Showing 69001 words to 72000 words out of 225093 words
idon ta tsura masa da alaman bata san tayi haka ba,..komawa yayi da baya kadan sai ya zare cap din ya bar suman kanshi tare da jingina kai yana kallon ta direct. .
Har zatayi magana kenan sai taji yace
"Serve!
Tace ok,cike da sanyin kamala ta langwasa Kamar wata marainiya Ta shiga bude buden plates din tana aje murafen su agefe.
Guda biyu ne that means nata da nashi yayi oder,haka ya sata suka fara cin abincin tare,sunayi suna kallon juna bawanda yace uffan
duk dama da kyar zuciyan ta ya amince mata da cewa ba mafarki take yi ba
Tana ganin su Yasmin suna lekowa amma ta dan kashe musu ido
Alaman kar su damu da ita.
Ruwa ta zuba a cup ta mika masa ya karba kamar wanda zaisha amma sai ya kawo setin bakin ta ya shiga bata ruwan slowly tana karba
Sau biyu ta kurba ya sauke cup din ya bita da wani close look yana duban yanayin ta,how are you?..bakinsa ya furta ya kuma kure ta da sanyin kallo alaman yana mai sauraron ta
Spoon din ta fara ajiyewa Ta danyi shiru ta sauke kanta kasa,zuciya tuni ya mule cikin tunanin duk abubuwan da suka same ta tun bayan rabuwar ta dashi har yau, cahn saiga hawaye suna zubowa dakan su...
Bata san meyasa ba amma haka kawai take jin shaukin gaya masa duk wani halin data ke ciki,musamman akan sadat da subaya.
Sai dai kuma shaidan yana ta kokarin dasa mata tsoro da fargaban halayen maza
Gani take kamar ayanzu she have learn alot of halin dan adam a wajen sadat toh tayaya khaldun din ma zai fahimce ta.
Shikuwa Ya dau lokaci yana kallon ta a hakan,daya lura da halin da take ciki tun kafin ta sauke boyayyen ajiyan zuciya ya mike tsaye baice komai ba ya tashi yafita ya barta, a hujajan sai ta mike ta shiga biyo sa abaya..
Tafiya suke kamar basu san juna ba har ya ja ta suka nufi wani waje wanda baida nisa da shop din sosai
Irin bishiyoyin nan masu dauke da cool down chairs abakin wani pondpool ya zauna,..a kusa da shi tadan dofane cikin sanyi murya tace khaldun sir,ure here, ure welcome.
Sai ya dan juyo ya hade rai ya harare ta....nifa lpya ta kalau...ta fada slowly tana neman sauke kan ta kasa
Yace shine kike min kuka?Did you have any problem?Ko dodo kika ga ni?gani zan cinye ki ko...ya tabe baki yayi kwafa
Wani sassanyar hawayen ne ya sake sauko mata ta dan girgiza kai...bata ce uffan ba sai ya juyo
U dont want to read..makarantar ya ishe ki?
Tace ah a ...am just
Suprise?
Tace ehmm...
Dan ciza labba yayi ayangace ya mike tsaye
" Ok...i am going
zo muce chan
rudaddun idanun ta dago tana binsa da kallo bugun kirjin ta na karuwa
Ya mika mata hands,ba bata lokaci ta riko hannun san, tin kafin tayi wani magana ya shiga janta suna tafiya har suka kai gaban wata bakar mota da alaman nashi ne
Zai shiga driver seat sai ya mata alaman ta bude seat din baya tana budewa taga manyan packages din daya taho dasu tun daga shoping mall yace take them out..
Batayi musu ba ta shiga fitarwa har ta gama,dasu a hannun ta karaso daidai ta inda yake ta jikin motar dan kadan ya sauke glasss yana kallon ta wani 3mint silence wajen ya dauka kafin yace to
Ayi karatu lpya..
Sai Tayi masa shiru fuskan ta adan daure..
..
Dan share ta yayi ya kau da kai kamar baisan tanayi ba, Yana kuwa kunna car din ta fashe masa da wani kuka mai sanyi da rauni kamar wata mai jinnu sai ta juya zata tafi abunta.
Kashe motar yayi atake ya Wani lumshe idon sa a bazata cikin saurin da baisan da shi ba ya sauko.
Irin kukan da baka san dalilin san nan ba takeyi ta daura tafukan hannun ta duka akan fuskan ta har goshin ta yana shirin taro zufa.
Sai ya dakata ya zuba hannayen sa a aljihu,yadda ya tsime yana kallon ta kallo daya ya ishe ka ka gane kukan nata na azabtar da shi har baisan ya zaiyi ba
Ranshi adan bace ya mata nuni da hanya
Just Go..
Kije aikin ki ni bana son shegen iyeyi
Dan kadan ta turo baki a shagwabe ta dan kalle sa da grey watery eyes din ta batace mashi uffan ba,sai ta juya kamar zata bar mashi shoping parks din amma kuma sai ta dawo cikin sanyin jiki ta dauka tana dan share fuskanta da tafin hannun ta so innocent kamar karamar yarinya yar 4yrs,tuni yarintar ta ya matikar tafiya da imanin sa
Yanayin nata na mugun kafa tarihi aransa
Tana kara one step Bata hankara ba taji ya cakumo arm din ta cikin zafin nama,"where did u think ure going like this?..ya dan dage mata giran. ..Wai kukan me kikeyi?tell ne now,ya dan daga muryan sa kamar wanda dama sunyi alkawari ne bazata yi kuka ba har abada
Ita kuwa tuni taji ta kara rudewa cikin waswasi,gaba daya bata san meyasa data gansa a hakan kukan yake zuwa mata dayawa ba
Dan fincike hannu
ta take kokarin yi batare da ta sani ba
Sai taji Ya jawo ta jikin sa daf,not too close ya mata rumfa da kirjin sa ya dan saukar da kansa cikin idanun ta yasa nashi suna maida ma juna kallo mai saurin bayyana tsananin soyayya da tausayi ..
"Wani ajiyan zuciya ne ya kufce mata yasa hannun sa ahankali yana share tears dake neman tare masa gani abunda ke idanun ta...
"Sarkin karatu da Dafe dafe,toh ai Bani nace ki sa kanki schl ko kiyi aikin ba,.har kin gaji ne ko,did you want to go home? Ki fada min..
Ta girgiza kai tace ah'a.
Baice uffan ba yana binta da Kallon nitsuwa a hankali ya sa finger daya ya lakato hawayen ta ya nuna mata, why tears? Mmmm
Bata amsa ba,ya karkace lips dinsa da mafin sanyin sautin sa ya firta "i hate it.
Wannan sautin murya nashi tasan yau datana da karfin sha'awa bazata iya cewa bata ji wani abu ba!
Wani Lumshe ido tayi a slow bata bude ba,Wani feeling din yarrr taji yabi jikin ta Sai data sauke boyayyen nishi kafin ta samu nitsuwa.
Sai ta shagwabe fuska ta turo masa baki tana langwame masa wuya ta kasa cewa komai,yasan bazai iya jira yayi ta kallon ta haka ba duk dama yau yaga mugun kokarin sa akanta,,a hankali ya zare jikin sa anata batare da ya sake hade ido da ita ba ya sake ta, .. .yana juyawa zai koma motan nasa itama sai ta daure ta cije ta dauki kayan ta wuce gaba,sai kowa yayi hanyar sa batare da sun sake tanka ma juna ba
Wani yanayi mai azabtarwa ke cin su arai dukan su, koda ya shiga motar shima zama kawai yayi ya kasa sa key bare ya tayar
Ita kuwa Tafiya take da kayan a hannu kamar wanda ruwa ya kwaso ta tana sauke silent tears dan sosai Take jin kamar shine zai iya kawo mata karshen matsalan ta a rayuwa but she just dint know how and what to do to let him know all her problems.
Dai dai wajen da suka zauna kan chair na gindin bishiyar ta kafe da ido da alamu khaldun din ne yake mata gizo,har ta isa wajen ta zauna shiru bata sani ba hankalin ta gaba daya kamar baya jikin ta,har ya iso ta bayan ta daff da ita bata ma sani ba.
Wani uban tagumi ta rafka da duka hannyen ta biyu,within two secnds hawaye suka shiga saukowa
This time bai wani jira ba,hannun sa ya sa yay tapping kafadan ta bai damu da yadda ta farga ta juyo arazane ba ya balla mata harara
Zata kara sautin yace,nidai kimin shiru,bazan sake zuwa ba....i can see you hate seeing anyone
Wasu tears din ne suka gangaro mata masu shegen yawa jikin ta har na neman daukar kyarrma,idon ta a rufe gam gam kuma cikin sautin kuka mai tada hankali tace... pls dont go...nidai kar ka tafi.. .i dont want you to go....dan Allah .
Sai yyi shiruu Fuskan sa bai cika nuna yanayin da yake ciki ba amma gaba daya ya rasa yadda zaiyi da azaban kukan nata a kirjin sa
deep inside him yake jin its hurts him badly..wani irin feelings mai karfi yake ji akanta.,ji yake kamar chan kasan zuciyan sa son ta ya shiga garari wajen nuna masa bakar tsana ma hawayen bahiyya.
Mika hannu kawai yayi ya kwashe kayan da hannu daya ya kuma Jawo ta da dayan har gaban motar sa ya bude ya dura ta suka bar wajen..
Su biyu a motar kowa yayi shiru basu ko kallon juna Tafiya sukayi mai dan nisa,tun da suka kama hanya kanta akasa bata lura da isowar su ba sanda hannun shi ya sauka anata mistakely.
Anan ta dago ahakan ma da sauri suka kau dakai shiya fara sauka sannan ya zago ya bude mata ta fito
Its just past 10 na safe wajen is still cool iskan bishiyoyi na ratsa ko ina,wani karamin estate ne mai kama da lodge dan yawanci dama travellers ne da taurist suka fi booking wajen.
Har cikin gidan ya mata jagora,yana tafiya tana binsa abaya kamar wacce bata da laka.
Yanzu kukan da zafin dake damun zuciyar ta duk ya washe,yanzu kuma wani uban tsoro ne ya fara shigo mata
Its seems like they are alone banda karnuka da mai gadi bata sake ganin kowa ba.
Yana bude door zai shiga ta tsaya cak,har sanda ya dawo ya daga mata gira kafin ta sa kafa ta shigo ciki arakube.
Its a simple one room apartment mai dauke da one kitchen one sanitary convenience,akan gadon sa ya zauna ita kuma tayi zaman ta akan grey cushions dake daff da bakin gadon
She looks very scared and uncompotble sai juye juye take a sadade kamar ba ita ke masa kuka ba
Shiru yayi yana satan kallon ta,cikin ransa yana tabe baki.
Alaman tsoron nata ya so ya dada bayyana masa cewa ita din kamila ce kumaa hakan ya burge sa
..duk dama yasan tasan bazai mata komai ba amma kebewar nasu ya dan razana ta
Sai ya tashi ya bude fridge,Sabon Ruwan goran daya dauka ya ke sha ya zuba mata a cup,sai ya fita ya dawo mata park din daya kawo mata..
Yana kawo wa gaban ta ya jingina mata su yace
Stay here ina zuwa
A Slow ta gyada kai,shikuma ya fita da wayar sa a hannu
After 20minutes har ta fara dan sakewa chan wani abun ya tinzira ta ta shiga bude parks din Wanda ko rabin ganin abunda ke ciki batayi ba ta fara murmushi,chokolate box ta aje shi agefe, sai ta dada zagwulo su tedy bears din tana kare musu kallo don sai ya so ya sata dariya,guda uku ne yan dai dai but thy are all in angry faces guda daya yasha red jan baki na harrarta da gefen ido
Komai gwanin shaawa kamar karamar yarinya tana jujjuyawa
Yadda simple murmushin ta ya fafadada sosai zaka gane cewa ta mugun karban wannan kyautar nashi
She was very happy looking at all the gifts boxs din ta bude chokolates din ta zare daya ta jefa abakin ta tana taunawa,wani lumshe ido tayi cikin dadin rai ta kwantar dakanta ragwaf akan cushion tana famar shakar sabon yanayin da yanzu take ji aranta
.
Ya dade rabon ta data ji irin wannan farin cikin,wani siririn sautin hamdala ya kufce abakin ta
Cikin haka ya turo kofar ya shigo,.
Gyara zama tayi da sauri,yayi sallama da gefen ido ya kalle ta,.
Ita kuwa hannu ta dora kan kayan a sukuwane tana maida su park dinsu kamar maijin kunyan sa.
Garin sauri Daya daga cikin tedyn din ya subuce ya fado atare suka sa hannu zasu dauka sai goshin su ya bugi na juna..cikin yauki da kasala tace ouch
Toh Bai yi reacting ba
Dan kadan ta yamutsa fuska ta riko wajen ta na mulmulawa,shikuma ya dago da teddyn slowly zai furta mata sorry sai duka suka kalle teddy bear din atare suka sake ma juna murmushi
Nashi baiyi nisa ba,yayi shiru yana kallon nata,.jin kadam ta farga ta yi shiru tana dan kamewa
*****
Mika mata abun yayi ana mata wani irin kallon nitsuwa daf da ita ya zauna yace happy?
Cikin sanyin murya
Tace yess
Dan murmushi yyi a boye kafin yace Toh muje nakai ki,im going back now ya dan duba wrist dinsa alaman time dinsa .
babu musu ta shiga daukan kayan suka fita tana bayan sa,
Wayarta ne ya fara ringing sai ta kasa cirowa
Maimaikon ya karbe kayan dan ya bata daman daga wayar sai shi ya karbe wayan ya fito da shi daga purse din ta ya nuna mata caller
Yasmine ce.. Im sure thy are worrid basu san inda nake ba
Yace emm,ok lets go
Sai Suka shiga car din shidai bai bata wayar ba,sai dayayi five minutes a hannun sa yana driving dashi.
Isar su bakin eatery lounge suka samu wajen a kulle,bai bari ta sauka ba sanda ta kira taji inda suke.
Ashe maman dija,alhaja kafayat ne ta zo tun daga nigeria amma yanzu haka sun mata nisa sosai kuma bazasu dawo ba sai gobe.
Gashi da alama khal ma tafiya zaiyi,duk sai taji wani iri aranta tuni mood din ta ya sauya.
Shikam yana shiru yana studyn din ta,ya mata kallon so u will end up alone?!chan dai yace sai hostel kuma ko?karfe nawa kike da class go and get ready mana
Tace fa ba class bane dama games ne,...yace ok...shall we? Ba kunya ta gyada mashi kai sai ya fara tuka su suna yawo suna zaga garin london
batayi namakin yadda yasan wajaje ba tasan zai iya yuwa yashasha zuwa london.
Ita dai binsa da ido Take har yayi parking a wani hadadden first class Amusement park
bana zallan wasan yara ba harda abubuwan ban mamaki na tarihi,manyan namumin jeji da hallowens masu sa nishadi tsoro harda da barkwanci,wajen is just like a jurasic park
Tare suka shigo ciki yana dan gaba da ita tana gefen sa,Kalle kalle takeyi dan Tsaban nishadin data keji Har ta mance da tunanin meya kawo su nan shida ma yake cewa yanzu zai tafi ya barta
Sanda ya gama zagaye zageya da ita truout basu tsaya ba
wani abun inta gani ya kan bata sha'awa sai tayi ta kallo tana so ta tsaya amma tasan shi bazai tsaya ba dan haka ta shiga sight seeing sama sama
Tana bin bayan sa tana more each moment dake sanya ma zuciyan ta jin dadi
Wani step ya bi dasu A Chan Wani wajen chan sama inda babu hayaniya sosai, nan ya kaita suka tsaya dai dai kun mutane ne awajen da cameras suna daukan selfie,gaban su kuma wani dark blue ruwa ne yake soukowa daga tsakiyan wasu duwatsu biyu suna xuba awani huge glass pond ga manyan shark an killace aciki suna wasa
Wani kawateccen murmushi bahiyya take ita kadai tana dada kare ma sauran abubuwan dake wajen kallo
Its very amusing karfen dataga ana kamawa a tsaya shi ta rike itama tana kallon ta hankali kwance.
Shikuwa yana daga gefe,google dinsa sa ya mayar idanun sa yana kallon ta ita kadai duka hanneyen sa acikin aljihun su
A zuciyar ta ji take tun ranar data bar nigeria gaban jahan,bata sake ganin ranan da taji ta free cikin farinciki da sakewa ba kamar Yau
Haka kuwa ta shiga
Taba komai tana jin dadin ta tana murmushi,shidai bai motsa ba dan murmushin nata yake kallo yana entertaining zuciyar sa.
A haka har basu hankara ba lokaci ya tafi sosai,daf da lokacin azahar suka bar wajen suka kama hanyar gidan nasa.
To a lokacin Dukan su suna jin yunwa,amma babu wanda ya iya furtawa aranta ita kuwa tana mugun jin sha'awar yin masa girki amma sai taga yana shirin kaisu wajen cin abinci ..
Da kyar ma ta iya taro karfin yin korfi tace masa ah a,
Ita ta fiso tayi da kanta
Suna tafiya,sai ya basar cikin jan aji da son samun cikaken amincewar ta yace mata a ina kenan zatayi girkin,sai ta sunkuyar dakai cikin yauki bata amsa ba tace ai girkin bazai dade ba
So da suka kai wani store A hankali ta furta,can i pls,..bai kalle ta ba dai yayi parking shima ya fita ya nufi wani dan karamin masjid kusa da street din dake gefe da su,ita kuma sai tayi sauri ta shiga store din ta siya duk abunda zata bukata,Babu wani kudin a purse din ta sai ta biya da katin bankin ta
vegies din kawai ta riko duk sauran abunda take bukata riki riki aka biyo ta dashi har gaban motar sa,sun iso jikin mota dai dai shima yana dawo kenan sai suka nufi gidan nashi ,basu dai cika magana ba amma Aranshi bakaramin zumudin jiran abunda zata dafa musu yake yi
He dint even cancel his flight dan har yanzu baisan meya nane masa kafa ya ke kuma sa zuciyar sa rashin jin ya tafi ya barta ba
In da yaga ta dan sake ranta a presence dinsa sai take bashi tausayi sosai, aransa ji yake kamar akwai abunda ke damun ta,he feels like ba jin dadi take yi a london din ba
Kallon ta kawai yake dan gaba daya ya rasa ya zaiyi ya gano asalin damuwar ta dayake ta harsashe aransa,gashi bai cika son bada kansa haka kawai ba kawai sai ya basar ya shiga binta da ido yana lura da ita sosai dan kuwa ko tari tayi sai ya motsa ya gani.
Yana daga zaune akan gadon ta aje kayan one by one tana deban su a hankali Ta nufi kitchen din mai kama da alaman ba ataba girki aciki ba ta hau shirya abinci
Bayan vegies komai a pack dinsa yake dan haka ta dauko bowl ta juye boneless chicken ta barbaje shi,Gishiri ta fara barbadawa kafin ta xuba red chilli powder
dan kadan ta sa turmeric,magi ginger, garlic paste da coriander powder sai ta sa hannu ta juya su sosai sai da komai yabi jikin
Daga nan ta debi flour da corn powder spoon biyu kowanne ta bada akai ta juya suka motsu,kafin ta fasa danyen kwai akai mai gaba daya ta kara motsawa,da suka hadu sai ta bi jikin su da man butter tayi marinating for 4minutes.
mai tasa akan Akan Fryn pan yayi zafi sannan ta juye su