Showing 27001 words to 30000 words out of 225093 words
mutuwa
Nan Nanah A ta juyo tace meya ne kuma,wai ma me ya kawo ki nan ne lpya kuwa bahiyya?are you ok...tana dada dafa ni tana bani close look ina dan kauce ido na
Tana sake cewa bahiyyah daga nan
Bansan lokacin dana fara mata hawaye ba.
Lpiyar ki kuwa?
Hankali tashe ta dago ni..
Tace Yaya?
Meye ne,wani ya miki wani abu ne kike kuka
Nayi saurin girgiza kaina cikin kuka nace mata na shiiga uku
"Tace kin shiga uku why?banamsa ba na cigaba da kuka tohh kar na sake jin kin fadi haka .
Cikin razannan shesshekan mai hade da fargaban sanin shi din wanene a duniyan nn na furta..nana To ya zanyi,nidai ina jin tsoro."I just ruined his shirt is he going to kill me?ni gaskiya zan gudu agidan nan nanah A pls help me escape.
Na dada sautin kuka na in cewa
...nikam na shiga uku ina yarfa hannu a rikice..
Mikewa nana A tayi tana kallo na Tun kafin ta bude baki
Saiga gurd ya shigo a hargitse
dana dube shi sai naga ma ashe wanda Ya bani kayan san dazu ne
Kana ganin fuskan shi gaka tashin hankali danko gaishe da nanah A bai tsaya yi ba naji coarse voice dinsa yace min kece bahiyyah?.
Na gyada masa kai
Toh maza kije khaldun yana neman ki da gaggawa.
Murya na narawa nace khaldun?
Yace eh,sai ziee hawaye suka saulo min..Sai ga soldier yabi ni da kallon tausayi.
Wani kukan na dada fashewa da shi na daura hannu a akaina..
Zai juya nanah A tace mishi dakata
Wai Meyafaru ne,sai ta dubi time 10 saura minti 5 tace min bahiyya dama baki gama dashi bane kika fito nan muke ta surutu?watoh
Baki kammmala aikin ki bako
A rude nace nafa kammala nanah its just that ...sai nakasa cigaba
..
Gaba daya na damar da ita da rudewar danayi sosai Tsaban ta nuna ta yarda da ni
Bata tsaya ma jin me zanje agaba ba ta kalle gurds din cikin masifa tace
what is the problem?meyasa yake neman ta..are you sure shiya aiko la
Ko dai kunga kyakyawar mace zaku fara irin bazan halayen kun nan to wannan dai ba yar aiki bace.
Kanshi a kasa Yace
Kiyi hakuri Nanah A ba haka bane,Ai ta bar mopping duck ne abakin kofar dakin khaldun shi kuma yafito yana sauri zai fito ya karbe wani set din kayan sawa dayace na kawo
..tsantsi ya debe shi saura kadan ya zame kasa ya fadi..
A cewar gurds badon yayi saurin tare shi ba daya buga kansa akasa
Salati nana A tayi tana toshe baki cikin mamaki tana kallo na,nikuwa duk na birkice ina taro hawaye masu ban tausauyi,vike da samuwa Tace ma gurds where is he now,baiji ciwo bako?
Gurds yace yanzu dai yana daki dan har ya buga kafar sa he looks ok amma da alaman kafan tana masa zugi, he has cancel all meetings for today shine yace na kira ta.
Ji nayi jini ya dauke a jiki na,A Kasa na sulale kamar mai shirin kurma ihu kirji na dukan tara tara..
Duk da na naga alaman tausayawa a fuskan nanah A amma bai hanata dakewa tayi min fada ba.
Tace ai lin kyauta
Toh Kije maza ki same shi..ta nuna min hanya ranta adan bace.
A sadade na mike ina kuka ina tahowa site dinsa
10 minute ina knocking kafin ya bani izini na shigo
Gaba daya jiki na yayi lagwas sai sum sum nakeyi,sai da na taho face to face dashi ma kfin nasake tsinkayo kamannin sa da soldiern.
Yana zaune Ya juya kansa kafafun sa amike akan tebur yana tattabawa
Daga nan Ban iya sake kallon sa ba kuma ko rusunawan ban samu karfin gwiwar yi ba na dai tsaya ina murde murde da yatsun hannu na.
Wani shiru ne ya ratsa wajen.
Yana sane da abunda nake amma ko kallo na baiyi ba,Sai chan dai yayi magana chan Kasan makoshi naji yanacewa i believe you know what you did..
Na sauke kaina a sanyaye A sulale na taho na yi kneeling kusa dashi, hawaye na bin kunci na dan
Ban san dawani kalma zan fara bashi hakuri ba ga wani mummunn tsoron sa da ya shake min wuya.
Hey Am talking to u..ya dan daka min tsawa
A firgice na tashi na matsa baya,i mentally shouted my throat out tsaban kuka.
Sai ya dauke kafan nasa daya aje kan tebur ya mayar kasa ya kalle ni yana mai daga min girar sa alaman jiran amsa wanda ahalin yanzu kwata kwata bani da shi abaki na.
Da kyar na dago da mumunnan rawan murya nace Dan Allah kayi hakuri!!!
Yace hakuri??
Kinsan me kikayi min kuwa?
Are you mad, kashe ni zakiyi ko?...
Nace Nooo nooo
what the hell are you thinking. ..,
Kin san suwaye suke jirana?...and u just let me cancel a multi billion dolla meeting kuma kike cemin nayi hakuri?
sorry Is all what you gat huhn?
Abunda ya tsanan shi na ke iyayi wato girgiza masa kai,khaldun ya tsani yayi tambaya abashi amsa da gyada kai ko girgiza kai
Dan haka nw ma ranshi ya dada baci dani Cikin wata birkitaccen tsawa yace Me kika dauki kanki..?u ruined my uniforms, did you know that Ko duka zuri'ar ku aka hada bazaku iya siyan kaya na da kika bata ba?
Wai daga wani kauye aka dauko ki? I can see that Baki da manners Don't you have a mum,ko bata koya miki aikata komai a nitse ba tare da kin bata shi bane.
She tot you how to ruing everything right? cikin bambami ya juya kansa baiko damu da kukan danakeyi ba
Nikuwa Sabida sunan mahaifiyata daya kira cikin maganan nashi yasa radadin azaban kuka ya dadu a kirji na
Silly brat,sai na koya miki hankali da kanki zaki ce kin sawwake aikin nan naki, ure just pestering me baki da wani amfanin komai.. idanun sa ya dada tsurawa akaina kamar zaice wani abu sani naji yace
very Stupid girl and u better say thank you .
Murya na rawa Thanks.
Thanks what
Na dade fashewa cikin kukan nace thank you sir.
Share wannan banzan hawayen naki da ba amfana ta da komai zasuyi ba....right now,ko na miki da kaina.
Da sauri na share ina kukan zuciya,jiki na duk rawa yake ban iya dago idanuna na kalle shi ba, don duk sanda mutum zai zage ni bana so ko acikin wasa ya hada da sunan iyaye na
I know im just an orpharn amma nasan yadda iyaye na suka tarbiyantar dani
Wayar sa ya dauka yayi kira inaji ya dada masife guards dinsa.
Sai da ya gama tsaf sannan yace nayi waje na bashi waje kar ya tatttaka ni.
Nayi sauri nafice masa adakin sa
Bansan me xanyi ba kuma dan haka na shiga daki na fada akan gado na fashe da kukan tsoro hr bacci ya dauke ni
Na tashi da murdawan ciki dan haka na fahimci cewa bana sallah amma dana je wanka sai naga jini bai sauko dayawa ba so ban saka wani pad ba
Zama nayi naci abinci,tsoro nake ji sosai musaman ta inda zan fara sake zuwa dakin sa yin wani abu.
Haka dai na daure na shiga kitchen da daddaren zan girka masa dinner.
Nanah A ne ta shigo ta dan min fada ta kuma bani hakuri tana ce min komai zai wuce kuma zan saba dashi.
Lura da ina dingishi yasa ta bani wani ointment akan idan nagama kafin nayi bacci sai na shafa.
Ina jera mashi abinci sai ga nana tace a daki zaki kai mashi..
I am sure kafar san ne ke damun sa har yanzu
Nima gashi ciki na sosai yake murdawa yana min kananun ciwo
Da abincin a tray na isa kofar dakin sa nayi knocking just few minutes ya bani izini sai na shigo
A tsaye na tarda shi
Muna hada ido na sauke kaina kasa.
Har na aje abincin baice min komai ba,sai ya juya ya shiga bathrum nikuma na rusuna na shiga serving din kowanne kalar abinci a plate
Ko kaiwa hannu sau uku banyi ba jiki na ya hau rawa,serving poon dakansa ya sace ya fadi Wani mugun murdawan ciki take ya dunkule ni da kyar na mike na zauna akan lallausan farar kujeran sa ina juyayi
Nishi nake saukewa slowly har na dan nitsu,daga nan cikin minti biyar naji saukowar dumi mai yawa ta cikin pants dina Abu kamar wasa na dan janye na duba,jinin period din ne ya fara zuba har gashi yayi staining masa kan cushion dinsa sosai.
Wani mugun faduwar gaba naji,oh Allah na wannan mutumin zaice da shi na tashi yau,after runing his shirt da safe yanzu jini na ya zuba masa akan cushion?
What shud i do now,sai na mike tsaye a rude,hasbiyallah its showing jinin ya nuna clearly,kafin na ce zan share har nayi waje
Sai Kyat naji alaman bude kofar sa i have no choice dan haka da sauri na koma a zauna akan jini
Ko kallo na sau biyu baiyi ba,amma daga yadda yake miko min harara nasan banyi dai dai ba dana zauna masa akan cushion.
Nima cijewa nayi na basar,duk hnkali na baijiki na,zafin ciwon cikin ma na dena kulawa
Tunanin yadda zan masa bayani nakeyi,duk na rikita kaina. .
Yana daga plates din zai fara ci, na fara kuka...sai naga ya aje spoon dinsa ya kalle ni.
Dan Allah kayi hakuri.
Tsaban rawan da jiki na keyi sai abun ya bashi mamaki
Ikon Allah What is this nonsense? Will you Get out..ya kafe ni da ido
Sai na dena kukan Nayi masa shiru na rike ciki na
Ina jin jinin na dada bulbula,hawaye na suka fara razana shi
I think saboda hakan ne bai sake min magana ba ya tsaya dai yana lura da motsi na gashi na kime sam sam bana so na tashi bare yaga jini
Cikin kankanin lokaci ya fahinci ciki na ne matsala
Sai naga ya aje plates din ya tashi tsaye.
Get up...dah inda yake ya furta
Girgiza kai na nayi nace dan Allah kayi hakuri
U can't get up?
Na gyada kai cikin sabon kuka nace yes sir am soryy sir
Ciki na kemin ciwo.
Sai yayi shiruuu yana ta kallo na ina kuka,it took him a while kafin ya gane asalin abunda nake ciki
Komawa bakin gadon sa yayi ya zauna ya na latsa waya.
In not less than 10minutes muna zaune,sai mukaji knocking abakin door,toh da kansa
Naga ya tashi ya bude nidai banga wanda yazo ba har ya juyo,
Batare da ya kalle ni ba ya aje min wani park akusa dani,sai ya juya ya fita ya barni adakin nasa.
Kallo kawai nabi closed door din kafin na daure na bude park din
Wanda sanitary pad ne aciki da white cotton pants,har cikin raina naji kunyar hakan but i know have to do quick tun kafin ya dawo na shiga uku.
Da kyar na tattara komai na goge wajen na shiga bathrum dinsa na wanke jiki na na saka sabun pant da pad din,bansan ya zanyi ba sai na daura towel dinsa akan kayan jiki na na fito'..
He is still not around bai dawo ba hakan ya bani dama na shige da gudu na koma daki na
Kayan kawai na sauya na kwanta dan kuwa sosai ciki na ya balle da azababben ciwon har ji nake kamar mutuwa zanyi.
After 1hr,idanuna sunyo luiii nayi lagwas kamar an tsoma akuya a ruwan sanyi
Bansan anshigo ba ma bare na gane ko waye ne,ji nayi an dan taba goshi na alaman ana feeling tempureture na wni nishi na sake sai naji mutum ya zauna agefe dani!
Its khaldun,i can feel his scent and warmth dan haka naki na bude ido na kalle shi da kyau
Kallo na yake yi his face isnt showing any emotion.
Bansan ko ya gane halin danake ciki bane ko bai gane ba all i know is har nayi bacci yana zaune awajen yana duba ni,bansan kuma yaushe ya fita ba.
#follow SURAYYAHMS
COMENTS And
SHARE WITH OTHERS💋
_*♡AHUMAGGAH🌺*_
_A nigerian historical fiction_
*WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_
_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_
_♡7⃣sempa fidelis_
Da safe na dade akan gado na kafin na sauko,wanka na shiga zuciya ta cike da mamakin abunda yayi jiya.
Ina gama shiryawa na fito na wuce kitchen Na girka masa abinci,bai amsa gaisuwa ta ba bare yace min ya jiki,kuma tun Ina jera mashi abincin ya kore ni ko bari nayi serving dinshi ba baiyi.
Haka rayuwata ta kasance like a living hell,ban isa bayi ignoring duties dina ba amma innaje inayi kuma baya kyalewa na karasa sai ya korani
Duk sai naji nagaji da ibadan,haka Nayi ta sa kunne ko zanji ance zamu tafi gida amma shiru har muka cinye kwana takwas
Kullum inna zauna sai na tuno kano
I seriously missed ammuh adama ita kadai ce nake tunanin zata warware min duk wani matsala ta,.
haka nayi ta zaman hakuri ban tashi jin meke faruwa ba kuwa sai da najiyo shi yana waya.
Ashe cewa sukayi ya sake saka musu lokaci wanda hakan ne ya jawo delay din tafiyar mu.
Aranar Cikin dare su kayi meeting dinsu,it was very successful komai ya tafi mashi dai dai.
Da safiyar Allah kuwa ko wanke ido banyi ba yasa aka tarkato ni da kaya na na shiga mota akan zamu koma kano
Tsaban iya shege shi sai yabi private jet dinsa nikuma yasa aka bi mota dani
Kusan tafiyar kwana biyu ana jan mu,banda yawan bacci ba abunda nake yi a motar har muka iso kano
Muna isowa naje na gaida jahan Aarah cikin sauki bata ce min komai ba har na fito.
Wajen Ammu adama naje,muka gaisa tana kallo na tace baaahi?..Meye faru ne naga kamar kin fada...
Nace banji dadi bane amma na warke.
Taje ayyah,Allah ya baki lpya khaldun ya sanda haka kuwa?
Ko da shike ma naga kamar tun shekaran jiya shi ya dawo me kuka tsaya yi to?
Nan na shiga bata labarin abunda ya wakana ina maganan bansan ma hawaye na sauko min ba
Kunya yasa Ban dai gaya mata abunda ya faru akan period ba
Nace sabida ni yayi kusan buga kansa ko meeting din ma adalili na aka daga har muka ja lokaci..
Ammu Adama Ta ji tausayi na sosai ita da shike ta fahimce mmbi sosai ko fadan ma bata min ba
Tace muje ki huta kici abinci,kafin anjima kije ki gyara mashi site dinsa kinga tunda baki gidan nan ba wanda yaje ta wajen
Ban yo musu ba,hakan kuwa ya faru ammu ta gama petting dina nayi wanka na huta
Chan anjima naf shirya naje site dinsa na shiga kimtsawa fiye smda kwana biyar bamu nan nayi aiki sosai sai dana gaji.
A Kitchen dinsa na tsaya na jira domin na mashi abincin dare mai gaba daya,koda nagama nayi serving dinshi baiko kalle ni ba yace min get lost
Dama nikam nagaji dan haka da murna na bashi waje,sai dai ko karasa isa site dina banyi ba ba sai ga aikan sa akan cewa naje na karbi kayan da aka shigo dashi yanzun na jera masa a closet kafin yayi bacci
Haka na koma na karbe tarin kayan nasa,wasu irin super huge designer shopping bags ne mai dauke da designers shoes perfs,watches and other clothings.
Zama nayi anitse ina jera su,ina kuma binsu da kallon sha'awa ,Allah kadai yasan yaushe za'a saka su dan anan dinma akwai kaya da uban yawa wanda ko taba shi baiyi ba.
Bayan kwana biyu ranar na tashi da safe sai naga ko ina agidan ya cike da motoci anata sharing plesantries da formalites.
I was surprised na fito inata raba idanu, koda naje dakin gogan nawa ma yau a kulle take kuma shima baya ciki.
Ammu adama ce ke sanar da ni ashe yan uwan mahaifin khaldun ne suka iso tun daga kasar iran din bada sakon jajen su akan abunda ya same shi kuma tace zasuyi mana Kwana biyu
So the house become 5 times busier than normal
Da shike gangamin jinin sarauta ne sai suka taho da dokokin su masu tsauri da ban mamaki
Wai tare za'a dinga cin abinci kuma duka masu girkin gidan zasu hada kai suyi girki dan haka aka hana abinci ako wani sashi akan bazamu koma normal duty ba har sai sun bar gidan.
Tun daga ranar ayyuka suka ragu ma kowa cos komai a dunkule ake yinshi Kullum akan shirya food gathering a babban royal hall din gifan kamar wani feast kuma haka zasuyi ta hira da jahan ana shakatawa.
Sai dai anata wannan shagali nr amma ban taba ganin gogan nawa ya fito ba .
Iya kaci yazo ya gaishe su ba a sake ganin sa.
Gashi jahan tace nabar aikin kar na dafa mashi komai ko dan yazo ya zauna acikin su
Amma taurin kai yasa yaki ya kula su har yanzu.
Daga haka Kusan kwana biyar ya dauka baya cin girkin gida,shiyasa ma kullum zaka ganshi a daki ranshi a bace
On the 6th day daya gaji,sai ya fara aikawa ana kira na yana kuma tursasa ni ina dafa mashi kananan abinci kamar su couslow,noodles,salad da pancakes curstad etc
Gaba daya abun nashi sai ya bi ya ishe shi,nikenan bazan dan huta ba duk dama kowa ya sami ragowar hutu?
I was literaly upset with him inna ganshi ma haushi nake ji
Wani bin sai yaga Anata abubuwa awaje masu sa nishadi zaisa a kirani na dafa masa abu,ko dan baya so kowa ya san yana sani aiki, kullum nakanyi kukuni sai yayi kamar baya jina
Toh Yau Ina kallon fire works da yamma ne sai ga kiran sa daga site
Ina tahowa naga kwanukan abincin jahan Aarah ta sa an kawo mashi dan dole wai yaci
Tsawa ma yamin tsaban ranshi abace yace min" kwashe wayannan abun agabana..
Bance ufffan ba na kwashe zan tafi,yace get me some Noodles..kiyi min sauri.
Da gafen idanuna na kalle shi,ina saita kaina zan dau hanya Bansan kukunin nawa ya fito sosai ba sai gashi na furta
"Mutum Yana xaune waje daya kullum sai ciye ciye Yake kamar mace mai karamin ciki,Har da dan guntun tsaki na.
Stop right there....Ji nayi yace me kika ce? Dan haka a firgice na juyo.
Yadda ya zaro idanun shi ya kalle ni nagane komai..
The answer Was clear
...ashe da karfi Na fadI Hakan kuma yaji ni
Shikenan yau na na mutu na lalace.!!!
One time jiki na ya fara rawa.
Da wani irin muryan fusata ya dube ni again yace just turn around.
Nayi saurin juyi baki n dakan sa yace