Showing 84001 words to 87000 words out of 89400 words

Chapter 29 - MY ENEMY BOOK 2 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

2534

Abbah ya nuna wa Razhdeen yana faɗin "ka gànshi nan yana cikin kulawa..."

Razhdeen ya karɓi wayar idonsa akan Roshan wanda eyes ɗinsa suke lumshe kamar mai yin bacci, ga yanda fuskar tayi fiyau ya ƙara yin kyau sosai...

A hankali Razhdeen ya furta "My twins..."

A ɓangaren Roshan kuwa jin an ambaci sunansa kamar muryar Razhdeen yasa shi buɗe eyes ɗinsa a hankali, yana kallon screen ɗin wayar dake yana sanye da oxygen ba halin yin magana sai ido, ga babu riga a jikinsa sai tin zuciyarsa alamun anyi aiki a wurin...

Razhdeen murmushi yayi ya ce "Quick recovery my lovely twins..."

Shima Roshan ɗaga masa kai yayi alamar amsawa,

Abba ne ya karɓi wayar yana sanar da sauran ƴan gidan akan suma su zo su duba shi, kowa yazo ya duba shi banda Baiwar Allah dake tsaye gefe guda har yanzu ta kasa dawo wa hayyacinta, sai da Abbah yaje har yanda take ya nuna mata Roshan yana faɗin "Daughter kinga mijin nakin ..."

Baiwar Allah idonta akan Roshan ga yanda hawaye yake faman zirya akan fuskarta,
Razhdeen kuwa wani irin kallo yake watsa mata na ƙiyayya da tsana....

Washe gari da safe Abba ne zai koma Ethiopia wurin Roshan har Razhdeen ya shirya zasu tafi tare Abbah ya bashi haƙuri akan ya zauna da iyalansa domin suma bazasu juma ba...

Razhdeen ya ce "Dad inason ganin twins..."
Abbah ya ce "ka kwantar da hankalinka yanzu jikin yayi sauƙi Insha Allahu yana samun ɗan sauƙi zamu dawo..."

Daƙer Abbah ya rarrashi Razhdeen ya zauna shi kuma Abbah ya nufi airport....

Razhdeen yana tsaye shima Ƴar Amana ta faɗo masa a rai domin jiya bai samu hankalin zuwa gidan sa,
A lokacin ya shiga mota shima ya tafi..

Yana isa gidansa a falo ya tarar da wata zugegiyar yarinya tana zaune idonta akan plasman,
a hankali ya ƙaraso yanda take tsaya kallonta yayi kamar bai santa ba domin ba ƙaramin chanza masa tayi ba,
A hankali ya furta "Sarah..."

waiwayo wa tayi ta tsaida idonta akansa, tana kallonsa ta zaro ido waje cike da mamaki ta miƙe tsaye bata san lokacin da ta rungume shi ba, shima rungumarta yayi sosai tare da ɗagata saman kafaɗar sa,
ta ɗago suna fuskantar juna da murmushi akan fuskarta ya ce "my Sarah I missed you..."

Haɗe rai tayi tana shirin yin kuka lokaci guda ta fara kai masa duka akan ƙirjinsa kuma yana ɗauke da ita yaƙi sauƙe ta, da haka ya haura da ita upstairs, daman ita kaɗai ce a gidan madam Blessing bata nan,
Daga baya aka shigo da jakakkunan sa...

Suna shiga ciki ya sauƙe ta akan gado fuska ɗauke da murmushi yana ja mata hanci, itama Ƴar Amana ba ƙaramin farin ciki ta shiga ba ganin Razhdeen domin tana muradin ganinsa, haka a wannan ranar suka sha soyayyar su
Domin bazan ce hira ba🤨.


★★★★★★★

Bayan wata biyu...

Ƙasar Jidderh.

Ramlat da Maamie yanzu zaman gava suke ta zabgawa babu mai kula kowa sannan Ramlat ta haɗa kai da Indo Amaryar Mai martaba hatta girki tare suke yi, haka zasu zauna su sha hirar su amma da zarar Maamie ta shigo falon sai Ramlat ta bar wurin,
Maamie tayi zaryar zuwa wurin bokan ta akan ta juyar da ƙwaƙwalwar Ramlat akan sai abun da ta ce mata amma har yanzu ba'ayi nasara ba, domin haɗewar da tayi da Indo yasa ta koyi yin ibada sosai, sallar dare da karatuttukan Alkur'ani da sauran litattafan addini,
Mai martaba ya yi wa Ramlat faɗa akan ta dawo kula Yayarta amma fur taƙi sai cewa tayi "babu abinda take ƙaruwa da shi a wurin Maamie sai jahilci don haka yanzu ta dawo hannun Indo..."

Abinda yasa Ramlat ta koma wurin Indo shine a lokacin da sukayi faɗa Maamie korar kare tayi wa Ramlat akan tabar gidanta tunda gidan mijinta ne...

Shine dalilin da yasa Mai martaba ya ce ta zauna a part ɗin Indo, shi ya karɓe ta...

Dalilin faɗansu kuwa shine Maamie ta dage akan sai Ramlat ta koma Nigeria taje tana shishshigewa Razhdeen ko hankalinsa zai karkata kanta kuma haka bokanta ya sanar mata akan dole sai Ramlat ta koma gidan Chief da zama,
Ita kuma Ramlat ta ce "nan duniya bazata ƙara shiga shirgin Razhdeen ba domin bazai je ya hallaka ta ba ita kuwa maamie tana gidan mijinta, hakan yasa suka fara musayar yawu har Maamie tayi wa Ramlat dukan tsiya, saboda Ramlat taƙi amince da Razhdeen dalilin haka yasa Maamie ta kori Ramlat shi kuma Mai martaba ya ce ta dawo hannunsa sannan ya bayarta a Indo ....
Kuma Ramlat tana mutunta Indo sosai daman can tanada hankali zugar Maamie ne yasa ta fita a ran kowa, Maamie ta shafa mata kashin kaji....

A wannan ranar ne Mai martaba ya gayyato Ramlat zuwa babban falonsa na masarauta akan zasu tattauna akan wani mahimmin magana,
Ramlat ce a durƙushe a gaban Mai martaba tana sauraron abinda zai ce mata..

Mai martaba ne ya fara kora jawabinsa kamar haka
"Ramlatu abinda nake so dake shine yanzu ke ba ƙaramar yarinya bace, kin mallaki hankalin kan ki kuma kinsan mai yake miki ciwo, Yayarki ta dage akan ki Auri Razhdeen ita damuwarta shine zaɓin ranta bawai zaɓinki ba, kuma har ga Allah yakamata ki so wanda yake sonki, duk da Razhdeen ɗa ne a wurina amma tunda baya sonki bana goyon bayan ki Aure shi duk da nasan ba Auren nakin zai yi ba,
yanzu abinda nake so dake shine a cikin waɗanda suke sonki da Aure ki zaɓi mutum ɗaya wanda ya kwanta miki a rai..."

Ramlat tayi shuru tana sauraronsa daga baya ta ce "Abul har cikin zuciyata ina son Yaya Roshan amma nasan shima ba sona yake ba dole zan haƙura acikin samari na zan zaɓi ɗaya, aban lokaci zuwa nan da kwana biyu Insha Allahu zan fitar..."

Mai martaba ya ce "Masha Allah..." kafin ya ƙara furta wata magana yaji wayarsa tana ringing, dubawar da zai yi sai yaga number Abbah, ɗagawa yayi suka gaisa ya kuma tambaye shi jikin Roshan duk da har yanzu basu koma Nigeria ba, daga baya Abbah yake sanar masa cewa "mai martaba daman inason sanar maka da wani abun mamaki ne..."

Mai martaba ya ce "lafiya dai ko?..."

Abbah ya ce "yanzu haka muna Ethiopia gobe Insha Allahu zamu koma Nigeria jikin Roshan yayi sauƙi sosai an sallame mu, amma ya sanar mun cewa wai zai yi Aure na zaɓa masa matar da zai Aura..."

Mai martaba ya ce "to ikon Allah ita kuma matar sa fa?..."

Abbah ya ce "wallahi ya ce haka kawai yake son ƙara Aure, amma yace duk matar da muka zaɓa masa shi zai zauna da ita, shine nace bari na tambayeka ko ita Ramlatu tana sonsa ne ko kuma?..."

Mai martaba ya ce "yanzu maganar da nake da ita kenan akan ta fitar da mijin Aure amma ta nuna mun cewa ita har cikin zuciyar ta tafi son Roshan..."

Abbah ya ce "shikenam faɗuwa tazo dai dai da zama, Insha Allahu muna dawowa zamu samu zama,
tinda shi Roshan halinka ya ɗauko marasa son zama da mace ɗaya..."

Dariya Mai martaba yayi sannan ya ce "mai son zama da mace ɗaya yau dai an wayi gari mata biyu gare shi...".

Murmushi Abbah yayi tare da katsar da wayar....

Mai martaba ya dubi Ramlatu sannan ya ce "kukan ki yazo ƙarshe Roshan yana son ƙara Aure shine Abbansa yake tambayar ki...."

Ramlat ta ce "Abul kana nufin Roshan Ni zai Aura?..."

Mai martaba ya jinjina kai yana ɗauke da murmushi...

Ramlat har da sujjadar ta tsabar farin ciki, ta rinƙa hamdala tana gode wa ALLAH, tare da faɗin "Allah ya amshi addu'a ta, ashe addu'a tana da rana, tabbas na yadda cewa boka ko malami basu isa su tsara abinda Allah bai tsara ba...."

Mai martaba shima fatan alkhairi yayi mata sannan ya bata umarni da ta tafi...

Ramlat tana koma wa falo ta tarar da Indo da Maamie suna zaune a kujerar falo babu mai cewa kowa komai, da gudu Ramlat ta ƙarasa wurin Indo da gudu tana dariya tare da faɗin "Albishirin ki Aunty Aisha..."

Indo ta ce "goro fari tass meya faru kamar anyi miki albishir da ƙasa mai tsarki..."

Ramlat ta ce "Aunty Aisha Yaya Roshan zai ƙara Aure kuma Ni zai Aura, kuma Allah yasa naga tsinannen bokan da ya isa ya raba yaga ikon Allah, tinda Allah ne ya tsara babu mahalukin da ya isa ya raba..."
ta ƙarasa maganar tana kallon Maamie wacce take ta kumbura, ita takaicin ta Ƙanwarta wacce suke uwa ɗaya uba ɗaya yau ta gujeta ta koma hannun kishiyar ta...

Itama Indo ba ƙaramin farin ciki ta shiga ba tana faɗin "Masha Allah! Allah ya sanya alkhairi..."

Maamie a fusace ta miƙe tare da jan wata doguwar tsuka ta haura saman upstairs can room ɗinta ....

Ramlat ta ƙara volume da cewa "bin maganar bokaye da malamai dai rashin imani ne da jahilci..."

Indo ta maki cinyarta tana girgiza mata kai alamar kar ta sake faɗin haka....


★★★★★★★


Bayan isar su Abbah Nigeria a babban falon Abbah suka zauna kowa sai dai yaje can ya gaishe da Roshan domin baya son hayaniya shiyasa ya fake a part ɗin Abbah wanda ba kowa ne yake zuwa can ba...

Razhdeen shima yazo duba twins ɗinsa duk da ya je har ƙasar Ethiopia duba shi, a falo suke zaune suna shan hirar su yanzu Roshan yayi garau,
Daman ya dawo da niyar zai sallami Baiwar Allah sannan ya yi Auren sa yayi alƙawarin duk matar da aka zaɓa masa zai yi haƙuri ya zauna da ita indai tana son sa, domin bazai ƙara Auran wacce bata sonsa ba, kuma yayi tunani a yanzu abinda kake so ba shine alkhairi ba, sai wanda Allah ya zaɓa maka....

Suna zaune a falon Abbah shi da Razhdeen sai suka ji yo sallama, Roshan ne ya juya yana kallon bakin ƙofa ganin Baiwar Allah ce yasa shi kawar da kansa gefe tare da amsa sallama domin shi daman Razhdeen ko ɗagowa yayi ya kalleta ma baiyi ba balle ya amsa sallamar ta...

Baiwar ALLAH ganin yanda Roshan ya sauya mata ne yasa ranta sosuwa, babu yanda ta iya haka ta durƙusa har ƙasi tana gaishe shi da jiki...

Amsa mata yayi cikin sassanyar murya daga ƙarshe ya miƙe tsaye dai-dai lokacin da shima Razhdeen ya miƙe zai basu wuri.

Roshan ya kalli Razhdeen sannan ya ce "ha'a My man ya dai ka tashi? nayi tunanin zaku ɗan fahimci juna ne...."

Razhdeen fuska a haɗe ya ce "what do you mean?..."

Roshan ya nuna Baiwar ALLAH yana ɗaga masa kai,
Dogon tsuka Razhdeen ya ja sannan ya fice shima Roshan bin bayan Razhdeen yayi yana ƙiran sa da haka duk suka bar falon, sai iya ita kaɗai a falo itama daga baya ta tashi ta fice....


Bayan kwana sati da dawowar Roshan gyare-gyare aka fara yi a part ɗinsa gaba ɗaya part ɗin an sauya kalan pantin gidan, duk kayan furniture an chanchanza su saboda Abbah yaje har ƙasar Jidder sunyi magana sosai da mai martaba akan bikin, sannan suka yanke cewa next week za'a ɗaura Aure, Abbah ya ce duk wasu ɗawainiyan kayan ɗaki da sauran abubuwan duk ya ɗauke nauyinsa zai yi,
Ramlat farin ciki kamar bazata mutu ba, amma sai dai Roshan bai ƙira wayanta ko sau ɗaya ba sannan idan ta ƙira baya ɗagawa, sai abun yake bata mamaki....

Pinky da Rukky suma murna Yaya Roshan zai ƙara Aure kuma Ramlat zai Aura daman ƙawarsu ce, kuma ba son Baiwar Allah daman suke ba...

Ummy ce kawai ƴar ɗakin Baiwar ALLAH..



Gaba ɗaya Baiwar ALLAH ta kasa kwantar da hankalinta, duk abin duniya yabi ya ishe ta ga yanzu Roshan zai ƙara Aure, ita kaɗai tana kwance akan gadonta sai sharar kuka take ga wani irin kishi da yake damun ta...

Tana cikin wannan halin taji ana knocking ƙofar bedroom ɗinta da sauri ta tashi tayi tunanin Roshan ne domin tinda ya dawo ko kallonta baya son yi balle ya saurare ta kuma tana muradin jin muryarsa...

Tana buɗe ɗakin ta gànshi yana tsaye sai ƙare ta yake da kallo, ita kuma goge hawayen fuskarta ta soma yi tana sakin murmushi, ko kulata bai yi ba haka ya shige ciki ya zauna a bakin gado ta, kallonta ya yi sannan ya ce "zauna mana..." itama zama tayi a bakin gadon zuciyarta na bugun uku-uku domin tana fargaban jin abinda zai ce mata yanda taga fuskar sa nan babu annuri....

Cije lips ɗinsa na ƙasi yayi cikin takaici ya ce "a ranar da na kwanta rashin lafiya kinje room ɗina da buƙatunki na cewa na rubuta miki saki ko?, ban manta ba kuma ina sane

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login