Showing 21001 words to 24000 words out of 89400 words
Daman Aunty Yolash ce kawai zata iya tsawatar wa Baiwar ALLAH akan ta buɗe TOH itama ga a halin da take ciki itama ta kulle kan natan, Ummy ma wacce itace Yakamata ta rarrasheta itama ta zama uwar ɗaki....
🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️
Razhdeen shi da Mohandas layin mabarata suka nufa da isar su tsayar da motar sukayi a dai-dain layin suna baza idanu ko zasu hango Ƴar Amana, a wannan lokacin ma sun yi rashin Sa'a basu ganta ba, ɗan tsuka Razhdeen yaja tare da jan mota zai bar wurin Mohandas yayi saurin dakatar dashi tare da faɗin "wait Major! Bayan barin ka Nigeria nasha zuwa nan duba yarinyar nan amma bata nan, banyi tunanin sauƙa daga motar zuwa tambayarsu ita ba amma a wannan lokacin dole zamu je mu tambayesu ita, ina tunanin rashin zamanta anan ba lafiya ba..."
Dasauri Razhdeen ya juyo yana kallonsa cikin yanayin damuwa, ƙirjinsa ba ƙaramin bugawa yayi ba jin abinda Marshall ya faɗa..."
Mohandas yace "let me go and check her, stay inside the car..."
yana kaiwa nan ya fice kai tsaye wurin tsofin ya nufa, shi kuwa Razhdeen yana daga ciki yana kallon wurin da take yawan zama...
Mohandas tsugunawa yayi a gaban tsohuwar da Ƴar Amana take suka gaisa sannan yake tambayarta labarin Ƴar Amana,
Nan tsohuwa ta fashe da kuka tana faɗin "Allah sarki kurmiyar Allah, Amanar Allah sun ɗauke ta..."
Mohandas cike da mamaki ya furta cewa "daman kurmiya ce?..."
Tsohuwa tace "ey kurmiya ce, ɓarayi ne suka sace ta..."
Dasauri Mohandas ya miƙe tsaye tare da faɗin "whattttt!!!!...."
Juyawa yayi da gudu ya nufi motarsu, buɗewa yayi ya shiga yana jan numfashi ido a zazzare,
Razhdeen ganinsa ba ƙaramin tsorita yayi ba ganin halinda ya kasance, tsoronsa kar wani mummunan abu ya faru da ita..
A ɗan ruɗe Razhdeen yace "what's wrong?..."
shuru Mohandas bai bashi amsa ba,
A tsawace Razhdeen yace "ina maka magana ka bani amsa mana ..."
Razhdeen bai taɓa buɗe murya yayi magana kamar yanzu ba, cike da mamaki Mohandas ya juya yana kallonsa ganin yanda ya rikice lokaci guda,
a ɗan tsorace Mohandas yace "someone kidnap her..."
Razhdeen cikin go slow ya juyo yana ƙarewa Mohandas kallo ido a zazzare,
Jin bai gamsu da maganar Mohandas ba yasa ya buɗe murfin motar ya fice, kai tsaye wurin tsofaffin ya nufa yana zuwa ya tsaya yana binsu da kallo, a tsawace ya fara magana yana faɗin "Who kidnap her?,
tell me please who come and kidnap my sarah?..."
Duk tsaya kallonsa suke domin babu wacce tasan mai yake faɗi domin da turanci yake maganar,
tsohuwar ƴar Amana ce tace "kayi haƙuri yaro Bama jin Yaren nan..."
Razhdeen hannu bibbiyu yasa a cikin sumar gashinsa yana cakurkuɗawa cikin zafin rai yace "nace waye ya sace mun Sarah? ..."
Anan duk suka sanar masa duk yanda akayi da cewar suma basu ga fuskarsu ba domin baƙar hula ce akan su...."
tsohuwar ta miƙa masa jitar Ƴar Amana...
Razhdeen kamar zai dungura haka ya nufi motar yana shiga ya finciki motar a ɗari suka bar wurin,
A wannan ranar Razhdeen da Mohandas ba yanda basu shiga ba neman Ƴar Amana amma babu ɗuriyarta, duk yanda suka san ƙungiyoyin Dabanci Saida suka je amma basu samu labarinta ba, Saida suka yiwa wasu ƴan Daba dukan tsiya ganin zasu raina musu wayo,
yanzu misalin ƙarfe 2 na dare suna hanya, Mohandas gaba ɗaya ya gama gajiya daƙer ya lallami Razhdeen suka koma gida akan washe gari zasu ƙara fitowa nemanta......
asmeetah writer ✍️
*MY ENEMY _*
🫦 مقىينا 🫦
Mallakin
أسماء محمد أولا 🥳
Asmeetah (giaɗe writer)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
STEP TWO
👇
*11_ TŌ _12*
Misalin ƙarfe uku na dare, agogo ne yake harbawa a hankali ƙit-ƙitt-ƙittt a yayin da Razhdeen yake kwance saman katafaren gadonsa, yana rufe da mayafi sai iya fuskar sa ne a waje yana kallon ceilling, kashe hasken ɗakin yayi sai ɗan hasken lamp da ya bari mai launin green,
A daren yau Razhdeen bai samu yin bacci ba sakamakon abin da yasa a ran sa, ɓatar Ƴar Amana ba ƙaramin girgiza shi yayi ba domin a halin yanzu bai san a wani hali take ciki ba, gashi an bayyanar masa cewa zuwa akayi har wurin da take aka ɗauke ta, duk yanda akayi sun haɗa mata tarko ne,
Tunani ne barkatai acikin kwakwalwar sa, mafita yake nema yanda zai samu yarinyar nan domin a halin yanzu ita ce raunin sa!...
Washe garin ranar ɗaurin Auren Roshan da Baiwar ALLAH, kowa ya hallaru baƙi ne a gidan Chief kamar basa mutuwa tsabar yawan family, misalin ƙarfe 12 na rana Ango da Abokan sa kowa yayi shirin zuwa ɗaurin Aure dake can babban masallaci, Abbah shima da abokansa waɗanda suka zo ɗaurin Aure sun sha manya-manyan kaya, kowa ya hallaru sai fita ake da wasu manya-manyan motoci ga motocin sojoji suma zasu yi rakiya, kowa ya tafi sai iya Ango ne kawai ya rage shima yasha farar gizner da babbar gariya sai shining giznar take, ga wani irin ƙamshin da yake fitarwa kai kace wanka yayi da zallar turare,
Roshan ba ƙaramin kyau yayi ba, ga hular kalar kayan, sai wasu Abokansa guda uku motar su ce kawai ta rage basu tafi ba, ganin Roshan yaƙi tafiya yasa suma suka ƙi tafiya domin saboda Angon za'aje wurin ɗaurin Auren shi kuma bai tafi ba, Roshan ba kowa yake jira ba illa twins ɗinsa Razhdeen, duk taron mutanen da akayi babu Razhdeen a ciki, kowa sai tambayar sa yake, domin shine twins ɗinsa kuma babban Abokin Ango, an ƙira wayarsa switch up, anje gidansa baya nan babu wanda yasan yanda yake hatta Mohandas shima ya halarci wurin ɗaurin Auren Roshan,
Ganin shuru babu labarinsa yasa Abokanan Roshan suka ja shi cikin motar nan da nan kamar walƙiya suka bar gidan domin iya su kawai ake jira a wurin taron ɗaurin Aure...
Baiwar ALLAH tana bedroom ɗinta tare da masu kula da ita ba abinda take sai kuka, gaba ɗaya fuskar nan tayi jawur tsabar kuka kamar ba Amarya ba, ji take kamar ta sanar cewa bata son Auren Roshan amma sai dai idan tayi hakan tayi butulci sannan aikin gama ya gama tinda an tafi ɗauro Auren, har cikin ranta bata cire son Razhdeen acikin zuciyar ta ba kuma gani take bazata taɓa cire soyayyarsa ba, kulle kanta da tayi a bathroom tayi niyar tasha poison ta kashe kanta amma tayi tunanin kashe kai ba abu ne mai sauƙi ba, tana ciki Abbah ya shugo domin a lokacin har anje an gayo masa dake tana jin shakkar Abbah,
tana zaune a bakin bed tunanin samawa kanta mafita take, amma zuciyarta na sanar mata cewa "kiyi haƙuri ki zauna da mijinki haka ƙaddarar ki tazo miki, a duk yanda kika tsinci kanki to ki gode wa ALLAH..."
Sauƙe numfashi tayi domin tayi na'am da shawarar da zuciyarta ta bata, a hankali take ɗago da kanta tana bin mutanen ɗakin da kallo, ganin kowa yana cikin farin ciki yasa ta yin maganar zuci cewa "Allah sarki farin cikin ku kawai kuka sani amma baku san tawa farin cikin ba..."
tana cikin saƙe-saƙe kwatsam taji an dafa kafaɗarta, da sauri Baiwar ALLAH ta juyo tana kallon wacce ta zauna gefenta tare da ɗora mata hannu akan kafaɗa,
Ramlat ce tasau mata murmushin takaici da kuma kishi ta ce "Sannu Amarya bakya laifi, Amma fah kin ciri tuta gaskiya duk da baki da asali amma haka Yaya Roshan ya nace miki, kuma ba wani dace wa kuka yi da juna ba, kina nan kamar wata farar goɗiya..."
Duk mutanen ɗakin ne suka juyo suna kallon su, wata daga ciki ne ta ce "toh ikon Allah duk meya kawo wannan maganar?..."
Ramlat ta kalleta sama da ƙasa sannan ta ce "bakin da Allah ya tsaga baya rasa ta cewa, don haka abin da ke raina na faɗa..."
wacce tayi maganar ce ta kuma cewa "Amma ai bai kamata kiyi irin wannan maganar a cikin mutane ba..."
Ramlat ta ce "Oh ashe dai a cikin mutane nake, ai Ni kuwa na ɗauka dabbobi ne..."
Duk shuru suka yi saboda ba mai iya tanka mata, tsoron Ramlat ake saboda Hajiya Maamie domin ba ƙaramar masifaffiyar mata ba ne, yanzu sai ta iya hargutsa taron bikin,
Ummy uwar masu gida wacce jugowarta cikin ɗakin kenam, kalmar da Ramlat ta furta ne ya daki dodon kunnenta, ai kuwa nan itama ta buɗi baki ta ce "dabbobin suna da yawa ai amma sai dai wacce take agolanci tafi dabbobin dabbanci..."
Ramlat miƙe wa tayi tsaye tana bin Ummy da kallo cike da mamaki ta ce "Ummy Ni kike ƙira da Agola?..."
Ummy ta ce "to ƙarya akayi miki ne? ko gidan Uncle mai martaba da kike zaune a gidan Ubanki ne shi? kin samu matsayi ne albarkacin zaman da kike a gidan sarauta amma in ba haka ba kin isa ki buɗe baki kiyi wani maganar banza ne anan, duk mutanen da kike gani acikin gidan nan duk jini ɗaya ne babu bare sai ke, Yayarki ce matar mai martaba ita kuwa ba haihuwa take ba hakan yasa ta jawo ki gidan sarauta kizo ki ci arziƙi babu a house..."
Ramlat ita kaɗai tasan takaicin da take shaƙa a yanzu buɗar baki tayi ta ce "au gorin haihuwa zakiyi wa Aunty nah? eh naji bata haihuwa amma ai ta kama kanta tana zaune a gidan mijinta, wata uwar kuma zubar da ƴaƴanta tayi take bin yawon hotel..."
Ramlat tana kammala fitar da abinda ke ranta tayi saurin barin room ɗin domin tasan uwar Ummy ce take yawon hotel,
wani abu mai kama da kibiya ne ya soki saitin zuciyar Ummy tsabar takaici da baƙin cikin har an fara mata gori akan mahaifiyarta,
Da sauri ta juya zata bi bayan Ramlat taji an riƙo ta juyawa tayi taga Baiwar ALLAH ce take ta faman girgiza mata kai alamar karta biye mata,
Ummy tsabar takaici bata san lokacin da ta rausa uban ihu ba tare da durƙusa gwiwowinta ƙasi, duk mutanen ɗakin ne suka rufu kanta suna bata haƙuri akan abinda ya faru, Ummy kuwa kuka take ko sauraron su bata yi domin abun da ciwo ta sanadiyar haka yasa Mahaifiyarta tabar gidan Mahaifinsu,
Jin Ihun ya jawo hankulan wasu daga cikin mutanen gidan, Aunty Yolash ce first ɗin shugowa dake tana kusa da ɗakin sai ga Rukky da Pinky wacce ba'a daɗe da fito da ita daga ɗakin duhu ba,
Ummy tambayarta ake meya faru da ita amma babu bakin magana sai waɗanda akayi a gabansu ne suka faɗi duk abin da ya faru, sam babu wanda yaji daɗin abinda ya faru a cikinsu,
Baiwar ALLAH dake tsaye ta kama kai tayi shuru sakamakon wani irin Jiri da hajijiyar da take ji, kanta ne yake mata wani irin matsanancin ciwo, ko kaɗan bata son hayaniya a halin da take ciki yanzu domin ba isasshen lafiya gareta ba,
a cikin tana jurewa har ƙarfinta ya ƙare ta yanki jiki ta faɗi a wurin, daga lokacin bata san ina hankalinta yake ba domin alamun suma tayi,
sai kuma kallo ya koma kan Amarya, nan da nan magana ta bazu cewa "Amarya ta yanki jiki ta faɗi ga babu maza a gida duk taron mata ne...
Ramlat kuwa ɗakin su ta shige ita da Auntyn ta Hajiya Maamie, tsaya wa tayi tana huci a yayin da Hajiya Maamie take zaune a bakin gado sai shan kwalliyarta take, ganin Ramlat a cikin wani hali yasa ta cewa "ke kuma lafiyar ki ƙalau kuwa?.."
Ramlat ta ce "ina kuwa lafiya Aunty Maamie, wannan ƙaramar Yarinya tana shirin raina mun wayo..."
Hajiya Maamie ta ce "koma wacece meyasa baki ci ubanta ba sai kuma kizo kina mun cika baki aikin banza kawai, ai indai bazaki buɗe baki kici mutuncin mutum ba to ke da raini kuwa yanzu kuka ƙulla, wai ma wacece yarinyar?..."
Ramlat ta ce "Ummy mana kodan a gidan ubanta take ne shiyasa zata nemi ta ci mun mutunci, har wani ƙirana take da Agola ke kuma ta ce bakya haihuwa..."