Showing 18001 words to 21000 words out of 89400 words

Chapter 7 - MY ENEMY BOOK 2 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

2511


🫦 مقىينا 🫦


Mallakin
أسماء محمد أولا 🥳

Asmeetah (giaÉ—e writer)


STEP TWO

9 to 10


Washe gari ranar Thursday manya-manyan baƙi ne suke ta sauƙa a gidan General, dake ranar Friday ne ɗaurin Aure,
Roshan da mai martaba tare da iyalansa gaba ɗaya duk sun iso, ƴan uwan mahaifiyarsu Razhdeen da Roshan kusan su Ashirin duk sun zo daga Saudiyya, ga family su Abbah wasu daga ƙasar Egyph wasu kuma London wasu daga Ethiopia banda waɗanda suka zo daga garuruwa Kano, Bauchi, Kaduna, pataskum jahar Yobe dadai sauran garuruwa,
Gidan General baƙi ne tam a gidan, tsabar girman gidan an raina yawan mutanen da sukazo domin gidan duk ya cinye su dan ma wasu da yawa basu zo ba,
Razhdeen ganin yanda ake ta baƙi yasa ya koma can gidansa yanda Mohandas yake, ita kuma Minal Roshan ne yabi ta gidan ya ɗauketa suka dawo gida,
Baiwar ALLAH gaba É—aya a takure take ganin yanda ake ta zuwa ganin Amarya, tin daga yau aketa faman shishshiryata dake yau da daddare akwai dinner hall da za'a taru ayi,
Roshan tin dawowarsa yake ɗaukin ganin fuskar Baiwar ALLAH amma ya kasa ganinta, taƙi fitowa daga room ɗinta, ga kuma yanda mata suke shiga cikin ɗakin, babu halin ya shiga ciki,
ya ƙirata a waya sau ba adadi amma taƙi yin picking balle ta ɗan fito ya ganta..

Daƙer ya samu ganin Ummy dake itama rawar kanta ya ƙaru sai gigiwa aketa yi anata shiri kamar wanda zasu fita ƙasar waje,
a waya ya sanar mata cewa tazo swimming pool ta same shi,
tayi mamakin jin haka sosai ganin yanda aketa shirin tafiya hall amma shi yana gida, amsa É—aya ta bashi cewa gata nan zuwa...
zuwa tayi ta same shi a swimming pool yana zaune akan kujerar wajen ya kifar da kansa akan table,
Dafa kafaÉ—arsa tayi tare da faÉ—in "Yaya Roshan lafiya kuwa, meya faru dakai?..."

ÆŠagowa yayi yana kallonta da shanyayyun idanuwansa alamunsa sun nuna yana cikin damuwa sosai, murya a sanyaye yace "zauna.."
zama tayi tana fuskantarsa, ba ƙaramin kyau tayi ba, tasha makeUp matuƙa tana sanye da Shadda-Less doguwar riga wanda har ƙasi yake ja, ga wani irin takalmi mai tudu sai ya ƙara mata tsayi sosai gata daman Ummy da ɗan tsayinta...
riƙo hannunsa tayi sannan tace "Yaya Roshan Please tell me what's wrong with you? gaba ɗaya ka chanza kamar ba Ango ba, kasan akwai Dinner amma har yanzu baka shirya ba why? ga can abokanka sunata nemanka amma basu sameka ba, kasan kuma akwai abokananka waɗanda suka zo daga Egyph da U.K and U.S but kazo nan ka ɓuya..."

Dogon numfashi yaja sannan yace "Ummy akwai matsala..."
tace "wani irin matsala Yaya Roshan?.."
ya kuma cewa "Ammata kamar bata sona, naga gaba É—aya ta sauya mun, hatta kalamanta sun sauya, bansan meke damunta ba..."

Ummy tace "Yaya Roshan haka zaka cigaba da haƙuri da ita har a ɗaura Auren domin yanzu kowa ma haƙuri yake da ita, bawai kai ɗaya ba, koda jiya ma Saida Abbah da Aunty Yolash suka tambayeta matsalarta kodai bata son Auren ne tace a'a, amma nafi tunanin ko tunanin iyayenta take shiyasa kasan baza taji daɗi ba ace ana Aurenta amma dangin mahaifinta ko mahaifiyarta babu wanda ya halarci wurin, babu ƴan uwanta ko ɗaya kaga dole zata shiga damuwa matuƙa, ina tunanin wannan ne matsalarta gaskiya...."

Sai yanzu Roshan yasau ƙayataccen murmushi har saida kyawawan dimple ɗinsa suka lotse yace "tabbas na gamsu da jawabanki My love, wannan shine matsalar sai yanzu nayi tunanin nan..."

Ummy tace "Hmmmmmmmmmm TOH yanzu zaka iya tashi kaje ka shirya?..."
Yace "TOH yanzun ba yanda za'ayi na ganta ko sau É—aya ne? kinsan tinda na iso ban ganta ba nayi missing É—inta over..."
yamutsa fuska Ummy tayi tare da faÉ—in "ku haÉ—u a wurin dinner, kasan dai yanzu Aunty Dota bazata iya ratsa mutane tazo nan ba koh?..."
Yace "okay shikenam mu haÉ—u a can..."

dariya tayi tareda barin wurin dasauri,
Bayan isar ta cikin babban Falo ta tarar da wani babban tashin hankali, duk mutanen wurin sun taru a falo suna ganin ikon ALLAH, Hajiya Kilishi ce tazo itama wurin hidimar tana durƙushe da gwiwowinta akan carpet ɗin falon tana roƙon Abbah akan ya dawo da ita,
shi kuwa Abbah ya dage akan saita tashi tabar masa gida tinda bai gayyato ta bikin É—ansa ba,
Minal kuwa tsabar kunya ko fitowa falon batayi ba balle taga kayan takaicin nan acikin bainar jama'a,
Rukky itama ɗakin su ta nufa domin bazata iya ganin wannan ƙasƙancin ba,
Pinky kuwa tin jiya da Razhdeen ya rufe ta a É—akin horo har zuwa yanzu bai fito da ita ba kuma key É—in É—akin yana hannunsa, ga baya zaman gida saboda taron mutane domin baya son hayaniya, shima Abbah ya manta da batun Pinky a É—akin horo, su kuwa sauran yaran gidan kowa yana fargaban yin maganar Pinky, Aunty Yolash ma a tunaninta an fito da ita dake yau ranar hidima ce,
Hajiya Kilishi fashewa tayi da matsanancin kuka tana roƙon Abbah tare da faɗin "Dan girman Allah Chief kayi haƙuri ka dawo dani kan ƴaƴana nayi kuskure sosai, sam bana jin daɗin zaman gidan mu ga kasa an dakatar dani a wurin Aiki bana zuwa ko ina, kayi haƙuri..."

Abbah yana huci yace "duk wanda ya bani shawarar na dawo dake wallahi tallahi ba masoyina bane, babban maƙiyi nane kuma Ni da shi zumunci ya yanke har abada saboda haka ki tashi kibar mun gida yanzun nan, ƴaƴanki koda ke ko babu ke zasu rayu cikin aminci, kuma ki dube su dakyau babu abinda ya ragu a jikinsu da bakya nan, saima girman jiki da suka ƙara, ina mai miki albishir da cewa a gobe ranar Jumma'at za'a haɗa Auren Roshan da Aurena a ɗaura, an bani ƙanwar Matata marigayiya Fatima akan na Aura, kuma Alhamdulillah ɗabi'unsu ɗaya da tarbiyyar su da duk wasu nau'ikan zamantakewar Aure, sunanta Ummu Salamah Amintacciyar yarinya daga Saudi Arabia,
Kilishi ki tashi kibar mun gida yanzun nan tin kafin nasa karnukana su korar mun ke...."

Jiri ta fara ji jin chief zaiyi Aure, nan ta ƙara fashewa da kuka ta buɗi baki zatayi magana yayi saurin daka mata wani irin gigitaccen tsawa har saida sauran mutanen wurin suka firgita, a gigice ta miƙe tsaye ta nufi bakin ƙofa tana kuka, anan ta tarar da Ummy tana tsaye bata ƙarasa shugowa ba duk ta wanke kwalliyar fuskarta da hawaye, tsayawa tayi Hajiya Kilishi a gaban Ummy ta kamo hannayenta biyu tana ƙiran sunanta ciki-ciki tace "Ummy ki gafarce Ni..."
Daga nan tayi wucewarta...

Abbah shima juyawa yayi ya haura saman upstairs rai a ɓace, kab mutanen wurin babu wanda yaji daɗin abinda ya faru amma masu faɗin madalla su sukafi yawa domin da yawan su babu wanda yake jin daɗin zama da Hajiya Kilishi saboda ta kasance mace marar son mutane, Aunty Yolash ɗan tsaki taja tareda wurga ƙwayar idonta kan Hajiya Maamie wacce itama tana wurin tace "waɗanda za'a kora ai sunada yawa, ina mai martaba shima yazo yahau kan layi, domin baza'a mayar mana da ɗan uwa bita zai-zai ba...."

Duk sauran mutanen suka tintsire da dariya tare da faÉ—in "wallahi kuwa..."

Hajiya Maamie dogon tsuka taja tana hararar Aunty Yolash da sauran Æ´an uwansu tace "Ni kuwa an mutu dani wallahi, babu yanda aka iya dani, mutu karaba takalmin kaza Ni da mai martaba, dole a ganni a barni domin na zamo ciwon ido..."

Aunty Yolash tace "yooo wa kika ajiye balle ki zauna dashi har ƙarshen rayuwa? To dai kina gani wacce ta ajiye har ƴaƴa biyar ma ta fita balle ke ko ɓatan wata baki taɓa yi ba...."

Hajiya Maamie tace "au gorin haihuwa ne ya tashi? ey gwara Ni a gidan mijina nake ba yawon tsinantaka ba, anyi shekara kusan arba'in amma babu mijin Aure..."

Aunty Yolash ta gama ƙuluwa matuƙa tace "bari kiji Madam! Bawai rasa miji nayi ba, niyya ne banyi ba kuma ko a yanzu naso yin Aure zanyi kuma na haihu da yardar Allah..."
Hajiya Maamie tace "to kiga dama mana yanzun ma, wa ya hanaki ƙirrr kutu kutu..."

Aunty Yolash tace "Uhmmm! Kin yanda nayi Aure yanzu ke kuma ki samu ciki a wata É—aya zuwa biyu?..."

Hajiya Maamie Saida taji bugun zuciya domin a asibiti an tabbatar mata cewa mahaifarta yayi ƙarami a ɗaukar ciki sannan ta gama yawon bin bokaye da dama amma ba'a dace ba,
Harara ta wurgawa Aunty Yolash sannan tace "shi haihuwa daga Allah ne Dan buro ubanki...."

Aunty Yolash a ruɗe ta dafa ƙirji tare da faɗin "buro ubanaaa?! kika ce buro ubanaaa?!! buro ubanaaa kika ceee?!!!..."
Nan danan idon Aunty Yolash ne ya kaÉ—a yayi jawur domin tin tana cikin mahaifiyarta ta rasa mahaifinta memakon a bishi da addu'a sai kuma zagi, ai bata san lokacin da tayi sufa ta cabko wuyan Hajiya Maamie ba,
Hajiya Maamie ta tsorata sosai da ganin yanayin Aunty Yolash, mutanen wurin ne suka rirriƙe Aunty Yolash domin ba ƙaramin shaƙa tayi mata ba, duk yawan mutanen falon babu wanda ya iya ɓanɓaran Aunty Yolash daga jikin Hajiya Maamie,
Abbah jin hayaniya yayi yawa ne yasa shi sauƙowa dasauri, shima daƙer ya iya fizgar Aunty Yolash ganin bazata saurari abinda zai faɗa ba,
Cikin faÉ—a yake magana tare da faÉ—in "wannan wani irin hauka ne? babu dama a barku ku kaÉ—ai sai an samu matsala?..."
ya kalli Aunty Yolash yace "ke meyasa bakida haƙuri ne? to ku same Ni acan falo ɗina yanzun nan..."
yana kaiwa nan yayi ficewarsa,
Aunty Yolash harara ta wurgawa Hajiya Maamie itama tayi gaba, Hajiya Maamie itama bayanta tabi, a falo duk suka tarar da Chief yana zaune akan tsararren Soparsa kai a sunkuye yanata karkaɗa ƙafafu, duk zama sukayi a ƙasin carpet domin falon Chief indai ba manya-manyan baƙinsa bane ba'a zama masa akan sopa,
Chief ɗaukar waya yayi ya ƙira wata dattijuwa a can falonsu wacce tana wajen akayi komai, can sai gata ta shugo da sallama a bakinta, amsa mata yayi tare da nuna mata saman kujera ta zauna, zama tayi tare da faɗin "to gani naga an ƙira Ni..."

Chief yace "Uma shin kina nan suka fara faÉ—a?.."

tace "tabbas kuwa "

Chief yace "toh inaso ki gaya mun gaskiyar abinda ya haɗasu kar kiga cewa kinada alaƙa da Yolash kawai tsakanin ki da Allah zaki sanar mun...."

Tsohuwa tace "tsakani da ALLAH kuwa zan gaya maka.."
nan ta kwashe komai ta sanarwa Chief abinda ya haÉ—asu...
Chief ya kalli Aunty Yolash yace "bakida gaskiya Auntyn Yara, meyasa bakida haƙuri ne? meyasa ZAKIYI mata gorin haihuwa? shin ba Allah ne yake badawa ba ne? ko kin isa ki bata haihuwar? ko kuma ita ta isa ta bawa kanta haihuwar? ko kuma mijinta ya isa ya bada haihuwar da Allah bai sauƙar ba? kuna abu da tunani mana, komai sai ku rinƙa nuna rashin ilimi akai, wannan ai zunzurutun jahilci ne gori akan abinda Allah ne mai bada shi bawai wani halitta ba, toh wallahi daga yau kar Na sake jin wannan kalmar daga bakin ki..."

Aunty Yolash tana hawaye tace "Amma Yaya itama tamun gorin Aure fah..."

Chief yace "Aure ai ke kika hana kanki, Allah ya baki damammaki da dama amma kin ƙi amfani dashi, nawa ne mazajen Aure suka zo nemanki amma duk kin ƙisu, kuma dan anyi miki gori sai kiji haushi?
Ai gorin haihuwa yafi na Aure ciwo, har yanzu damarki bai wuce ba, akwai waɗanda suke zuwa neman Aurenki, aciki akwai Governor Kaduna da Governor Bauchi ga Alhaji Tafidan Bauchi ga manya-manyan shuwagabannin nan Abuja da dai sauransu idan kuma kince a'ah TOH saiki cigaba da toshe kunnuwanki da jin duk wasu ƙananun maganganu akan ki,
Ku tashi ku ban wuri...."

Dasauri Aunty Yolash ta miƙe ta fice tana kuka,
Hajiya Maamie kuwa zaro idanuwa ta fara yi jin manya-manyan mutanen da suke neman Aunty Yolash da Aure, da hassada acikin zuciyarta tabar falon Chief,
Ita kuwa Tsohuwa zama tayi ta cigaba da tattaunawa da Chief akan yanda bikin zai kasance gashi É—aurin Auren har da nashi....

Aunty Yolash tana shiga babban falonsu kai tsaye room É—inta ta wuce ta danna sakata,
Mutanen da suke falo babu yawa duk sun kutsa kai ɗakin da Amarya take itama Baiwar ALLAH ta kulle kanta a cikin Bathroom taƙi buɗewa, sunyi da ita akan ta buɗe amma taƙi, gashi har lokacin dinner yayi, sauran yaran gidan ma ko wacce tana ɗakinta cikin damuwa ganin yanda Abbah ya wulakanta Mommynsu kuma sannan sunji labarin shima zaiyi Aure,
Angwaye sun jira har sun gaji basu ga ko mutum É—aya ba acikin matan gidan balle suga idon Amarya,
Da haka har lokaci ya ƙure aka bantsar da hidimar Dinner, amma ba ƙaramin takaici suka shaƙa ba kaf Abokanan Ango da shi kanshi Angon,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login