Showing 150001 words to 153000 words out of 225093 words

Chapter 51 - AHUMAGGAH COMPLETE HAUSA NOVEL

06 Jan 2025

26819

wani buga sai ta waigo a tsanake,Jikin ta ne ya fara bata khaldun is already here looking at her

ganin shi akansun ya sa ta hade ranta da sauri..

Kallon su yake da gefen idon shi idanun sa sunyi luff alaman kishin ta na damun sa matuka har ji yake kamar zai shakure ta.

Duka su biyun Suka share sa,Bayan ta cire shoes din mai gaba daya Kaamil sai ya sake ta yana yake yace

Gudnite cup...c..ake

Wani harara khal ya banka masa to bai jira jin amsa ba yayi sauri ya bar wajen

Itama sai ta yunkura Zata bishi a aggauce khal ya fizgota yana cigaba da mata mugun kallo..,ya bude baki zaiyi mata magana tayi sauri ta riga shi.
Site din su zanje
"Nifa sauri nakeyi.."
Kallon ta kawai yayi yama rasa me xaice mata,"move"..ya bata rai ya tura ta hanyar site din su

Gefe ta koma Ta ja ta tsaya cike fa taurin kai tana cewa "nifa wajen shi zanje..

Wani miskilyar kallo ya mata yace Kina wasa da nine?

Ta dauke kanta kammar bada ita yake ba,ihu ta tsala jin ya cafko hannun ta d karfi yana jan ta zasu bar wajen.
Ta dadage tana fincika,."Let me go,ana dole ne?..ni bana son zama dakai,ai mum tace maka sake ni,ni shi nake so.. ai ba dole bane naje bacci dakai yanzu,nidai ka kyale ni..banayi

Tsaban hanjin cikin ta ya kada Ita kanta bata san metake cewa ba muryan ta sai shaking yake yana ta fixge hannun ta anashi duk a aikin banza

Har suka isa room dinshi Khal bai ce mata komai ba,ya turata jikin bango a fusace ya juya mata baya yana calming kanshi

"har wani karkarwan sanyi ta shiga yi don tsoro amma ko kadan hakan bai nuna a fuskarta ba.

Drawar dayake aje guns ya nufa taji kamar ta tsala ihu sai da Ta jira ya fito sannan ta dauke idanun ta akansa.

Da Bata ga komai a hannun shi ba sai ta ja karamar tsuka
ta shiga jan kafarta da kyar tana bin sa a baya.

,. "oh ko wani irin hukunci kuma xai mata yau,kin shiga falon san tayi ta tsaya daga bayan shi, Khal ya dau wayar sa bai kulata ba ya fice,wajajen 10pm ya dawo kwance ya sameta kan 3sitter ta juya baya a falon nasa kamar wacce ta dade tana minshari,

ya karasa kusa da ita a hankali ya duka yana lekan fuskarta don duk a tunanin sa bacci take, ido hudu suka yi ya koma baya da sauri ta mike xaune fuskarta a daure ahankali tace "meye kake wani lekana" dauke kai yayi ya nufi kofar falon ya bude yana nuna mata waje yace "zo ki fita"..mikewa tayi kamar zata fice daga dakin tana tafiya kamar xata tashi sama ya bita da kallo har zata karasa sannan ya jawo ta ta fado jikin shi

Ta make muryan kamar mai shirin yin kuka
"Ai kai Kace na fita maka adakin ...ta hade rai

"Yace ashe baki da hankali?..wai meke damunki kike jin kanki hakan,ohh an daure miki gindi ko?..toh
bakomai,.bari kiji.. Ki gama dik haukar ki ki bari zaman auren nan sai kinyi shi ,a kina so ko baki so..

Tana dagowa ta banka masa harara Ta fashe da kuka mai sanyi,"haka kawai taji ranta ya baci dayace ko tana so ko bata so din nan..

Azafafe ta fincike jikin ta anashi tace
'Ni matar ka?Allah ya sawwake I will neva be ur wife..i neva want to..cikin wani matsancin sautin kuka ta karashe tana sunkuyar da kanta kasa

"..kawai dan bani da gata?to ni ba haka nake son nayi rayuwa ta ba,i want someone that care for me,someone that trust me,ni bazan yi zaman auren dole ba.
..
"hakan datace ya kashe masa jiki da sauri ya sake ta ya juya mata bayan shi amma bata fasa ba

" wani sabon masifa ma takw mashi cike da rawan murya da tsoro
What makes u think
U can force me,i migh have been ur maid before amma yanzu ni ba baiwar ka bace..

"I understand,ka aure ni dan cikar burin ka ne...but have u eva imagine what i want in my own life?ka taba tunanin ko ina son auren ko bana so?I was just tryng to protec us,now i want my freedoom..

" baijin dadin inta nacewa hakan sai ya juyo da razannun idanunsa yace
"U want ur fredoom to be with my brother??

Tace Yes,what difernce does it make to u ..ina ruwanka da hakan..its my life
In kaamil na zaba so be it

"shut up,wata tokarriyar muryansa ta dakatar da ita
Toh da aurena akanki... sai ki jira freedom din kigani ko zan baki shi

Tace Fine ... kar ka banin i will give my self.

Ta juya a mugun fusace zata fice ya finnciko ta ya hada ta da bango..wani raxannaen kuka ta fashe da shi ganin ya mugun daga hankalin sa har jikin sa na rawa kamar wanda zai mare ta

Yana kallon ta hakan sai yaji ya kasa komai "He is lost..wani mugun bugun zuciya ke taso masa mai tsanantawa,Yasan akwai kuskure sosai a al'amarin kuma duk laifin shi ne mafi akasari.

Yana son yarinyar sosai amma yana jin kamar he lack the potential to make it up for her.

Damuwar baifi Taya xai sa ta gane cewa shi baisan zafin soyayya ba sai akanta

,..Idanun shi a take suka kada sukayi ja Yarasa meyey xaiyi gwara daya dazai sa ta yafe mashi ko ta fahimce shi

Bahiyya Kuka mai sauti take yi tana kare kanta da fuskan ta da taffin hannun ta a tsorace tana cewa
"Dont touch me pls..."Im not ur wife..
Duk saita birkice masa Sai yaji duk tausayin ta ya kama shi,ganin yadda t takure tana kuka sai yaji Wani turirin hawaye na neman taruwa a idanun sa shima,musamman in yanajin tana ce masa ita ba matar san bane..

Hannun shi har rawa yake ya dunkule yana huci,aransa sosai yake jin haushin kansa,Ya buga wall din datake manne da shi in a slow and defeating manner kamar wanda ke cikin tsananin rudanin,wani rufe ido tayi Ta kwala ihu arazane..jin ba ma ita ya sauke ma naushin ba ya sata ta sulale kasa bayan ta jingine da bango ta cigaba da kukan a rude.

Ya tsaya gaban ta bai motsa ba Gabobin jikin sa duk sun mutu Ya rasa me zaiyi mata guda daya,chan sai ya durkusa zai tallafota cikin sanyin murya da lallami

Bahiyya.....twin. .

Tayi saurin katse shi azafafe
"Get out ta tura sa a firgice..ni ka barni..ka fita.. ka fita
...Go away...im not ur twinkle

Alokacin Ji yayi kamar tana tsaga xiciiyar shi

Ta mike tsaye a zafafe ta shige tura sa cikin tsananin fushi like she is very upset and tired of him.

Wani karayar gabobin jiki ne ya xiyarce shi,Khal yayi sanyi abun tausayi
Ya kasa ce mata komai

,..Gaba daya jinin dake bada jijiyoyin jikin sa saida suka amsa,ya zamto kamar bai da laka, ahaka har bahiyya ta tura sa bakin door ta rufe kofar yana ta kallon ta baice uffan ba..

Bayan ta rufe ta aje bayan ta jingine da door din Ta cigaba da kuka,shima bai motsa ba idanun shi ya kure kofar da shi kamar ita yake kallo

Maganganun ta yake masa yawo akai,zuciyar sa ta riga y shiga wani mugun halin nadamar duk yanayin yadda ya dauki raywar sa da bahiyya..

Bai tashi sauke dan karamin tears ba sanda ya jingine yana mai dora kunnen sa ajikin door din,duk kukan datake yi yayi tsamm ya lumshe idanun sa yana jiyo ta a cikin kunnen sa with each drop of her tears din sai yaji wani axaban zafi aransa sosai

Idanun shi na dama ke fitar da hawayen,dayan idon abushe kamar baisan ma anayi ba..wani fat fat
Kirjin sa ke bugawa
Yafi awa biyu awajen yana kaikawo da ita a cikin tunanin sa..

Sai yaji duk bai kyau ta mata,he tots she will understand evrything dan kanta amma ba haka abun yake ba

Idan ya tuno ko sau daya baitaba cewa yana son ta a gaban idon ta ba sai yaji duk gabobon jikin sa sunyi rauni

Bahiyya dake wajen itama tayi shiru tana shessheka tana ji yana knocking amma bata kula ba har yayi ya gaji ya bari..dan karamin tsaki taja tana jin kamar wani nauyi ta sauke aranta data masa hakan

daurewa tayi ta wuce kan gadon na sa tayi kwanciyar ta
'Cike da suke ajiyayyun numfashi tana kwato dim eyes din ta,dan Wani hutaccen bacci ke neman daukan ta.

Chan ta waigo ta dubi dayan gefen Jikin ta ne ya bata khaldun na kallon ta tana juyi kuwa sai taga gashi nan tsaye ta back yard din dakin ya dafe jikin glass wall din dakin, Nan inda ya taba barin ta kwana On Her first weding nite...

Ta taso ta zo da sauri ta danna ma kofar security lock..

Yana kallon ta banka masa harara ta dauke kai yanaji yana gani ta janye curtains din bata sake duban inda yake ba...

Ya shafa kanshi,yayi wani furxan iska mai rauni waje ya nemi ya zauna ya hade kanshi da gwiwa..

Almost 3hrs bai dago ba tsaban yadda ya nitsu yana famar tunanin rayuwar su..

Yasan Bahiyya dersev his love his craxinest his other special part da yake dannewa..

dan aynzu ji yaje in duniya ne zasu taru akansa dan yace zai iya rabuwa da ita bazai iya ba.

Ya dago jajayen idanun sa yana mai sauke wasu wahallalun nunfashi

,mikewa yayi yana zagawa ta kasa yana kai kawo yana mai cigaba da tunanin ta..

Ji kawai yayi an dafa sa ta baya,ya jiyo adan gaggauce
Sukayi ido da aunt murja sai kallon shi take bata kifta ba..ya mata kallon sunna ya dauke kai,fuskn ta ba kwalliya hijabi dogo fari har kasa tasa hannun ta dauke da carbi.

Tace mr Prince of persia..me kake anan

"Ya share ta,Dik jikin sa a sanyaye yake baijin dadin zuciyar sa sai ya ki ya ma sake kallon ta ya juya kansa gefe

Aunt murja tace tofa"Yau dai ranka ba abace yake ba, naga alaman wani abu ne ke damun ka...Whats wrong,?ta karashe tana gyata tsayuwarta

Da Kamar zai cigaba da share ta amma sai ya juyo ya dora mata razannun idanun sa da suka rine da damuwa..

"in fada maki damuwa ta dan ki samu na cusa min bakin ciki ko?

Wai ma Meya kawo ki nan ne..gobe dole a zanja min dukkan masu aiki anan

"Incompetents"

Ya furta kasan makoshi..ya dube wrstt watch dinsa 2pm in the nite ya ja tsaki

Aunt murja dake binshi da kallon kurel mai cike da kulawa da nitsuwa ta furta

Tace nidai banda time dinka wllhu"Sallah nayi..sai na tuno da piece din jewry inaga anan ya fadi

"Yace uhm ..Ya dauke kansa tun kan yayi responding tace"gen sa'ood hamood pls can we have a word?

Ya daure fuskan sa ya kalle ta ta zuba masa idanun ta itama...

About wat?
Meye ne sai kin takura ni..cikin dare

Murmushi mai ban tausayi tayi ta jawo hannun sa dan dole ta xaunar da shi,..

Ydda take binshi da ido ya sa shi ya kasa boye mood dinsa sai shafe fuskn sa yake da tafin hannu yana sauke ajiyann numfashi,

"Why r out so late..ni kar kamin karya kwana biyu na lura baka shigowa da wuri..ko duk akan raba auren ne.

"Murja pls Dont start,..

dont start what?Tayi sauri ta tare nunfashin sa

Ok fine ..ya jingina kansa da chair..yana kallon ta da gefen ido

"Daki na is locked shine matsalar..sai ki kama hanya ki tafi

" aunt murja ta gwalo ido..tace i see

Ehen, Bahiyya kuma tana ciki kake waje?Meyasa bazaka kira ta ta bude maka ba,if mum hear of this kasan dai bazata ji dadi ba jibi yadda idanun ka sukayi ja,Saood walhy bacci kake ji

"Yayi tsaki yana tura hannun ta dake shirin ware idanun shi,

Ke Ki barni..she is...she locked the door ..idanun sa take suka lumshe kansu daya furta hakan.

"Aaban tell me something,wai kuka kake yi ne?

Yce ke Dan Allah ki rabu dani...

no i wont..meyasa kake kore duk wani abun da zaisa maka farin ciki..yayi mata shiru dada lumshe idanun sa yayi .

"I know u had a fight with her kuma ni ina bayan ta,sabida kwatakwata bason yarinyar kake ba

Yace ko?ya dago ya banka mata kallon banza..
"Waya fada maki.."

Ko tsaban iya samun idon da kike yi yasa kika shirya hakn

"Stop pretending Aaban..muryan ka har na rawa..ure hurting deeply
Ure not even ok..

Sai yayi shiru kamar ansa shi ya lumshe ido

Cike da nuna damuwa da seriousness aunt murja tayi tsaye gabansa bata kifta idanun ta akansa ba

Ya bude lumshdhun idanun sa kamar mai shirin fashe mata da kuka yanaji aransa kamar yayi dismissing din ta amma sai yaji ya kasa yin hakan...

Ta lngame mai wuya cikin sanyin murya tace "Gobe fa ummah zata sake jin shawarar da kuka yanke kai da bahiyya.

Ai Naji jahan tana gaya ma hjya komai toh wallhy zasu maka abunda baka tsammani akan yarinyar nan

..what have u done yet.?ko ka hakura rabuwar kawai zakuyi?

Cikin mugun yanayin sacewar zuci ya girgiza kansa yaki ma ya hade ido dabita dan kar taga hawayen shi...a hankali ya furta"I dont know..yayi ajiyan zuciya cikin wani sarkaffafen yanayin da sanda taji tausayin sa ya kama ta.

Tsawon mintuna uku Wajen ya yanke tsit,yayi tsam Yana shanye tarin zafin da ke hurowa acikin ranshi..

Da kyar ya iya bude idanun sa da suka mugun bayyana halin dayake ciki..

Tace Talk to me...ant ta furta cikin sassanyar murya yadda zata dada bashi himman jin ta damu dashi sosai

yana gyara zama ya sauke wata kasallaiyar ajiyan zuciya

..saood pls speak..ta fadada sautin sanyin jikin itama tana gyara zaman ta alama ya nuna cewa yanayin sa ya dan daga mata hankali.

Yace I love her..

Wallhy ina son ta kuma nasan tana sona..anan ya sunkuyar da kanshi kamar dan karamin yaron dayayi laifi

..nidai dan Allah kuyi hakuri kar ku raba nida ita

Ya maida kansa kasa kasa ya wani lumshe ido kamar ranshi yake fitawrwa mai gaba daya..
In kukayi min hakan bansan ya zanyi ba

Sigar tausayi aut murja ta kalle shi,"Saood u love her,kuma kasan tana sonka to Me kake jira ne tuntuni?why r u having so muuch feuds wirh her

"Ya dago..yace Murja daga nine badaga ita ba,i think im not being easy on her,yanzun ma fada take dani,tayi fushi sosai, kamar tagaji dani,Ni bansani ba,tace ina sata zama dani dole,kuma na aure ta ne dan cikar burina..and she did it just to protect me.

"Nayi mata laifi,i know...i tried to see ko zan shawo kanta idan anyi renewing auren nan amma
..naga ta nace sai ta rabu dani wai kamil take so?
.
Nidai I cant bear it...mezanyi ne..how will i go about it..o think zan iya mutuwa kan wannan abun..u have no idea how much i love her

Tayi sauri ta riko hannun sa dan tayi calming rawar da jikin sa yake yi A hankali..

"Relax.. ta fada tana kallon shi kamar bata son wani yaji su..

Khal ka aje hankalin ka waje guda ka dena daura makan ka damuwa da yawa..

Its true that kaine makasudin lalacewar abun,shud i tell u ur mistakes?

Rana na biyu dataga saukar hawaye a idanun sa,

Yayi sauri Yana gogewa yaa gyada mata kai

Wani azaban sanyi taji jikin ta yyi,..sai ta daure ta karaso kusa da shi ta riko hannun shi as in heart to heart talk

"Ure not too hard on her,yanayin rayuwar kane yake affecting din situation din ka..bahiyya karamar yarinya ce she is just 19 goin to 20 u need to be gentle with her

..baxata yi wani tunanin da kai ko ni ko su umma zasuyi ba. .Ni Tunda naji abunda tayi akanku dan ta kare ku daga sharrin sadat nasan yarinyar tana matukar kaunan ku.

Dont you think she deserve the other you?sa'ood nasan ka fa..ure so special ta wannan faniin
Kasan xaka iya bi da kowa ta irin mace in kana so

Sa'ood soyayar taku ce fa kai da ita kunajin sa aranku
Ai yarinyar tayi kokari ko?
...to ya zakayi kai ka rike naka aranka sannan kayi tunanin zata fahimce nauyin sa

...she wont understand that u care..kuma a kullum gani zatayi kamar aikin banza ziciyan ta yake yi akanka
..da haka kuma har zaka rasa ta.

Nasan zaiyi maka wuya ka canza kanka ma wata, amma kayi tunani sosai shin son dakake mata yakai ka sauke mata kai kuyi rayuwar amana da amana,so, kauna da kwanciyar hankali?

In yakai then u better act fast,ure intelligent basai an gaya maka me xakayi ba ..kar ka bari gobe yayi axo a akwace maka soyayyar ka akan abun da bai kai ya kawo ba...

Bet me zaka fi shan wuya fiye da yarinyar ita ai yarinta ke damun ta...She just want to know if u love her..

Tana so ne tasan gaskiyar abunda yake zuciyar ka,sabida tasan kasan tana son ka.

Ya bata shiru yana jin ta tana gaggaya masa zantuka irin hakan,..sai yake jin ba saukar da kai ba koma miye ne ayanzu km bazai fasa ba zai iya yi ma bahiyya

Har tagama Baice mata komai ba sai ure right..

Tadan lallashe shi cike da nuna damuwar ta,har tana dada wyar masa da kai akan su fa ba dagaske suke yi akn magana bahiyya da kaaamil ba ko dan ya sake ransa .

Ya raka ta har kofar site dinsu sukayi sallama ya dawo falourn ya nitse cikin lallausan cushion dinsa yana tunani anan har bacci ya debe sa

sanyin asubahi ne ya daga shi sai ya fita agidan mai gaba daya ya wuce masallaci

1 hr ya dauke sa sallahn fajr da duk wani nafila da azhar din safiya da neman sasaucin abun daya keji aransa..

Wajajen 6.,bahi ta farka,har Allah Allah take ta iso bakin drapes din ta yaye kamar munafuka tana lekowa kadan ko zata gansa.

Bata gansan ba kuwaa ya sa ranta bai mata dadi ba taja tsiririn tsaki ta bara wajen tana kukkuni
..she want to see him a cikin yanayin nadamar abubuwam dake faruwa tsakanin su

Dan A duk sanda taga ya nuna abin ya dame shi hakan nasa ta jin sauki sosai aranta..

"..Bayi ta shiga bata yi wanka ba tayi Alwala ta fito ta kimtsa kanta tana murda door suka ci karo dashi,yana kallon ta ta dauke idanun ta..bai kulata ba ya tabe baki..da sauri ta rabe ta jikinsa bata ma bari sun hada ido ba ta sauka akan steps.

Ya murda kofar dakin shi ya shiga har yanzu yanajin sautin saukar nata sai ya kada kansa yana murmushi..

Daga nan har rana ya rufa bai sake ganin ta ba,dan tunda ta isa sashin su jahan komai ya kacame game da shiryen da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login