Showing 72001 words to 75000 words out of 89400 words

Chapter 25 - MY ENEMY BOOK 2 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

2519

Razhdeen shima ya amince indai har zata musulunta zai amince Razhdeen ya Aure ta.

Daddy ya sanar cewa "yana son Amreesh tayi aikin soja itama..."

Razhdeen ya amince da batun domin shima yana son macen soja...

Har zuwa yanzu akwai photunan Amreesh da yawa a wurin Razhdeen tin tana yarinya ƴar shekara uku...

Gyaran murya Daddy ya yi sannan ya ce "idan na ɗau alƙawari bana karyawa, ƙudiri na har yanzu yana nan, ko a yanzu Allah ya bayyano mun da Amreesh zan Aurar da ita a Razhdeen ne..."

Daddy ya kalli Razhdeen sannan ya ce "M.G kar fa kace abinda ya hanaka yin Aure saboda Amreesh ne..."

Jikin Razhdeen ne ya yi sanyi haka yake jin zuciyar sa tana bugawa, lokaci guda fuskar Amreesh ya fara masa gizo lokacin da take yarinya ga kalar dariyar ta irin na yara sai ƙyalƙyalewa take da dariya a yayinda yake lilata a lilon wasan yara,
wani irin haɗiyar yawu yayi sauran kaɗan hawaye ya gangaro masa yayi saurin goge wa.

Kowa a wurin ya lura da damuwar da Razhdeen ya shiga lokaci guda kuma an san duk akan Amreesh ce domin kowa yasan tsananin so da ƙaunarta da yake...

Razhdeen ya kalli Daddy sannan ya ce "har yau har gobe ina tsananin ƙaunar Reesh, ina son Reesh nasa a raina itace matar da zan Aura kuma har kullum ita nake kalla a matsayin nan, hakan yasa babu wata mace a gaba na, babu macen da nasa a raina cewa zan Aura har yanzu, kullum mafarki na da tunani na shine Reesh zata dawo gare ni ne, har yau ban daina neman ta ba, ina aiki na amma kuma ina bincikar yanda take,
har yanzu ban yadda cewa Reesh ta mutu ba, na rantse da sarkin dake busa mun numfashi wallahi tallahi Reesh tana nan a raye, har yanzu ɓangare guda na zuciyata wanda na sadaukar wa Reesh tana kan bugawa hakan na nufin Reesh tana nan a doron duniya,
zuciyata gida biyu ta kasu ɓangare guda na Reesh ce ɗayan ɓangaren kuma...."

Lokaci guda ya tuno da Ƴar Amana videon ta daya kalla ne ya faɗo masa a rai sai kuma yake hasasho fuskar ta,
Girgiza kai yayi cikin sassanyar murya ya ce "gaba ɗaya zuciyata ba tawa bace...."

Lokaci guda hawaye duk ya wanke masa fuska, a ruɗe ya miƙe tare da nufan hanyar fita,

Madam Parveen a rikice ta ce "Razhdeen abinci kazo mu ci kar ka tafi da yunwa....."

Lokaci guda itama ta kife ƙasin carpet tare da rausa uban ihu tana faɗin "ku nemo mun Amreesh ɗin ta, tana raye wallahi, Allah yasa tana rayeee, wayyo Amreesh ɗinta...."

Daman tana maƙale da kukan ta ganin bazata iya riƙe wa ba yasa ta fara kuka na gaske,
Rakesh ne yayo kanta ya ɗago ta yana rarrashinta shima yana kukan,

Daddy shima a cikin damuwa ya miƙe ya koma cikin room ɗinsa, yana jin takaicin ya kasa cika wa Razhdeen alƙawarin da ya ɗaukar masa gashi har zuwa yanzu Allah bai ƙara basu haihuwa ba balle in ya ƙara samun mace ya ba shi......


Tin daga lokacin aka fame wa Razhdeen ciwon da ke cikin zuciyar sa, yanzu da Amreesh yake kwana sannan ya tashi da ita a cikin zuciyar sa, ya kuma ƙudurta a ransa cewa zai cigaba da jiran Amreesh har ta bayyana, ya furta cewa "in har yayi Aure kafin bayyanowar Amreesh to sai dai rabin zuciyarsa ce ta daina harbawa nan ne zai san Amreesh ta mutu....


★★★★★★★


A ɓangaren Abbah kuwa damuwa na yau daban na gobe daban ƙarfi da yaji Uwar masu gida da Ƴar tinny sun ƙi dawowa yau tsawon wata guda, da haka har ya haƙura ya barsu...

Da misalin ƙarfe 9 na dare Abbah ne yake zaune a falo shi da Ammy ga kuma Baiwar ALLAH itama a zaune domin yanzu mafi lawanci tafi zama a part ɗin Abbah saboda rage kewa, Roshan ya nemi ta nesanta kanta daga gare shi hakan yasa tin safe in tazo part ɗin su Abbah bata komawa part ɗinta sai ƙarfe 10 na dare, shima Roshan baya wuni a gidan saboda kar a fahimci wani abu rashin zamansa a gida shi zai sa a kau da ido akan daɗe War da Baiwar ALLAH take a part ɗin su Abbah,

Suna zazzaune sai ga ƙiran wayan Abbah, yana dubawa sai yaga ƙiran su Pinky da Rukky ne dake can ƙasar London,
Yana ɗagawa yaji muryar Pinky suka gaisa take sanar masa cewa "gobe zasu yi graduation..."

Abbah ya nuna farin cikin sa sosai ya ce musu "Insha Allahu gobe zaku gan mu mun zo London..."

Ta ce "tam Abbah sai kun zo..."
ta kuma cewa "yawwa Abbah daman muna son sanar maka wani albishir..."

Abbah ya ce "my Twins female ina sauraron ki..."

Gashi yanda yasa wayar a speaker kowa na falon yana ji dake iya Ammy ne da Baiwar ALLAH.

Pinky ta ce "kafin nan dai Albishirin ka..."

Abbah ya ce "goro fari tass..."

Pinky ta ce "Abbah Ni da Rukky mun fahimci juna zamu yi Aure..."

Cikin rashin fahimta Abbah ya ce "kuna nufin kun samu mijin Aure ne?..."

Pinky ta ce "a'ah Abbah Ni da Rukky ne zamu Auri juna saboda anan makarantar mu duk haka suke yi suna Auran junan su, namiji ya Auri namiji haka itama Mace ta Auri mace wallahi kuma fa Abbah kar kaga yanda ake dacewa da juna har party ake yi, mu ma za'a ɗaura mana Auren ina zaku zo partyn bikin bayan graduation ɗin ?...."

Abbah jin kansa yayi ya tafi zuuuu ya rasa ganewa hajijiya ne ko kuma mai?

Ammy da Baiwar ALLAH kallon juna suka yi cikin zaro ido waje jin abinda Pinky ke faɗi..

Pinky ta ce "Hello Abbah kana ji na kuwa..."

Abbah ya ce "wait! wait wai kina nufin ke da Rukky zaku Auri juna? kuma haka ku ka ga anayi?..."

Pinky ta ce "eh mana Abbah ai shiyasa nake cewa Nigeria ƙauye ne duk basu waye ba, domin ban taɓa ganin anyi ba..."

Abbah ya ce "kenam iya Auren ku ka ga anayi? idan akayi Auren mai ake yi?..."

Abbah yayi tambayar nan ne saboda yasan shin suna aikata mummunan aiki ne ko kuma...

Pinky ta ce "idan akayi Auren Ni zan zama miji ita kuma Rukky mata ita zatana mana girki da aikin gida, Ni kuma sai ina fita yawo na, bayan wasu shekaru sai mu haifi ƴaƴan mu...."

Abbah ya ce "kenam kun taɓa sanin junan ku yanzu haka?..."

Pinky ta ce "kamar ya Abbah ban gane ba..."

Abbah ya ce "kamar dai miji da mata su kwana gado ɗaya har suyi sex kun taɓa? ai dai kinsan sex kam..."

Pinky ta ce "haba Abbah wannan ai sai an ɗaura mana Aure a school ɗin kafin nan, cab ai mun san haramun ne yin sex kafin Aure shiyasa zamu jira muyi Auren...."

Abbah ya ce "kenam Auren da zaku yi ku biyu ke da ita ba haramun bane ba ko?..."

Pinky ta ce "Abbah ka taɓa jin Aure ya zama haramun? ai ko wani irin Aure halal ne, Auren Mace da namiji halal ne haka Auren namiji da namiji shima halal ne haka kuma Auren mace da mace shima halal ne, saboda hakane yasa na sanar maka ko kuma zaku zo hidimar bikin..."

Zuciyar Abbah ne yake bugun uku-uku cikin tsoro da fargaba ya ce "wannan gaskiya ne, zancen ki hakane Malama Balkisu,
Yanzu abinda nake so da ku shine kuzo ayi bikin nakun a cikin ƴan uwanku domin abun alfahari ne ace ƴan uwa sun taru a gidan ku saboda Auren ku ko..."

Pinky ta ce "Abbah ga ƙawayen mu anan har yaushe sai mun koma Nigeria ƙauye kuma..."

Abbah ya ce "haba Balkisu baki ga Yayan ku Roshan shima a gida yayi Aure bane, dan ALLAH ku dawo kuyi Auren nan, Ni zan ɗauki ɗawainiyar komai da komai duk abinda kuke so, na tanadar muku da gidan da zaku zauna, in ma bazaku zauna ba zan kai ku ƙasar waje kuje ku huta duk ƙasar da ku ka zaɓa...."

Pinky ta ce "gaske Abbah wow munyi farin ciki sosai...."

Abbah ya ce "yanzu abinda nake so da ku shine graduation ɗin ma ku bari sai kun dawo gida sai a haɗa da bikin ku Koh?..."

Pinky ta ce "ai gobe ne graduation ɗin..."

Abbah ya ce "eh gobe da sassafe ku hau jirgi ku dawo da wuri kun ji Daughter's ɗina...."

Pinky ta ce "to shikenam Abbah zamu fara shiri tin yanzu gobe zaku gan mu a Nigeria..."

Abbah ya amsa mata cikin kulawa amma cikin zuciyar sa tafasa yake kawai jurewa yake....

Sai bayan sun kammala wayar ya ɗorata akan ƙirji yana sauƙe nannauyar numfashi har zuwa yanzu ƙirjinsa bugawa take, a ransa yana faɗin "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, Allahumma ajurni fi musibati wa akhlifli khairan minha, wannan wani irin ƙalubale nake fuskanta ne kam, duk ƴaƴa babu na gwara, ɗaya tabi saurayi sun gudu wacce take ji da ita ta zaɓi uwarta tare da Auta ta, ga kuma sauran biyun suna son kauce hanya wai Auren jinsi..."
haka yake ta wannan tunanin a ransa...

Ammy ta ce "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, waɗannan yaran basa jin magana, gwara da kayi musu kalamai cikin kulawa da fahimta, inda ace kayi musu magana ta zafi yanda kake cikin damuwan nan ai ba'a san mai zai faru ba, gashi yanzu cikin lallami zasu dawo hankali a kwance....."

Baiwar ALLAH kam abun ma dariya yaso bata, kamar waɗanda basu shiga islamiyya ba, kodan rayuwar can ta chanza su sosai, dan ma Aski yazo gaban goshi sun kammala school ɗinsu,

Abbah a yanda hankalinsa ya tashi nan ai ko basu gama school ɗin ba ma zai cire su a makarantar....




*MA SHA ALLAH*

*DAGA WANNAN SAI LAST PAGE SAI KUMA MU SHIGA BOOK 3 TAKUN ƘARSHE..."*

*WAƊANDA SUKA BIYA KUƊIN SU NA BOOK 3 300₦ ZAKU GA NA FARA SAKA KU A PAID GROUP, ZUWA NEXT WEEK ZAMU FARA BOOK 3 TAKUN ƘARSHE...*

*DALILIN DA YASA NA ƊAGA SAI NEXT WEEK SABODA WAƊANDA BASU BIYA BA SU SAMU DAMAR BIYA KAFIN ZUWA LOKACIN, SABODA A FARA A TARE...*

*GOBE INSHA ALLAHU ZAMU YI LAST PAGE*


*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL*

*9065443871 OPAY BANK*

*PAY 300₦ ONLY 👌*

*SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER 09065443871*


*DAGA YAU ZUWA KULLUM I'M AVAILABLE*
*09065443871 CALL OR WHATSAPP*


*TO MASOYA KAMAR YANDA NA SUBURBUƊO MUKU TYPING NIMA INASO KU SUBURBUƊO MUN SHARHI😅😅😅*

FATAN ALKHAIRI 🙏



asmeetah writer ✍️


🤦‍♀️ *MAƘIYI_NAH*🤦‍♀️


*MY ENEMY _*

🫦 مقىينا 🫦


Mallakin
أسماء محمد أولا 🥳

Asmeetah (giaɗe writer)



https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

STEP TWO
👇
*46_ TO_50*


*THE END OF BOOK TWO*

*wannan shine ƙarshen littafi na biyu sai mun haɗu a littafi na uku wato takun ƙarshe...*

*Ku biya kuɗin ku domin samun cigaban littafin 300₦ 👌*

*Domin samun ƙarin bayani a tuntuɓe ni ta wannan number*
09065443871 call or whatsApp ....









Bayan Dawowar su Pinky da Rukky da kwana biyu suka ga Abbah ko sauraron su baya yi abun sai ya basu mamaki, Pinky ce tayi ƙarfin halin zuwa har part ɗin Abbah ta same shi yana zaune akan sopa kansa na kallon sama da duk kan alamu dogon nazari ya shiga, jin sallama yasa ya ɗago yana kallon wacce ta shigo.

Pinky zama tayi a gefen Abbah tana gaishe shi, Abbah amsa mata yayi tare da faɗin "ji ta kamar ta Allah..."

Pinky ɗago wa tayi tana kallon Abbah cikin rashin fahimta,
Abbah cewa ya yi "tashi kije ki ƙira mun ƴar uwarki kuzo tare..."

Pinky cikin murna ta tashi tana magana a cikin ranta haɗi da cewa "yawwa Abbah yanzu za'a tattauna akan batun party graduation da kuma engagement ɗin mu Ni da Rukky..."

Abbah bin bayan ta yayi da kallo yana girgiza kai domin ba ƙaramin tausayawa yaransa yake ba...

Bayan wasu mintuna sai ga Rukky sun shigo duk suka zauna akan carpet suna sauraron abun da Abbah zai sanar musu...

Abbah ne ya buɗi baki ya ce "Balkisu, Ruƙayyat ban taɓa sanin cewa ku dabbobin tumakai bane sai yau...."

Kallon juna suka shiga yi cikin rashin fahimtar Abbah, Pinky ta ce "Dabbobi dai?..."

Abbah ya ce "ai kun fi dabbobin ma dabbanci domin su dabbobi basa taɓa zama mutane amma mutane sukan zama dabbobi to ku kuna daga cikin su..."

Rukky ta ce "innalillahi....."
Bata ƙarasa ba Abbah ya darara mata tsawa da cewa "ki mun shuru dallah, ke kinsan innalillahi kuwa? Inda kun sani da baza kuyi ƙoƙarin aikata ɓarna a doron ƙasa ba,
inda ace ban saka ku a islamiyya ba sai naga laifin kaina amma yanzu na rigada na sauƙe hakkin ku a kaina sauran abu ɗaya ya rage shine na samu na Aurar da ku, amma saboda daƙiƙancin ku wai har kuna ƙirana a waya cewa zaku yi Auren jinsi abu ko daɗin faɗi babu, in banda rashin ilimi da jahilci tin daga furucin sunan zaku san cewa wannan baya daga cikin addinin Musulunci, a cikin litattafan musulunci aina ku ka taɓa jin an sanar cewa ayi Auren jinsi?...."

Rukky ta kalli Pikky tana hararar ta cikin ranta tana faɗin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login