Showing 33001 words to 36000 words out of 225093 words

Chapter 12 - AHUMAGGAH COMPLETE HAUSA NOVEL

06 Jan 2025

26796

dai take famar susuce masa fuska tana lalllaba shi har sai da ya masife su tass kafin yayi shiru.

Cikin lallami da taushin murya jahan tace "kayi hakuri its ok komai ya riga ya wuce!

Daga nan sai bai kuma sake magana ba.

Nan magana ya ta da magana inda subaya ta nace sai dai a abada bahiyya matsayin ta da suka yi niyya tun farko..

Jahan dama bata da matsala da hakan dama kawai neman izinin su da kuma karin yarda tsakanin ta da bahiyyah ya rage mata yanzu

dan iya zaman bahiyya a gidan bataji ankawo karar ta cewa tayi mummunan abu ba.
And tunda taga khaldun bai kore ta ba to lallai yarinyar akwai hakuri


Subaya kam is super excited already she cant even wait to call bahiyyah her sister.

Bangaren Khaldun kuwa ko sake kallon su ba bare yayi responding haka
Kuma ya tashi ya bar su a dakin suna ta fayyace fayyace.

By noon suka tattauna su uku da jahan da subaya da Alhj gen hamood ta video call

Inda ya basu goyon baya dari bisa dari akan tunda sun gamsu da halayen ta kawai suyi adopting din bahiyyar ta dawo one of the hamoods.

Murna wajen subaya kamar zatayi tsalle,dan sosai take jin bahiyya aranta duk dama bata zauna da ita ba.

Washe gari koda suka sanar ma khaldun cewa za'ayi adopting bahiyya shiru yayi daga bisani yace shi babu ruwansa da wata bahiyyah...

He object the fact that yarinyar dake masa dafe dafe ce za'a laka masa dawowa yayan ta.

Yama ki shiga zancen Kuma Dan dolen su suka kyale shi.

*****

Nikuwa Ummah adama ita ta dinga bani shawarwari tun kafin su jahan Aarah du tumtube ni akan maganan.

Tace min Allah ne ya kashe ya baki bahi...dan haka idan suka kawo miki maganan adoption maza ki amince

Anan har tarihin kywawan halayen su sai da ummah adama ta bani.

Kamar wasa aka kira ni a sashen jahan su biyun suka tambaye ni ko zan amince da qudirin su!

Babu abunda ya bani sha'awa kamar yadda Jahan ta bani tabbacin cewa kar na amsa su dan na faranta musu ko dan tsoro domin kuwa maida ni cikin jinin su ya wuce yanke hukuncin cikin wasa.

Sai kawai na amince
nayi godiya sosai harda kuka mai ban tausayi

Nan suka jawo ni for the first time duwawu na ya zauna kan lallausan chairs dinsu..

Da yamma aka kira ni again babban lawyen alhaji gen hammod ne ya ziyarce gidan Domin aiwatar da proper official adoption procedures

Anan aka maida suna na asali wato bahiyyah Ahmad alba kafin aka sa HAmood a karshe.

My file name was reading bahiyyah A. hamood

Sai Aka bani official papers din adoption nayi signing
Haka ma na family property and rights da suka bani kyauta duk na sa hannu.

Wallhy ji nake kamar mafarki nakeyi dan ko murmushi bana iyayi sai yake.

"TAbbas Tsarki ya tabbata ga ubangijin mai yin yadda ya so,
shikenan fa rana daya na dawo cikakkiyar doughter of gen hamood and jahan Aarah, Sister to a brigadier genaral khaldun sa'ood and his sister subayah.

A take rayuwa ta sauya min,ranar kwana nayi ina godiya ina salloli

Na tuno ammu abbu da junnut sosai har na rasa wani kalman zan faranta ma ubangiji na rai da shi.

Kawai sai na daura niyyar yin azumi guda daya batare da na fada ma kowa ba.


Haka ammuh adama ta sake maida ni wani site daban wanda yake asalin cikin sashen da jahann
Aarah da su subaya ke zama.

Nima yanzu inada whole flat site mai dauke da wata kafurar neutral background.

Ko ina An tsime shi da monochromic additives,dark beige drapery curtains,a tsakiyar space din dakin akwai stylish ottoman bench mai square pattern Tv sets da katoton silk bedding with plenty maching cushions da cubic headboad agefe.

Wayyyo duniya sabuwa..

Closet dina kawai wani dakin ne mai zaman kansa...

Duk da yadda abubuwa sukayin kyakwan juyin masa,sai dai Ban taba komai ba tukun don jikina ko kadan bai sake ba.

Umma adama ce ma tasa ni dan dole na dauki daya daga cikin doguwar rigunan abaya dake closet din na saka sabida nasan na shiga wani matsayi arayuwa, da shike da azumi abaki na sai ban fito ba nayi kwanciya ta.

Ina farkawa As expected subaya ce na gani,cike da fara'a ta rungume ni tana cewa happy sisters day"
Sai da na tsinci kaina da mayar mata da dariya

Ta riko hannu na tace min,ki sake jikin ki kinji ,mum is already calling Zakuyi magana da dad

Wani dam naji kirji na ya buga,sai nayi yake kawai nace toh muje..

Tana gaba nabiyo bayan ta,na samu khaldun na zaune awajen alaman magana sukeyi har zan zauna kasa jahan tayo saurin riko ni tace kar na rusuna ..

Nikuwa Duk hankali na nakan sa shi ko kallo na baiyi ba
Har ya gama amsa wayar sa ya tashi ya fice abunsa

I was lost in tot of him,gani nake dan banje aiki site dinsa ba nakeji wani iri ko yaya yau ya yi?waye ya dafa masa abinci oho?

Come here BAhiyyah Jahan ce ta tsare min tunani da mika min waya

Anan Dukan su suna ji Mukayi magana mai cike da girmamawa da Alhj hamood

Shima karfin gwiwa ya dada min harda tuno min cewa na taba kiran sa mahaifi na a da chan dana taimake shi dan haka shima yanzu na dawo yarsa na har abada.

Hawaye na su suke dada nuna musu sincerytin godiya ta.

Dan dole na na sake da su, yanzu na fara ce ma Subaya big sis..

Jahan Aarah kuma ta sakamin suna mai dadi wato
BAHIYYATUL NOOR.

Sai aka dawo cemin baahi, ko ace min Noor

bahiyyahn ma ba kasafai suke kira na da shi ba

Duk wannan hidiman mu ukun mu muke yinshi sai idan alhj hamood ya kira gashi sadaat mijin subaya baya nan Yayi tafiya.

Tun ranar ba wanda ya sake cemin nayi wani aiki agidan amma zuciyata cike take da damuwa da yadda khaldun saood ke yi anashi shashin He dindt say a word about me Ni dai nasan bai amince da ni a matsayin yar uwansan bane.

Gashi haka kawai nake jin i really missed him,i wanna be with him ko da kallon sa nayi

Bayan kwana biyu Jahan ta kira mu da rana da shike khaldun da ita yake yin lunch kowa ni lokacim

Wani daure fuskn sa yayi da yagan mu akan dinning table da alaman fada jaahan tayi masa akan kin accepting dina dayayi..

Nikuwa ko iya hada ido dashi banyi ba
Amma sosai naji dadi dana gansa ko na komai naji sauki

Gashi dan kwana biyun kacal danayi cikin gata har kalar fatar jiki na ya fara amsa sabon ya nayin daula da ake zuba mashi.

Bayan mun zauna Anan Har jahan ta kare Maganan ta ba wanda ya amsa fiye da subaya.

Last last cewa tayi zata yi tafiya akan zata je kasar turkey..


Wayar sa nayin kara ya mike tsaye
"Ya dora mata kiss a goshi yace safe jouney mother".ya hade rai bai jira amsa ba ma ya tafi abunsa.

Bayan sun bishi da ido sai duka suka dawo suka kalle ni,kaina akasa yake dan nasan muddin ina waje nasan he will remain pissed off.

Fuskata ya nuna damuwar hakan Amma bansani ba nadaiyi shiru na sunkuyar da kaina kasa.!

Har Subaya zatayi magana Jaahan tace wait sai ta kira sunana cikin lallami tace
Baahi?
sai Na dago a sanyaye
Nace yes ma..

Tace kar ki daga hankalin ki,zai saba da ke amma ba yanzu ba ko!..

Sai Nayi murmushi nace bakomai na fahimta.
.
Sai dai alfarma daya nake nema

Tace mebene?

Jahan pls ki bari na cigaba da yi masa aiki kamar yadda na saba masa da chan.

With full objection jahan tace a'ah ban amince ba
Bazaki yi wani aiki agidan nan ba

Ban taba sanin inada liver ba sai yau

Tsintar kaina nayi ina ce mata,zanyi hakuri da khaldun ni dai Tayi hakuri ta barni nayi masa aiki dan nafijin dadin kula dashi fiye da dawowa equal dinsa

Besides am his sister now duk abunda zanyi mashi is out of family bonding so no quest.

Da wannan kalmomin nawa sai na burge su matukar burgewa
Duk dama da kyar jahan ta amince

subaya har da cemin zata rinka ta yani wasu Abubuwan domin mu jawo shi har ya aminta dani.

"Cike da raha da fahimtar juna muka watse kan tebur

Karfe 2 Jahan Aarah ta bar kasar nigeria zuwa turkey.

So washe gari da safe khaldun saood ya sha mamaki ganin nayi resuming duty sai dai ko kallon arziki ban samu ba bare cikan ki!

Daga yadda naga yaci abincin sosai I can tell that he misses me too.

Naji dadin hakan araina,dana gama mashi komai sai na je dakin big sis subayah,she was all excited murna take sosai kawai dan mijin ta sadaat zai dawo.

Anan nayi wanka har ta koya min salon hade haden bathing gels ta inda zai goge min fata na nayi kyau nayi tass

Anan na fahinci Wanka ma iyawa ne fa,dan akallah abubuwan tttala jiki dake bathrum din mu yaci ya dauke ka awa biyu yana wanka bai gama ba

Haka ma ta cancada min kwalliya ta koya min yadda zan nayi,gashi nayi dan karan kyau

Da shike ina kama da Ariana grande sai kawai take bin salon parking gashin ta kamar yadda takeyi alwys on pony tail

Idan ta tattala min shi sai ta sake sauran jelar cukun ya zube abaya na

Yau ma Doguwar abaya bakake muka sa iri daya sannan mu kaje shoping mall.

We had fun,har sai da naji ina kaunar big sis subaya sosai
Dan kuwa tsakanin ta da Allah ta bude min zuciyar ta tana jan ajikin ta

Munyi shoping kamar wanda zasu bar duniya.

Ina da komai agida amma Komai ta sake siya min,shoes bags,make up lingeriea da jewries gani take kamar zabi na zaifi min

Haka ma iphone11pro din kamar bai ishe ni ba ta kara min da samsung galazy x10.

Cikin wata kafurar jeep kirar jaguar ake tuka mu

Dan dole na na koyi surutu dan kuwa subaya is quiet intresting and jovial...


Tun da muka dawo Gidan shiru,tana dakin ta tana shirye shiryen tarban mijin ta nima ina daki na ina damar tausasa kaina domin har yanzu zuciyata tana dauke da fargaban abubuwan dake faruwa dani wani bin sai naga kamarr duk karya ne

But I have no choice than to accept my new life this way.

Wanka nayi irin yadda big sis ta koya min

My choice of body wash was makari,honey,goat milk set nivea,da wasu set of papaya scrub banda ma hand wash feet wash knuckle da under arm and pits
Wasu abun ma bansan su ba.

And My hair was going milk and egg sets both shampoos and conditioners
,wani handle din zakaga an shake su da zallan ogarnics wasu kuma irin su
himalaya sets ne And little of revlon da oriflame.

Kirji na daure da baby pink towel na fito na yi yan shafe shafe na

Ban fara lura da jyaun na ba sabida tunanin khaldun sa'ood ya cike min kirji na.

Simple mermaid
Gown nasa sabo daga shoping stuff din da mukayi dazu

Kalar ja da baki ne dan haka dana tufke pony tail dina sai na lullube shi da bakin turban cap


At Around 5.45 pm na fito zan nufi site din khaldun

Taku nake dayan biyu ina jin dadin jiki na kwasam sai nayi tuntube kamar zan fada naci da baki naji an riko ni a hanzarce

Wani lumshe ido nayi Kirji na saida ya buga dana dago thinking and wishing ina bude ido zanga khaldun amma sai naga wani halittar daban

Da uban sauri na kwace hannu na
Shikuwa mutumin ya sakankance ya zuba min hadadden idanun shi akan surar jiki na baya ko kiftawa


A kadaddafe na bude baki Nace sorrry, na juya zan haura bansake kallon sa ba...

Da alaman ya sume dan kuwa sautin takalmi na ne ya fargan da shi Da Har zai yi magana sai Charaf big sis subaya ta shigo ta iske shi.

Da saurin ta cikin fara'a ta rungume shi tana cewa baby is back,sai na juya kadan ,naga dai yana wani jajjan aji

Suna gaisawa,basai an fada min ba na gane mijin ta ne

Inaji yana ce mata who is this?
Yana nuna ni.

Subaya batayi kasa a gwiwa ba ta Kwalla min kira
Dan dole na sake dawowa gaban su

Wani shu'umin kallon kurel da gayen kemin yasa kaina ya daure Bai daga idanun sa ba har sanda subaya ta riko hannuna na zuwa gaban sa da kyau

Tace this is bahiyyatul noor..
My new sister ka tuna?wanda na gaya maka a phone

Uhhhhhh...yess yace adan dakile daga ji kasan bai ma saurare ta da kyau lokacin datake gaya masan bane
Ita kuwa sai da ta sake ware masa bayanai akaina har sanda ya gamsu

Sai yamin murmushi Yace ure welcome to the family..nace thanks
..ya fada min sunanan sa barister sadaat adeel

Ba yabo ba fallasa nayi murmushi.
I was not comfotable dai na yi excusing dinsu na nufi part din khaldun

Dinner na shiga hada mashi,still thinking of yadda mijin big sis yayi ta kallo na dazu
Toh shikuma haka yake!l?

Kaina na bi da kallo "Ko dai laifi nane dana sa shaped gown, kowa dai yasan mermaid gown na nuna shape din mace sosai So I started regreting

Da nasan dressing din baiyi dace da na wanda za'ayi ma kallon mutunci ba da bazan sa ba.

A wanni fannin kuma i was kind of happy hala tunda yau nasa kayan da wannan kyakwar mijin big sis din ya rude maybe i will get to catch khaldun's attention

Bansan meyasa ba har cikin raina nake jin tsananin bukatar sanin matsayi na a zuciyar khaldun sa'ood.
#follow #SURAYYAHMS

SHARE SHARE WITH OTHERS
[10/7, 9:34 PM] 0mer Farouk: _*♡AHUMAGGAH🌺*_



_A nigerian historical fiction_
*WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_




_9⃣-mr sadat Adeel♡_




Ni kadai a kitchen din inata sake sake don tunanin khaldun na cigaba dayi har na kammala hade haden abinci na.

Da shike dinner ne ban dafa abubuwa masu nauyi ba,i left the kitchen unkept sai naje site dina,ina shiga daki ban wani bata lokaci ba bayi na shiga na dauro alwala nayi sallahn magrib da isha kafin na nazo na gyara ma simple make up dina zaman sa.

Misalin karfe 7.55pm na sauko da serving trays na aje kan dinning dinsa ko gama jerawa banyi ba na tsinkayo
sallamar sa da tamkar ma kanshi yakeyi.

Na gaishe shi kasan wuyar sa ya amsa with his face bayabo ba fallasa
Direct ya taho zai zauna kan dining chair kamar yadda ya saba,so i quicky compose my self na tara dan karfin hali na ja masa seat kamar sarki ya zauna gently still bai kalle ni ba..!

Plates na shiga jerawa gaban sa na bude wata mayyar girki mai dadin qamshi, rich spaghetti shingella jolloff mai dauke da fresh brown meat meals..

I notice how he look at the food da gefen idon sa sai nayi boyayyen murmushi

Spagehtin na zuba dan dai dai sai na zuba meat balls guda hudu manya aciki.

Redberries na zuba a wine glass,nasan yana matukar kaunar fresh mango juice shima na aje masa shi agefe.
Daga nan tsayuwa nayi a gefe yana ci,sai dai yau din na lura kamar he is not comportable da hakan daddaya ma yake ci kamar wanda abincin bai masa dadi ba.

Qamshin jiki na ne ya ruda shi,nikuwa Ko kadan ban kawo araina cewa na birkita ogan da qamshin turare na ba,nasan zai iya yiyuwa yana son qamshhin lavender sabida jahan Aarah shi take yawan amfani da shi.

Bandai kawo tunanin komai araina ba,don nasan turarrukan sa aduka arabian designers ne daga qatar, saudi arabia, dubai ko kuwait,
Idan bai saka su ba toh clive christain ne ajikin shi hardly yake shafa made in srilanka duk dama yana dasu kuma sun hadu.

Kusan rabin awa yau nayi agaban sa ababu ababu sai da yayi rabin cinye duka abincin dake warmer ahaka ma Baima sha beries din ba naga da kanshi yau ya mika hannu ya zuba mango juice ya sha,da cup din ya nufi dakin shi bai sake duban inda nake ba.

Nikuwa a Kullum burge zuciya na yake i so much love his hard nature..
khaldun Namiji ne mai ji da control, karyan ka kagano abunda ke sa shi farinciki cikin sauki bare kuma weak point dinsa.

He is one of a kind,bazan boye muku ba har mafarkin fuskan sa nakeyi most times ko da ba a bacci ba.

Haka kawai Kwana biyu Sai na lura da na dage da aiki na na kula dashi,toh da shike ma yasan yanzu nima yar gida ce kona yi mistake baya ce min komai.

Sai ya dawo tsakani na dashi We are back in the era of few words and blatard queitness.

Yau Kwana biyar kenan ina zuwa site dinsa amma baifi sau daya yayi mun magana sentence daya ba.

Ko ajiki na musamman da na tursasa zuciya ta tunanin sa a kullum

Gashi inata shirin rubuta waec next month,tunanin khaldun sa'ood gaba daya ya hana ni lura da duk wani abun dake gaba na.

Har da Sadaat mijin anty subayah da kullum sai naga ya zuba min shanyayyun idanun sa yana bina da kallo.

I begin toh dislike him,ban cika ganin yana tarairayar big sis ba amma sai naga sis subaya kamar wacce bata da aikin yi sai nashi .

He is a demigod to her,as she practically worship him.

tsaban so da nuna biyayyar ta a gareshi har bacci abinci bata iyawa sawa abaki inbata gansa ba.

Shikuma babu ruwan sa,in gaka yana wasa da dariya mai tsayi da da ita to yace taje ta kira ni ne kuma nazo din..

Na lura da shi Yana so muyi ta hira anma nikam jinina bai hadu da shi ba sam

Akwai indian serie da nake yawan kallo na mance sunan sa but akwai khushi da arnav toh babu maraban wannan sadaat din da mijin anjali wato shyam.

I just dislike his looking attitudes
Shiyasa idan big sis subaya bata kusa nakan yi sauri naje daki na na rufe kaina na ina karatun dole,bana sake saukowa sai ta dawo Haka ma da safe ko da daddare a site din khaldun zan bata lokaci na.

Nidai Sam naki na sake fuska ta wa mijin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login