..yanzu zan iya tafiya koko?
Dan lumshe ido subaya tayi Tare da sauke ajiyan zuciya Ta Dan kalle shi cikin taushin murya tace toh me kakeyi anan din? I just hope she is alright,sai ta kalle fuskan bahiyyar duk bata jin dadi
Khaldun baice uffan ba dan ya tsani raini,batasan duk abunda take fada yanzu ba wanda baya bata masa rai ba,yo shine zata sa agaba da titsiya kamar karamin yaron ta? wani Miskilin murmushi ne ya so ya kufce masa irin gani mugu inna shigo waje ba alheri ba ko.
Aransa yace ba laifin ki bane sis nasan wannan shashan ne yake gurbata Miki tunani
Amma zanyi maganin sa kwanan nan.
Dan Hararar kasan ido ya bishi da shi "Very useless guy..ya furta cikin ransa Sai ya juya ya barsu anan.
Subaya da sadat ne suka karasa Shiga dakin suka duba bahiyya,she look untouched har minshari take kamar ta jima akan gado tana bacci.
sai abun baiyi ma sadat dadi ba yaso ace yau an kama khaldun da laifi mai karfi akan Bahiyya
Sabida yanaso subaya ta daga hankali sosai ta Kai maganan wajen dad dinsu ko Dan araba ta da site dinsa na har abada.
Sai gashi Babu wani prove har suka bar daki na ban farka ba...
Sadat bai kuma cewa uffan ba har suka koma site din su,wanka ya fada yana mai sakar ma kansa ruwan shower mai karfi yana huci yana maganganu kamar zararre
"Naso ace wawan nan ya fadi asalin meya faru akan juice din dana sa masa poison a gaban subaya,
mswww but gosh he dindt.
toh meya faru ne? ni ko kadan bangane komai ba
Bloody bastard!!
...Cike da huci mai zafi ya buga hannun shi akan shower wall yana maganan zuci sam ransa baiyi dadi ba..
A cikin dakin kuma Subaya ce akan vanity table tana lailaya jikin ta da night toners sai gashi ya fito daga wankan.
Baiko kalleta ba ya cigaba da Tsantsame jikin sa don ayanzu tunanin yadda zai bullo da wani abun duk ya gama sha masa kai Har ta taso ta dafa shi ma bai sani ba.
Darling?cikin sanyin murya ta kalle shi
"Shikuwa hannun ta yadan sauke kadan yace..What is it?...ya kuma Dan jan tsaki a gajiye ya daure fuskan sa..
Dan shiru tayi kamar wanda tasha jinin jikin ta chan kafin tace
Me yafaru ne sadat? Sai Naga kamar hankalin ka baya Nan.
Yace Uhh really?I'm just thinking,kuma ma ya wuce dan bana son na cika miki shishhigi akan harkan dan uwanki.
A dan dame subaya tace kamar yaya shishhigi?
Shikuwa kamar jira yake Nan ya juyo with full attention ya kalle ta.
'Subayah in fada miki gaskiya?,..Egon sa'ood yayi yawa..he is too full of himself infact He is senseless!
Aranta Tace what? Shikuwa sai faman zuba yake
Ko Gani yake kamar don yana comanding 4000 troops a filin yaki sai kowa ma sai ya zamto yana tsoron sa?ni din nan ma na girme shi amma kina ganin yadda yake raina ni,kawai bana son tsayar mashi ne sabida ni nasan darajar ki
Ina son farin cikin ki,but Look babe Ya kamata kisa Ido sosai fa,nidai inajin tsoro ma yarinyar Nan bahiyya,i mean she is just a girl bai kamata azuba mashi ido yana cin zarafin ta haka ba ..
Subaya kam ma bajin sauran bambamin san tayi ba Cike da jin haushin yadda ya zagi khaldun din ta numfasa fushin ta
"Amma ai yace babu abunda ya mata and we saw her right?Sadat nasan Khaldun bai amince da ita ba tukun but I know he won't lie to me
Inda yayi mata wani abu da na tambaye shi dazun zai fada min pls try to understand him
Khaldun fa kamar yadda ka dauke shi bane..i dont think zai taba iya dukan wata ya mace ... So pls relax ka fahimce shi pls.
Wani rau da ido sadat din yayi ya mata kallon sama sa kasa"Yeah,..ai dama nasan haka zakice 'i shud try to understand this fool..sai ya mike tsaye ya harde hannun sa.. Look subaya,am a lawyer kuma nasan menake yi, in ke kin yarda dashi nikam ban yarda da shi ba..Something is wrong with him,tare dake fa muka gansa a bakin kofar dakin yarinyar yana rufe mata kofa has Eva been to that place?
Wai Meyasa kike son boye laifin shi ne?
Itama mikewa tsayen tayi ta kalle shi tace
"Noo darling ba maganan boye laifi bane,dani da kai mun ganta lpyar ta lau..bai bari ma ta gama ba ya ce
Toh Ya isah....Ohhh for godsake ki aje wannnan maganan agefe mana, sai yaya in mun ganta haka?does that mean baiyi mata komai ba.?
Ai bacci takeyi ko!so how can you be soo sure cewa babu abun da ya faru?
Tabe baki kawai subaya tayi tace ...hmmm toh Sai ajira gobe ai aji daga bakin ta
A zafafe ya mayar mata amsan
"Nikuma Ina tabbatar miki da za kiji sabanin labarin daga wajen ta,domin ina da tabbacin khaldun din naki yayi ma yarinyar nan wani abu...kawai bazai fada miki ba.
"Cike da damuwa subaya ta sauke ajiyan zuciya,tace ok, enough sadat khaldun is my brother and i realy trust him,
Yakamata mu aje maganan nan haka
..shikenan,ni zan tambaye bahiyyan gobe...so
Can we go to bed now?
Tsaban haushin data bashi Wani tsaki mai sauti yaja kasar wuyan sa yace "im not in the mood..ya dada harde ransa Ya bude closet Yana kokarin jawo pjamas dinsa zai fice
Sa murmushi tayi Cike da mamaki Tace Sadat ka sassauta haka pls dont take this too personal
Sai ya tsare ta da hannu yana jefa mata mugayen yatsine yana bambami
Ni kar ki ishe ni Naji ai Khaldun is your only Brother shi kadai ne yake da iko dake,sai kuma ki kirashi yanzu ku kwana tare am out.
A hargitse ta dada dagowa cikin mamaki tana cewa meyayi zafi haka?
Ko kula ta baiyi ba ma ya ja mata kofa aka barta tana kiran sa Sadat..darling..
sad...duk yanajin ta hakan bai kula ba ya bar site din mai gaba daya.
Iya bayani tayi mashi amma Gaba daya daren yaki ya saurare ta
She slept unhappy zuciyan ta cike da zimman warware wannan matsalan.
Tasan Kuma hanya daya ne kawai zai jawo hakan shine intaji bayanin abunda ya kawo khaldun site din bahiyya a gobe
And why was she uncounsious?..
Washe gari da safe ma Iya kokari sadat yayi dan ya nuna mata laifin khaldun amma dashike bata gani da idon ta ba so tana tsoron sake tuhumar khaldun kai tsaye batare da taji nashi fashin bakin ko na bahiyya ba
***
Bangare na kuwa da safe ina farkawa na
Shiga toilet a gurguje na dauro alwala nayi sallah
Banmayi wanka ba a tsaban yadda naga time ya tafi so ban tsaya ko ina ba sai site din khaldun
I started making his breakfast nomally araina ma ko tunanin abunda ya faru da ni jiya banayi.
Bread halwa da south indian egg masala nayi sai dai na rasa wani irin juice zan hada masa,gaba daya cike nake da tsoro dan bansan asalin musababin abun da daya sa shi tarin a jiya ba.
But i think That mango juice was poisoned ko hala yayi expire ne oho?
Ni dai tunda na tashi naji ni garau sai bandamu ba..
But Dan na kaucar da irin wannan matsalan sai na tuno da wani recipe din smoothie wanda da hannu na ma zan iya yinsa ba sai nayi amfani da wani processed drink ba.
Da sauri na bude fridge na fara dube duben ingredient din hada shin.
Nan na dauko ayaba guda daya na saka a freexer na kara masa karfin sanyi don kuwa so nake ayaban yayi kankara sosai.
Anan na fito da green matcha tea powder na debe kopi daya,na hado da ground flax seed rabin tea spoon da kopi guda na fresh almond milk.
vanilla extract dina na gefe and finally sai na dauko cocunut na yi shredding dinsa yayi kyau na hade su waje guda cike da kwarewa na hada abunda ake kira "Cocunut matcha smoothie"
Its soo yummy and pleasant to the eyes ga dan uban qamshin shi daya cika min hanci har bana jin qamshin sauran abunda na soya.
Ko da naje ina shirya tray din jan dinning bansani ba ashe Tsaye yayi daga baya na yana ta kallo na
Nasan dai Ya danji dama dama dayaga na warke but his face wasnt showing any emotion.
Bansan yana baya na ba Dan haka da muka ido sai nayi saurin kau da idanuna cikin sanyin jiki hade da tuno duk abunda ya faru jiya tsakani na dashi,wani boye murmushi na nayi sannan nace ina kwana?
Sama da kasa ya kalle ni,ko ya amsa ko bai amsa ba oho,dan ni dai banji ba.
Zama yayi idanun sa na kan wayar sa yana latsawa.
Nikuwa Cucunut macha Smothie din na fara serving dinsa a cup dan haka ya dauki cup din batare da wani tamtama ba ya shiga kurban abunsa.
Abun ya matukar bani bani mamaki Does that mean khaldun sa'ood ya yarda dani?Ko dan yaga nima nasha drink din ne?Nidai Sosai naji dadi araina
Toh har na juya plates kenan zan zuba mashi sauran abincin Sai naga ya dago fararen idanunshi Ya kalle ni sai ya kuma juyawa ya dubi seat din gefen sa
"Sit...ya furta yana kure ni da wani makalallen kallon aji mai tafe da kasaitar data kafa tarihi araina.
...tuni mamaki ya balbale ni don bansan ko naji abunda ya fada da kyau bane ko banji ba.
But wait oo Did he just asked me to sit with him? Ai naji ance babu mai zama dashi anan sai jahan dan ko abokinsa shahrul dayaxo ma banga ya zauna da shi anan ba.
Tsaye nayi ina murda hannu cikin rudani,ina dai so na tambaye shi dan nayi clarifyng
Amma kuma nasan khaldun baiya maimaita magana so i just took the risk sai na matso kusa da shi na ja seat din na zauna a dan dofane.
Shikam Baima sam inayi ba,Looking very calm yaa aje Cup din smothie akan table..ya kalle fuskata dake dan sunkuye.
Da wani irin daddan husky voice dinsa Yace Serve!! Banma san lokacin da na dago ba.
But Ganin tuni ya dauke kansa ya mayar kan wayar sai nima na shiga serving dinsa daga inda nake a xaunen
Halwa bread din na fara ajewa kafin na bi da South indian egg masalan agefe
Ganin yayi rabin smoothie dana sa yasa na kara zuba mashi wani shidai Baice min uffan ba har nagama.
Daga nan Wayar sa naga ya aje agefe sai ya turo min plates din abincin gaba na.
Tsoro yasa nayi rau rau da idanu na,..tunani na ko abunda nayi jiyan ne za ayi min hukunci..but i tot he has forgiven me, a take naji na shiga rudani ma fara tunanin ko dai bai yarda bane?
Ban ko gama haukar tunani nan ba naga ya juya another plate ya aje agaban sa a cikin salon da banyi zato ba naga yana serving kanshi da kanshi..
Waje idanuna suka fito suna rau rau da kansu ina ta satan kallon shi baima san dani ba,duk mamakin shi ya kure min tunani barin ma Yadda naga salon daya zuba abincin a plate dinsa simplified and classic cikin iya tsara space tamkar tsohon wanda ya kwarance a aikin dafe dafe wanda ko ni nasan ban iya ba...
Yana gamawa kuwa ya dada gyara zaman shi,Loma biyu yayi masu kyau kafin ya dago ya kalle ni,..fuskan sa adan daure Yace
Eat"..arude nayi saurin cewa ok..
Hannu na tuni ya daga spoon da fork din amma ban iya komai da shi ba sai mu kaji sallama akan mu.
Jahan ce da kanta ta shigo dan haka a take nayi yunkuri zan mike tsaye Ban ma lura da shigowar subaya da saddat ba sai da khaldun ya balla min wata hararar daya maida ni kan seat dina batare da niyya ba.
Spoon da fork din na dauka idanuna a kasa na shiga juya abincin cikin fargaba
Dukan su fuskan su sai da ya nuna alaman mamakin ganin mu a hakan
To top it all ga abinci agaba na.
Jahan was like is this for real?ta dan kalle mu da kyau dukan mu..
Na dada sunkuyar da kaina cike ladabi da sanyin murya nace good morning mum.
Sai Ta dan dafa kafadata da sauri ta dago ni nikuwa sai cire idanu nake tsaban bugun kirji na,noor are you ok?u r suposed to be on ur bed,Ashe jiya baki ji dadi ba shine bazaki zo ki fada mun ba ko?
A yadda tayi min maganan cikin tsananin kulawa
Duk sai Na rasa me zance mata sai kawai nayi mata shiru
Cikin kasaita mai nuna sanyin bacin rai khaldun Yace mum pls Alaman an yi distrupting din breakfast dinshi kuma baiji dadi ba.
Jahan dai Batace masa komi ba ta narka masa kyakywan idanun ta akan nashi
lips din ta dauke da miskilallen murmushi mai masa alaman ya dakata mata
Yana dauke idanun shi ta dan dafa shi Kasa kasa tace mashi ayi hakuri
..dole ne ya sani na zo nan khaldun,i need To check on my doter.
A dan yangace yace not now mum..karya wa muke yi and i need my space.
Wannan maganan da su subaya ya ke
Nikuwa wannan phrase din nasa na karyawa "muke yi" yasa na dago da kyau na kalle shi
Jahan Tasan halinshi sarai dan haka bata tsaya maimaita abunda subaya da sadaat suka fada mata akanshi da safen ba.
Itama Zama tayi tare da mu Cikin ido ta dube shi calmy tace Aaban,are we good?da kamar zai amsa sai ya basar abincin shi ya cigaba da ci bai ko kula ta ba,ta kalle shi ta dan kalle ni..
Sai tayi murmushi.
Sadat ma ya kalle subaya itama ta kalle shi abun ya matukar basu mamaki
Wani shiru ne ya ratsa wajen kowa da abunda yake sakawa aransa
A Bazata khaldun ya sake Wani miskilillan murmushi wanda ko lips dinsa basu san yayi shi ba sai ya kada kansa batare daya sake daga idon sa ba.
Allah kadai yasan meke gudana aransa a time din
Abincin sa yake ci ya hade ransa,sadat daya ga nayi tsuru tsuru bana iya motsi agaban sa'ood da jahan sai lafe ta kunne yace ma subaya ta je ta dago ni a tsakiyan su,... looking like he cares da razanar da nayi
Babu musu kuwa subaya ta karaso dan ita kadai tasan wahalar data sha wajen shawo kansa da safen nan
Tana kuwa dafa ni khaldun ya balla mata wani mugun harara,amma da shike taga jahan agaban su sai ta share shi tace min get up little sis wa yace miki kizauna anan din zo muje daki,...a hankali na dago na kalle ta sai naga ta na kokarin jawo hannu na.
Wani karar Stop it din da mukaji sai da yasa ta sake ni da sauri ta kalle shi adan tsorace,pls let her have her breakfast....sai ya dan saukar da murya ya bita da kallon dagaske yake
wani mamaki ne ya turnuke subayan har ta kasa cewa komai sai kallon shi data keyi itama...
Agefe kuma bakin ciki,haushi da rudewa ya hana sadaat cewa uffan subaya kamar zatayi kuka ganin dik na razana,jahan dake lura da shi tace pls ka barsu su tafi mana naga kamar ma bacin komai takeyi ba
Bai jira ta karasa ba ya dago spoon dinsa ya debo abincin yana kallon jahan din yace zata ci mana..
Sai ya juya gare ni cikin jan aji ta salon yin wasa da tunanin su, nan ya kawo abincin dai dai setin baki na a hankali yace min open
Chak wajen ya dauke da ji..
Rawa ma baki nan ya fara yi tun kafin na bude shi,yau nidai naga takaina yau ga khaldun of all ppl wai zai bani abinci abaki,.
slowly na bude baki nawa ya sa min spoon din ban ko iya taunawa ba na gumse shi dan mamaki da rudani ya hana zuciya ta sakat
And More than anyone awajen zuciyan sadat kamar zai fice daga kirjin sa tsaban bakin ciki.
Jahan kam murmushi tayi,ta mike tare da cemin idan na gama break in nazo tana nema na.
Ban iya amsawa da words ba na gyada kai,am sure jahan ta fahimci halin da nake ciki alokacin sai bata juyo ba har na dena kallon ta
Subaya gaba daya ta kasa kamu kan tashan.
Dan sosai sadaat ya zugata da safen ma har suka je wajen jahan da magana akan abunda ya faru jiya gashi khaldun sai juya abubuwa yake.
ayadda suka juya ma jahan labarin ta dauka ko zata zo ta samu bahiyyya na kwance awani hali
Sai gashi khaldun is set to suprise them
..babu wanda ya yi tunanin zaiyi abunda yayi yanzu
Khaldun ya cigaba da bani abinci abaki har hawaye suka gangaro min tsaban tsoro ban ma sani
Subaya tayo shiru akan mu dan ko uffan baice mata ba bare ma ya kalle mijin ta
Daga nan Bamu ma san lokacin da sadaat din ya fice ba,sabida inda za'a bude kirjin sa aga bacin ran dake ciki da tabbas gobara ne zai tashi awajen
Da ya rage saura mu ukun,wani kallon barazana yamin ataikaice alaman naci gaba da ci da kaina shi ya gaji,dan haka yana mika min spoon din ya tashi ya haura sama ya barmu nida big sis munyi lumui muna bin bayan sa da ido.
A gurguje ta dan kalle ni tace are you alright?
Uhmm kawai nace Na gyada kai kafin na sunkuyar da kai ina tare hawaye na.
Jira ni anan Ina zuwa...kafin na dago ma ta haura sama ta bi bayan sa.
Kofar dakin shi ta nufa Tayi knock bai