Showing 33001 words to 36000 words out of 89400 words

Chapter 12 - MY ENEMY BOOK 2 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

2535

sosai kuma bai juma da bawa Baiwar Allah jini laida biyu ba, kuma son samu sai ya yi wata biyu kafin ya ƙara bada jininsa, duk da anyi masa wannan bayani amma fur Razhdeen yaƙi yadda wai shi sai an ja mata jininsa, babu yanda kowa ya iya a cikin su haka aka ja jininsa aka je aka ɗaura wa Ƴar Amana...

Bayan an gama da ita shima aka zo akayi treat ɗinsa sosai,
daga nan Doctor ya yi tafiyar sa...


Bayan kwana biyu da faruwar haka sai a lokacin su Abbah suka ji labarin abinda ya faru da Razhdeen, hankalin Abbah ba ƙaramin tashi ya yi ba ko jinkiri baiyi ba haka ya kama hanya da sojojinsa masu raka shi zuwa gidan Razhdeen, a ruɗe Abbah ya shiga cikin wantalelen gidan bai tsaya a ko ina ba sai a babban falon gidan, anan ya tarar da Razhdeen yana zaune a kujerar falon ga jiki fari sol babu riga sai tilin bandaje, ga kuma Mohandas ata gefen sa shima dake shine mai masa duk ɗawainiyoyinsu shi da Ƴar Amana,
Abbah zama yayi yana facing ɗin Razhdeen ya ce "Razhdeen ashe akwai abinda zaka iya ɓoye mu dan gane dakai? idan ka ɓoye mun komai ai bai kamata ka ɓoye mun rashin lafiyar ka ba kuma a wurin yaƙi haba Razhdeen? shin ka kyauta mun kenam? ban tashi jin maganar ba sai a television cewar kun ceci wasu yara da aka yi kidnaping ɗinsu har kaima kaji rauni sosai..."

Razhdeen sunkuyar da kansa ya yi ƙasi yana sauraron Abbah, sai ji ya yi Abbah ya ƙira sunan sa cikin sassanyar murya,
Razhdeen ɗagowa yayi yana kallon Abbah,
Abbah ya ce "yanzu ya jikin nakan?..."
Ya ce "naji sauƙi..."
Abbah ya kuma cewa "Sosai?..."
Kai Razhdeen ya ɗaga masa..

Mohandas already ya bar wurin tin shugowar Abbah, ya gaishe da Abbah amma sam yaƙi sauraronsa..
Abbah ya juma sosai a wurin Razhdeen kafin daga baya ya yi tafiyar sa ya sanar masa cewa zuwa dare zai ƙara zuwa ya duba shi...

Bayan fitar Abbah ba jumawa sai ga Roshan da Baiwar ALLAH sun shugo, gaba ɗaya hankalin Baiwar ALLAH akan Razhdeen yake, zumuɗinta tazo taga a wani hali yake ciki domin tinda taji labarin hankalinta yaƙi kwanciya, Roshan shi kaɗai yayi niyar zuwa ya duba twins ɗinsa amma Baiwar ALLAH ta dage akan cewa zata zo duba shi itama, babu yanda ya iya haka ya taho da ita...

Roshan ba ƙaramin tausayawa twins ɗinsa ya yi ba ganin a halin da yake ciki, bayan sun kammala gaisawa ya kalli Baiwar ALLAH sannan ya ce "Ammata ganan My Man ki gaishe shi da jiki mana, kinyi shuru bayan ke kika damu akan zaki zo ki gànshi..."

Jin haka yasa Razhdeen ɗagowa ya kalle ta sannan ya kawar da kansa gefe tare da haɗe gira, saboda ya tuna maganganun da ta rinƙa yi a hospital wanda sam bai ji daɗin hakan ba.

Itama kallon sa tayi gaba ɗaya kamar wanda aka ɗaure mata baki, ta kasa cewa komai lokaci guda taga yayi mata wani irin Mungun kwarjini da kuma shakkarsa, wani irin harara ya wurga mata ta wutsiryar ido ba tare da Roshan ya gani ba, da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasi kamar zata fashe da kuka...

Roshan ne ya ce "am ina Mohandas yake ne?..."
Razhdeen murya ciki-ciki ya ce "yana ciki..." ya nuna yanda yake da hannu can part ɗin da aka ƙwantar da Ƴar Amana..
Shi sam ya manta da cewa a part ɗin Ƴar Amana take sai daga baya ya tuna, da sauri ya juya zai yi wa Roshan magana yaga har ya tashi ya nufi part ɗin,
Razhdeen bai damu ba saboda yasan Roshan idan aka sanar masa cewa secret ne bazai sanar ba...
Ɗagowar da zai yi kwatsam suka haɗa eyes da Baiwar ALLAH ta zuba masa ido ko ƙibgawa babu, cike da mamaki ya ce "what are you looking for?..."

Ciki ƙwarin gwiwa ta ce "You..."
haɗe fuska ya yi tare da faɗin "whatt?..."

Roshan kai tsaye upstairs ya haura room ɗin farko ya fara buɗe wa yaga babu kowa still ya yi gaba ya buɗe room na biyu sai kawai ya tarar da Mohandas zaune kan kujerar ɗakin yayi tagumi kansa na kallon ƙasi,
Roshan har zai yi sallama idonsa suka sauƙa akan Ƴar Amana dake kwance saman gado, sake baki yayi yana kallon wurin, daga bisani ya ce "Marshall aina ku ka samo yaro?..."

A ruɗe Mohandas ya ɗago yana bin Roshan da kallo ganin ya yi masa shugowar bazata,
Ƙarasa shugowa ya yi still yana faɗin "yaron nan fa meya same shi?..."
Mohandas ya ce "samu wuri ka zauna tukun, wannan ba yaro bane yarinya ce..."
Haɗe gira Roshan ya yi tare da faɗin "taya ya zai zamo mace bayan ga kansa a tanɗe kamar lale kobo..."
Mohandas ya ce "bazaka fahimta bane in har ba bayani aka yi maka ba..."
Roshan ya ce "okay ina jinka..."

Mohandas ya ce "kai ma kasan kalar mafarkin da Razhdeen yake yi ko? kuma kasan me yake ƙunshe acikin mafarkin, yarinyar da yake gani koda yaushe a cikin mafarkin ba kowa bace illa wannan yarinyar, tin da Allah yasa Razhdeen yayi ido huɗu da yarinyar bai sake yin mafarkin nan ba sakamakon kasan itace maganin mafarkinsa..."
Nan Mohandas ya sanar wa Roshan duk halin da ake ciki da irin ƙalubalen da yarinyar ta fuskanta a hannun mutanen nan,
Roshan yana tsaye bai san lokacin da ya nemi wuri ya zauna ba, yayi matuƙar tausayawa yarinyar kuma yana mamakin meyasa take yawan fitowa a cikin mafarkin Twins ɗinsa, tambayoyi ne tarin-tarin a cikin zuciyarsa.

Mohandas ne ya kuma cewa "mun ɓoye ta ne a cikin gidan nan ba tare da kowa ya sani ba, kuma bama buƙatar kowa ya sani daga Ni sai kai sai kuma uban gayyar wato Razhdeen da kuma likitan da yayi musu magani..."

Roshan ya ce "to amma meyasa Twins ya damu da yarinyar har haka?..."
Mohandas ya ce "meyasa bazai damu da ita ba? ita ce fa mafarkinsa..."
Jinjina kai Roshan ya yi sannan ya ce "Okay ba damuwa zamu cigaba da tsare ta ba tare da kowa ya sani ba Insha Allahu..."

Mohandas ya ce "gud! Amm daman Roshan inaso zanyi magana da kai Please..."
Roshan ya ce "about Minal ko?..."
Mohandas ya ce "of course, sannan Abbah yazo na gaishe shi amma he didn't answer me I don't know why..."
Murmushi Roshan ya yi sannan ya ce "kafi sanin kowa dalilin da yasa ba zai kula ka ba, amma mun kusan kawo ƙarshen wasan..."

Mohandas ya ce "tayaya kenam?..."
Roshan ya ce "ta hanyar ɗaura muku Aure ba tare da kowa ya sani ba, tinda Allah yasa kai ka musulunta, idan Abbah yasan ka musulunta ma bazai taɓa Aura maka ɗiyarsa ba saboda iyayenka kuma na farko ba shiri suke yi ba..."

Mohandas ya gamsu da bayanan Roshan yasau numfashi tare da faɗin "Nima iyaye na baza su taɓa sani ba sai lokacin da aka kawo ƙarshen wasan, don haka Roshan inaso a cikin satin nan a Aura mun Meenat ko hankali na zaifi kwanciya Please..."

Roshan ya ce "a kwai wurin da zamu je a ɗaura gobe da safe Insha Allahu, domin har nayi magana da malaman wurin, za'a yi hakan ba tare da My Twins ya sani ba tinda ya nuna shima baya son harkar munafurci..."
Jinjina kai Mohandas ya yi tare da faɗin "that's gud, but ita Meenat da ita zamu je?..."
Roshan ya bashi amsa da "Eh".

Sai da suka kammala tattaunawarsu tsab tukun suka baro ɗakin,
Ƴar Amana har zuwa ɗan kwanakin nan bata samu farfaɗowa ba..


Razhdeen suna zaune zaman kurmanci babu wanda ya kula kowa a tsakanin sa da Baiwar ALLAH, sai dai su kalli juna su kawar da kai amma ko wannensu da saƙe-saƙen da yake a cikin zuciyarsa,
Razhdeen ganin har yanzu su Roshan basu fito ba yasa shi miƙe wa zai bi bayansu, ai kuwa nan bayansa ya riƙe sosai haka ya yi baya zai faɗi da gudu Baiwar ALLAH tayo kansa ta rungume shi sosai tana ƙoƙarin tare shi, dai-dain lokacin da su Roshan suka fito, idonsu ne ya sauƙa akan Baiwar ALLAH yanda ta rungume shi, shi kuwa ya dafa saman kujera da hannunsa ɗaya, ba wai riƙe shi da tayi ne yasa bai faɗi ba domin bata da ƙarfin da zata tare shi idan yazo faɗuwa, already ya rigada ya dafe kujerar, ita dai kawai ta an ƙara ne domin a tsorace tayo kansa kamar wanda take jira ya goce...

Ganin yanda ta rungume shi ne yasa shi fusata da ɗayan hannunsa ya hankaɗata baya har sai da ta doku akan kujerar da take before,
Komawa yayi ya zauna yana binta da kallon takaici
ya ce "You are ingratitude fool, Nonsense girl wannan wani irin hauka ne? shin idan aka barki zaki iya dakatar da ni ne idan nazo faɗuwa? bana son wannan gangancin kada ki sake mun irin haka na gaya miki idan kuma ba haka ba sai na miki abinda bakiyi zato ba, mtsws useless girl..."

Ita kuwa baiwar ALLAH kanta a ƙasi ba abinda take sai kuka domin ba ƙaramin ci mata mutunci yayi ba...

Roshan da Mohandas ne suka ƙarasa shigowa cikin falon bayan sun gama jin duk chakwakiyar da suke yi,
Roshan ne ya zaune kusa da Razhdeen tare da dafa kafaɗarsa ya ce "haba My Man abun gwaninta fa tayi maka bai kamata kayi mata haka ba, Please am so sorry na amshi bakin ta..."

Razhdeen kallonsa yayi fuska a haɗe ya kuma kawar da kansa gefe yana faɗin "ka tashi ka fice mun da ita daga gida, next time idan har kasan da ita zaka zo mun to kaima kayi zaman ka bana buƙatar ku..."
Murmushi Roshan ya yi tare da faɗin "duk mai ya yi zafi haka My Man?..."

Tsuka Razhdeen ya yi tare da ƙoƙarin tashi zai bar wurin, kasa tashi yayi sai da Mohandas ya tallafa masa tukun daman shine mai taimaka masa da wasu abubuwa, suna tafiya hankali sai da suka ɗan yi nisa kaɗan sannan Razhdeen ya waiwayo idonsa akan Roshan wanda shima miƙewa yayi zasu tafi
ya ce "Please kana zuwa kana duba mun jikin Yarinyata..."

Da murmushi kwance saman fuskar Roshan ya ce "Okay ana kan duba ta zata samu sauƙi Insha Allahu, naga jikin natan ya fara warware wa kawai farfaɗowa ne bata samu damar yi ba..."

Razhdeen bai bashi amsa ba ya juya gaban sa, Mohandas ne ya kuma cewa "kar ka manta Yarinyar kasan a Kashmir take..."
Roshan ya ce "Okay don't worry..."
Duk sunyi wannan maganar ne saboda kar Baiwar ALLAH ta fahimci wani abu..

Da haka suka kammala Roshan ya ja matarsa suka tafi, Razhdeen kuma kai tsaye room ɗin da Ƴar Amana take ya nufa shi da Mohandas domin hawan upstairs zai bashi wahala indai ba riƙe shi akayi ba ...

Baiwar ALLAH wani irin ƙololuwar baƙin ciki ne ya daki saitin zuciyar ta jin Razhdeen ya ambaci sunan wata da Yarinyarsa,
Da wannan tunanin a cikin zuciyarta suka isa gida....


asmeetah writer ✍️


🤦‍♀️ *MAƘIYI_NAH*🤦‍♀️


*MY ENEMY _*

🫦 مقىينا 🫦


Mallakin
أسماء محمد أولا 🥳

Asmeetah (giaɗe writer)



https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

STEP TWO
👇
*17_ TO_18*




WASHE GARI

Baiwar ALLAH ne zaune akan sopar falon ta tana kallon plasman abin ta,
Daga ganin yanda take ta zuba murmushi kasan Film ɗin yayi matuƙar burge ta, Minal ce ta shigo tana lanƙaye da handbag ɗin ta ko sallama bata samu damar yi ba, tazo ne saboda Roshan ya riga da ya sanar wa Abbah cewa zasu fita unguwa,
Baiwar ALLAH a bazata taji Minal ta ce "ina Yaya Roshan?..."

Baiwar ALLAH ɗago wa tayi tana binta da kallo ko amsa bata ba ta ba.
Minal ta ce "Malama magana nake miki dai ko dai kin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login