Showing 24001 words to 27000 words out of 89400 words
Hajiya Maamie data bugi ƙasa da ƙafarta ta wani narka uwar ashar ta ce "buuuuro uban nan, ke kuma me kike ce mata dan durun uwarki?..."
Ramlat ta ce "ce mata nayi ai kinfi uwarta da take yawon bin hotel tinda ke kin kama kanki kina zaune da mijinki..."
Hajiya Maamie washe baki tayi tare da faɗin "kin burge ni da kika gaya mata haka, kinga gaba bazata sake miki gori ba tinda abun gori yana gindin su, ai wallahi da baki tamka mata ba saina zabga miki mari sannan na kora ki garin Kaka can ƙauye..."
Ramlat ta ce "cab ɗin ai wallahi bazan iya zaman ƙauye ba hakan ma a wurin Kaka,
wai ma Aunty Maamie ya batun Aure na ne kam? an fasa ne?..."
Hajiya Maamie taja dogon numfashi tana hura iskar baki ta ce "ai ki bar batun nan kawai, domin sai bokan nan yayi mun aiki tuƙuru akan Razhdeen, ko ba yanzu ba za'ayi Auren, a duniyan nan babu wanda tsafi baya kamashi don haka ki kwantar da hankalin ki, domin idan muka cika yin maganar tsab Razhdeen rabaki zaiyi da duniyan nan gwara mu bi komai a hankali ba'a gaggawa da rayuwa..."
Ramlat ta ce "Ni dan Allah kibar batun Uncle Deen ɗin nan, mu koma kan Yaya Roshan ni nafi son sa wallahi, kuma kinga shi da wuri za'a iya shawo kan sa..."
Hajiya Maamie ta ce "Dan ubanki Roshan ɗin da aka tafi ɗauro masa Aure shine zakiyi batun sa? ki bar komai a hannu na dole fa sai Razhdeen ya Aure ki..."
Ramlat ta ce "wallahi ban gama warkewa da dukan da yayi mun ba, har yanzu gaɓoɓina ciwo suke mun hakan ma ki duba yanda ya ɗaure ni a saman fanka kamar wata lauje, Ni gaskiya bazan iya zama da Uncle Deen ba..."
Hajiya Maamie har ta buɗe baki zatayi magana suka ji kururuwa a falo, hayaniya duk ta baza ko ina na gidan, da sauri suka fice domin gane wa idonsu,
suna fita suka tarar an fito da Baiwar ALLAH a sume, wasu sun riƙe hannayen ta biyu wasu kuma sawaye da haka suka fito da ita,
Aunty Yolash ce tayi gudun shiga room ɗinta ta ɗauko key ɗin motar ta zata kai ta hospital,
A ruɗe take faɗin "dan Allah ku taya ni ɗaga ta mu kai ta wurin parking kunga ba maza a gidan sannan duk sojojin ma babu wanda aka bari..."
wata tsohuwa ce ta ce "wai ma duk meya jawo haka ne..."
Ummy tana kuka ta ce "duk ata sanadiyar waccan Agolar yarinyar ce..."
ta ƙarisa maganar tare da nuna yanda Ramlat take tsaye.
Ramlat kama kunkumi tayi ta tari yawun ta da cewa "Hmmm! Allah na gode maka a iya Agolanci na tsaya, ke bari kiji in banda tsautsayi da kuma tsananin soyayyar Yaya Roshan a cikin zuciyata ba mai zai sa na tsaya haɗa kishi da wannan yarinya mai kama da farar goɗiya..."
Ummy ta ce "ai wallahi ko mata sun ƙare a duniya Yaya Roshan ba zai taɓa Auran ki ba domin bakya cikin lissafin tsarin matan da yake so..."
Ramlat tayi dariya tare da tafa hannayenta biyu tana faɗin "ai kuwa you should see what am going to do yarinya, Yaya Roshan Auren ta kawai zai yi amma ainihin shi ɗin nawa ne..."
Pinky dake wurin ta ce "wai duk akan wancan marar asalin ake wannan ce ce ku cen? Lallai kun haɗu da aiki..."
Rukky itama buɗar baki tayi ta ce "ai daman tsautsayi da ƙaddara ne zai sa Yaya Roshan Auren marar asali..."
Ramlat ta kalle su tare da sau wata ƙayatacciyar murmushi ganin an goya mata baya ta ce "yawwa ƴan gari shiyasa nake ƙara ji da ku twins saboda akwai faɗan gaskiya sannan bakwa goya wa ƙarya gindi..."
Rukky ta ce "Ni fa dalilin da yasa bana ƙaunar Baiwar ALLAH saboda Abban mu ya fi nuna mata kulawa, bai damu da mu kamar yanda ya damu da ita ba, ni kuma inada kishi gaskiya..."
Pinky ta tari yawun ta da cewa "ni kuma daman can bata raina, haka kawai nake jin tsanar ta wallahi, na rasa mai Yaya Roshan ya gani a jikin ta har ya nace akan Auren ta..."
Ummy tana zaune akan kujera ta kifar da kanta akan gwiwowin ta tana jin duk tsegumin da suke amma ta kasa tanka musu,
Aunty Yolash kuwa daman ko tsaya sauraron su bata yi ba tin tinin sun fice da Baiwar ALLAH, a can wurin parking suka tsaya ganin an tsayar da wata jibgegiyar baƙar mota, cikin nuna damuwa Aunty Yolash ta ce "yawwa ga Razhdeen ya zo..."
Da gudu ta nufi wurin da yayi parking motarsa ko fito wa bai samu damar yi ba,
zuwa tayi ta fara ƙonƙosa masa murfin motar domin tasan halin sa kafin ya fito sai ya ja musu aji,
ganin tana shirin takura masa ne yasa shi fitowa fuska a turnuƙe ba alamun annuri, kafin ya buɗi baki ya yi magana har Aunty Yolash takai ƙarshen maganar ta tana faɗin "dan Allah Razhdeen ka taimaka ga can Amarya a kwance ta faɗi, kuma kaga ba wani namiji a gidan..."
kallon gefen ido ya yi mata tare da faɗin "zanje ɗaurin Auren twins ne, tinda kun fito da ita ku kaita mana..."
yana kaiwa ƙarshe ya juya zai shige motar sa Aunty Yolash tayi saurin riƙo hannun sa tana faɗin "wai kai wani irin murɗaɗɗen mutum ne kam, ga can yarinya rai a hannun Allah amma kai ko a jikin ka? na tabbata inda Mijin ta ne kafin na ƙarasa magana ta zai nufi yanda take..."
Razhdeen haɗe gira ya yi tare da faɗin "Mijinta fa kika ce, ba Razhdeen ba don haka sai ku jira mijin natan ya dawo tinda muharramar sa ce..."
Aunty Yolash fuska ɗauke da damuwa ta ce "Please Razhdeen ka taimaka dan Allah, ba dan ni ba..."
Lumshe idanuwan sa yayi tare da buɗe su a hankali ya sauƙe su akan Baiwar ALLAH dake kwance ƙasin floor kanta na kan cinyar wata tsohuwa...
ratsa gefen Aunty Yolash ya yi sannan ya nufi yanda Baiwar ALLAH take kwance, yana zuwa kuwa nan take yayi mata ɗaukar jaririya ya nufi motar sa da ita, iya Aunty Yolash kawai ya buƙaci su tafi tare, sauran kuwa komawa ciki suka yi...
Nan da wasu ƴan mintuna har sun isa hospital, a harabar hospital ya yi parking da motar sa, lokaci guda wasu nurses sun kai biyar suka fito da gadon tura wa,
Razhdeen da Aunty Yolash suma facility ɗin hospital suka shiga, a wasu kujeru suka zauna domin har an shiga da Baiwar Allah emergency room,
Bayan wasu mintuna sai ga Doctor ya ce musu yana son ganin su a office ɗin shi, hakan kuwa suka yi a office suka tarar da shi zaune yana duba wasu files,
suma zama suka yi suna fuskantar Doctor,
numfashi Doctor ya sauƙe idon sa akan Razhdeen ya ce "Major meyasa zaku bar yarinya ciwo ya ci jikin ta har haka? ta juma tana fama da rashin lafiya domin zazzaɓi ne mai zafin gaske yake damun ta, rashin tarar abun da wuri ne yasa duk jinin jikin ta tsotse wa, zata iya rasa rayuwar ta a cikin ɗan kwanakin nan in har bata sha ledar jini biyu zuwa uku ba..."
ya ƙarasa maganar tare da miƙa musu file ɗin ta,
Razhdeen ne ya karɓa yana duba wa daga ƙarshe kuma ya ce "yanzun mai ake jira ne?..."
Doctor ya ce "jinin da zai yi dai-dai da nata domin a yanzu ana wahalar samun jini sosai..."
Jin jina kai Razhdeen ya yi sannan ya ce "okay kaja mata jini na indai zai yi mata..."
Aunty Yolash murmushi tayi ganin yanda Razhdeen ya damu da rashin lafiyar Baiwar Allah lokaci guda,
Doctor ya ce zamu duba mu gani in har zai yi mata, a take Razhdeen ya miƙa hannun sa aka ja jinin da za'a gwada da nata,
Bayan wasu ɗan mintuna sai ga Doctor ya dawo fuska ɗauke da murmushi ya kalli Razhdeen sannan ya kai idon sa kan Aunty Yolash ya ce "Ma sha ALLAH! group ∅ negative zaka iya bawa kowa, amma ita ɗin matar ka ce ko wacce zaka Aura?..."
haɗe gira Razhdeen ya yi tare da faɗin "daman ina ba da jini na a kowa duk wanda ya buƙaci jini, ba a kanta na fara ba kuma bazan dai na akan ta ba, taimako ne kuma nayi niyar yinsa..."
Doctor ya ce "sorry Major yanzu za'a iya jan jinin..."
lokaci ƙanƙani aka ja jini leda ɗaya daga ɓangaren sa, nan da nan Doctor ya je ya ɗaura mata har zuwa yanzu bata farfaɗo ba...
After 4hours har zuwa wannan lokacin Razhdeen da Aunty Yolash suna nan babu mutum ɗaya da ya zo hospital sakamakon rashin sanin halin da Baiwar ALLAH ke ciki, already Aunty Yolash ta sanar wa mutanen gidan cewa kada wacce ta sanar wa su Abbah da Roshan cewa Baiwar ALLAH tana hospital har sai ta farfaɗo, saboda kar su shiga wani hali gashi a ranar biki,
An ɗaura Aure lafiya Roshan da Baiwar ALLAH wacce ta amsa suna (AMATULLAH),
Roshan Abokan sa sun ja shi sun tafi yawon shakatawa sai zuwa dare ya gana da Amaryar sa, shima Abbah an ɗaura Auren sa da ƙanwar Matar sa ta farko wato mahaifiyar Razhdeen da Roshan, Amaryar Abba mai suna Ummu Salamah, bazawara ce mijin ta shine Marigayi Alsheikh Mahmoud Shureim babban malamin ƙasar Saudiyya, Ummu Salamah yau shekara guda da gama takaban mijinta kuma a yau Abbah ya Aure ta, yaron su ɗaya tak mai suna ARASH!
ya kammala master's ɗinsa a ƙasar Pakistan a ɓangaren lawyer, yanzu ya zama babban lawyer a ƙasar Saudiyya (according to Qur'an)..
Gobe za'a ɗauko Amaryar Abba daga Saudiyya zuwa Nigeria...
A ranar Baiwar ALLAH sai da ta sha jini laida biyu duk daga jikin Razhdeen aka ja,
an basu dama sun shiga duba ta amma sai dai ta tafi dogon bacci bayan ta farfaɗo, laidar jini na biyun ma har ya kusan ƙare wa, Aunty Yolash tana zaune akan kujerar gefen gadon shi kuma Razhdeen yana tsaye ta saitin kanta yana ƙare ta da kallo, Doctor ne ya shigo yana faɗin "Insha ALLAHU a yau za'a sallame ku domin ba ƙaramin duba ta muka yi ba, yanzu haka bacci ta samu yi ne zuwa an juma kaɗan zata farka..."
Aunty Yolash ta ce "Allah yasa ta farka da wuri domin bana so su Abba su san muna hospital balle shi Roshan, bana so hankalin kowa ya karkato kan Amarya saboda ba kowa ne yasan muna hospital ba a cikin matan gidan ƴan biki, amma gobe ko wacce zata koma yanda ta fito idan aka kawo Amaryar Yaya General..."
Razhdeen yana tsaye gaba ɗaya ya gama gajiya da zaman hospital ɗin nan, ga tunanin kurmiyarsa wato SARAH (Ƴar Amana)
Meaning of Sarah (princess)
Razhdeen kallon Aunty Yolash ya yi sannan ya ce "zan tafi gida..."
Aunty Yolash ta ce "gaskiya ya kamata kaje ka huta kayi ƙoƙari sosai Uncle Deen, cire laida biyu na jini a jikin mutum kuma a rana ɗaya ba wasa bane, mun gode sosai..."
Razhdeen kawar da kai ya yi zai tafi yaji an damƙo hannun sa, a hankali ya juya bayan sa yaga hannun Baiwar ALLAH tana riƙe da na shi,
Aunty Yolash itama tsaya kallon ta tayi cike da mamaki,
Idon ta a lumshe ta fara motsi da lips ɗinta a hankali ta soma furta
"Uncle Deen jinin jikin ka ne yake gudana a jiki na? daman ina jiran wannan ranar ta zo na haɗakar jini, shikenam ka zamo jinin jiki nah, ina muradin ganin jinin jikin ka a cikin jikina, ina matuƙar ƙaunar ka da son kasance tare da kai har kullum, dan Allah ka ce wa Yaya Roshan ya yi haƙuri ya bar maka ni ..."
Jin haka yasa a zabure Aunty Yolash miƙe wa tsaye tare da faɗin "whattttt?..."
shima Razhdeen fizgar hannun sa ya yi cike da mamaki babu bakin magana,
Baiwar ALLAH duk wannan maganganun da tayi shi ba'a cikin hayyacinta ta faɗe su ba, domin har zuwa yanzu idonta a rufe suke, sambatu kawai take tana cigaba da ɓare-ɓaren maganar ta...
Aunty Yolash zuwa saitin ta tayi tare da sa hannu tana ɗan bubbugan fuskar ta tare da ambatar sunan ta,