Showing 78001 words to 81000 words out of 89400 words

Chapter 27 - MY ENEMY BOOK 2 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

2527

zamu tattauna akai..."

Kowa ya nutsu yana sauraron Ummy domin ita kanta Hajiya Kilishi bata san wani irin magana Ummy zata sanar ba..

Ummy tana zaune a ƙasin ledar ɗakin kusa da Mommyn su, suma twins suna gefen Mommy domin duk cikinsu kowa ba son yin nesa da ita yake ba, sai Ƴar tinny dake bayan Abbah a kwance kan katifa..

Ummy tana kallon Abbah ta ce "Abbah..."

Abbah ya amsa mata cikin sassanyar murya domin har yanzu jikinsa bai gama warkewa ba.

Ta ce "dole a cikin abu biyu ayi ɗaya ko a rasa ko kuma a samu shine kawai..."

Abbah ya ce "muje zuwa Uwar masu gida..."

Ummy ta cigaba da cewa "idan kanaso mu kasance da kai cikin farin ciki da annashuwa to dole sai muna tare da mahaifiyar mu a kusa, in har zamu bika mu tafi to dole sai da mahaifiyar mu, ƙafar ta ƙafar mu,
Idan kuma hakan bazai yu ba to zaka iya barin mu anan in yaso idan kana son ganin mu zaka zo ka gan mu amma da sharaɗin bazaka ƙuntata wa mahaifiyar mu ba domin ba wurinta kazo ba, wurin mu kazo, idan kuma tafiyar tayi maka nisa ai kanada gidaje a cikin Abuja sai ka kai mu can mu zauna da mahaifiyar mu, amma baza mu taɓa yin nesa da ita ba sai dai mutuwa...."

Abbah kawai tsaya kallon Ummy yayi tana ta zayyano da zance, daga bisani ya ce "okay duk naji abinda kika ce an ɗauke ku har ita na maida ku gidana domin hankali na bazai taɓa kwanciya idan bana ganin ku a kusa dani, gani nake wani abu zai faru da ku especially idan kuna fita yawo koda yaushe dole wasu samari zasu dakatar da ku daga lokacin da ku ka fara tsayawa da wani namiji a titi shikenam rayuwar ku ta fara tafiya, especially Balkisu da Ruƙayyat sun fiye rawan kai dole sai idanuwa na suna kansu, idan suka yi nesa dani hankalina bazai taɓa kwanciya ba, dan haka na zaɓi ku koma gida yanda zaku samu tsaro na musamman..."

Pinky da Rukky farin ciki kamar zasu fidda fikafiki su fura da Mommynsu jin da ita zasu koma gida....

Ummy murmushi tayi sannan ta ce "Abbah nayi farin cikin jin haka amma sai dai akwai abu a ƙasa...".

Abbah ya ce " to sarkin ƙorafi ina jinki..."

Ummy ta ce "in har Mommy zata koma gidanka to a tabbatar an maida Auren ku domin bazata taɓa komawa gidanka babu Aure ba, kayi haƙuri Abbah..."

Dogon numfashi Abbah ya ja sannan ya ce "Uwar masu gida meyasa kike haka ne? meye laifi don ta koma gidana da zama ba tare da Aure ba? duk wata ɗawainiyar ta zan ɗauka, ci da sha sutura kuɗin kashe wa duk zan bata, sannan zan mayar ta wurin aikin ta..."

Ummy ta ce "duk da haka Abbah domin idan ta zauna da Auren ta zata fi yin daraja a idon mutane, bayan haka Mommy ba tsufa tayi ba balle ace tayi tsufar da bazata yi Aure ba, idan ka barta a haka zaka cutar da ita ne, kuma sannan idan tana gidanka babu wanda zai zo neman Auren ta kuma mu ma bason ta Auri wani muke ba, nasan Ammy bata da matsala zata yi farin cikin kasancewa da Mommy, please Abbah wannan shine Alfarmar da zakayi mana, sannan ka jawo mana mutunci Please..."

Abbah ya ce "shikenam idan har kasan shi zai sa kuyi farin ciki sannan ku zauna a inuwar mahaifinku nima na amince amma saboda ku..."

Ummy tsabar murna bata san lokacin da ta tafo ta rungumi Abbanta ba, duk sauran haka suka tafo duk suka rurrungumi Abbah..

Ummy ta hango Mommynsu tana zaune kai a sunkuyar ita kaɗai sai zabga murmushi take..

Ummy ta ce "Mommy ke ma tafo gurin mijinki mana..."

Hajiya Kilishi ta girgiza kai tana dariya, dai dai lokacin ƴar tinny ta tashi daga bacci, ganin Abbah yasa ta nufo wurin sa da gudu tana faɗin "Abbah nah! Abbah nah..." ta rungume shi...

A yau suka magantu Abbah da Hajiya Kilishi suka fahimci juna da cewa tayi alƙawarin bazata sake ƙuntata wa kowa ba, zata yi ƙoƙarin ganin ta zama mutumiyar arziƙi, kuma zata cigaba da zama a gidan mijinta har ƙarshen rayuwar ta...

Gaba ɗaya hamdala suka yi Abbah sai da ya jira aka kammala girki sannan suka ci su ka sha, kuma a wannan ranar Abbah zai tattare su a mota ya tafi da su tinda ba wani shirgi ne da su ba, duk wasu kayan ɗakin Hajiya Kilishi ta sayar da su taci abinci da kuɗin,

Kafin su tafi sai da Abbah ya biya kuɗin hayan gidan da suka zauna sannan suka fiffito da akwatina da jakakkuna kowa ya kasance cikin shiri tsab, daga nan suka nufi Abuja...


★★★★★★★


Baiwar ALLAH gaba ɗaya garin ya yi mata zafi, tayi kukan har ta gaji, ga yanzu duk halin da zata shiga bata samun mai rarrashin ta, domin Roshan ko leƙa ɗakinta baya yi sannan itama bata zuwa yanda yake, suna gida ɗaya amma sai suyi kwana biyar basu haɗu ba...

Tana kuka tana tura kayayyakinta cikin akwati domin a halin yanzu bazata iya cigaba da zama a haka ba, ta yanke hukuncin barin gidan gaba ɗaya, ta shirya kayanta tsab ta fito falo hannunta riƙe da takarda da biro, ajiye akwati tayi a falo ta nufi part ɗin Roshan, a hankali take knocking cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi ya buɗe fuskar nan tayi fiyau ga yayi fari tass kamar ba jini a jikinsa da duk kan alamu bashi da lafiya ne..

Ganin Baiwar ALLAH yasa zuciyarsa bugawa ganin hawaye shaɓe-shaɓe a fuskarta, a hankali yake motsi da lips ɗinsa ya ce "meya faru da ke?..."

Miƙa masa takardar hannunta tayi tare da biro tana kuka ta ce "ga shi nan, ban ga amfanin irin wannan zaman ba, dan ALLAH yau a kawo ƙarshen zaman nan Ni na gaji, wani sa'in har manta wa nake da inada Aure, dan ALLAH yau kam ka sallame ni, gidan zan bari gaba ɗaya, zan fita naje na nemo iyaye na..."

Roshan ya ce "ki kwantar da hankalin ki Razhdeen ya kusan dawowa..."

Cikin ɓacin rai ta katse shi da cewa "Ni babu ruwana da wani Razhdeen ban sanshi ba, dan Allah Yaya Roshan ka dawo hayyacin ka, ka tantance abunda nake so da kuma abunda bana so, amma yanzu komai yazo ƙarshe, yanzu dai ka sallame ni kawai...."

Lumshe idanuwansa yayi cike da damuwa ya ce "shikenam.." yasa hannu ya karɓi takardar da biro ya juya zai je ya rubuta mata, wani irin suka yaji zuciyarsa tayi tare da bugawa da ƙarfin gaske a firgice yasa hannu ya dafe sai tin zuciyarsa yana shirin kaiwa ƙasi.

Ganin yana shirin faɗuwa yasa Baiwar ALLAH shugowa ciki da gudu tayi saurin riƙo shi tana ambatar sunansa
"Yaya Roshan! Yaya Roshan dan ALLAH ka daina Please ka tashi bana son irin wannan wasan..."

Shi kuwa lokaci guda idanuwansa suka fara ƙaƙƙafewa yana fitar da numfashi daƙer, ga yanda yake sama da ƙasa da ƙirjinsa alamun bugawa yake sosai,

Baiwar ALLAH fashe wa tayi da matsanancin kuka tana faɗin "dan Allah Yaya Roshan ka tashi, wannan wani irin wasa ne haka, bana son kalar wasan nan, ni idan baka son rabuwa da ni zan cigaba da rayuwa da kai a haka, nima ba son rabuwa nake da kai ba, ka rufa mun asiri dan Allah..."

Tana cikin wannan halin yana kwance saman cinyar ta sai ga wani irin jini ya burtso masa daga cikin bakin sa..

A ruɗe Baiwar ALLAH ta zaro manya-manyan idanuwanta ta ce "na shiga uku Yaya Roshan..."

wani irin tari yake yana Amar da jini, eyes ɗinsa har sun chanza color sun koma green, jikinsa gaba ɗaya ya koma yellow alamun babu jini a jikinsa, yana kaiwa ƙarshen tarin sa numfashin sa ya ɗage gaba ɗaya, sai wuyansa da ya karye..."

Hannu ta ɗora aka ta zabga wani irin gigitaccen ihu tana faɗin "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un Yaya Roshan ɗina, wayyo nashiga uku Dan girman Allah ka tashi, Yaya Roshan ka taimake ni ka tashi wallahi ina sonka, ina matuƙar ƙaunar ka mijina, ina sonka mijina wallahi, bazan iya kasancewa da kowa ba inba kai ba, wallahi idan ka mutu Nima rayuwata bata da wani amfani Yaya Roshan..."


★★★

Abbah kuwa suna isowa cikin gari basu tsaya a ko ina ba sai a babban masallacin juma'a anan ya sanar da ɗaurin Auren sa da za'a gabatar a yau Jumma'at, ya ƙira manya abokansa a waya, ya sanar musu cewa yana gayyatar su zuwa masallacin juma'a, waɗanda ya gayyato basu san meye dalilin ƙiran su ba sai da suka zo tukun suke jin labarin ɗaurin Aure, za'a mayar da Auren sa da uwar ƴaƴansa Hajiya Kilishi ba tare da wasu daga cikin mutanen sa sun sani ba, sai iya waɗanda yake da kusanci da su, anan ya bayar da sadaki ya wakilci wasu a mazannin wakilai ga kuma shaidu...

Hajiya Kilishi da ƴaƴanta kuwa suna cikin mota suna jiran zuwan Abbah domin ko su basu san a yanzu za'a mayar da Auren ba..

Suna zaune sai suka hango Abbah da abokansa waɗanda ya gayyato sun nufo motar, har an kammala ɗaurin Aure cikin ƙoshin lafiya,
Bayan isowar su Abokanan Abbah fatan alkhairi suka rinƙa musu tare da nasihohi da wa'azi especially Hajiya Kilishi an fi ja mata kunne kafin daga baya Abbah ya ja su suka nufi gida, amma yaso ace ammy ta sani bawai ta gani kai tsaye ba, amma babu yanda ya iya gwara ayi abu a wuce lissafinsa...

Hajiya Kilishi ta sha mamaki sosai da taji a yanzu har aka maida Auren ta, ba ƙaramin farin ciki ta shiga ba, anan ta ƙara jinjina wa ikon Allah, Addu'ar ta yayi tasiri lokaci guda Allah ya karkato mata hankalin Chief...

Suma yaran ba ƙaramin farin ciki suka shiga ba...

Wayar Abbah ne ya fara ringing ganin Razhdeen ne yasa shi sakin murmushi ya ɗaga yana faɗin "Ogan Sojoji ya akayi ne?..."

Razhdeen cikin sassanyar murya ya ce "Dad me yake faruwa ne?.."

Abbah ya ce "me ya faru?..."

Razhdeen ya ce "gaba ɗaya hankali na ya kasa kwanciya, zuciyata sai bugawa take, i think so akwai wani mummunan abu da yake shirin faruwa a gida..."

Gaban Abbah ne ya yanke ya ce "mummunan abu kuma Razhdeen? a'a babu wani abu da ya faru duk muna cikin ƙoshin lafiya..."

Razhdeen ya ce "where is my twins?..."

Abbah ya ce "na bar shi a gida cikin ƙoshin lafiya..."

Razhdeen ya ce "okay fine..." Yana kaiwa nan ya katse ƙiran.

Abbah shima hankalinsa kasa kwanciya yayi jin abinda Razhdeen ya sanar masa domin in irin haka ta faru da Razhdeen to akwai abinda ya faru ko kuma zai faru, most especially idan abun akan Roshan zai faru...

Haka Abbah ya ƙarawa motarsa gudu yana son isa yaga shin da gaske ne abinda Razhdeen ya sanar masa ko kuma! In har ya haɗu da Roshan cikin ƙoshin lafiya to sai dai akan wani nashi ne abun zai faru...

Cikin lokaci ƙanƙani Abbah ya isa gida, a rikice ya shige bayan an bubbuɗe masa gate gate ɗin da suke gidan.

Su Ummy ne suke ta tambayar sa meya faru amma Abbah ya kasa basu amsa sai ya tabbatar da idonsa..

Abbah bai tsaya a ko ina ba sai a part ɗin Roshan ko tsaya sauƙe su Hajiya Kilishi bai yi ba, yana sauƙa ya nufi cikin babban falon gidan, suma sauran haka suka bi bayansa,
suka tarar falon ba kowa, Abbah ya kalli Ummy ya ce "shiga ciki ki ƙira mun Daughter..."

Ummy ta nufi part ɗin Baiwar ALLAH, can ta dawo tana faɗin "Abbah bata nan fa..."

Abbah ganin tsayuwar bashi da amfani yasa shi nufan room ɗin Roshan domin yafi son yayi ido huɗu da shi,
yana zuwa ya samu ƙofar ɗakin a buɗe, ganin Baiwar ALLAH tana rungume da Roshan a ƙasin carpet yasa shi ƙarasa shiga da sauri yana faɗin "lafiya kuwa Daughter me ya faru da shi..."

Ɗagowa tayi da jajayen idanuwan ta waɗanda suka kaɗa sukayi jawur tsabar kuka ga bakinta duk jini yanda ta haɗe bakinta da na Roshan tana hura masa iskar bakinta ko numfashin zai dawo...

Abbah ganin halin da Roshan yake ciki ne yasa shi firgita yayo kansa da gudu yana "faɗin innalillahi wa inna'ilaihi raju'un ashe gaskiyar Razhdeen, gaskiyar Razhdeen, ciwon sa ne ya tashi..."

Haka yasa hannu ya ɗago shi yana faɗin "Daughter taya ni ɗaukar sa mu fita..."
Itama Baiwar ALLAH hannu tasa suka ɗago shi, suka fice falo da shi, su Ummy ganin halin da Roshan yake ciki ne yasa duk suka nufo su...

Ba ƙaramin tashin hankali suka shiga ba Abbah ko leƙa gidan sa bai yi ba haka ya ƙara shiga mota security ɗaya yaja su suka nufi hospital,
Baiwar Allah hankalin ta ba ƙaramin tashi yayi ganin haka ne yasa Abbah ya dakatar da ita suka tafi iya su biyu daga Abbah sai Roshan da kuma security,

Gaba ɗayan su kuka suka soma yi domin a halin da Roshan yake ciki ba mai cewa yana da rai, haka suka shige cikin gidan tamkar anyi musu mutuwa, duk a falo suka zazzauna Hajiya Kilishi ta zabga uwar tagumi tana tunani kala-kala a ranta, maimakon tazo ta samu kowa cikin ƙoshin lafiya sai kuma ta tarar da wani tashin hankali,
tana cikin wannan tunanin taji Pinky tana faɗin "ai duk kece kika jefa shi cikin wannan mun sani, wancan lokacin ma saboda ke ciwon zuciyarsa ya tashi..."

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login