Showing 138001 words to 141000 words out of 225093 words
ta har abada,yasan tunda bahiyya tayi tunanin sadaukar da rayuwan ta akansa babu abunda zai saka mata dashi face ya bata dukkan yardan sa da dukkan kaunar sa
...,kuma yana so lallai yau ya nemi gafarar ta akan abubuwanda ya mata tun farkon haduwan su,a karshe yana so ya kuma bayyana mata sirrin dake ranshi,..
..yanzu yaji kaamil yace za asake musu aure
Yana so ne yayu amfani da wannan daman dan ya bata duk wani farincikin da zai iya goge mata duk wani ciwo azuciyar ta
...ayanzu ji yake babu abunda bazai iya bayarwa sabida farincikin ta ba
...damuwar sa ayanzu bai wuce su fahimci juna ba..
#SURAYYAHMS
Follow @surayyahms
VOTE AND SHARE STORY WITH UR FRIENDs....
_*♡AHUMAGGAH🌺*_
_The love triangle_
_A nigerian historical fiction_
*WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_
_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence._
_bismillahirrahmanirahim._
*For my durling Ahumaggaress siyamah ibrahim*
*And all members zauren littafan hausa da*
*Taskar billy galadanci*
_3⃣6⃣-frail heart♡_
Forgive my typing errors i wll sort it out a next page.
tare da sauke ajiyan zuciya Hannun shi duka biyu ya zura cikin aljihun wandon sa Yana tsaye yana bin closed doors din da kallo kamar marar aikin yi.
"..Minti uku masu kyau ya dauka bai motsa ba..,shikansa yasan Daurewa yayi ya bar wajen dan kuwa yasan shiyafi bukatar ganin ta ayanzu fiye da kowa,ita kuwa bahiyya daga shigar ta dakin ta doka sallama..
'Sallamu alaikum" sai Ta tsaya daga baki baki bata shigo ba
Tayi sau uku ba ansa ba,Da har zata juya ta fita sai tajiyo muryan sa daga dayan part din
"2 minute pls"
Ta dan tabe baki fuska ba yabo ba fallasa ta dawo ta nemi waje ta zauna
cike da nitsuwa take jiranshi
Bai fito sarari ba amma ko ina adakin ya dau qamshin wanderlust wato iren turaren mazan nan masu karfi da dadin qamshi.
Babu tantama tagane yana daga closet ne, after like 3minutes ta dan motsa.... Jikin ta ne kawai ya bata ya shigo tana juyi kuwa taganshi jingine da wall scounce idanun shi tsam akanta kamar yaune ranar daya soma ganin ta arayuwar sa,ya fito rass dashi kamar babu abinda ke damun shi,Golden Versace shirt da bakin wando ne sanye ajikin shi.
.. mikewa tayi tsaye batare da tace mashi uffan ba,soft and girlish drape skirt da pink top din ta ya dada kara fallasa tsarin kyaun jikin ta tasan shi ya dauke mashi hankali,..
Tunani take ko ta fice ne ma kawai ta bar mashi dakin
Sai taga da sauri kaamil din ya dauke idanun shi yana mai gyara zaman haddaden golden clive cristain watch Dinsa cikin salon basarwa da nuna alaman baiji komai aranshin ba.
"ganin tayi shiru ta nitsu kamar marainiya yasa shi ya karaso inda take..,jin saukar iska a fuskan ta yasa ya ta farga suka hade ido bata dena kallon shi ba...he looks cool amma fadawar da yayi a kwana biyun ya nuna a jikin sa da idanun sa sosai
...murmushi mai sanyi yayi,cikin muryansa mai dadinji yace cupcake..
Batayi kasa agwiwa ba tace
Ya jikin?
Bai amsa ba
...adan rude ta sauke kanta bayan ta furta hakan
Wajen Yayi shiru sanda ya nemi waje ya xauna cike da neman tsokanan ta cikin saukakkeen sautin murya yace twinkle ta cupcake kenan, sai yanzu zaki zo gaishe ni?..ok..sai ya tabe bakin shi..,ba damuwa ni nayi fushi ma.
Wani kallon kasan ido tayi mishi..cikin rashin sanin me zatace masa
.....ta turo masa
Baki a hankli ta furta kayi fushi?to ai shikenan,nima bana yi....Ba cewa ma mum karya ake maka bakace kana so ba?...meyasa kayi karyan toh...nima karya kake min ko?
..yar tsirirayar dariya ce ta kufce masa.. shagwabben sigar fitinar nata yake duba dan ya lura kamar she is serious about what she is saying ....
wani bata ranta take neman tayi ta masa surutu
..yace hey babe..sit down zan fada maki gaskiyar toh..
Ta basar shi
"Nifa bazan zauna ba,kawai dama nazo ne ince dakai ya jiki...im going Allah ya kara sauki...
A bazata ta wani hade rai cikin fushi zata fice,jitayi an riko hannun ta dam dam an dawo da ita"look ni bana son fitina...ya dawo da ita normal position din ta,claiming sturbon ta kau da kanta gefe,..she is intensed,kuma sosai take jin wani bangaren xuciyan ta ya amince da hankali da nagartan kaamil
Ayanzu ma shawarar sa take nema amma bata san ta ina xata fara ba
Ayayin da take kau da kai..cikowar hawayen ta da suke neman subuce mata ya gani muryan sa na dan shaking yace twinkle cupcake dina wai me haka ne?...me yayi zafi
"..Ta share sa ta dada bata ranta kamar bashin maganar take binshi na asali
...Kinsan dalilin dayasa nace musu hakan ne?
..im not lying to u bahiyya,Ba karya nayi ba.
kawai bana son kowa yasan nace ina sonki ne Sabida wallhy na hakura dake har Abada..
ke matar dan uwa na ne yanzu
...even if i know ur love derseve a fight back from me
..amma saood ya fi karfin komai a waje na...Ana barin halak kodan kunya ko?..
Tin da ya zage yana maganan nashi bata daga ido ta kalle shi ba,Dada sanyi jikin ta tayi data ji wayannan kalaman nasa
Da sautin magiya
...yace kar ki bata ranki dan Allah kinji
...comon sit let me tell u who saood is to me nasan zaki fi fahimta ta
...jikin ta ya mutu amma bata so ya fahimci hakan,a haka ta kyale shi ya jawo ta dan dole ya aje ta kan cushiion dinsa,shima gefe da ita kadan ya zauna yana fuskantar ta
Nan ya fara bata labarin rayuwar sa da saood tun suna kanana...
Tayi shiru ta nitsu..,dukan hankalin ta ta mayar kanshi har ya gama bata labarin
Cike da kyakwar nazari a kwakwalrta sai taga kamar Kusan abu daya ne ya faru daga cikin labarin amana da sadaukarwan da ke tsakanin ta da junnut babu maraba acikin labarin face su da suka kasance yan uwan juna..
Kaaamil ya bata labarin yadda saood ya dawwama acikin sadaukar da farin cikin sa da rayuwar sa akansa tun suna yara har suka girma..
Yace cupcake,zan iya fitowa bodly nace shikadai ne zai iya mallaka min ranshi babu tantama...
wani labarin daya rike aranshi tsawon lokaci bai manta ba ya shiga bata atlast yace
Alokacin da mukaje wani yakin hadin kai cikin wani makaken jeji achan kasan syria,..yaki yayi muni sosai dan munyi kan biri da makiya kuma munsha wuya sosai nikaina da harbi uku ajiki na nake numfashi.
ayakin duk sojoji na sun mutu saura nikadai,hakan yasa aka hada da taimakon team din sa'ood har aka samu sassauci.
To kusan dukan mu da raunuka masu nauyi ajikin mu bazaiyi mu cigaba da ayyana komai ba
Aka bamu other daga sama akan mu bar wajen cikin minti 10..100mtrs run tsakanin mu da jirgin mu kuma jiki na yayi laushi bana iya daurewa sosai..
saood ne comander so ya sa aka rirriko ni
"Daga nan Gudu mukeyi kowa na neman ceto ransa at dying minute wani sniper ya harbe wanda ya riko nin sai ya sake ni ya fado gawa agaba na
tsoron kar nima asame ni yasa na dunkule awajen naki na ta shi,..
...da ba aganni ba so,atake aka bada saood oder ya tuka jirgin da ni dama ya kamata na tukashi
Ga Abokan gaba suna daf da riske ni niyyar ogogin mu alokacin shine a barni ajejin su suyi tafiyar su,saood ya kasa hakura kwalla min kira yake againts oll odds yana nema na,anan sai da ya rufe idon sa ya taka babban dokar kasa ya kuma saka dukan rayuwar sojojin sa a hatsari Dan ya ceto rayuwa na...
Kar kice dayayi hakan ba asamu nasaran kashe su ba,amma babban laifi ya aikata wanda yasa aka azabtar da shi azaban da ko mahaifina daya haife ni bazai iya karban rabin shi sabida dani ba...
Da muka dawo kwana uku bangan shi ba,aje shi sukayi a dakin horo He was beaten and tortured by a wicked comando..
..kwanan sa sha hudu a prison sanda suka galabaita shi...kinga wannan labarin?bazan taba mancewa da shi ba a kundin tarihin rayuwa ta..
Har yau nasan iyaye na da suka haife ni ma baza suyi min hakan ba.
To meye soyayya da bazan sadaukar masa ba?
..agani na wannan wani dama ce da Allah ya bani dan na saka mashi da iya abunda yayi domina arayuwar sa
..kaamil din dakike gani ba shi bane idan babu sa'ood.
In kinga hali mai kyau awaje ne ya birge ki dauka Shi ya bani tarbiyar sa..
Ya kalle ta calmy with much seriouness a muryan shi..Kiyi hakuri cupcake nidai wallhy na hakura dake.
..ki rike min shi amana kinji?. bro yana son ki kuma kece mace ta farko a rayuwar sa..
Labarin san ya bata tausayi,kallon sa take duk dama hankalin ta na kan
Yanayin mood din daya dora akan fuskan sa
Wani Nannauyan ajiye zuciya kawai ta sauke ta masa shiru kamar mai tunanin wani abu aranta,..cikin ranta har mamaki take yi sosai daya kasance
Rayuwar ta kusan iri daya ne dana mijin ta saood
thy always secrifice..
farin cikin su kullum na wasu daban ne bana su ba.
Yanzu kam Ta fahimce kaaamil din sosai.
,...taso ace haka junnut ma tayi tunani..but ta bata uzuri..ta karbi rashin gaskiyar,but a ganin ta bai dace suyi nisa cikin wannan hali batare da sun fahimci juna ba.
Tayi ajiyan zuciya ta dago ya kalle ta..,nan ta gaya masa abubuwan da ta raya aranta game da al'amarin tana mai wayar masa da kai akan kamancecceniya dake tsakanin yanayin rayuwar sa da khaldun da wanda tayi da kawarta junnut..
Ayanzu Tasan ita khal ya fara cewa yana so ba junnut ba,amma yanayin yadda junnut ta birkice yanzun shine take neman shawarar sa akai.
Rimi rimi ta gaya mashi abunda suke ciki da junnut ayau din.
Akarshe Tace mashi"wallhy She is upset with me, bata taba yin fushi dani irin haka ba..muryan ta a maraice looking so down to earth kamar marainiya ta karashe
Dan dariya kawai Kaamil yayi,he relax his head first kafin ya dago ya bata amsar ta
"ai halin ku ne na mata,wai ku kishi,.
Dama dai haka kawar ki takeyi
Ko a Us ma ita dai dama bata da hakuri ne..
Am sure da wata daban ne ma da zaki ga drama Amma nasan tana sonki sosai,ki kyale ta kawai intagama fushin zata fahimce ki...
"Tace Allah ko?..sai naga kamar bazata yafe ni ba...taki fa ta saurare ni..kaamil yace chill cupcake,just let her be..
kedai kije kiyi tunani shin zaki iya zama da ita a matsayin kishiiya? if ure sure zaki iya din,sai ki fada min.. toni zan tayaki mata bayanin komai zakiga komai ma wuce..
Bahi ta sauke numfashin ta cike da sauke ajiyan zuciya ta kalle sa tana masa godiya.. ..
murmushi kawai yayi baice uffan ba yafara tsokanan ta yace mekeki shirya mana ne na honeymoon..saura kuma akashe yaya na da soyayya...
Ta harare shi ta dan turo baki kasar wuyar ta ta furta,wani soyayya?
Ya gwalo idanun sa dake kin buduwa da kansu Yace ahh baki son shi ne?nafa san kina son shi...
Tace nidai bance ba,aifa shima cewa kawai yayi a aura masa ni bacewa yyi yana sona ba nima bance yamin ba..
Ya gwalo idun shi
"So R u managing him?..tun kafin ta bada amsaa kaaamil ya fashe da dariya yana kallon ta...cikin salo ta tabe bakin ta kamar zata sake fuskan ta amma sai taki sam
"ni dai wallhy bana jin wani soyayyar kawai dai an mana Aure..."
Yace hey kifadena fada min haka..so nake kafin azo hidiman bikin nan naganki da little Aaban kina turowa..
Tayi saurin rufe fuska da tafin hannu, da dan zakin sautin murya tace mashi what?little who?tab di..ta turo baki
Yana murmusawa Yace miye?..what is tab di..yanzu ke me kike so yamiki bayan kinsan ba laifin shi bane yayi fushin dake
Ta sauke hannun da sauri ta harare shi.."...ba laifin shi ba?wato nice zan na yarda da shi nikuma bazai yarda dani ba kenan ko,he knows me more than anyone . ya rufe idanun shi daga yaji ance nayi abu sai ya fara min wulakanci...
Ni wallhy na dena son nashi.
ta langwame wuya a lalace tamkar daga zuciyar ta furucin ke fita tone din voice din ta cike da mita
Dariya kawai kaaamil yakeyi yana mamakin ta, tsokanan ta ma ya shiga yi yana cewa karya kike wallhy kina son saood
Ta bata ranta tana kawo masa reasons din ta bai dau abun serious ba,..duk dama yasan da gaske takeyi..
Ganin ta mike zata tafi ya tashi da sauri yace sister twinkle wai baki san wasa ba?To me kike so ayi masa dan ki huce..uwar gida, ran gida ina jinki sai yaya kenan?
Tadan harare shi tace nidai kawai ka taimaka min na rama,ni wallhy sai na rama ..dan bana son yaga kamar bai cutar dani ba..
nima fa mutum ce ai inajin zafi araina.
In ba huce ba bazan dena ganin shi da abun da yayi ta min ba
Kaamil ya waro idanun shi yana kallon ta
"Amma dai kinsan bada son ran shi bane ko?
Tace eh..nima ai bada son raina bane
Yace ok to me zan miki,tayi shiru can tace mashi ranar da mukaje abuja jahan tace mashi ya sake ni..but i know he wont..kawai dai zan nuna mashi bana son auren ne..so that he will learn how to value it..
And i want u to be my acomplice...ta dan kalle shi da gefen idanun ta silently ta furta hakan kamar wata munafuka
Kaamil yaja cheeks din ta yana murmuushi yace ok..amma nidai kar amasa da tsauri ...kinsan bro akanki fa baida wani dauriya
...hararar sa tayi cos she dont realy belive that saood yanason ta..nidai kayi min alkwarin... yace promise duk abunda ake ciki ki gaya min..
Haka suka rabu ta koma site dinsu,
junnut aranar gaba daya bata fito ba,tana kwance akan gadon ta bataci ba bata sha ba juyi take yi from one end to end tana jin tsananin kishi da zafin al'amarin.
To bawanda ya sani har ta aike hilda wajen bokan su a india akan a duba mata kan maganan
Inda halin raba auren a saukake tana bukatar ayi hakan da gaggawa
Tuntuni take latsa wayar ta, kirar wayan hilda ta take amma bata dauka ba...
Ayanzu ji take ko zata mutu ne bazata iya sharing saood da bahiyya ba,gashi tana son ta kam.. amma bata jin zata iya saukowa ta saurare ta akan sa'ood
iya dannewa tayi amma zaman kishiya da kawartan har yanzu yaki kwanta mata arai.
Wuraren 8:30 saood yatashi da kyar, ya shiga bayi yayi brush yayi wanka yayi alwala, yadau mai ya shafa sannan ya shirya cikin dogon black jeans da soft cotton t-shirt maroon bakaramin kyau kalar yamai ba,cikin nitsuwa ya shafa man gashin shi dake kara saka gashin kanshi kyalli sannan yadau turaren shi mai kama jiki ya fesa kafin yahau dadduma yay salla raka 'a biyu yana idarwa ya mike yana kallon agogo dan baida lokacin yin azkar din sosai, takalmin shi mai kyau ya zira sanan yadauwayar shi ya fito ya nufi inda ya shirya musu yin date din su
A cahn sama ne a bene na karshe dake gidan,inda babu hayaniyar komai bare sautin maganan kowa.
Bai bari kowa ya gansa ahakan ba,dan musamman sabida bahiyya yayi wannan shigar..
A sama chan inda ya shirya date din shiya fara isowa komai yayi ras dashi wajen shiru daga shi sai hasken watan Allah.
...Ya tura mata sakon text few minutes ta amsa da ok..shiru shiru bata zo ba kuma a kowani sako ya tura mata zatayi reply dan ma yasan ta gani,tun 9 yake Jiran ta shiru har 10.30 ya gauce bai ganta ba...
Bai dai nuna wani alama na bacin rai a fuskansa ba still He called her,yayi ta kira har ya gaji bata daga ba..
Ya tashi ya tsaya yana waige waige chan ya sauke ajiyan zuciya cikin ransa Abun baimasa dadi ba..
,cike da naci ya jira har 11oclk daya ga ya cika sai yaji baxai iya ba sai ya sauko yana ta jin haushin abun aransa,adaidai zai shige site din san suka gamu da mahaifiyar sa maids guda biyu suna binta da trays wanda baisan meye aciki ba..
Ya dan rusuna da sauri..
daga irin kallon data ke mashi ma kawai yasan ta yaba da kwalliyar nashi..
Yace fatan lpya naganki haka ?
ta amsa mashi da ka Tana mai dan daga idanun ta akanshi,ita dai har ila yau tana fushi da shi akan auren hushe haushi dayayi da noor din ta..
sallamar bayin tayi kafin tace masa dama ina neman ka.
Yace ko zamu je site dina ne tace ah'a...
ba wani magana mai tsayi zan maka ba,tasani sarai yaji cewa za sake renewing auren nashi amma sai bata maimaita masa ba,aranta bawai bata son auren ya dawwama ba ne amma ita so take ta gasa shi sosai dan ko a mafarki bata so ya sake tunanin zai jefa rayuwar bahiyya a wani matsala tunda tasan nan gaba wani auren iyayen nasa zasu masa
...sai tace angel banji kace komai ba, kar kaga nayi maka shiru kadauka ko zaka rike min yata a kyauta..she is not a comodity da zaka aure ta yadda kake so...to me auren nan naka is invalid
...noor ai maza dayawa na nan zasu zo sunemi auren ta a mutunce ..
As for u Is eida kaje kasakar min ita ko kajira na tambaye ta muddin tace min bata son auren nan
Ba mahaifin ka da kakar ka ba koma waye yakenjin zaisa maka baki wallhy sai na warware shi..
Wani mugun mugun faduwar gaba yaji,a hargitse ya dago ya dube ta da fuskan magiya xaiyi magana ta tsare da da manyan idanun ta tace in kaje ka turo min ita da safe..gudnite
Ya mike Muryansa har na rawa Yace ok ..1 secnd bata kara ba ta barshi awajen.
Yayi luff Yana kwance rasa inda zaisa kanshi yayi gashi yau kwana uku kenan rabonsa da su hada daki daya da matar san ga haushin rashin zuwan ta date din nacin shi a wuya jiyake kamar zai shake shi..
Babu irin tunanin da baiyi ba..shi ayanzu tsorone yake neman shiga zuciyar sa game da al'amari..
Sam bai gane me suke nufi da shi ba
Da safe yana idar da sallah plain black vest ne ajikin shi ta dan matse shi wandon sa itama na sport fari da vertical strips kanshi